Salati
- Wannan wata maƙala ce game da fahimtar salati, domin fahimtar aya ta 56 suratul ahzab ku duba shafin ayar salati.

Salati, (Larabci: لصلاة على النبيصلی الله عليه وآله وسلم) yana daga cikin umarnin Kur'ani wanda a cikin aya da take da alaƙa da salati an umarci muminai da yin salati. Wannan aiki yana matsayin alama ta nuna godiya da girmama Annabi kuma sababi ce ta ƙarfafa soyayyarsa wanda cikin adadin litattafan hadisi aka yi bayani game da fa'idojinsa, ciki har da goge zunubai, buɗe ƙofofin sama da samun ceton Annabi.
Mafi shaharar sigar salati shi ne «اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَی مُحَمَّدٍ وَ آلِ مُحَمَّد» (Allahumma Salli Ala Muhammad Wa Ali Muhammad) wace cikin ba'arin riwayoyin Shi'a aka yi umarni da ita, bayan salati ana faɗin "Wa Ajjil Farajahum". Bisa fatawar malaman Shi'a, wajibi ne yin zikirin salati a zaman tashahhud na sallah (Zaman tahiya), barinsa da gangan yana ɓata sallah, haka nan wajibi yin zikirin salati cikin huɗubobin sallar juma'a da sallar jana'iza.
Yin salati abun yabawa ne a ko wane lokaci, amma yayin jin ambaton sunan Annabi, ruku'u da sujjada a sallah cikin da wasu lokuta na musamman, an yi nasiha mai yawa da yin salati a waɗannan wurare.
Salati a wurin ƴanshi'a ƙari kan ɓangare na ibada da ya ƙunsa, a cikin bukukuwa, tarurrukan addini da ayyuka na yau da kullun ya yaɗu sosan gaske, ƴanshi'a su kan yi salati domin neman biyan buƙatunsu, kuma suna yin khatamar salati.
Falsafa da hikimar salati ta haɗa da neman rahama da ƙarin ɗaukaka ga Annabi da iyalansa, tunawa da su da sunansu da biyayya ga sunnarsu. A cikin al'adun Shi'a, ƙara Alu (Ahlul-Baiti) cikin sigar salati ya yaɗu matuƙa kuma cikin da yawa-yawan madogarai ana lissafa hakan cikin hukunce-hukunce na larura, sai dai kuma Ibn Taimiyya da mabiyansa wahabiyawa, suna rinjayar barin irin wannan sigar salatin na (Allahumma salli ala Muhammad wa ali Muhammad) saboda gujewa kamanceceniya da ƴanshi'a.
Wasu daga Ahlus-Sunna suna fifita salatul Ibrahimiyya kan dukkanin sauran sigogin salati.
Matsayi Da Muhimmanci
| Roƙo |
Litattafan Addu'a
Mafatihul Al-Jinan•Sahifa Sajjadiyya•Misbahul Mutahajjid•Iƙbalul A'amal•Miftahul Falah |
Kwanaki Da Watanni
Lailatul Ƙadri•Nisfu Sha'aban•Ranar Arafa•Ramadan•Rajab•[[Zil-Hijja]•Lailatul Raga'ib |
Salati, umarni na Kur'ani[1] cikin ayar salati, Allah da mala'iku sun yi salati ga Annabi (S.A.W) kuma Allah ya umarci muminai da su yi salati ga Annabi.[2] Yin salati ɗaya ne daga cikin Sha'a'ir na addini (Alamomi na addini).[3]Salati wata al'ada ce da ta yi matuƙar yaɗuwa tsakankanin ƴanshi'a.[4]
Wasu daga Ahlus-Sunna suna fifita salatul Ibrahimiyya kan dukkanin sauran sigogin salati. sigar salatul Ibrahimiyya shi ne "Allahumma salli 'ala Muhammad, wa-'ala ali Muhammad, kama sallayta 'ala Ibraheema wa-'ala ali Ibraheem, innaka Hameedun Majeed, allahumma barik 'ala Muhammad, wa-'ala ali Muhammad, kama barakta 'ala Ibraheema wa-'ala ali Ibraheem, innaka Hameedun Majeed"[5]
Zikirin salati ya zama wata al'ada da baka raba Musulmi da ita cikin tarurrukansu da ya haɗa da bukukun farin ciki da makoki.[6] Cikin al'adun Shi'a da zarar sun ji ambaton sunan Annabi sai kawai ka ji suna salati suna faɗin Allahumma salli ala Muhammad wa ali Muhammad, haƙiƙa ana ƙyamar barin yin zikirin salati musamman a irin wannan wurare da ake ambaton sunan Annabi.[7] Wasu ƴanshi'a sun kasance a kodayaushe cikin ko wane hali da lokaci ba sa rabuwa da yin salati, ko kuma yin bakance idan buƙatarsu ta biya za su yi wani ayyanannen adadi na salati.[8]
Bayan wajiban shari'a da karatun Kur'ani haƙiƙa salati ya kasance daga mafi ɗaukaka da darajar ibada,[9] Cikin addu'o'i da aka samo daga Ma'asumai musamman Sahifa Sajjadiyya salati ya zo wurare da daman gaske a cikinsu.[10] Cikin Riwaya an bayyana cewa marowaci na gaske na haƙiƙa shi ne wanda zai ji an ambaci sunan Annabi amma tare da haka ya yi rowar yi masa salati.[11]
Malaman fiƙihu na Shi'a sun yi ittifaƙi kan wajabcin yin salati cikin tashahhud (Zaman tahiya), kuma idan wani da gangan ya ƙi yin salati to sallarsa ta ɓaci.[12] Wasu malaman fiƙihu na Ahlus-Sunna suma suna kan wannan ra'ayi.[13] Ƙari kan tashahhud (Tahiya) yin salati ga Annabi da iyalansa a cikin huɗubobin sallar juma'a[14] da sallar jana'iza wajibi ne.[15] Haka nan a cewar Nasir Makarim Shirazi, sanannen malamin tafsiri a Shi'a, bisa abin da ya zo a ayar salati, yin salati ga Annabi (S.A.W) a sau ɗaya wajibi a cikin rayuwar ko wane.[16]
Salati A Cikin Al'adun Musulmi
Salati a cikin al'adun Musulmi yana faruwa a wurare daban-daban kamar lokacin rarrashin jarirai da ƙananan yara, cikin karin magana, lokacin shuka da girbar amfanin gona.[17] A wuraren wasan gargajiya na Zurkhune a ƙasar Iran, musamman ma nau'ukan salawate carke miyan dari (Wani nau'i ne na girmamawa da ake yi ga ɗan wasa yayin da yake gabatar da wasan gargajiya)[18] A ƙasar Iran yana da sasanni na siyasa da zamantakewa, a lokacin da sarki Rida Shah Pahlawi ya kori Imam Khomaini daga Iran, ta kai ga mutane da sun ji an ambaci sunan Imam Khomaini sai su yi salati wanda hakan ya taimaka sosan gaske cikin ƙarfafuwar marja'iyya da jagorancinsa cikin al'umma.[19]
Khatamar salati, wani aiki ne da wasu mutane suke yi da niyyar Ma'asumai kuma domin samun biyan buƙatunsu,[20] sai su yi wani ayyanannen adadin nasalati kamar ƙafa 100, 100 ko 1400 akai-akai babu yankewa[21] Galibi wannan aiki yana kasancewa ne bisa bakance.[22] Khatamar salati ana yinsa da tsarin tara jama'a da za su yi wani ayyanannen adadi a tare da juna.[23] A ƙasar Iran bayan idar da sallar jam'i ɗaya daga cikin masu sallah zai ɗaga murya ya karanta ayar salati sai sauran masallata su yi salati da sigar Allahumma salli ala Muhammad wa ali Muhammad har sau uku. A cikin littafin Misbahul Mutahajjid an yi nasiha da karanta ayar salati a matsayin ta'aƙibat na sallah (Addu'a da ake yi bayan idar da sallah).[24]
Hikimar Yin Salati
Salati, wani nau'i ne na girmamawa da godiya ga ƙoƙari da wahalar da Annabi ya sha tsawon shekaru 23 kuma ana ɗaukarsa tsani da hanya da yake ƙarfafa soyayyar Annabi a zukatan muminai.[25] Masu bincike suna da ra'ayin cewa yin salati, muminai suna ajiye Annabi da iyalansa a matsayin tsani da tsakaninsu da Allah domin samun rahamar Allah.[26] Kwakwayon kammalallen mutum,[27] girmama Annabi da iyalansa, tunawa da sunansa da tunawa da zaɓaɓɓun Allah, himmatuwa cikin bin tafarkin annabta da wilaya da kuma nuna cewa annabta da imamanci ba sa rabuwa da juna.[28]
Dangane da batun cewa ko yin salati ga Annabi da iyalansa yana da wani alfanu da amfani ko babu, akwai ra'ayoyi guda biyu[29] Mutane kamar Shahidus Sani babban malamin fiƙihu na Shi'a,[30] Allama Ɗabaɗaba'i marubucin Tafsirul Almizan[31] da almajirinsa Hassan Hassan Zade Amoli[32] suna da ra'ayi cewa matsayi da maƙamin Annabi ya kasance da girma da ɗaukakar kuma ya wadatu daga buƙatuwa da salatin muminai, saboda haka alfanu da fa'idojin yin salati suna komawa zuwa ga masu yin salati[33] Akasin wannan ra'ayi, Muhammad Baƙir Majlisi da Murtada Muɗahhari suna da ra'ayin cewa duk da kasancewar Annabi da iyalansa suna da maɗaukakin matsayi da maƙami, amma tare da haka sun kasance suna tafiya kan tafarkin kamala da kammaluwa kuma yi musu salati zai taimaka wajen ƙara ɗaukakuwar matsayi da maƙamansu a wurin Allah.[34]
Idan aka danganta salati ga Allah, to yana da ma'anar rahama, idan kuma aka danganta shi ga mala'iku to yana nufin istigfari, idan kuma aka danganta shi ga mutane to yana nufin addu'a.[35]
Falala Da Fa'idoji
Cikin litattafan hadisai an lissafa lada da fa'idoji masu tarin yawa na ruhaniya da zahiri ga salati. Wasu daga cikin fa'idojin salati sun kasance kamar haka:
- .Kaffarar zunubai[36]
- .Goge zunubai[37]
- .Mafi nauyin aiki kan sikelin auna ayyuka shi ne salati[38]
- .Buɗe ƙofofin sama da zubewar zunubai[39]
- .Soyayya tare da Allah[40]
- .Samun ceton Annabi[41]
- .Daga cikin abin da yake tafiyar da munafunci daga cikin zukata (Ɗaga murya da salati)[42]
- .Tunatar da mutum abin da ya manta[43]
- .Mala'iku suna istigfari ga masu rubuta zikirin salati[44]
- .Amsa addu'a[45]
- .Tsira daga shiga wutar Jahannama[46]
- .Samun biyan buƙata[47]
- .Allah da mala'iku suna salati ga mai yin salati[48]
- .Mafi kyawun aiki a ranar Juma'a[49]
- .Riskar Imam Zaman (A.F) (Zikirin salati bayan sallar asubahi da azahar)[50]
- .Buɗe ƙofa daga cikin ƙofofin lafiya.[51]
- .Mafi alherin addu'a a Ka'aba[52]
- .Tsarkake ayyuka[53]
- .Haskaka kabari, siraɗi da aljanna[54]
- .Mai yin salati zai kasance mutum mafi kusa da wurin da Manzon Allah yake a ranar alƙiyama[55]
- .Zikirin salati daidai yake da zikirin hailala da tasbihi da takbir.[56]
Shin Dole Ne Mu Yi Salati Ga Muhammad Da Iyalansa
Cikin jama'ar Shi'a duk sanda za su yi salati ga Annabi suna haɗawa da ali (Iyalansa)[57] A cewar Sahibul Jawahir, ƙara ali cikin sigar zikirin salati yana daga cikin hukunce-hukunce na larura a mazhabar Shi'a[58] Sayyid Abul Ƙasim Khuyi, daga cikin shahararrun maraji'an taƙlidi na Shi'a, tare da dogara da wasu riwayoyi[59] ya rinjayar da cewa yin salati ga Annabi ba tare da haɗawa da iyalansa ba haramun ne.[60]
Haka nan bisa wata riwaya wace aka naƙalto ta a madogaran Shi'a da Ahlus-Sunna, an yi hani da yiwa Annabi gutsirarren salati, cikakken salati shi ne wanda aka haɗa da iyalansa (Allahumma salli ala Muhammad wa ali Muhammad).[61] Ƙazi Nurullahi Shushtari ya tattaro waɗannan riwayoyi cikin littafinsa mai suna Ihƙaƙul Haƙƙi.[62]
Abin nufi da Alu bisa ittifaƙin malaman Shi'a, suna mutanen biyar na cikin bargo (Annabi, Ali, Faɗima, Hassan da Husaini) waɗanda ayar taɗhir ta sauka game da sha'aninsu. A cewar Muƙaddasul Ardadili babban malamin Shi'a, wannan ayar ta haɗa da baki ɗayan Imamai Ma'asumai da Sayyida Faɗima, saboda haka dukkaninsu ana lissafa su a matsayin Alu Muhammad.[63] Ahlus-Sunna suma suna ɗaukar cewa abin da ake nufi da Alu su ne mutanen da ayar taɗhir ta sauka game da su, duk da cewa akwai saɓani tsakanin malaman Ahlus-Sunna game da su wane ne masu amsa wannan take da suna.[64]
A cewar Ibn Hajar Haisami daga malaman Ahlus-Sunna, ingantaccen salatin Annabi da aka sani shi ne (Allahumma salli ala Muhammad wa ali Muhammad) da wannan dalili ne a mazhabar shafi'iyya wajibi yin salati ga Muhammad da ali Muhammad.[65] Amma tare da haka, Ibn Taimiyya daga malamai mabiya tafarkin salafiyya yana cewa duk da cewa daidai da umarnin da Annabi ya bayar wajibi ne idan za a yi salati ga Annabi a ƙara da alu Muhammad, amma sakamakon kasancewar wannan sigar irin wannan salati ta zama wata alama ga ƴanshi'a, to rashin haɗawa da alu Muhammad ya fi alheri.[66] San'ani shima ya yi ishara da cewa goge kalmar "Alu" ta faru a zamanin mulkin Banu Umayya ne sakamakon tsoro da taƙiyya da mutane ke yi.[67]
Bisa wata riwaya da aka naƙalto a cikin Sihahus Sitta na Ahlus-Sunna (Ingantattun litattafai guda shi na Ahlus-Sunna), wajibi yin salati ga Annabi tare da jumlar "Alu Muhammad"[68] Subki daga malaman Ahlus-Sunna, a cikin littafinsa Shifa'us Saƙam ya tattaro lafazi guda (52) da suka zo cikin hadisan Annabi game da salati, mafi yawansu sun ƙunshi "Alu Muhammad" baki ɗayan riwayoyin babu wace aka kawo salati ga sahabbai kamar yadda galibi Ahlus-Sunna suke aikatawa.[69]
An ce Ahlus-Sunna suna da saɓani game da yin salati ga waɗanda ba Annabawa, wasu suna ganin hakan matsayin makaruhi wasu kuma suna ganin cewa yana halatta idan da farko an fara da salatin ga Annabi daga baya aka yi wa wani mutum daban.[70]
A Wanne Wurare Ne Ya Kama Mu Yi Salati

Bisa shahararren ra'ayin malaman fiƙihu na Shi'a[71] yin salati yayin ambaton suna ko alkunya ko laƙabin Annabi (S.A.W), hatta a cikin sallah yana daga cikin aiki na mustahabbi.[72] Wasu malaman suna ɗaukar wannan aiki a matsayin wajibi.[73] Husaini Wahid Khurasani, daga cikin maraji'an taƙlidi na Shi'a yana da ra'ayin cewa yin salati yayin ambaton sunan Imam Ali (A.S) aiki ne mai kyawun gaske.[74]
Bisa wasu riwayoyi,[75] an bayyana cewa mafi alherin lokacin yin salati, shi ne dare da ranar juma'a.[76] daga cikin sauran wurare da aka yi nasiha da yin zikirin salati za a iya ishara da wuraren da bayaninsu zai zo a ƙasa:
- Cikin ruku'u da sujjada na sallah[77]
- Farkon fara huɗubobi da laccoci
- Yayin ɗawafi da sa'ayi tsakanin safa da marwa
- A cikin watan Rajab da Sha'aban da Ramadan
- Yayin shiga masallacin harami
- Farko da ƙarshen alwala
- A cikin addu'o'in bayan idar da sallah
- Lokacin ido biyu da masallacin haramin Annabi (S.A.W)
- Kafin da bayan addu'a
- Lokacin shaƙar ƙamshin fure
- Yayin atishawa
- Lokacin tafiye-tafiye.[78]
Mabambantan Sigogi Da Lafuzzan Salati
Mafi shaharar sigar salati shi ne "Allahumma salli ala Muhammad wa ali Muhammad", amma cikin wasu riwayoyi akwai wasu sigogin daban da aka yi bayaninsu.[79] A cewar wasu masu bincike haƙiƙa a cikin littafin Sahifa Sajjadiyya an kawo bayanin sigogi 210 na zikirin salati.[80]
Bisa wani hadisi, Annabi ya bayyana ingantacce salati da sigar "Allahumma salli ala Muhammad wa ali Muhammad" ya kuma hana faɗin "Allahumma salli ala Muhammad wa ala ali Muhammad"[81] Sayyid Ali Khan Kabir, marubucin littafin Riyadus Salikin, bai yarda da ingancin wannan hadisi ba,[82] amma Muhammad Baƙir Majlisi yana da ra'ayin cewa haƙiƙa sira tana tabbatar da ingancin hadisi.[83]

Salati Tare da Faɗin Wa Ajjil Farajahum
Wasu daga cikin ƴanshi'a bayan zikirin salati suna faɗin jumlar "Wa ajjil farajahum" ma'ana Allah ka gaggauta sauƙaƙawarsu"[84] wannan zikiri da aka ƙara wata addu'a ta neman gaggauta bayyanar Imam Mahadi (A.F). Bisa wata riwaya da aka naƙalto daga Imam Sadiƙ (A.S), cikin wasu sharuɗɗa da ayyanannen adadi, an yi alƙawarin lada ga wannan aiki, ciki har da samun dacewa da ganin fuskar Imam Mahadi (A.F).[85] kasancewa cikin keɓantattun mataimakansa[86] samun cetonsa a ranar alƙiyama.[87]
Bayanin kula
- ↑ Zamani, "Kayfiyyat-i Salawat az Nigah-i Fariƙayn" , shafi na 31.
- ↑ Ibrahimi, Athar wa Barakat al-Salawat, 143ƙ, shafi na 27-28.
- ↑ Alawi, Athar al-Salawat fi Rihab al-Riwayat, 1437 ƙ, shafi na 17.
- ↑ Musawi, "Salawat, Ahkam wa Athar-i An", shafi na 3.
- ↑ MuryarHausa:https://www.muryarhausa24.com.ng/2019/09/Me-Ne-Ne-Salatin-Annabi-Muhammad-SAW-Karanta-Yadda-ake-Yin-Salatin-Annabi-Muhammd-SAW-a-Mahangar-Sunnah-Falalar-Salatin-Annabi-Muhammad-SAW.html
- ↑ Fayyad, "Fiƙhe Fariƙayn wa Jaygah-i Ahlulbait (A.S.) dar Salawat" , shafi na 165.
- ↑ Rida'i, "Kayfiyyat wa Chigunagi-yi Salawat bar Payambar-i A'zam (S.A.W.) Nazd-i Fariƙayn" , shafi na 74.
- ↑ Rida'i, "Kayfiyyat wa Chigunagi-yi Salawat bar Payambar-i A'zam (S.A.W.) Nazd-i Fariƙayn" , shafi na 74.
- ↑ Musawi, "Salawat, Ahkam wa Athar-i An" , shafi na 21.
- ↑ Musawi, "Salawat, Ahkam wa Athar-i An" , shafi na 21.
- ↑ Misbah Yazdi, Sahba-yi Huzur, 1391 SH, shafi na 459.
- ↑ Rida'i, "Kayfiyyat wa Chigunagi-yi Salawat bar Payambar-i A'zam (S.A.W.) Nazde Fariƙayn" , shafi na 63.
- ↑ Mawardi, Al-Hawi al-Kabir, 1419 ƙ , juzu'i na 2, shafi na 137.
- ↑ Najafi, Jawahir al-Kalam, Dar Ihya al-Turath al-Arabi, juzu'i na 11, shafi na 213-214.
- ↑ Husayni Amili, Miftah al-Karamah, Dar Ihya al-Turath al-Arabi, juzu'i na 1, shafi na 478.
- ↑ Makarim Shirazi, Payam-i Imam Amir al-Mu'minin, 1386SH, juzu'i na 3, shafi na 200.
- ↑ Shayesteh Rukh, "Karburd-shenasi-yi Salawat dar Taraneh-hayi Kasht wa Bardasht-i Kishawarzi" , shafi na 165-167.
- ↑ Jawad, "Salawat-khani Hunar-i 'Ibadi-yi Mazhabi az Yad Rafteh" , shafi na 58.
- ↑ Ruhbakhsh, "Salawat-i Siyasi" , shafi na 40.
- ↑ Ƙazawi, "Khatm-i Salawat" , shafi na 371.
- ↑ Nassaji, "Rayihah-yi Ruh-afza-yi Salawat" , shafi na 59.
- ↑ Ƙazawi, "Khatm-i Salawat" , shafi na 371.
- ↑ Ƙazawi, "Khatm-i Salawat" , shafi na 371.
- ↑ Shaykh Tusi, Misbah al-Mutahajjid, 1411ƙ, juzu'i na 1, shafi na 50-51.
- ↑ Zamani, "Kayfiyyat-i Salawat az Nigah-i Fariƙayn" , shafi na 30.
- ↑ Durudgar, "Asrar wa Athar-i Salawat bar Payambar (S.A.W.) wa Al-i Payambar (S.A.W.)" , shafi na 15.
- ↑ Musawi, "Salawat, Ahkam wa Athar-i An" , shafi na 24.
- ↑ Kamali, "Naƙde Didgah-i 'Adam Intifa'-i Payambar (S.A.W.) az Du'a wa Salawat-i Ummat, ba Ta'kid bar Imkan-i Rif'at-i Darajah-yi An Hazrat dar ƙaws-i Su'ud" , shafi na 175.
- ↑ Shahid Thani, Al-Rawdah al-Bahiyyah, 1427ƙ, juzu'i na 1, shafi na 13.
- ↑ Duba: Tabatabai, Barresi-hayi Islami, 1388SH, juzu'i na 1, shafi na 150..
- ↑ Shahid Thani, Al-Rawdah al-Bahiyyah, 1427 Hijira (2006-2007 Miladiyya) , juzu'i na 1, shafi na 13.
- ↑ Amoli, Hezar wa Yek Nukteh, 136SH, shafi na 186.
- ↑ Shahid Thani, Al-Rawdah al-Bahiyyah, 1427ƙ, juzu'i na 1, shafi na 13. .
- ↑ Majlisi, Mir'at al-'uƙul, 1404ƙ, juzu'i na 12, shafi na 112-113; Mutahhari, Majmu'ah-yi Asar, 1389SH, juzu'i na 23, shafi na 316..
- ↑ Tabatabai, Al-Mizan, 1417ƙ, juzu'i na 16, shafi na 329.
- ↑ Shaykh Saduƙ, Uyun Akhbar al-Rida (A.S.), 1378 Hijira (1958-1959 Miladiyya) , juzu'i na 1, shafi na 294, Hadisi na 52.
- ↑ Shu'ayri, Jami' al-Akhbar, Al-Matba'ah al-Haydariyyah, shafi na 59.
- ↑ Himyari, ƙurb al-Isnad, 1413ƙ shafi na 14, Hadisi na 45.
- ↑ Shaykh Saduƙ, Al-Amali, 1376 SH , shafi na 580, Hadisi na 18.
- ↑ Shaykh Saduƙ, Al-Amali, 1376 Hijira SH, shafi na 580, Hadisi na 18.
- ↑ Shaykh Saduƙ, Ilal al-Shara'i', 1385ƙ , juzu'i na 1, shafi na 34, Hadisi na 3.
- ↑ Shu'ayri, Jami' al-Akhbar, Al-Matba'ah al-Haydariyyah, shafi na 59.
- ↑ Kulayni, Al-Kafi, 1407ƙ, juzu'i na 2, shafi na 493, Hadisi na 13.
- ↑ Shahid Thani, Munyat al-Murid, 1409ƙ, shafi na 347.
- ↑ Shaykh Tusi, Al-Amali, 1414ƙ, shafi na 172, Hadisi na 42.
- ↑ Shaykh Saduƙ, Thawab al-A'mal, 1406 Hijira (1985-1986 Miladiyya) , shafi na 155.
- ↑ Shaykh Saduƙ, Thawab al-A'mal, 1406ƙ, shafi na 156.
- ↑ Kulayni, Al-Kafi, 1407ƙ, juzu'i na 2, shafi na 492, Hadisi na 7.
- ↑ Shaykh Saduƙ, Al-Khisal, 1362SH , juzu'i na 2, shafi na 394, Hadisi na 101.
- ↑ Shaykh TusƙHijira (1990-1991 Miladiyya) , juzu'i na 1, shafi na 368.
- ↑ Shu'ayri, Jami' al-Akhbar, Al-Matba'ah al-Haydariyyah, shafi na 59.
- ↑ Kulayni, Al-Kafi, 1407ƙ, juzu'i na 2, shafi na 494, Hadisi na 17.
- ↑ Ibn Ash'ath, Ja'fariyyat, Maktabat al-Naynuwa, shafi na 215-216.
- ↑ Rawandi, Al-Da'awat, 1407ƙ , shafi na 216, Hadisi na 581.
- ↑ Tabrisi, Makarem al-Akhlaƙ, 1412ƙ, shafi na 312.
- ↑ Shaykh Saduƙ, Al-Amali, 1376 ƙ, shafi na 73, Hadisi na 4.
- ↑ Fayyad, "Fiƙh Fariƙayn wa Jaygah-i Ahlulbait (A.S.) dar Salawat" , shafi na 165.
- ↑ Najafi, Jawahir al-Kalam, Dar Ihya al-Turath al-Arabi, juzu'i na 10, shafi na 262.
- ↑ Alal misali, duba: Kulayni, Al-Kafi, 1407 ƙ, juzu'i na 2, shafi na 495, Hadisi na 21; Shaykh Saduƙ, Al-Amali, 1376SH, shafi na 200, Hadisi na 9.
- ↑ Khuyi, Mawsu'at al-Imam al-Khu'i, 1418 ƙ, juzu'i na 15, shafi na 256.
- ↑ Alal misali, duba Kulayni, Al-Kafi, 1407ƙ, juzu'i na 2, shafi na 495; Khargushi, Sharaf al-Mustafa, 1424ƙ, juzu'i na 5, shafi na 107; Haytami, Al-Sawa'iƙ al-Muhriƙah, 1417ƙ juzu'i na 2, shafi na 430.
- ↑ Shushtari, Ihƙaƙ al-Haƙƙ, 1409 Hijira (1988-1989 Miladiyya) , juzu'i na 9, shafi na 524-611.
- ↑ Muƙaddas Ardabili, Majma' al-Fa'idah wa al-Burhan, 1403 ƙ, juzu'i na 2, shafi na 277.
- ↑ Rida'i, "Kayfiyyat wa Chigunagi-yi Salawat bar Payambar-i A'zam (S.A.W.) Nazd-i Fariƙayn" , shafi na 74.
- ↑ Haytami, Al-Sawa'iƙ al-Muhriƙah, 1417ƙ, juzu'i na 2, shafi na 667.
- ↑ Ibn Taymiyyah, Minhaj al-Sunnah al-Nabawiyyah, 1406ƙ, juzu'i na 4, shafi na 154.
- ↑ San'ani, Subul al-Salam, 1427ƙ, juzu'i na 1, shafi na 554.
- ↑ Alal misali, duba Bukhari, Sahih al-Bukhari, 1410ƙ, juzu'i na 5, shafi na 351; da juzu'i na 7, shafi na 385; da juzu'i na 10, shafi na 103; Ibn Hajjaj Nishaburi, Sahih Muslim, Dar Ihya al-Turath al-Arabi, juzu'i na 1, shafi na 305.
- ↑ Duba: Subki, Shifa' al-Siƙam, 1429ƙ, shafi na 407-412.
- ↑ Musawi, "Salawat, Ahkam wa Athar-i An" , shafi na 11.
- ↑ Naraƙi, Mustanad al-Shi'ah, 1415ƙ, juzu'i na 5, shafi na 336.
- ↑ Tabatabai Yazdi, Al-'Urwah al-Wuthƙa (Al-Muhashsha) , 1419ƙ , juzu'i na 2, shafi na 619.
- ↑ Alal misali, duba: Fadil Miƙdad, Kanz al-'Irfan, 1373SH, juzu'i na 1, shafi na 133; Shaykh Bahai, Miftah al-Falah, 1405ƙ , shafi na 38.
- ↑ Wahid Khurasani، «صلوات فرستادن هنگام شنیدن نام امیرالمؤمنین(ع) در اذان و اقامه»،Shafin yanar gizo na hukuma na Ofishin Mai girma Ayatullahi al-Uzma Wahid Khorasani.
- ↑ Alal misali, duba Kulayni, Al-Kafi, 1407 Hijira ƙ, juzu'i na 3, shafi na 429.
- ↑ Nassaji Zawareh, "Salawat Ramz-i Mahabbat wa Wafadari ba Payambar (S.A.W.) wa Khwandanish (A.S.)" , shafi na 64.
- ↑ Kulayni, Al-Kafi, 1407ƙ, juzu'i na 3, shafi na 324.
- ↑ Nassaji Zawareh, "Salawat Ramz-i Mahabbat wa Wafadari ba Payambar (S.A.W.) wa Khwandanish (A.S.)" , shafi na 65-66.
- ↑ Fayyad, "Fiƙh Fariƙayn wa Jaygah-i Ahlulbait (A.S.) dar Salawat" , shafi na 168-169.
- ↑ Samadaniyan, da Saburi, "Salawat wa Payambar (S.A.W.) dar Sahifah-yi Sajjadiyyah" , shafi na 76-77.
- ↑ Majlisi, Lawami' Sahibƙarani, 1414ƙ, juzu'i na 6, shafi na 647.
- ↑ Madani Shirazi, Riyad al-Salikin, 1409ƙ, juzu'i na 1, shafi na 427.
- ↑ Majlisi, Lawami' Sahibƙarani, 1414ƙ, juzu'i na 6, shafi na 647.
- ↑ «فرستادن صلوات با عجل فرجهم»، Shafin Tibyan.
- ↑ Shaykh Tusi, Misbah al-Mutahajjid, 1411ƙ, juzu'i na 1, shafi na 368
- ↑ Daylami, A'alam al-Din, 1408ƙ, shafi na 367
- ↑ Sayyid Ibn Tawus, Jamal al-Usbu', 1330ƙ, shafi na 450
Nassoshi
- Alƙur'ani Mai Girma
- ««کیفیت صلوات از نگاه فریقین»،»، (Yanayin Salati (Hanyar Salati) daga Mahangar Firkoki Biyu (Ahlus-Sunnah da Shi'a) a Mujallar Hikima da Falsafar Musulunci, lamba ta 8, bazara ta 2003 M.
- Alawi, Adil, Athar al-Salawat fi Rihab al-Riwayat (Tasirin Salati a Fagen Ruwayoyi), Qom, Cibiyar Musulunci ta Wa'azi da Shiryarwa., 1437ƙ.
- Ibrahim, Ali, Asare Barkate Salawat, Bairut,1432ƙ.
- Askari, Sayyid Murtada, Min Sunan al-Nabi (S.A.W.) al-Salat 'ala Muhammad wa Ali Muhammad (S.A.W.) Tehran, Mash'ar, babu ranar bugawa .
- Ibn Ash’ath, Muhammad bin Muhammad, Ja’fariyat, Tehran, Mawallafar Ninawa, babu kwanan wata.
- Baƙiri Bidahandi، «کتابنامۀ صلوات»، (Takardar Salati) A cikin mujallar Ilimin Hadisi (Ulum al-Hadith), lamba ta 13, kakar kaka ta shekarar 1999.
- Bukhari, Muhammad ibn Isma'il, Sahih al-Bukhari, Alƙahira Ma'aikatar kula da waƙafi, 1410ƙ.
- Dailami, Hasan ibn Muhammad, A'lam al-Din fi Sifat al-Mu'minin, Qom, Cibiyar Al al-Bait (A.S.), 1408ƙ.
- Durudgar, Muhammad Jawad، «اسرار و آثار صلوات بر پیامبر(ص) و آل پیامبر(ص)»، ("Sirrika da Sakamakon Salati ga Annabi (S.A.W. da kuma Alayansa (A.S) " ko "Asrar da Falalolin Salati ga Annabi da IyalanSa ") aA cikin mujallar Al'adun Ziyara (Farhang-e Ziyarat), lamba ta 7, lokacin rani na shekarar 2011M.
- Fadil Miƙdad, Miƙdad ibn Abdullah, Kanz al-'Irfan fi Fiƙh al-ƙur'an (Taskar Ilimi a Fikihun Alƙur'ani), Tehran, Murtadawi, 1373SH.
- Husaini Ardakani, Ahmad, Sharh wa Fada’il Salawat, Tehran, Miƙat, 1375SH.
- Fayyad, Muhammad Ishaƙ, Al-Istifta'at al-Shar'iyyah (Fatawoyi na Shari'a), babu wurin bugawa, Al-Kalimah al-Tayyibah, 1435ƙ.
- Fayyad, Muhammad Sadiƙ«فقه فریقین و جایگاه اهلبیت(ع) در صلوات»،(Fikihun ɓangarori biyu (Sunnah da Shi'a) da matsayin Ahlul-Baiti (a.s) a cikin salati.) A cikin Mujallar Binciken Fikihi, lamba ta 5, kakar kaka ta shekarar 2011M.
- Hasanzadeh Amoli, Hasan, Hezar wa Yek Nukteh (Dubu da Daya Nuktehi), Tehran, Rija', 1365SH.
- Haytami, Ahmad ibn Muhammad, Al-Sawa'iƙ al-Muhriƙah 'ala Ahl al-Rafd wa al-Dalal wa al-Zandaƙah, Beirut, Cibiayr al-Risalah, 1417ƙ.
- Himyari, Abdullah ibn Ja'far, Ƙurb al-Isnad, Qom, Cibiyar Al al-Bait (A.S.), 1413ƙ.
- Husayni Amili, Sayyid Muhammad Jawad, Miftah al-Karamah fi Sharh Ƙawa'id al-'Allama, Beirut, Mawallafar Gidan Raya Gadon Larabawa., babu ranar bugawa.
- Ibn Ash'ath, Muhammad ibn Muhammad, Ja'fariyyat, Tehran, Mawallafar al-Naynuwa, babu ranar bugawa.
- Ibn Hajjaj Nishaburi, Muslim, Sahih Muslim, Beirut, MawallafarGidan Raya Gadon Larabawa., babu ranar bugawa.
- Ibn Hanbal, Ahmad, Musnad Ahmad, Beirut, Cibiyar al-Risalah, 1421ƙ.
- Ibn Taymiyyah, Ahmad ibn Abd al-Halim, Minhajus Sunnah al-Nabawiyyah fi Naƙḍi Kalam al-Shi'ah al-ƙadariyyah, Riyadh, Jami'ar Muhammad ibn Sa'ud ta Musulunci, 1406ƙ.
- Jawed, Hawshang، «صلواتخوانی هنر عبادی مذهبی ازیادرفته», ("Salati (Karatun Salati) Fasaha ce ta Ibadar Addini da aka manta" ko kuma "Salati: Fasahar Ibadar Addini da ta ɓace")A cikin mujallar Fasahar Al-farma (Astan-e Honar), lamba ta 4 da 5, lokacin rani na shekarar 2013M.
- Kamali, Muhammad Hadi, da sauransu«نقد دیدگاه عدم انتفاع پیامبر(ص) از دعا و صلوات امت، با تأکید بر امکان رفعت درجه آن حضرت در قوس صعود»، (Sukar ra'ayin da ke cewa Annabi (s.a.w) ba ya amfana da addu'a da salatin al'umma, tare da jaddada yiwuwar daukaka matsayinsa a cikin tafiyar daukaka ta ruhi (ƙaus al-Su'ud).)A cikin mujallar Ilimin Kalam (Ma'rifat-e Kalami), lamba ta 26, lokacin bazara da rani na shekarar 2021M.
- Khamseh'i ƙazwini, Ali, Al-Salawat Miftah Hall al-Mushkilat, Beirut, Mawallafar Kamil, babu ranar bugawa.
- Khargushi, Abdul al-Malik ibn Muhammad, Sharaf al-Mustafa, Makkah, Mawallafar Gidan Busharorin Musulunci., 1424ƙ .
- Khuyi, Abul Ƙasim, Mawsu'at al-Imam al-Khu'i, Qom, Cibiyar Ihya Athar al-Imam al-Khu'i, 1418ƙ.
- Kulayni, Muhammad ibn Yaƙub, Al-Kafi, Tehran, Mawallafar Gidan Littattafan Musulunci, 1407ƙ. .
- Madani Shirazi, Sayyid Ali Khan Kabir, Riyad al-Salikin, Qom, Ofishin Wallafe-wallafe na Musulunci 1409ƙ.
- Majlisi, Muhammad Baƙir, Mir'at al-'Uƙul fi Sharh Akhbar Al al-Rasul (S.A.W.), gyara da bincike: Sayyid Hashim Rasuli Mahallati, Tehran, Gidan Littattafai na Musulunci, 1404ƙ.
- Majlisi, Muhammad Taƙi, Lawami' Sahibƙarani, Qom, Isma'iliyan, 1414ƙ.
- Makarim Shirazi, Nasir, Payame Imam Amir al-Muminin (A.S.), Tehran, Gidan Littattafai na Musulunci, 1386 SH.
- Mawardi, Ali ibn Muhammad, Al-Hawi al-Kabir fi Fiƙh Madhhab al-Imam al-Shafi'i, Beirut,Gidan Littattafai na Musulunci, 141ƙ.
- Misbah Yazdi, Muhammad Taƙi, Sahba-yi Huzur, tsarawa da rubutu: Asadullah Tusi, Qom, Cibiyar Koyarwa da Bincike ta Imam Khomeini, shekarar 1391 Hijira Shamsi (2012-2013 M.
- Muƙaddas Ardabili, Ahmad ibn Muhammad, Majma' al-Fa'idah wa al-Burhan fi Sharh Irshad al-Adhhan , Qom, Ofishin Wallafe-wallafe na Musulunci, shekarar 1403ƙ.
- Musawi, Sayyid Rida«صلوات، احکام و آثار آن»، (Salati: Hukunce-hukuncensa da Tasirinsa) A cikin Mujallar Ilimin Addini da Shari'a (Ilahiyat wa Huƙuƙ), lamba ta 30, lokacin hunturu na shekarar 2009M.
- Mutahhari, Murtada, Majmu'ah-yi Asar, Tehran, Mawallafar Sadra, 1389SH.
- Najafi, Muhammad Hasan, Jawahir al-Kalam, Beirut, Mawallafar Gidan Raya Gadon Larabawa., babu ranar bugawa.
- Naraƙi, Ahmad ibn Muhammad Mahdi, Mustanad al-Shi'ah fi Ahkam al-Shari'ah, Qom, Cibiyar Alul al-Bayt (A.S.), 1415 ƙ.
- Nasa'i, Ahmad ibn Shu'ayb, Sunan al-Nasa'i, Halab, Ofishin Wallafe-wallafe na Musulunci, 1406ƙ.
- Nassaji Zawareh, Isma'il«صلوات رمز محبت و وفاداری به پیامبر(ص) و خاندانش(ع)»، (Salati: Alamar ƙauna da biyayya ga Annabi (s.a.w) da iyalansa (a.s).) A cikin mujallar Darussan Mazhabar Musulunci (Darshaye az Maktab-e Islam), lamba ta 6, watan Shahrivar shekarar 2003M.
- Ƙazawi, Iffat, "Khatm-i Salawat, , wanda Rasul Ja'fariyan ya rubuta, babu wurin bugawa, babu mawallafi, 1393sh.
- Rahimi, Ma'suma«جایگاه صلوات بر پیامبر(ص) و اهلبیت(ع) در قرآن، حدیث و ادعیه مأثوره»،(Matsayin salati ga Annabi (s.a.w) da Ahlul-Baiti (a.s) a cikin Alkur'ani, Hadisi, da kuma addu'o'in da aka ruwaito.) A cikin mujallar Tunanin Alkur'ani (Andishe-haye ƙur'ani), lamba ta 15 da 16, lokacin bazara da hunturu na shekarar 2021m.
- Rawandi, Sa'id ibn Hibatullah, Al-Da'awat (Addu'o'i), Qom, Madrasat Imam al-Mahdi (A.S.), 1407ƙ.
- Rida'i, Asadullah«کیفیت و چگونگی صلوات بر پیامبر اعظم(ص) نزد فریقین»، (Siffa da yadda ake yin salati ga fiyayyen Annabi (s.a.w) a wurin ɓangarori biyu (Sunnah da Shi'a).)A cikin Mujallar Binciken Hikima da Falsafar Musulunci, lamba ta 23, lokacin hunturu na shekarar 2008M.
- Ruhbakhsh, Rahim«صلوات سیاسی»، (Salati na Siyasa) A cikin mujallar Zamane, lamba ta 21, watan Mayu/Yuni shekarar 2004 M.
- Sajistani, Abi Dawud Sulayman ibn Ash'ath, Sunan Abi Dawud, Beirut, Al-Maktabah al-'Asriyyah, babu ranar bugawa.
- Samadaniyan, Muhsin, da Omid Saburi«صلوات و پیامبر(ص) در صحیفه سجادیه»، (Salati da Matsayin Annabi (s.a.w) a cikin Sahifatul Sajjadiyya) A cikin mujallar Alkur'ani ta Kausar, lamba ta 23, lokacin hunturu na 2007 da bazara na 2007 M.
- San'ani, Muhammad ibn Isma'il, Subul al-Salam Sharh Bulugh al-Maram, Riyadh, Mawallafar al-Ma'arif, 1427ƙ.
- Shafi'i, Ali, Gawhar-hayi Mansur, Tehran, Gustarish-i Rayaneh, 139SH.
- Shah Ni'matullah Wali, Diwan-i Ash'ar-i Shah Ni'matullah Wali, Kerman,Ofishin Hidima ga Al'adu na Kerman1380SH.
- Shahid Thani, Zayn al-Din Amili, Al-Rawdah al-Bahiyyah fi Sharh al-Lum'ah al-Dimashƙiyyah, gyara da bincike: Hasan Ƙarubi Tabrizi, Qom,Mawallafar Gidan al-Tafsir, 1427ƙ.
- Shahid Thani, Zayn al-Din ibn Ali, Munyat al-Murid fi Adab al-Mufid wa al-Mustafid, Qom, Ofishin Yaɗa Labarai na Musulunci. 1409 ƙ.
- Shayesteh Rukh, Elaheh«کاربردشناسی صلوات در ترانههای کاشت و برداشت کشاورزی»، (Amfani da Salati a cikin Wakokin Shuka da Girbi na Manoma) A cikin mujallar Al'adun Al'ummar Iran (Farhang-e Mardom-e Iran), lamba ta 71, lokacin hunturu na shekarar 2023 M.
- Shaikh Bahai, Muhammad ibn Husayn, Miftah al-Falah fi 'Amal al-Yawm wa al-Laylah min al-Wajibat wa al-Mustahabbat , Beirut, Mawallafa al-Adwa', 1405ƙ.
- Shaikh Mufid, Muhammad ibn Nu'man, Al-Irshad fi Ma'rifat Hujaj Allah 'ala al-'Ibad, Qom, Taron Sheikh Mufid, 1413 ƙ.
- Shaikh Saduƙ, Muhammad ibn Ali, Al-Amali, Tehran, Mai sayar da littattafai, 1376SH.
- Tha’labi, Ahmad bin Muhammad, Al-Kashf wal-Bayan an Tafsiril Ƙur’an, Beirut, Gidan Raya Gadon Larabawa., 1422ƙ.
- Shaikh Saduƙ, Muhammad ibn Ali, Al-Khisal (Halaye), Qom, Ofishin Wallafe-wallafen Musulunci, 1362SH.
- Shaikh Saduƙ, Muhammad ibn Ali, Ilal al-Shara'i', Qom, Shagon littafi Dawari, 138ƙ.
- Shaikh Saduƙ, Muhammad ibn Ali, Ma'ani al-Akhbar, Qom, Ofishin Wallafe-wallafen Musulunci, 1403M.
- Shaikh Saduƙ, Muhammad ibn Ali, Thawab al-A'mal wa 'Iƙab al-A'mal, Qom, Mawallafar al-Sharif al-Radi, 1406 ƙ.
- Shaikh Saduƙ, Muhammad ibn Ali, Uyun Akhbar al-Rida (A.S.), Tehran, Mawallafar Jahan, 1378ƙ.
- Tirmizi, Muhammad bin Isa, Sunan Tirmizi, Al-ƙahira, Shirkat Maktabat wa Matba’at Mustafa al-Babi al-Halabi, 1395ƙ.
- Shaikh Tusi, Muhammad ibn Hasan, Al-Amali, Qom, Mawallafar al-Thaƙafah, 1414ƙ.
- Shaikh Tusi, Muhammad ibn Hasan, Misbah al-Mutahajjid wa Silah al-Muta'abbid, Beirut, Cibiyar Fiƙh al-Shi'ah, 1411ƙ.
- Shu'ayri, Muhammad ibn Muhammad, Jami' al-Akhbar, Najaf, Al-Mabugar al-Haydariyyah, babu ranar bugawa
- Shushtari, Nurullah ibn Sharif al-Din, Ihƙaƙ al-Haƙƙ wa Izhaƙ al-Batil, Qom, Laburaren Ayatullah Mar'ashi Najafi, 1409ƙ.
- Subki, Ali ibn Abd al-Kafi, Shifa' al-Siƙam fi Ziyarat Khayr al-Anam (S.A.W.), Tehran, Mawallafar Mash'ar, 1429ƙ.
- Tabarani, Sulayman ibn Ahmad, Al-Mu'jam al-Kabir, Alƙahira, Mabugar Ibn Taymiyyah, 1415ƙ.
- Tabatabai Yazdi, Sayyid Muhammad Kazim, Al-'Urwah al-Wuthƙa fima Ta'ummu bihi al-Balwa (Al-Muhashsha) Qom, Ofishin Wallafe-wallafen Musulunci, 1419ƙ.
- Tabatabai, Muhammad Husayn, Barresi-hayi Islami, tare da ƙoƙarin Sayyid Hadi Khosrowshahi, Qom, Mawallafar Bustane Kitab, 1388SH.
- Zahra Nassaji«رایحه روحافزای صلوات»، (Kamshi Mai Ratsa Ruhi na Salati)A cikin mujallar Pasdar-e Islam, lamba ta 303, watan Fabrairu zuwa Afrilu na shekarar 2007 M.
- MuryarHausa:https://www.muryarhausa24.com.ng/2019/09/Me-Ne-Ne-Salatin-Annabi-Muhammad-SAW-Karanta-Yadda-ake-Yin-Salatin-Annabi-Muhammd-SAW-a-Mahangar-Sunnah-Falalar-Salatin-Annabi-Muhammad-SAW.html Shigarwa: July 12 2019, dubawa: September 30, 2019 M.