Shifa'us Saƙam Fi Ziyarati Khairil Anam (Littafi)
| Marubuci | Subki |
|---|---|
| Maudu'i | Ziyartar Annabi (S.A.W) |
| Salo | Raddi/Suka |
| Harshe | Larabci |
| Mai bugawa | Da'iratul Ma'arif Al-Usmaniyya |
| Tarihin bugawa | 1419 hijira ƙamari |
Shifa'us Saƙam Fi Ziyarati Khairil Anam, (Littafi: شِفاءُ السَّقام فی زیارَةِ خَیرِ الاَنام) wani littafi ne na Taƙiyyud-dini Subki malami a mazhabar shafi'iyya a ƙarni na 8 ya rubuta wannan littafi matsayin raddi kan mahangar Ibn Taimiyya Harrani game da haramcin niyyar tafiya domin ziyartar Annabi (S.A.W).
Subki a cikin wannan littafi, ya tabbatar da halasci da kuma irin falalar da take cikin zuwa ziyarar Annabi, ya kuma ba da amsa kan shubuhohin Ibn Taimiyya.
Gabatarwa Da Kuma Matsayin Wannan Littafi
Shifa'us Saƙam Fi Ziyarati Khairil Anan (Warakar cututtuka cikin ziyartar mafificin mutane) wani littafi ne da Taƙiyyid-dini Subki ya rubuta wanda a cikinsa ya yi suka kan mahangar Ibn Taimiyya game da zuwa ziyarar Annabi (S.A.W). cikin wasu bincike da aka yi, wannan littafi an bayyana shi matsayin mafi cikar fashin baƙi da aka yi kan riwayar Shaddu Rihal (Wata riwaya ce da take bayani kan falalar masallacin Harami, masallacin Annabi da masallacin Al-aƙsa da yin tafiya domin yin sallah a cikin waɗannan masallatai).[1] Wasu jama'a daga malaman Ahlus-Sunna da suke kan ra'ayin Subki suna ganin halascin zuwa ziyarar ƙabarin Annabi, kuma sun yabawa Subki da littafinsa.[2] Wani suna na daban na littafin shi ne "Shannul Gara Ala Man Ankara Fadliz Ziyara".[3]
Mahangar Ibn Taimiyya Game da Ziyartar Annabi
Ibn Taimiyya babban malamin mai matuƙar tasiri a tafiyar salafiyya tare da jingina da hadis Shaddu Rihal, ya haramta ɗaure jaka domin zuwa ziyarar ƙaburbura, hatta ƙabarin Annabi, a wasu wurare kuma ya bayyana hakan a matsayin bidi'a da aiki na shirka. A ra'ayin Ibn Taimiyya kan asasin wannan hadisi[4], ɗaure jaka don zuwa ziyara kaɗai yana halatta ne cikin ziyartar masallatai guda uku, masallacin Harami, masallacin Al-Aƙsa da masallacin Annabi.[5]
Game da Marubucin Wannan Littafi
Taƙiyyud-dini Subki (Rayuwa: 683-756) ya kasance daga malaman mazhabar shafi'iyya, kuma an haife shi a garin Sabak a Misra.[6] Bayan ya yi karatu a wurin malamai kamar Dimyati da Ibn Aɗa'ullahi Sufi, ya samu muƙamin alƙalanci a Sham ya ci gaba kan wannan muƙami har zuwa ƙarshen rayuwarsa.[7] Subki daɗi kan koyarwa da shugabancin makarantar Darul Hadis Ashrafiyya, ya yi rubutu kan sukan ra'ayoyin Ibn Taimiyya, Durratul Mudi'a da Shifa'us Saƙam suna daga jumlarsu.[8] An binne shi a birnin Al-Ƙahira na Misra.[9]
Tsarin Littafin Da Kuma Abin da Ya Tattaro
An gabatar da bahasosin wannan littafi cikin babuka guda goma da khatima guda ɗaya:
- Babukan 1-3: Binciken nassosi da sira ta ilimin Musulmi game da ziyara. Riwaya ta farko daga Ibn Umar wace cikin ta Annabi ya ce: مَنْ زَارَ قَبْرِي وَجَبَتْ لَهُ شَفَاعَتِي (Duk wanda ya ziyarci ƙabarina cetona ya wajaba gare shi).[10]
- Babuka 46: Bincike kan mahangar malamai, halasci na ibada da falalar tafiya domin ziyara
- Babuka 7-10: Raddi kan shubuhohin Ibn Taimiyya, rayuwar barzahu ta Annabawa da halascin tawassuli da kuma batun shafa'a da ceto
- Khatima: Naƙalin nassosin salati ga Annabi da aka naƙalto daga littafin Al-A'alam Bi Fadlis Salati Alan Nabiyyi.[11]
Raddi Da Aka Rubutu Kan Wannan Littafi
Ibn Abdul-Hadi Hanbali, ya rubuta raddi kan wannan littafi na Subki, kuma cikin raddin ya bayyana cewa da'awar da Subki ya yi wace ta ginu cewa Ibn Taimiyya yana adawa da zuwa ziyartar Annabi (S.A.W) ba gaskiya ba ce. A cewarsa Ibn Taimiyya bai yi inkarin asalin ziyara ba, bari ma dai ya lissafa ta cikin ayyuka na mustahabbi.[12]
Buga Wannan Littafi Da Yaɗa Shi
Bugu na farko ya kasance ta hannun Intisharat Amiriyya Al-Kubra Misra a shekarar 1919m. Bugu na biyu a Turkiyya, na uku da na huɗu a ya kasance a Intisharat Da'iratul Ma'arif Al-Usmaniyya da Haidar Abad Dakan..[13]
Bayanin kula
- ↑ Abbasi-Moghaddam, Barrasi Matani Wa Sanadi Rewayat Shaddu Rehal. shafi. 198.
- ↑ Duba: Hosseini Jalali, “Muƙaddima”, 2011, shafi 37-39.
- ↑ Sarhadi, Radde Fatawaye Wahabiyat shafi. 199.
- ↑ Misali, duba Ibn Taimiyyah, Minhaj al-Sunnah, 1406H, juzu'i. 2, shafi. 440.
- ↑ Ibn Taimiyyah, Minhaj al-Sunnah, 1406H, juzu'i. 2, shafi. 440..
- ↑ گزارش کتاب شفاء السقام فی زیارة خیر الأنام تألیف قاضی سبکی،Ayatullah Makarem Shirazi'in yada labarai.
- ↑ گزارش کتاب شفاء السقام فی زیارة خیر الأنام تألیف قاضی سبکی،Ayatullah Makarem Shirazi'in yada labarai..
- ↑ گزارش کتاب شفاء السقام فی زیارة خیر الأنام تألیف قاضی سبکیAyatullah Makarem Shirazi'in yada labarai.
- ↑ Sabaki, Shafa al-Saqam, 1419 AH, shafi. 7.
- ↑ Sabaki, Shafa al-Saqam, 1390, 1433 AH, shafi. 66.
- ↑ Sabaki, Shafa al-Saqam, 1419 AH, shafi na 51-56;«سلسله گزارشهایی از آثار اهل سنّت در نقد افکار وهابیت»،Cibiyar Yada Labarai Ayatullah Makarem Shirazi; Asgharinejad, Gabatarwa ga littafin Shifa' al-Saqam fi Ziyara Khair al-Anam, shafi. 191.
- ↑ Sabaki, Shafa al-Saqam, 1419 AH, shafi. 44.
- ↑ شفاء السقام فی زیارة خیر الانام، Noor Digital Library.
Nassoshi
- Ibn Taimiyyah, Ahmad bin Abdul Halim, Minhasu Sunnatin Nabawiyya Fi Naƙdi Kalam Shi'a Qadriyya, Riyad, Imam Muhammad bin Saud Jami’ar Musulunci, 1406 Hijira.
- Asgarinejad, Muhammadمعرفی کتاب: شفاء السقام فی زیارة خیرالأنام،Farhang Kowsar, bazara 2009, No. 77.
- Hosseini Jalali, Seyyed Mohammad Reza, Muƙaddima, Shifa'us Saƙam Fi Ziyarati Khairil Anam, na Ali bin Abdul Kafi Sabuki, Tehran, Mashaar, 2011.
- Sabuki, Ali bin Abdul Kafi, Shifa'us Saƙam Fi Ziyarati Khairil Anam, Hyderabad, Encyclopedia Ottoman, 1419 Hijira.
- Sarhadi, Mehdi, «رد فتاوای وهابیان»، A cikin Mujallar Miqat Hajj, fitowa ta 57, Fall 2006.
- Jerin rahotanni kan ayyukan Ahlus-Sunnah wajen sukar tunanin Wahabiyawa, rahoto kan littafin Shifa’ al-Saqam, Cibiyar Watsa Labarai ta Ayatollah Makarem Shirazi, ranar ziyarar: 1 ga Disamba, 2020.
- Shifa’ al-Saqam Fi Ziyarati Khair al-Anam, Noor Digital Library.
- Abbasi-Moghaddam, Mustafa، «بررسی متنی و سندی روایت شد رحال»،Mujallar Nazarin Hadisi Bi-Quarterly, Fitowa ta 8, Faɗuwa da Lokacin hunturu 2012.