Daƙiƙa:Mutum Mai Shekaru 250 (Littafi)
- Wannan maƙala ce game da mutum mai shekaru 250. domin sanin nazariya da take da irin wannan suna, ku duba shafin Nazariyar Mutum Mai Shekara 250.
![]() | |
| Marubuci | Ayatullhi Khamna'i |
|---|---|
| Maudu'i | Rayuwar Imaman Shi'a a fagen siyasa |
| Salo | Tarihi-Bincike |
| Harshe | Yaren Farsi |
| Da taimakon | Cibiyar Iman Jihadi (Sahba) |
| Adadin Jildi | Guda uku |
| Tarjama zuwa sauran harsuna | Larabci, Turanci, Faransanci, Hausa, Ƙurdanci, Turkanci Istanbuli, Jamusanci, Urdu da Azeri |
| Mai bugawa | Cibiyar Sabha (Cibiyar jihadi) |
| Wurin da aka buga shi | Tehran |
| Tarihin bugawa | Halƙa na biyu 2010 miladiyya, halƙa na uku 2019 miladiyya |
| Sunan littafi | Mutum Mai Shekaru 250 (Halƙa na biyu) |
| Mai tarjama | Majma Jahani Ahlul-Baiti (Hausa) |
Mutum Mai Shekaru 250 wani littafi ne da ya ƙunshi wasu sassa daga bayanai da jawabai na Ayatullah Sayyid Ali Khamna'i, jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran, game da rayuwar siyasar Imaman Shi'a. Wannan littafin ya ginu a kan nazariyar Mutum mai shekaru 250, wadda take ɗaukar rayuwar Imaman Shi'a duk da bambance-bambancen bayyanarta a matsayin mahanga da matafiya gudu ɗaya mai ci gaba wanda ta fara daga lokacin wafatin Annabi (S.A.W) kuma ya ci gaba har zuwa shekara ta 260 Hijira, wato kusan shekaru 250, inda dukkansu a wannan lokaci suke neman kafa gwamnatin Musulunci.
Abubuwan da ke cikin littafin an zaɓo su ne daga cikin jawabai na jagoran Iran a tsakanin Mayu 1980 zuwa Maris 2011 miladiyya. Bayan wani lokaci da buga littafin, an sake fitar da wasu abubuwan cikinsa tare da sabon tsarin rabewa da ƙarin wasu jawabai na Ayatullah Sayyid Ali Khamna'i, a ƙarƙashin taken halƙa ta farko da halƙa ta uku.
An rubuta littafin Mutum Mai Shekaru 250 da harshen Farsi, kuma an sake bugawa fiye da sau 85. Haka kuma an fassara shi zuwa harsuna daban-daban.
Matsayi Da Muhimmanci
Littafin Mutum Mai Shekaru 250 ya ƙunshi jawabai na Ayatullah Sayyid Ali Khamna'i jagoran jamhuriyar Musulunci ta Iran, wanda ɗaya daga maraji'an taƙlidi na Shi'a, game da nazariyar mutum mai shekara 250, wanda ya gabatar tun kafin Juyin Juya halin Musulunci na Iran na 1979 lokacin gwagwarmaya da ɗauki babu daɗi tsakanin al'ummar Iran da gwamnatin Pahlavi.[1] An sake buga wannan littafi a lokuata da dama da harshen Farsi kuma an fassara shi zuwa harsuna sama da goma.[2]A Iran ana kuma shirya kwasa-kwasai na ilimi[3] da gasa da suka shafi wannan littafi.[4]
A cewar Sayyid Hassan Ali Imad, babban sakataren ƙungiyar Tanzim Mustaƙbal al‑Adalah ta Yaman, wannan littafi ya canza tunani da fahimtar, ƴanShi'ar Yaman game da jihadi da gwagwarmaya..[5]
Sunan Littafi
Sunan Mutum Mai Shekaru 250 yana nufin shekaru 250 na Imamancin Imaman Shi'a, daga wafatin Annabi (S.A.W) a shekara ta 11 Hijira har zuwa farkon gaiba sugra a shekara ta 260 Hijira. Ayatullah Sayyid Ali Khamna'i yana kallon wannan tarihin kamar rayuwar mutum guda mai shekaru 250.[6]
Jigo Da Hanyar Bincike
Kamar yadda aka bayyana a gabatarwar littafin:
- Imaman Shi'a ba su taƙita kan cikin a iya gwagwarmayar yaɗa ilimi, akida da tauhidi kawai ba; rayuwarsu ta kasance tare da manufa ta siyasa.[7]
- Dukkanin Imama'i ma'asumai suna da manufa guda ɗaya, hali guda da hanya guda ɗaya. Tun daga wafatin manzon Allah (S.A.W) har zuwa shekara ta 260 Hijira, dukkanin sun kasance suna ƙoƙarin kafa gwamnatin Musulunci.[8]
- Imamai ba su mayar da hankali ga yaƙin makami ba, amma kuma ba su yi wa masu ɗaukar makami suka kai tsaye ba; amma ba su shiga irin wannan yaƙin kai tsaye ba.[9]
Tsarin Littafin
Littafin Mutum Mai Shekaru 250 ya ƙunshi ishara guda, gabatarwa da babi guda 17:
- Fasali na farko: Annabi mafi girma (S.A.W)
- Fasali na biyu: Imamanci
- Fasali na uku: Amirul Muminin (A.S)
- Fasali na huɗu: Sayyida Faɗima Zahra (S)
- Fasali na biyar: Imam Hassan (A.S)
- Fasali na shida: Imam Husaini (A.S)
- Fasali na bakwai: Gwagwarmayar Zainabul Kubra da jakadun Karbala
- Fasali na takwas: Yanayin zamantakewa da siyasa bayan waƙi'ar Karbala
- Fasali na tara: Imam Sajjad (A.S)
- Fasali na goma: Imam Baƙir (A.S) zamanin gina tunani da tsari
- Fasali na sha ɗaya: Ƙarshe-ƙarshen mulkin Banu Umayya da Imancin Imam Sadiƙ (A.S)
- Fasali na sha biyu: Imam Sadiƙ (A.S)
- Fasali na sha uku: Tsarin ƙungiya na ɓoye
- Fasali na sha huɗu: Imam Kazim (A.S)
- Fasali na sha biyar: Imam Rida (A.S)
- Fasali na sha shida: Imam Jawad (A.S), Imam Hadi (A.S) da Imam Hasasn Askari (A.S)
- Fasali na sha bakwai: Manufar ƙarshe ta tafiyar Mutum Mai Shekaru 250
Bugawa Da Tarjama
An buga littafin Mutum Mai Shekaru 250 a shekara ta 2011 a Iran ta hannun maɗabba'ar Sahba cikin shafuka 375,[10] kuma zuwa ƙarshen 2020 an sake bugawa fiye da sau 85.[11]
An tarjama wannan littafin zuwa harsuna da dama kamar:Larabci, Turanci, Urdu, Azeri, Ƙurdanci, Turkanci Isntanbuli, Indiyanci, Sindi, Jamusanci, Tailan,[12] Hausa Farasanci.[13]
Tarjamar Larabci ta fito da taken Ahlul-Baiti Insan Bi Umri 250 Am, wanda Ahmad Sami Wahbi ya tarjama, yana da shafuka 398 kuma maɗabba'ar Dar al‑Wala ta buga a Bairut a shekarar 2015.[14]
Maƙaloli Masu Alaƙa
Bayanin kula
- ↑ Gafari, Az Nimeh Khordad, Khamna'i, Insane 250 Saleh, 1391sh, sh 15
- ↑ «انسان ۲۵۰ ساله تبیین استراتژی امامان در جریانِ مبارزه سیاسی»، Kamfanin Dillancin Labarai na Fars."
- ↑ «Za a fara daurar horar da malamai masu koyar da littafin mutum mai shekaru 250، Kamfanin dillancin labari na Hauza.
- ↑ «دوره تربیت مدرس کتاب «انسان ۲۵۰ ساله» آغاز میشود»،Kamfanin Dillancin Labarai na Hausa..
- ↑ توزیع کتاب آیتالله خامنهای در یمن، نگاهها را تغییر داد، Kamfanin Dillancin Labarai na Tasnim.
- ↑ Insane 250 Sale, sh 16
- ↑ Insane 250 Sale, sh 16-17
- ↑ Insane 250 Sale, sh 17-18
- ↑ Insane 250 Sale, sh 17
- ↑ Khamna'i, Insane 250 Sale, sh 4-5
- ↑ «انسان ۲۵۰ ساله تبیین استراتژی امامان در جریانِ مبارزه سیاسی»Kamfanin Dillancin Labarai na Fars.
- ↑ «انسان ۲۵۰ ساله تبیین استراتژی امامان در جریانِ مبارزه سیاسی»،Kamfanin Dillancin Labarai na Fars.
- ↑ ترجمه «انسان ۲۵۰ ساله» به اردو و آذری،Kamfanin Dillancin Labarai na Tasmin..
- ↑ Wahbi, Ahlull-Baiti, Insani Bi Umri 250 Am, darul Wala, Bairut
Nassoshi
- Insane 250 Saleh: Bayanat-e Maqam-e Mo‘azzam-e Rahbari darbare-ye Zendegi-ye Siyāsi-Mobārezāti-ye A'emme-ye Ma‘sumin". Tehran, Cibiyar Sahba, 1390Sh,
- Gafari, Musɗafa, Az Nime Khordad, Cibiyar Binciken Al'ada Juyin Juya Halin Musulunci, 1398SH.
- Khamna'i Sayyid Ali, Insane 250 saleh, Cibiyar Sahba, 1391SH.
- «مسابقه کتابخوانی انسان ۲۵۰ ساله برگزار میشود»»,(Za a yi gasar karatun littafin mutum mai shekaru 250), Babban Darakta na Al'adu da Jagorancin Islama na Lardin Tehran, an buga shi ranar 11 ga Nuwamba, 2019, an duba shi ranar 24 ga Afrilu, 2022.
- «00213 «انسان ۲۵۰ ساله تبیین استراتژی امامان در جریانِ مبارزه سیاسی»، (Mutum mai shekaru 250 Bayyana dabaru da tsare-tsare Imamai Cikin gwagwarmaya ta siyasa), Kamfanin labarai Fars, an buga shi ranar 1 ga Disamba, 2020, an duba shi ranar 24 ga Afrilu, 2022M
- ««دوره تربیت مدرس کتاب «انسان ۲۵۰ ساله» آغاز میشود،»، (Za a fara daurar horar da malamai masu koyar da littafin mutum mai shekaru 250), Kamfanin labarai na Howza, an buga shi ranar 26 ga Satumba, 2019, an duba shi ranar 24 ga Afrilu, 2022
- «توزیع کتاب آیتالله خامنهای در یمن، نگاهها را تغییر داد»،(Rarraba littafin Ayatullahi Khamna'i a Yemen ya sauya yadda mutane suke kallon al'amura.), Kamfanin Dillancin Labarai na Tasnim, ranar wallafa labarin: 8 Oktoba 2016 Miladiyya, ranar dubawa: 24 Afrilu 2022 Miladiyya.
