Yankan Shari'a

Daga wikishia
Wannan wani rubutu ne ne mai bayyanawa game da ra'ayi na fikihu kuma ba zai iya zama ma'auni na ayyukan addini ba. Koma zuwa wasu tushe don ayyukan addini.
Risala Ilmiyya

Yankan shari’a (Larabci: الذبح الشرعي) shi ne: yanke kawunan dabbobi ta hanyar da Shari’a ta yarda da ita, ya halatta a ci naman halastattun dabbobi da suke rayuwa a doron ƙasa (banda Fara da Raƙumin da ba a Soke shi ta hanyar da ta halatta ba) . Hakama dabbobi da ba su halatta aci Namansu ba za'a iya amfani da wasu ɓangarorin jikinsu bayan an musu yankan Shari'a, za a iya amfani da su a ko'ina amma banda sallah, kamar yanda fatawowin malamn fiƙhu suka tabbatar . Sharuɗan da addini ya gindaya wajan yanka dabbobi su ne: dole ne abin da za ai yankan da shi ya zama daga jinsin ƙarfe, dabbar ta fuskanci alƙibla, dabbar ta kasance tana raye kafin yanka, mai yanka ya kasance musulmi, ya ambaci sunan Allah a lokacin yanke kan dabbar, kuma a yanke jijiyoyi guda huɗu na wuyanta. hakama a addinin Yahudanci akwai wasu sharuɗɗa da aka gindaya wajan yanka dabbobi. A addinin musulunci akwai ladubba na yankan dabba don kada dabbar ta ji zafi, amma a wasu ƙasashen da ba na musulunci ba ana hana yankawa ta hanyar da musulunci ya tanadar. a wani binciken da akai ya nuna yanka dabba ta hanyar addini yana haifar da ingantaccen nama da da kuma daɗewa bai lalace ba.

Mafhumi Da Matsayi

Yanka yana ɗaya daga cikin hanyoyin da yake tsarkake naman dabbobi, wanda yake samuwa ta hanyar yanke jijiyoyin wuyansu guda hudu.[1] Gaba ɗaya halattattun dabboin da suke kan doran ƙasa (banda Raƙuma da Fara) da wasu daga dabbobin cikin ruwa da suke da jini mai gudana ajikinsu,[2] ana kiran dabbar da aka yanka ta hanyar addini (mai tsarki ) wanda ta saɓawa mushe kenan,[3] wanda ya yanka dabbar ana kiransa (zabih) Dabban da aka yanka kuma "zabiha" ko “Mazbuh”.[4] Alkur'ani mai girma ya haramtawa musulmi cin naman dabbobin da ba a yanka su, ta hanyar shari'a ba.[5] a cikin littafin fiƙihu an kawo sharuɗɗan yanka dabba a babin said da zabbaha.[6]

Sharuɗɗa

A addinin musulunci an kawo wasu sharuɗa na yanka dabba waɗannan sharuɗɗan su ne: A yanke manyan jijiyoyi hudu na wuyan dabba daga karkashin maƙogwaro.[7]

A yayin yankawar mai yankawar zai kira sunan Allah. A cewar mai littafin Jawahir, dukkan malaman fiƙihu sun tafi kan cewa wannan sharaɗin dole ne.[8] A daidaita dabbar ta fuskanci alƙibla.[9] kamar yadda fatawowin malaman fiƙihun Shi’a suka yi bayani, idan wanda zai yanka dabba ya yankata ba bisa wannan ƙa’idar ba Alhalin ya san wannan sharaɗin, tabbas naman dabbar haramun ne.[10] Abin da za'a yanka dabbar da shi ya zama daga ƙarfe; Tabbas idan akwai larura da fargabar rasa dabbar, ana iya amfani da dutse ko duk wani abu mai kaifi na yanka domin yanka ta.[11] Dola ne mai yanka ya kasance musulmi.[12] a cewar Shahid Sani malamin fiƙihu na ‘yan Shi’a a ƙarni na 10, bisa fatawar dukkanin malaman fiƙhun musulmai, mai yanka ba zai iya zama Kafiri ko wanda ya yi ridda ko ya yi guluwwi ba,[13] Tabbas, akwai mahanga guda biyu game da Ahlul-Kitabi; Mafi yawan malaman fiƙhu na Shi'a suna ganin abin da ya fito daga hanunsu na yanka haramun ne kuma najasa ne,[14] Haka nan malaman fiƙhu na Shi'a suna ganin yankan Nawasib shima a matsayin najasa kuma haram.[15] Dole ne dabbar ta kasance da rai kafin a yanka. wasu malaman fiƙhu sun ce dole ne dabbar ta motsa jikinta ko hannayenta da ƙafafunta bayan an yanka ta don nuna cewa tana raye kafin a yanka ta.[16]

A fatawowin malaman fiƙhu na duk musulmai, ya halasta a yanka dabbobi da sabbin na’urori; Sai dai kuma wajibi ne a ambaci sunan Allah a lokacin yanka da sauran sharuɗan yanka kamar yanke jijiyoyi guda huɗu tabbas dole a kiyaye su.[17]

Naman da ba a san shin an yanka dabbar ta hanyar Sharia ba koba ta hanyar shari’a aka yanka ta ba, halal ne in har daga hannun musulmi ko kuma daga kasuwar musulmai ya fito.[18]

Ladubba

Akwai wasu ladubba a cikin littattafan malamai da suka zo da za a kiyayesu lokacin yanka: Mustahabbi ne mai yanka ya fuskanci alƙibla.[19] Abin da zai yankan da shi ya zama mai kaifi kuma a gaggauta yin yankan. Kafin a yanka, a sanya ruwa a gaban dabbar. A shirya dabbar a hankali cikin nutsuwa. Idan Tunkiya za'a yanka a ɗaure hannayenta biyu da ƙafa ɗaya sannan a hankali cikin nutsuwa a saki ɗaya ƙafar. Idan za'a yanka Saniya za'a ɗaure hannayenta da ƙafafunta guda hudu sannan a saki jelarta. Bayan an yanka Kaza za a bar ta ta shi ta yi tsalle da fuka-fukanta.[20]

Abubuwan Da ba a So

Yanke ƙashin baya kafin yanka dabba. Yanka Dabba a gaban sauran Dabbobi Yanka Dabbar da aka kiwata a gida Yanka dabba a dare . Yanka kafin zawali a ranar Juma'a. Caka wuƙa a bayan maƙogaro sannan a ja ta zuwa gaba, ta yadda za a yanke makogwaro daga baya.[21]

Kufaifayi

A wajen malaman fiƙihun musulmai bayan yanka dabba tana zama halal, haka cin namanta ma yana zama halal, haka sassan jikinta, Amma idan aka yanka dabbar da cinta haram ne, to duka sassan jikintama haram ne, sai dai a fatawar wasu malaman fiƙihu, ana iya amfani da fata ko gashin su amma banda wajan sallah.[22] Haka nan idan ba a yanka dabbar ba bisa ka’ida, ta mutu kuma ba ta da tsarki.[23]

Wani bincike ya nuna cewa yanka ta hanyar addini yana da tasiri mai kyau a kan ingancin nama saboda rashin jini a cikin naman da aka yanka, wannan naman yana da inganci da ɗorewa idan aka kwatanta da sauran hanyoyin yanka.[24]

Yankan A Addinin Yahudu Da Kiristoci.

A cikin addinin Yahudawa, akwai hanyoyi na yanda ake yanka dabbobi, yazo a Talmud cewa kada dabbar ta kasance a sume ko kuma ta kasa tsayawa kafin a yanka ta.[25] Haka nan, ya kamata mai yankan yazama ya koya a hannun malaman yahudawa (rababai) sun horar da shi.[26] A yahudanci ana kiran yanka da (shechita).[27] A addinin nasara babumaganar yanka.[28]

Haramcin Yankan Addini A Wasu ƙasashe

A wasu ƙasashe kamar Netherlands.[29] Denmark.[30] da Belgium.[31] an haramta yanka dabbobi ta hanyoyin musulunci dana Yahudawa. Dalilin da ya sa aka kafa wannan doka shi ne hana jin zafi da raɗaɗin da ake samu a lokacin yanka,[32] Hakika falsafar wasu al’adun Musulunci wajen yanka, kamar kaifin wuka da saurin yanka, suna. Rage jin raɗaɗi ga dabba das za a yanka [33]A wasu ƙasashen Kiristoci, dole ne a fara sumar da dabba kafin a yanka ta.[34] A cewar malaman fiƙihu na Shi’a, babu matsala idan aka sumar da dabba kafin a yanka ta sai dai hakan kar ya kai ga mutuwar dabbar.[35]

Bayanin kula

  1. Bani Hashemi Khomeini, Tauzihul Al-Masa'il al-Marjah, 1392, shafi na 742.
  2. Hashemi Shahroudi, Farhang Fiqhu mutabik mazhab Ahlul Baiti, 1382, juzu’i na 3, shafi na 702.
  3. Sarami, “Tazkiyeh”, shafi na 795.
  4. Hashemi Shahroudi, Farhang Fiqhu mutabik mazhab Ahlul Baiti, 1382, juzu’i na 3, shafi na 701
  5. Suratul Ma'idah, aya ta 3.
  6. Hashemi Shahroudi, Farhang Fiqhu mutabik mazhab Ahlul Baiti, 1382, juzu’i na 3, shafi na 701
  7. Shahid Sani, Masalak al-Afham, 1413 AH, juzu'i na 11, shafi 473.
  8. Najafi, Jawahirul Kalam, 1362, juzu'i na 36, ​​shafi 113.
  9. Najafi, Jawahirul Kalam, 1362, juzu'i na 36, ​​shafi 110.
  10. Najafi, Jawahirul Kalam, 1362, juzu'i na 36, ​​shafi 111; Tabatabaei Yazdi, Al-Arwa Al-Wuthghati (Al-Mahshi), 1419 AH, Mujalladi na 2, shafi na 315.
  11. Shahid Sani, Masalak al-Afham, 1413 AH, 1413 AH, juzu'i na 11, shafi na 470.
  12. Shahid Sani, Masalak al-Afham, 1413 AH, 1413 AH, juzu'i na 11, shafi na 451.
  13. Shahid Sani, Masalak al-Afham, 1413 AH, 1413 AH, juzu'i na 11, shafi na 451.
  14. Shahid Thani, Masalak al-Afham, 1413 AH, juzu'i na 11, shafi 451; Najafi, Jawahirul Kalam, 1362, juzu'i na 36, ​​shafi na 80.
  15. Najafi, Jawaharul Kalam, 1362, juzu'i na 36, ​​shafi na 95.
  16. Bani Hashemi Khomeini, Tauzihul Masa'il Maraji, 1392, juzu’i na 2, shafi na 745
  17. Duba Bani Hashemi Khomeini, Risalah Tauzihul al-Masa'il al-Mara'ah, Beta, juzu'i na 2, shafi na 579 da 582.
  18. Hashemi Shahroudi, Farhang Fiqhu mutabik mazhab Ahlul Baiti, 1382, juzu’i na 2, shafi na 427.
  19. Tabatabaei Yazdi, Al-Arwa Al-Wuthghati (Al-Mahshi), 1419 AH, Mujalladi na 2, shafi na 312.
  20. Bani Hashemi Khomeini, Tauzihul Masa'il, Bita, Mujalladi na 2, shafi na 580.
  21. Bani Hashemi Khomeini, Tauzihul masa'il Beta, Juzu'i na 2, shafi na 583-580.
  22. Najafi, Majma al-Rasaleh (Mohshi Sahib Javaher), 1415 AH, p.
  23. Tabatabaei Yazdi, Al-Arwa Al-Wuthghati (Al-Mahshi), 1419 AH, Mujalladi na 1, shafi na 125.
  24. Khizrulu wa Digaran , "Usul Zibhi Islami wa Nakhshe An dar Irtika kaifiyat gusht", shafi na 80-84; Sattari wa Digaran, “Tasiri zibhi halal bar kaifiyat gusht wa mukayese an ba sayir kushtarha ”, shafi na 38-36.
  25. Kohn, Gunjineh az Talmud, 1350, shafi na 257.
  26. Kohn, Gunjineh az Talmud, 1350, shafi na 257.
  27. Sheikh Baha'i, Hurmatu Zaba'ihi Ahlul Kitab, 1410H, shafi na 50.
  28. Sajjadi, "Zibhu wa nahri dar fikihi Islami", shafi na 164-165.
  29. ذبح اسلامی و یهودی در هلند غیرقانونی شد»، سایت بی‌بی‌سی فارسی
  30. [https://www.independent.co.uk/news/world/europe/denmark-bans-halal-and-kosher-slaughter-as-minister-
  31. says-animal-rights-come-before-religion-9135580.html Denmark bans kosher and halal slaughter as minister says ‘animal rights come before religion]
  32. [https://www.nytimes.com/2019/01/05/world/europe/belgium-ban-jewish-muslim-animal-slaughter.html Belgium Bans Religious Slaughtering
  33. ذبح اسلامی و یهودی در هلند غیرقانونی شد
  34. Sajjadi, "Zibhu wa Nahri dar fikihu Islami", shafi na 150.
  35. Sajjadi, "Zibhu wa Nahri dar fikihu Islami", shafi na 164-165.

Nassoshi

Sajjadi, Marzieh Sadat, "Zibhu wa Nahre dar Fikihi Islami", a cikin Mujallar Nazarin Addinin Musulunci, lamba 43, bazara da bazara 2018.

  • Shaheed Thani, Zain al-Din bin Ali, Masalak al-Afham ili Tankih Shaaree al-Islam, Qom, Islamic Encyclopaedia Foundation, 1413 AH.
  • Sheikh Baha'i,Muhammad bin Hossein Zabaih Ahl-Kitab,Beirut,Labarin Al-alami,1410H.
  • Sarami, Saifullah, "Tazkiyeh", dar daneshname Buzurg Jahan Islami, Tehran, Islamic Encyclopedia Foundation, 1375.
  • Tabatabaei Yazdi, Seyyed Mohammad Kazem, Al-Arwa Al-Wuthghati (Al-Mahsh)i, edited by Ahmad Mohseni Sabzevari, Qum, Islamic Publications Office, 1419 AH.
  • Fatemi, Seyyed Hassan, "Pajuheshi Tadbiki dar Ahkam Zibhi ", kitabe Mah Din, lamba 28, Fabrairu 1378.
  • Kohn, Abraham, Gunjineh Talmud, wanda Amir Fereydoun Gorgani ya fassara, Tehran, Gidan Bugawa na Yahudawa, 1350.
  • «معرفی و دانلود کتاب روش‌های مختلف ذبح و اثر آن بر کیفیت گوشت»، کتاب‌راه، مشاهده: ۴ آبان ۱۴۰۱ش.
  • Najafi, Mohammad Hasan, Javaher al-Kalam fi Sharh Shar'e al-Islam, bincike daga Mahmoud Quchani, Beirut, Darahia al-Trath al-Arabi, bugu na 7, 1362
  • Najafi, Mohammad Hasan, Majma al-Rasal (Mohshi Sahib Javaher), Sahib al-Zaman Institute, Mashhad, 1415 AH.
  • Hashmi Shahroudi, Mahmoud, Farhang Fikihu mutabik Ahlul Baiti, Qum, Cibiyar Shari'ar Musulunci, 1382.

Template:چپ‌چین