Daƙiƙa:Algina'u (Littafi)
Don sauran amfani, duba Gina (Bambancewa).
| Sauran sunaye | Darasin Algina'u da Kiɗa (ko Littafin darasi kan Gina da Kiɗa) |
|---|---|
| Marubuci | Sayyid Ali Husaini Khamna'i |
| Maudu'i | Gina da Musik |
| Salo | Darasul Kharij |
| Harshe | Farsi |
| Adadin Jildi | 1 |
| Mai bugawa | Bugun Juyin Juya Halin Musulunci |
| Wurin da aka buga shi | Tehran |
| Tarihin bugawa | Bazara Maris zuwa Yuni 2019 |
| Bugu | bugu na farko |
| Lambar littafi | 3000 |
Gina ko kuma Darasin Ginada Kiɗa wani rubutu ne da aka wallafa daga darasul Kharij na Fiƙihu na Ayatullahi Khamna'i game da batun Gina da kiɗa. An koyar da wannan darasi daga watan Azar 1387 Sh. zuwa Bahman 1388Sh.
A cikin wannan littafi, an mayar da hankali kan hadisai da suka shafi Gina, inda aka yi bayani kan ma'anar Gina da kiɗan da yake haram, sannan aka nazarci waɗannan hadisai da kuma ra'ayoyin malamai na fiƙihu. Haka kuma an amsa tambayoyi 48 da suka shafi wannan batu.
Bisa ga ra'ayin Ayatullah Khamna'i da aka bayyana a cikin littafin, Gina ba haram ba ne da kansa; abin da ke sa shi haram shi ne idan yana cikin Lahawu da nishaɗi mai kai mutum ga ɓata, yana kuma fitar da mutum daga tafarkin Allah. Haka kuma ma'aunin kiɗan haram shi ne idan yana kai yanayi zuwa rashin kulawa da addini da kuma aikata zunubi.
An wallafa wannan littafi a karon farko a shekara ta 1398 SH, ta hannun Cibiyar Bincike ta Al'adu da Juyin Juya Halin Musulunci, cikin harshen Farisanci.
An wallafa wannan littafi a karon farko a shekarar 1398 SH, (2019 Miladiyya)ta hannun Cibiyar Bincike ta Al'adu da Juyin Juya Halin Musulunci, cikin harshen Farisanci.
Marubuci
Ayatullahi Khamna'i shi ne Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran, kuma yana daga cikin maraji'an taƙlidi na Shi'a[1] Ya fara koyar da darasin Kharij na fikihu tun a shekara ta 1369 SH (1990 miladiyya), kuma ya koyar da babi‑babi kamar jihadi, ƙisasi, mu'amalolin da aka haramta (makasib al‑muharrama), da sallar matafiyi.[2]
Abin da Yake Cikin Littafin
Darasin "Gina da Kiɗa" rubutu ne da aka tsara daga darussan Fiƙihu na Kharij na Ayatullahi Khamna'i, wanda ya ƙunshi darussa 75, kuma an gabatar da su daga 4 Azar 1387 SH zuwa 6 Bahman 1388 SH (wato daga 24 Nuwamba 2008 zuwa 26 Janairu 2010 miladiyya).[3]
Wannan littafi yana bayyana ma'anar Ginada kiɗan da ake haramta, tare da nazari mai zurfi kan fannoni daban‑daban na batun.[4]
A lokacin nazarin hadisai, an dogara da littattafan fiƙihu da kuma ra'ayoyin malaman Shi'a.[5] A ƙarshen littafin kuma, batun rawa ya zama abin nazari.[6]
A cewar Rida Mukhtari, ɗaya daga cikin tushe na wannan littafin darasi shi ne littafi mai juzu'i huɗu mai suna «Gina, Musiƙi» da Muhsin Sadiƙi da Rida Mukhtari suka rubuta.
Tsarin darasin Kharij na Ayatullah Khamna'i asalin ya dogara ne da littafin "Makasib" na Shaikh Ansari, amma da zarar ya kai ga batun Gina, sai ya bar "Makasib" ya ɗauki littafin "Gina, Musiƙi" a matsayin ma'aunin tattaunawa.
Ya nazarci dukkan hadisai na wannan littafi daga bangaren isnad (asalin ruwaya) da matn (abun cikin ruwaya), sannan ya tattauna binciken malamai da ke cikin sauran juzu'i na littafin bisa dangantakar batun.[7]
Baya ga wannan, malaman fiƙihu sun yi la'akari da ɓangaren tarihi na batun Gina da kiɗa, wanda yake kallon fahimta mai daidai na hadisai da ruwayoyi da suka shafi wannan batu.[8]
Hanyar Gabatar Da Muhawarori Na Ilimi
A cikin littafin Gina, an tattauna batutuwan Gina, kiɗa, da rawa. Ayatullahi Khamna'i a cikin darasin Kharij na fiƙihu game da Gina, ya raba hadisai da suka shafi Ginazuwa rukuni biyar, sannan ya yi nazari da bincike kan isnadi (silsilar ruwaya) da kuma dalalar (ma'anar) kusan hadisai 100.
Wadannan rukuni biyar su ne:[9]
- Ruwayoyin da suka zo a ƙarƙashin ayoyi: Wannan ya haɗa da ruwayoyin da suka yi tafsirin ayoyi kamar: Ku nisanci maganar ƙarya»[10] «Ba sa shaida ga ƙarya»[11] Maganar nishaɗi marar amfani»[12] Idan suka wuce wajen ɓatanci, sukan wuce da mutunci»[13] .Haka kuma akwai ruwayoyin da aka yi istishhad, wato ruwayar da take kiran ayoyi a matsayin shaida.[14]
- Ruwayoyin da ba su zo a ƙarƙashin ayoyi ba: Waɗannan su ne ruwayoyin da suka yi magana kai tsaye kan haramcin Gina.[15]
- Ruwayoyin sauraro Gina (Sauraron waƙar Gina): Wadanda suka yi bayani game da jin ko sauraron Gina.[16]
- Ruwayoyin samun kuɗi ta hanyar mawaƙiya (mughanniyah):[17] Ruwayoyin da suka tattauna yin kasuwanci ko samun samun kuɗi daga Gina.
- Ruwayoyin da suka shafi Ginaa cikin karatun Alƙur'ani:[18]
Siffofi
'Nuna Kayan Kiɗa A Talabijin:'
Nuna waɗannan kayan kiɗa a talabijin wani nau'i ne na yaɗawa da kuma sa su zama abin da mutane suka saba da shi. Amfani da waɗannan kayan wajen samar da sautukan nishaɗi na banza (Lahwi) ya fi yawa fiye da amfani da su a sautukan da ba na banza ba. Wato ɓangaren da ake ɗauka haram ya fi na halal yawa. Duk lokacin da muka yaɗa wannan, to muna yaɗa abin da yake haram da kuma wargi.[19]
An ambaci wasu siffofi na littafin "Gina" kamar haka:
- Mayar da hankali kan riwayoyi da suka shafi batun gina (Riwayoyi 100)[20] An ce dukkan hadisai na gina da abubuwan da suka shafi shi an bincika su dalla‑dalla ta fuskar isnadi da matani.[21]
- Gabatar da ma'aunai daban‑daban na gina da kiɗan haram.[22]
- Cikakken tattara ra'ayoyi da nazarin malamai na Shi'a na farko da na baya‑bayan nan[23]؛ an kuma duba dukkan risaloli da aka rubuta kan gina.[24].
- Amsa tambayoyi 48 da suka shafi gina da kiɗan haram.[25]
- Tsara littafin a matsayin tsarin darussa.[26]
Darasin "kharij" na fikihun gina ana ɗaukarsa ɗaya daga cikin mafi tsawon darussa a hauzoci kan wannan batu.[27]
Ra'ayoyi
Wasu daga cikin ra'ayoyin Ayatullahi Khamna'i a cikin wannan littafi sun kasance kamar haka:
Gina
- Ginaa kankin kansa, ba haram ba ne. Abin da ke sa haramcinsa shi ne lahawanci (Wargi) da kau da mutum daga hanyar Allah (ya rude shi ya fita daga tafarkin Allah).[28]
- Fayyace lahwanci "da kau da mutum daga hanyar Allah" ta ɗaya daga cikin abubuwa kamar: tayar da sha'awa, angiza mutum zuwa aikata haram, hana mutum yin abin da ya zama wajibi,
ko sa mutum ya zama ba ya damu da addini.[29]
- Abubuwan da ake yi musu shakka, ba su zama haram. A irin waɗannan abubuwa, ana aiki da ƙa'idar bara'a..[30]
'Ƙa'idar gaba ɗaya game da Kiɗan Haramun'
Duk wani waƙa ko sauti da yake jawo yanayi, yanayin da sautin yake yaɗuwa a cikinsa, zuwa rashin kula da addini, zuwa aikata zunubi, da zuwa watsi da wajibi da nauyin shari'a, to haram ne.[31]
Musik (Kiɗa)
- Ma'aunin kiɗan haram shi ne jawo yanayi zuwa rashin kula da addini da kuma zunubi.[32] Kiɗa a kansa ba haram ba ne, kuma sai idan an tabbatar da cewa yana jawo zuwa zunubi da rashin kula da addini, sannan za a iya bayar da fatawar cewa haram ne.[33]
- Al'ada (Urufi) ce ake komawa gare ta wajen tantance Ginada kiɗan haram.[34] Idan mukallafi ya yi shakka ko kiɗan a wajen al'adar mutane ana ɗaukarsa mai kau da mutum daga hanyar Allah kuma haram ne ko a'a, to bisa asalin halacci za a hukunta cewa halal ne.[35]
Rawa
- Rawa haram ce, kuma ma'aunin haramcinta shi ne kasancewarta lahwiyya (Nishaɗin banza). Amma rawar mace ga mijinta ba a ɗaukarta lahwiyya ba, don haka ba ta cikin wannan haramcin.[36]
Bugawa
An buga littafin Gina shekarar 1398 Sh (2019 miladiyya, ta hannun Cibiyar Bincike ta Al'adu da Juyin Juya Halin Musulunci, cikin shafuka 560. Wannan littafi shi ne na farko daga jerin darussan fikihu na Ayatullahi Khamna'i da wannan cibiyar ta wallafa.[37]
Maƙaloli Masu Alaƙa
Bayanin kula
- ↑ Behbudi, Sharhe Ismi, Sh 78.
- ↑ «.ir/memory-content?id=5467#602 نگاهی گذرا به زندگینامهی حضرت آیتاللهالعظمی سید علی حسینی خامنهای, Ofishin Kiyayewa da Wallafa Ayyukan Ayatullahi Uzmā Sayyid Ali Khamene'i.
- ↑ Khamna'i , Gina" Moqaddame‑ye Ketab, sh g.
- ↑ Khamna'i , Gina, Moqaddame‑ye Ketab, sh.zad.
- ↑ Khamna'i , Gina, 1398 Sh., Moqaddame‑ye Ketab, sh. ẓ.
- ↑ Khamna'i , Gina, sh 511.
- ↑ «تلاش بینظیر آیتالله خامنهای برای فقه موسیقی/ مفصلترین درس خارج فقه در موضوع غناء»،Kamfanin Labarai na Khabar Online.
- ↑ «تلاش بینظیر آیتالله خامنهای برای فقه موسیقی/ مفصلترین درس خارج فقه در موضوع غناء»،Kamfanin Labarai na Khabar Online.
- ↑ Khamna'i , Gina, shafi 8.
- ↑ Surat Hajj, aya 30...
- ↑ Surat Furqan, aya 72.
- ↑ Surat Luqman, aya 6.
- ↑ Surat Luqman, aya 6.
- ↑ Surat Furqan, aya 72.
- ↑ Khamna'i , Gina, shafi 85.
- ↑ Khamna'i , Gina, 1 shafi 99.
- ↑ Khamna'i , Gina, shafi 110.
- ↑ Khamna'i , Gina shafi 139.
- ↑ Khamna'i , Gina, shafi 155.
- ↑ Khamna'i , Gina, shafi 444.
- ↑ «book.ir/book/%D8%BA%D9%86%D8%A7-%D9%88-%D9%85%D9%88%D8%B3%DB%8C%D9%82%DB%8C غنا و موسیقی»،Shafin Intanet na Wallafe-wallafen Juyin Juya Halin Musulunci.
- ↑ Khamna'i , Gina, shafi 252, shafi 444.
- ↑ Khamna'i , Gina, shafi gh.
- ↑ «book.ir/book/%D8%BA%D9%86%D8%A7-%D9%88-%D9%85%D9%88%D8%B3%DB%8C%D9%82%DB%8C غنا و موسیقی»، Shafin Intanet na Wallafe-wallafen Juyin Juya Halin Musulunci.
- ↑ Khamna'i , Gina, shafi 449–510.
- ↑ Khamna'i , Gina, Moqadde Kitab shafi gh.
- ↑ «book.ir/book/%D8%BA%D9%86%D8%A7-%D9%88-%D9%85%D9%88%D8%B3%DB%8C%D9%82%DB%8C غنا و موسیقی»، Shafin Intanet na Wallafe-wallafen Juyin Juya Halin Musulunci.
- ↑ Khamna'i , Gina, shafi 452.
- ↑ Khamna'i , Gina, shafi 444.
- ↑ Khamna'i , Gina, shafi 337.
- ↑ Khamna'i , Gina, shafi 444.
- ↑ Khamna'i , Gina, shafi 444.
- ↑ Khamna'i , Gina, shafi 444.
- ↑ Khamna'i , Gina, shafi 465.
- ↑ Khamna'i , Gina, shafi 466.
- ↑ Khamna'i , Gina, shafi 525.
- ↑ Khamna'i , Gina, moqadde Kitab
Nassoshi
- «نگاهی گذرا به زندگینامهی حضرت آیتاللهالعظمی سید علی حسینی خامنهای»،, (Kallo a taƙaice kan tarihin rayuwar Ayatullah al‑Uzma Sayyid Ali Husayni Khamna'i .), Ofishin Kula da Kuma Wallafa Ayyukan Ayatullah al‑Uzma Khamna'i , ranar wallafa: 21 Maris 2014, ranar dubawa: 3 Yuni 2021M.
- «تلاش بینظیر آیتالله خامنهای برای فقه موسیقی/ مفصلترین درس خارج فقه در موضوع غناء»،, (Ƙoƙari na musamman na Ayatullah Khamna'i a fikhun kiɗa / Mafi tsawon darasin kharij na fikihu a kan batun Algina'u.), Kamfanin Labarai Khabar Online, ranar wallafa: 23 Yuli 2019, ranar dubawa: 2 Yuni 2021M.
- «غنا و موسیقی»، (Waƙa da Kiɗa) Shafin yanar gizo na Entesharat‑e Enqelab‑e Eslami (Bugu na Juyin Juya Halin Musulunci), ranar dubawa: 6 Janairu 2026M.
- Behbudi, Hedayatullah, Sharhe Ismi: Zendegi nameye Ayatullahi Sayyid Ali Khamna'i (1318–1357), Tehran, Cibiyar Nazari da Binciken Siyasa, shekarar 1391 Hijirar Sh.
- Khamna'i, Sayyid Ali Gina, Tehran,Bugu na farko cibiyar "Juyin Juya Halin Musulunci", shekarar 1398 Sh.