(Pishwaye Sadiƙ (Littafi
| Marubuci | ُSayyid Ali Husaini Khamna'i |
|---|---|
| Tarihin rubutu | 1979M |
| Maudu'i | Rayuwar Al’adu da Siyasa ta Imam Sadiƙ (A.S) |
| Harshe | Farsi |
| Adadin shafuka | 113 |
| Girman littafi | Ƙarami |
| Mai bugawa | Ofishin Buga da Yaɗa Al’adu na Musulunci |
| Wurin da aka buga shi | Tehran |
| Tarihin bugawa | 2004M |
| Bugu | Na farko |
| Yawan bugawa | kwafi 3000 |
Pishwaye Sadiƙ ko Jagora Mai Gaskiya littafi ne da ya ƙunshi jerin jawaban Ayatullahi Sayyid Ali Khamna'i game da rayuwar al'adu da siyasar Imam Sadiƙ (A.S). An gabatar da waɗannan jawaban kafin juyin juya halin Musulunci na Iran, tsakanin 1966 zuwa 1971 miladiyya.
Daga baya kuma, a 1979, an wallafa waɗannan bayanai a matsayin jerin makaloli a cikin jaridar Jamhuriyar Musulunci (Jomhuri‑ye Eslami). Bayan haka, tsakanin 1979 zuwa 1981miladiyya, aka tattara su aka buga su a matsayin littafi.
Babban dalilin rubuta wannan aiki shi ne gyara wasu fahimtohi marasa daidaito game da Imam Jafar Sadiƙ (A.S). Wasu suna zaton cewa Imam ya nisanci harkokin siyasa kuma ya yi sulhu da sarakunan zalunci na zamaninsa. Littafin ya yi ƙoƙarin warware wannan shubuha ta hanyar bayani mai zurfi kan ma'anar Imamanci, manufofinta, da kuma tushen Nazariyar Mutum Mai Shekara 250". Ta haka ne aka bayyana matsayi da ayyukan Imam Sadiƙ (A.S) a tarihin Ahlul‑Baiti.
Maudu'in Littafin
Pishwaye Sadiƙ (Jagora Mai Gaskiya) littafi ne da ke nazarin rayuwar al'adu da siyasar Imam Sadiƙ (A.S) bisa jawaban Sayyid Ali Khamna'i. An ce ɗaya daga cikin dalilan rubuta wannan littafi shi ne gyara fahimtar da wasu mutane suka yi a farkon shekarun juyin juya halin Musulunci game da rayuwar Imami na shida.[1]
A cikin wannan fahimta, ana ganin cewa Imam Sadiƙ (A.S) ya kauce wa gwagwarmayar siyasa kuma ya yi sulhu da sarakunan da suke mulki a zamaninsa.[2] Littafin ya yi ƙoƙarin nuna da hujjojin tarihi cewa wannan fahimta ba daidai ba ce; domin Imam Sadiƙ A.S) bai nisanci siyasa ba kuma bai taɓa yin sulhu da sarakunan zalunci ba.[3]
Babban Ra'ayin Marubucin
Marubucin a cikin littafin Shugaba Mai Gaskiya ya kamanta rayuwar Imaman Shi'a da mutum guda mai shekaru 250, wanda yake zaɓar hanya mafi dacewa domin cimma manufofin Musulunci gwargwadon yanayin zamaninsa.[4]
Daga cikin irin waɗannan hanyoyi akwai: yin shiru, haɗin kai,[5] tsagaita wuta, jihadi,[6] gwagwarmaya a ɓoye, da kuma aikin al’adu da bayani (wayar da kai).[7]
A cikin wannan tsari, Imam Sadiƙ (A.S) ya taka muhimmiyar rawa mai tasiri a tarihin siyasar Ahlul‑Baiti (A.S), kuma ya yi ƙoƙari wajen kafa gwamnatin da Imaman Shi'a suke buri.[8]
A cikin wannan littafi kuma, ta hanyar bayyana manufofin Imamanci da kuma yin bayani kan tushen nazariyar Mutum Mai Shekara 250", an bayyana matsayin Imam Sadiƙ (A.S) da ayyukansa.[9]
Rahoto Kan Abin da Littafin Ya Ƙunsa
A rabin farko na littafin Shugaba Mai Gaskiya, an yi bayani kan falsafar Imamanci bisa ra'ayin Mutum Mai Shekara 250, har zuwa zamanin Imam Baƙir (A.S).[10]
Marubucin a wannan ɓangare na littafin ya gabatar da "hukunci" guda uku game da Imam Sadiƙ (A.S);[11]] ya soki hukunci biyu da, a cewarsa, suka yi fice a tsakanin mutane, sannan ya bayyana hukunci na uku wanda shi ne ra’ayinsa:
- Hukunci mai son kai (Ɓangaranci):
A bisa wannan ra’ayi, Imam Sadiƙ (A.S) ya samu wata dama ta zinariya wajen koyarwa da tarbiyya, sai ya nutse sosai cikin yaɗa ilimi da addini har ya kasa aiwatar da farillar umarni da kyakkyawa da hani daga mummuna. Saboda haka, aka ce ya zama dole ya yabi shugabannin zalunci da danniya. Wannan ra’ayi yana fitowa ne daga wasu da suke kiran kansu masoya Imam.[12]
- Hukunci na masu adawa (Ƙorafi):
A bisa wannan ra’ayi kuwa, Imam Sadiƙ (A.S) a lokacin da zalunci ya cika ko’ina, ya zaɓi hanyar jin daɗi da kariyar kai, ya yi sakaci da nauyin jagoranci na ɗan Adam, ya shagaltu da karatu da koyarwa; alhali mabiyansa (Shi’a) suna fuskantar bin‑diddigi, kurkuku, azabtarwa, kora daga ƙasa, kisa, da ƙwace dukiya.[13]
Matsalolin Waɗannan Fahimtoci Guda Biyu
Marubucin ya bayyana cewa fahimta ta farko ta samo asali ne daga ruwayoyi da aka ƙirƙira, domin idan aka yi nazari a cikinsu za a fahimci cewa ba su dace da darajar Imamanci ba. Matsayin Imamai ya fi tsarki da girma fiye da ya haɗu da yabon azzalumai da Ɗawagitai.[14] Hukunci na biyu ma a cewar marubucin rauni ne kuma ba na ilimi ba, kuma yana kama da hukuncin wasu masu binciken yammacin duniya (Orientalists) waɗanda a mafi yawan lokuta hukuncinsu yana gauraye da son zuciya ko kuma yana fitowa daga jahilci da rashin sani.[15]
Fahimta Ta Uku, Mahangar Marubuci
A fahimtar marubucin, hukunci mafi daidai game da Imam Sadiƙ (A.S) da sauran Imamai (A.S) shi ne cewa Imaman Shi'a, kamar Annabi Muhammad (S.A.W), ba su da wani buri face kafa ko kuma ci gaba da tabbatar da tsarin Musulunci mai adalci da halaye da manufofin da Alƙur’ani ya fayyace; domin Imamanci ci gaba ne na Annabci.[16]
Sannan marubucin ya shiga nazarin rayuwar Imam Sadiƙ (A.S), kuma ya bayyana cewa hanya mafi kyau ta fahimtar rayuwar Imam ita ce a duba ta cikin ginshiƙai uku:[17]
- .Bayyanawa da yaɗa aƙidar Imamanci.[18]
- .Yaɗa da bayyana dokokin addini bisa tsarin fikihun Shi'a, tare da tafsirin Alƙur’ani bisa fahimtar Shi’a.[19]
- .Samuwar wata ɓoyayyiyar ƙungiya ta akida da siyasa (Tsari na sirri da ke aiki a bayan fage).[20]
Tarjama Da Wallafa
Littafin "Pishway‑e Sadiƙ" (Jagora Mai Gaskiya) ya samo asali ne daga jawaban Sayyid Ali Khamna'i da ya gabatar tsakanin 1966 zuwa 1971 (1345–1350 SH) game da rayuwar Imam Sadiƙ (A.S).[21]
Da farko, waɗannan jawaban an wallafa su ne a matsayin jerin rubuce‑rubuce daga bayanan marubucin a cikin jaridar Jamhuriyar Musulunci a Yuni 1979 (Khordad 1358 SH), inda aka buga su a fitowa goma sha bakwai na jaridar.
Bayan haka, tsakanin 1979 zuwa 1981 (1358–1360 SH), an tattara su aka buga su a matsayin littafi da sunan Pishwaye Sadiƙ.[22]
Daga baya an dakatar da bugawar littafin saboda kurakuran buga rubutu (Typin errors).[23] Sai daga baya Cibiyar Juyin Juya Halin Musulunci, ta koma ga asalin bayanan marubucin, ta gyara su, sannan a 2004 (1383 SH) Ofishin Bugawar Al’adun Musulunci ya sake wallafa littafin a cikin shafuka 113.[24] Haka kuma Majalisar Duniya ta Ahlul‑Baiti ta fassara littafin zuwa harsuna uku:Turanci Larabci Sindi.[25]
Maƙaloli Masu Alaƙa
Bayanin kula
- ↑ کتاب پیشوای صادق برداشتهای اشتباه از سیره امام صادق(ع) را تصحیح کرده است, Kamfanin Labarai na Hukuma na Hauza.
- ↑ کتاب پیشوای صادق برداشتهای اشتباه از سیره امام صادق(ع) را تصحیح کرده است, Kamfanin Labarai na Hukuma na Hauza..
- ↑ Khamna'i, Pishwaye Sadiƙ, shekara ta 1383 Shamsi, shafuka 69 zuwa 113.
- ↑ Khamna'i, Pishwaye Sadiƙ, shekara ta, shafuka 11.
- ↑ Khamna'i, Pishwaye Sadiƙ", shafi na 16.
- ↑ Khamna'i, Pishwaye Sadiƙ, shafi na 19.
- ↑ Khamna'i, Pishwaye Sadiƙ, shafi na 19-113.
- ↑ Ku duba: Khamna'i, Pishwaye Sadiƙ, shafuka 72 zuwa 87.
- ↑ Khamna'i, Pishwaye Sadiƙ, shafuka 67 zuwa 113.
- ↑ Khamna'i, Pishwaye Sadiƙ, shafuka 11 zuwa 67.
- ↑ Khamna'i, Pishwaye Sadiƙ, shafi na 1.
- ↑ Khamna'i, Pishwaye Sadiƙ, shafi na 2.
- ↑ Khamna'i, Pishwaye Sadiƙ, shafi na 5.
- ↑ Khamna'i, Pishwaye Sadiƙ, shafi na 8.
- ↑ Khamna'i, Pishwaye Sadiƙ, shafi na 10.
- ↑ Khamna'i, Pishwaye Sadiƙ, shafuka 11 zuwa 13.
- ↑ Khamna'i, Pishwaye Sadiƙ, shafi na 67.
- ↑ Khamna'i, Pishwaye Sadiƙ, shafi na 69.
- ↑ Khamna'i, Pishwaye Sadiƙ, shafi na 88.
- ↑ Khamna'i, Pishwaye Sadiƙ, shafi na 96.
- ↑ سیره فرهنگی و سیاسی «پیشوای صادق (ع)» از زبان امام خامنهای, Kamfanin Labarai na Anā (ANA).
- ↑ معرفی کتاب |کتاب پیشوای صادق تألیف امام خامنهای, Shafin Yaɗa Labarai na Ƙungiyar Mayakan Musulunci."
- ↑ کتاب «پیشوای صادق» در قم معرفی شد, Kamfanin Labarai na Mehr.
- ↑ کتاب «پیشوای صادق» در قم معرفی شد, Kamfanin Labarai na Mehr..
- ↑ Kermani da Roozbeh, Ayin‑e Asar: Karnama‑ye Tarjamar Majmae Jahanī Ahlul‑Bait, shafi na 19.
Nassoshi
- Khamna'i, Sayyid Ali. Pishway‑e Sadiƙ,Tehran: Ofishin Bugawar Al’adun Musulunci, 1383 SH.
- «سیره فرهنگی و سیاسی پیشوای صادق(ع) از زبان امام خامنهای»,(Tsarin rayuwa na Al’adu da Siyasa na Imam Sadiƙ (A.S), daga hangen Imam Khamna'i)،Kamfanin Labarai na ANA, Ranar wallafa labari: 29 Yuni 2019M, Ranar ziyara/duba shafin: 13 Yuni 2021M.
- «کتاب پیشوای صادق برداشتهای اشتباه از سیره امام صادق(ع) را تصحیح کرده است»،(Littafin Shugaba Mai Gaskiya ya gyara fahimta kuskure game da sīrar Imam Ja’far al‑Sadiƙ (A.S)),Hukumar Labarai ta Hukuma ta Hawza.Ranar wallafa: 27 Yuni 2019.Ranar ziyara: 13 Yuni 2021M.
- «کتاب پیشوای صادق در قم معرفی شد»، (An gabatar da littafin Pishwa‑ye Sadiƙ a birnin Qum.), Kamfanin Labarai na Mehr. Ranar wallafa: 27 Yuni 2019. Ranar ziyara: 13 Yuni 2021M..
- Kermani, Abdulkarim da Sayyid Ali Rouzbeh. Ayine Asar: Rahoton Ayyukan Fassara na Majalisar Duniya ta Ahlul‑Baiti. Qum: Majalisar Duniya ta Ahlul‑Baiti, 2022M.
- کتاب پیشوای صادق تألیف امام خامنهای»، (Gabatar da Littafi: Pishwa‑ye Sadiƙ, rubutun Imam Khamna'i), Shafin Bayanan He’at‑e Razmandegan (Ƙungiyar Mujahidan Yaki) Ranar ziyara: 13 Yuni 2021M.