Jump to content

Ahmad Yasin

Daga wikishia
(an turo daga Shaik Ahmad Yasin)
Ahmad Yasin
Shi ne wadan ya kafa Hamas
LaƙabiShaikul mujahidin
Tarihin Haihuwa28 Yuni 1936 miladiyya
Wurin HaihuwaAljura Falasɗinu
Tarihin Shahada22 Maris 2004 miladiyya
Wurin ShahadaGaza
ƘabariShaikul Redwan a tsakiyar garin Gaza
Sunan MataHalima Hassan Yasin
AddiniMuslunci
MazhabaAhlus-Sunna
AikiMalamin addini, ɗan siyasa
KafinAbdul-Aziz Rantisi


Shaik Ahmad Yasin (Larabci: أحمد ياسين) wanda ya rayuwa tsakanin shekaru 1936-2004 hijira ƙamari, ya kasance malamin addini, wanda ya assasa Hamas kuma ɗaya daga cikin fitattun fuskokin gwagwarmaya a Falasɗinu gaban Isra'ila. A shekarar 1987m tare da wasu jama'a masu fafutikar muslunci suka kafa ƙungiyar Hamas, duk da naƙasar a jikinsa, ya taka rawa ta jigo cikin samar da gwagwarmaya a Falasɗinu. A shekarar 2004m ne Isra'ila ta aikata kisan gilla kan Ahmad Yasin, wanda haka ya motsar raddi da martani daga sassan duniya, kuma hakan ya ƙara samar masa da farin jini da nuna shi matsayin wata alama ta dakiya da gwagwarmaya.

Shugaba Kuma Alama Ta Gwagwarmaya

Shaik Ahmad Yasin wanda ya fi shahara da sunan Shaikul mujahidin,[1] Ya yi fice a matsayin fitattun fuskokin gwagwarmaya a Falasɗinu.[2] An ce matsin lamba ta siyasa da zamantakewa kan Falasɗinawa, da kuma kafa gwamnatin Isra'ila da shan kayen da Larabawa suka yi a yaƙoƙin da aka yi a yankin Asiya ta yamma, duka sun yi tasiri kan mahangar tunaninSa.[3]

Yasin ya yi karatun addini a jami'ar Al-Azhar Misra, a wannan lokaci da yake karatu a Misra ne ya fara sanin tunaninnikan Ikhwanul muslimin. Kuma anan ne ya tasirantu da tunaninnikan Ikhwanul muslimin, kuma mutum ne da ya yi imani kan cewa Falasɗinu ƙasa ce ta musulmi da Isra'ila ta mamaye, kuma a kodayaushe yana kan jaddada larurar shugabancin Muslunci kan garuruwan Falasɗinu.[4] Tare da tasiri da karɓuwar Hamas, sai Ahmad Yasin ya zama wani sanannen ɗan adawa da mamaye Falasɗinu.[5]

Sheikh Ahmad Yasin ya bayyana wani hasashe mai ƙarfi a wata hira da aka aka yi da shi, inda ya nuna cewa Isra'ila za ta mutu kafin ƙarshen rubu'i na farko na ƙarni na 21—wato kafin shekarar 202m, kuma ba za ta kai shekarar 2027m ba

Bayan kashe shi da Isra'ila ta yi, sai aka mayar da gidansa matsayin gidan adana kayan tarihi domin tunawa da shi.[6] ShahadarSa ta haifar da guguwar fushi da bore a garuruwan Falasɗinawa; dubunnan mutane ne suka kwarara titunan Gaza tare da jerin gwano da nuna rashin amincewa kan ta'addancin Isra'ila, ƙungiyoyin gwagwarmaya sun ɗauki alwashin ɗaukar fansar kashe shi da Isra'ila ta yi.[7]

Bayan Ahmad Yasin, an zaɓi Abdul-Aziz Rantisi matsayin sabon shugaban ƙungiyar Hamas.[8]

Tarihin Rayuwa

An haifi Ahmad Yasin, a ranar 28 Yuni 1963m, a ƙauyen Aljura da yake ƙarƙashin garin Asƙalan kudancin Falasɗinu wace ta kasance ƙarƙashin kulawar Birtaniya..[9] Bayan mutuwar babanSa, sakamakon yawaitar mutanen da suke da suna Ahmad a cikin dangin Yasin, sai aka dinga amfani da sunan Ahmad Sa'ada kansa, wanda suna ne da ya samo shi daga dangin babarsa, (Assayida Sa'ada Abdullahi Alhabil).[10]

A lokacin ƙuruciyarsa ya yi hatsari wanda ya sabbaba masa naƙasa a hannu da ƙafarsa, sai dai cewa wannan larura ba ta iya kawo cikas gare shi ba kan ci gaba da karatu da ayyuka gwagwarmaya ba, a shekarar 1964m ne ya tafi ƙasar Misra domin ci gaba da karatu a fannin harshen Ingilisi a jami'ar Ainul Shamsi.[11] Tare da faɗuwar Larabawa a yaƙin 1967m, da kuma mamaye Zirin Gaza da Isra'ila, sai ya dagatar da ci gaba da karatu ya dawo Gaza domin kiran mutane zuwa ga ƙalubalantar mamaya da ƙarfafa musu gwiwa.[12]

Ganawar Ayatullahi Khamna'i tare da Ahmad Yasin a lokacin da ya je Iran

A shekarar 1961m ya auri Halima Hassan, kuma Allah ya azurta su da samun ƴaƴan 11, maza uku mata guda takwas.[13]


Tafiya Zuwa Iran

A watan Afrilu 1998m, sakamakon tafiya da Ahmad Yasin ya yi zuwa Iran ya gana da ƙusoshin gwamnatin Iran, daga cikinsu akwai Ayatullahi Khamna'i jagoran juyin juya halin Muslunci na Iran. Har ila yau, ya amsa gayyata Majma Jahani Ahlul-Baiti a birnin ƙum.[14]


Shahada

A ranar 22 Maris 2004m, bayan idar da sallar asubahi a Gaza, Isra'ila ta kai hari kan Shaik Ahmad Yasin, lamarin da ya yi sanadiyyar shahadarSa.[15] Wannan hari kai tsaye ya kasance da umarnin Ariyal Sharon firaministan Isra'ila na lokacin.[16] An binne Ahmad Yasin maƙabartar Shaik Redwan a tsakiyar Gaza.[17]

Wani ɓangare na saƙon ta’aziyya daga Ayatollah Khamenei bayan shahadar Sheikh Ahmad Yasin: Jinin Sheikh Ahmad Yasin zai shayar da bishiyar gwagwarmayar Musulunci kuma zai ƙara tunzura wutar fushin al’ummar Falasɗinu. Zaluncin da ya fuskanta zai ɗaga tutar zaluncin da ake yi wa Falasɗinu. Abin da aka karɓa daga Shaikh Ahmad Yasin da al'ummar Falasɗinu a cikin wannan kisan gilla, jiki ne mai rauni da nakasa. Amma tunaninsa, hanyar da ya tsara, da tafarkin da ya buɗe ba za a iya ƙwacewa daga al'ummar Falasɗinu ba. Ruhin Shaikh yana raye, kuma darasin da ya bayar wanda yanzu ya fi dacewa da tsayawa saboda jinin shahadarsa, zai kasance rera wa da zaburar da matasa da samari da zuriyar Falasɗinu nan gaba.

[18]

Sakamakon shahadar Ahmad Yasin Ayatullahi Khamna'i[19] da Ayatullahi Sistani[20] sun aike da saƙon ta'aziyya, haka nan Sayyid Hassan Nasrullah babban sakataren Hizbullahi Lubnan ya gabatar da jawabi a taron tunawa shahadarSa.[21]

Ayyukan Siyasa

Ahmad Yasin da farin farko ya fara ayyukan siyasa a ƙungiyar Ikhwanul muslimin reshen Falasɗinu, amma har zuwa shekara 1987m bai kasance sananniyar fuska ba.[22] Sai dai kuma tare da fara bore na farko a shekarar 1987m, Ahmad Yasin tare da sauran masu fafutikar Muslunci, sun kafa ƙungiyar Hamas a matsayin reshen Ikhwanul Muslimin a Falasɗinu, ƙarƙashin taken "ƴanto baki ɗayan ƙasar Falasɗinu" sannan shi ne ya ja ragamar shugabancin wannan ƙungiya.[23]

Da farko Isra'ila ba ta nuna damuwa da wannan ƙungiya ba, amma bayan faɗaɗuwar ayyukanta, da ƙarfafuwa. A shekarar 1989m, Isra'ila ta kama Shaik Ahmad Yasin tare da ɗaure shi ɗaurin rai da rai bisa tuhumar kashe Falasɗinawa da suke yi wa Isra'ila aiki leƙen asiri, sai dai kuma a shekarar 1997m a lokacin musayar fursunoni tsakanin Isra'ila da Falasɗnawa ne Shaik Ahmad Yasin ya shaki iskar ƴanci, bayan nan ya zama wata alama ta gwagwarmaya.[24]

Matakai

  • Adawa da ƙudurin sulhu: Ahmad Yasin bai taɓa aminta da sulhu da Isra'ila ba, ya yi imani da cewa baki ɗayan garuruwan Falasɗinu mallakar dukkanin musulmi ne. a shekarar 2003m ya yi suka kan zaman aƙaba da aka shirya domin tattaunawa kan ƙudurin sulhu da Isra'ila..[25]
  • Goyan bayan ofireshin na neman shahada: Ahmad Yasin duk da cewa kai tsaye bai bayyanar da rawar da ya taka ba cikin ayyukan soja, amma mutum ne da ya kasance yana yaɗa ma'anar shahada, kuma yana kiran waɗanda suka shahadantar da kansu ta hanyar ɗaura bom a jikinsu da sunan mujahidai..[26]
  • Hidima ga jama'a: Hamas ƙarƙashin jagorancin Yasin, sun gina makarantu, cibiyoyin kula da lafiya da akwatun taimakon jin ƙai duka kyauta, wanda haka ya ƙara sanyawa ya samu karɓuwa da farin jinni.[27]

Kafa Gidauniyar Ahmad Yasin

Gidauniyar ƙasa da ƙasa ta Ahmad Yasin, wata cibiya ce ta nuna jin ƙai ga raunana da kuma ayyukan al'ada wace aka kafa ta a shekarar 2018m a garin Gaza. A rahotan tashar Aljazira, manufar wannan gidauniya, wanzar ayyuka da tunawa da Ahmad Yasin, haɓɓaka tanade-tanade da kwarewa cikin kare haƙƙoƙin ɗan adam, faɗaɗa ayyukan jin ƙai da kuma yaɗa ma'anonin ƴanci da ƴantaccen mahalli, kamar dai yadda shi Shaik Ahmad Yasin ya sadaukar da rayuwarSa kan waɗannan manufofi.[28]

Bayanin kula

  1. Mazi, Ahmad Yasin Amir al-Shuhada, 1425H, shafi. 11.
  2. شیخ احمد یاسین؛ بنیان‌گذار حماس و سمبل مقاومت،Kamfanin Dillancin Difa Moqaddas.
  3. زندگینامه شیخ احمد یاسین، BBC Farsi
  4. في الذكرى الـ18 لاغتياله.. تعرف على الشيخ أحمد ياسين مؤسس "حماس"، Tashar Aljazira
  5. زندگینامه شیخ احمد یاسین، BBC Farsi
  6. دوازدهمین سالگرد شهادت شیخ احمد یاسین، مؤسس حماس،Anatolyy Agency.
  7. اسرائیل رهبر گروه اسلام‌گرای حماس را ترور کرد، BBC Farsi
  8. رهبر جدید جنبش حماس در غزه اعلام شد، BBC Farsi
  9. خامنه‌ای، توهم سلطه، ۱۳۹۲ش، ص۴۷۹؛ دوازدهمین سالگرد شهادت شیخ احمد یاسین، مؤسس حماس،Anatoly Agency.
  10. Mazi, Ahmad Yasin Amir al-Shuhada, 1425H, shafi. 9
  11. في الذكرى الـ18 لاغتياله.. تعرف على الشيخ أحمد ياسين مؤسس "حماس"، Tashar Aljazira
  12. خامنه‌ای، توهم سلطه، ۱۳۹۲ش، ص۴۷۹؛ زندگینامه شیخ احمد یاسینBBC Farsi
  13. في الذكرى الـ18 لاغتياله.. تعرف على الشيخ أحمد ياسين مؤسس "حماس"، Tashar Aljazira
  14. حضور شیخ احمد یاسین در ایران، Shafin Fardanews.
  15. Khamenei, Tawahhum Sulteh, 2013, shafi. 479.
  16. Mazi, Ahmad Yasin Amir al-Shuhada, 1425H, shafi. 15.
  17. حضور هنیه بر سر مزار شیخ احمد یاسین، Kamfanin dillancin labaran Quds.
  18. Solh Mirzaei, Palestine Az Manzare Ayatullah Khamenei, 2012, Shafi. 373..
  19. پیام تسلیت در پی شهادت شیخ احمد یاسین رهبر جنبش مقاومت فلسطین حماس،Ofishin kiyayewa da buga ayyukan Ayatullah Khamenei.
  20. بيان مكتب سماحة السيد ( دام ظله ) حول اغتيال الشيخ احمد ياسين، Ayatullah Sistani's website..
  21. كلمة السيد نصر الله في تأبين الشيخ أحمد ياسين،Alakar yada labarai a Hizbullah.
  22. زندگینامه شیخ احمد یاسینBBC Farsi.
  23. Rouhani, Ashnayi Ba Kishwarhaye Islami, shafi. 160; Hazrati, Khorshi Dar Saye, 2018, shafi. 281
  24. Ruze Shomare tarikh, 1391, shafi. 1781
  25. زندگینامه شیخ احمد یاسین،BBC Farsi
  26. زندگینامه شیخ احمد یاسین، BBC Farsi
  27. "Ahmad Yasin Al-Sheikh Al-Mujahid Al-Shaheed", shafi. 16
  28. في الذكرى الـ18 لاغتياله.. تعرف على الشيخ أحمد ياسين مؤسس "حماس"،Tashar Aljazira.

Nassoshi

Kamfanin dillancin labaran Anatoly, ranar bugawa: 23/03/2016.