Ziyartar Mara Lafiya

Daga wikishia

Ziyartar mara lafiya, (Larabci عيادة المريض) ko dubiya, tana daga cikin ladubban muslunci da bayani kansu ya zo cikin hadisai, kuma ana ƙidayata cikin mafi falalar kyawawan ayyuka, cikin litattafan riwaya na shi'a an naƙalto hadisai game da ziyartar mara lafiya, haƙiƙa ziyartar mara lafiya ta kasance daga al'adar Annabi (S.A.W) da Imamai, an yi bayaninta cikin riwayoyi cewa tana cikin haƙƙoƙi musulmi kan ɗan'uwansa musulmi wadda wajibi a kiyayeta kan sauran Musulmai, sannan amsa addu'a, rahamar Allah, amfana daga istigfarin mala'iku suna daga cikin ladan da aka ambata kan ziyartar mara lafiya. Wasu ba'ari daga ladubban ziyartar mara lafiya kamar yanda bayani ya zo a hadisai su ne: nuna tausayawa ga mara lafiya, bashi kyauta, tsagaita ganawa da shi da kuma biya masa buƙatar da yake da ita. Kitab Adab Iyadat na Muhammad Baƙir ɗa'ati da Adabul Iyadat Az Mariz, na Muhammad Jawad Nuri da sauran ɗaiɗaikun litattafai suna cikin jumlar ɗaiɗaikun rubutu da aka yi kan wannan maudu'i.

Matsayin Ziyartar Mara Lafiya A Muslunci

Ziyarar dubiya da sayyid Abu Kasim Kashani ga Sayyid Muhammad Taki kuwansari

Ziyartar mara lafiya ko zuwa dubiyar mara lafiya [1] Ana daukar ta a matsayin daya daga cikin al'adun Musulunci [2] kuma daga cikin mafifitan ayyukan addini [3] An ruwaito hadisai da dama game da haka a cikin masadir na shi'a. a wannan maudu'i, [4] sannan wannan al'amari yana da tasiri da kufaifayi tun daga nan gidan duniya da kuma a lahira [5] ga masu zuwa ziyarar duba mara lafiya.[6] Zuwa duba mara lafiya al'ada ce ta Annabin muslunci (S.A.W) [7] da Imamai (A.S), [8] cikin hadisai da aka naƙalto daga Annabi (S.A.W), [9] da Ahlul-Baiti (A.S), [10] an ƙidaya ziyarar dubiya ga mara lafiya cikin haƙƙoƙin musulmi kan ɗan'uwansa musulmi wanda wajibi ne kiyaye su. Haka nan kuma a cikin hadisai an yi umarni da ziyartar wanda bai ziyarci mara lafiya ba a lokacin rashin lafiyarsa [11] da sanar da sauran mutane da ba su da labarin rashin lafiyarsa don su samu ladan ziyartarsa. [12]

Ladan Da Addini Ya Tanada Kan Ziyartar Mara Lafiya

Cikin riwayoyi daga Annabin muslunci (S.A.W) da Imamai (A.S) an yi bayanin kufaifayin na duniya da lahira dangane da ziyarar duba mara lafiya, waɗannan kufaifayi sun kasance kamar haka: amsa addu'a, rahamar Allah, Aljanna, da kuma amfanuwa da istigfarin da Mala'iku suke yi. Cikin littafin Makarimul Al-Akhlaƙ na ɗabarsi, an naƙalto wani hadisi daga Annabin muslunci (S.A.W) cewa duk wanda ya je duba mara lafiya Mumini bawan Allah, zai samu Ubangiji a wurin wannan bawa nasa mara lafiya, idan yana da wata buƙata daga Allah za a biya masa ita, [13] haka nan an naƙalto daga Imam Rida (A.S) duk Muminin da ya ziyarci ɗan'uwansa Mumini mara lafiya, Mala'iku dubu saba'in za su kasance tare da shi, rahama Allah za ta sauka a kansa kuma Mala'iku za su ta nema masa gafara har zuwa duhun dare, idan kuma da daddare ya je ziyarar to za su ta nema masa gafara har zuwa wayewar gari. [14] Kan asasin wata riwaya wacce Shaik Saduƙ wanda ya rasu shekarar 381 h ƙamari, ya naƙalto daga Imam Ali (A.S) idan wani mutum ya ɗaura niyyar ziyartar mara lafiya, sannan ya fito daga gidansa sai Allah ya karɓi ransa a kan hanya kafin zuwa wurin mara lafiyar, lallai Aljanna ta wajaba a kansa. [15]

Bayanin kula

  1. Ibn Manzoor, Lasan Al-Arab, 1414 AH, juzu'i na 3, shafi na 319.
  2. Mahdavi Kenny, Akhlaƙ Amali, 2005, shafi na 199.
  3. Noori, Mostadrak al-Wasail, 1408 AH, juzu'i na 2, shafi na 77.
  4. Faƙih Imani, “Iyadat Bimar”, shafi na 57.
  5. Tabarsi, Makarem al-Akhlaƙ, 1370, shafi na 361-361.
  6. ƙomi, Akhlaƙ wa Adab, 2009, shafi na 376.
  7. ɗabarasi, Makarem Al-Akhlaƙ, 1370, shafi na 19 da 361; Ibn Ash'ath, Al-Jaafriyat (Al-Asha'athyat), Beta, shafi na 159; Ibn Asaker, Tarikh Madina Dimashk, 1415 Hijira, juzu'i na 39, shafi na 114.
  8. Nouri, Mostadrak al-Wasail, 1408 AH, juzu'i na 2, shafi.80; Majlesi, Jala al-Ayoun, Beta, juzu'i na 2, shafi na 460; Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 44, shafi na 189.
  9. Majlesi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 74, shafi na 236; ƙashiri Nishabouri, Sahih Muslim, Bita, juzu'i na 4, shafi na 1704.
  10. Kulaini, Al-Kafi, 1392, juzu'i na 2, shafi na 169.
  11. Ray Shahri, Mizan Al-Hikma, juzu'i na 10, shafi na 500.
  12. Majlesi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 78, shafi na 218.
  13. ɗabarsi, Makarem Al-Akhlaƙ, 1370, shafi na 361-361.
  14. ɗabarsi, Makarem Al-Akhlaƙ, 1370, shafi na-361.
  15. Sheikh Sadouƙ, Man Laihzara al-Faƙih, 1413 AH, Mujalladi na 1, shafi na 140.

Nassoshi

  • Dhahabi, Shams al-Din, Mizan Al-Etidal, Beirut, Dar al-Marafah, 1382.
  • Faiz Kashani, Mohammad Mohsen, Al-Wafi, Isfahan, Library of Imam Amirul Momineen Ali (A.S.), 1406H.
  • Hurrul Amili, Muhammad bin Hassan, Wasa'ill Al-Shia, Tehran, Islamia, 1403H.
  • Ibn Asaker, Ali Ibn Hasan, Tarikh Madinati Damashƙ, Beirut, Darul Fikr, 1415H.
  • Ibn Ash'ath, Muhammad bin Muhammad, Al-Jaafriyat (Al-Asha'athyat), Tehran, Nineva New Library, Beta.
  • Ibn Manzoor, Muhammad Ibn Makram, Larabci, Beirut, Darul Fakr - Dar Sadr, 1414H.
  • Kulaini, Mohammad bin Yaƙub, Al-Kafi, Tehran, Islamia, 1392.
  • Mahdavi Kenny, Mohammad Reza, Practice Ethics, Jamkaran Mosƙue, ƙom, 2005.
  • Majlesi, Mohammad Baƙer, Bihar al-Anwar, Beirut, Al-Wafa, 1403H.
  • Majlesi, Mohammad Baƙer, Jala Al-Ayoun, Tehran, Islamia, Beta.
  • Motaghi Handi, Ali bin Hussam al-Din, Kanz al-Amal, Beirut, Risala, 1401 AH.
  • Noori, Hossein bin Mohammad Taƙi, Mostadrak al-Wasail, ƙum, Al-Bait, 1408H.
  • Nouri, Mohammad Javad wa Digaran, Adab Iyadat Bimar, ƙom, Abedandish, 1395.
  • Sheikh Sadouƙ, Mohammad Bin Ali, Al-Amali, Tehran, Kitabchi, 1376.
  • Sheikh Sadouƙ, Muhammad Bin Ali, Man Lay Hazara Al-Faƙih, ƙum, Islamic Publication, 1413H.
  • Taati, Mohammad Baƙer, Visiting Eƙuette, Hamedan, Barkat Kausar, 2006.
  • Tabarsi, Fazl bin Hasan, Makarem al-Akhlaƙ, ƙom, Al-Sharif al-Razi, 1370.
  • ƙashiri Nishabouri, Muslim bin Hajjaj, Sahih Muslim, Beirut, Dar Ihya al-Tarat al-Arabi, Bita.
  • ƙommi, Sheikh Abbas, Akhlaƙ wa Adaab, ƙom, Nur Mataf, 2009.