Sharhin Littafin Nahajul Balaga

Daga wikishia

Sharhin Nahajul Balaga (Larabci: شرح نهج البلاغة) littafi ne na Ibn Abil Al-Hadid Al-mu'atazili ɗaya daga cikin malaman ahlus-sunna a ƙarni na goma sha bakwai, kuma wannan littafin yana daga cikin mafi muhimmmancin sharhi da aka yi kan Nahjul balaga, daga cikin abubuwan da wannan sharhi ya keɓanta da su akwai anfani da litattafai mabanbanta daga ahlu-sunna da Shi'a, kuma kazalika wannan sharhi yana ɗauke da abin da ya shafi tarihi da adabi da aƙida.

A sharan fagen farkon wannan littafi Ibn Abil Al-Hadid ya anbaci wasu daga cikin ra'ayoyinsa, misali ya yi imani da cewa Imam Ali (A.S) ya fi falala da fifimk daga Halifofi uku, sai dai kawai shi baya ganin cewa akwai nassi (aya ko hadisi) daga Annabi kan Halifancin Imam Ali (A.S), kuma ya yi imani cewa Kawarij da waɗanda suka yaƙe shi a Jamal da sojojin Sham waɗanda suka yi tarayya kan yaƙar Imam Ali (A.S) duk ƴan wuta ne.

Ya zo a cikin wannan littafin Sharhu Nahjul Bala abin da ya dace da aƙidar ƴan shi'a shi ne cewa Imam Ali (A.S) shi ne imami na farko, sabo da haka aka rubuta littafi mai mujalladi ashirin, kuma anbugashi a karo daban-daban xikin zirin mujalladi guda biyu da kuma mujalladi guda huɗu da kuma mujalladi ashirin.

Marubucin Wannan littafi

Tushen Kasida: Ibn Abil Al-hadid

Shi ne Abdul-hamid ɗan Hibatullah wanda aka fi sani da Ibn Abil Hadid an haife shi a shekara ta 586 zuwa 656 hijira[1] a garin Mada'in,[2] kuma ya fara karatu a can kafin daga baya ya koma Bagadaza domin yin karatu gurin malaman zamaninshi.[3] Ibn Abil Al-Hadid ya kasance mabiyin fiƙihun Shafi'i[4] amma a aƙida shi bama'utazile ne,[5] kuma yana da rubuce-rubuce a aƙida da Manɗiƙ, tarihi da kuma waka,[6] daga cikinsu akwai Sharhu Nahjul balaga da kuam ƙasa'id Assaba'a Al'alawiyya, kuma ya sami shahara ne ta sanadiyyar littafin shi na sharhu Nahjul balaga[7] bahasosi da ya yi a Nahjul balaga suna nuna cewa ya mallaki ilimi mai zurfi da faɗi kan abin da ya shafi Adabi da Aƙida da akhlaƙ da tarihin farkon musulinci da kuma wake-waken Larabawa.[8]

Bayani A Dunƙule

Haka nan Ibn Abil Hadid ya yi bayani a karshen littafin Sharhu Nahjul Balaga cewa tsawon lokaci wannan aiki ya dauki shekaru hudu da watanni takwas, kuma ya lissafa shi a matsayin lokacin halifancin Imam Ali (A S).[9] Ibn Abil Hadid ya fara aikinsa ne a ranar farko ga watan Rajab a shekara ta 644, kuma ya kammala shi a karshen Safar a shekara ta 649.[10]

Ibn Abil Hadid ya gabatar da littafin Nahjul Balaga ga wazirin ƴan Shi'a cikin daular Abbasiyawa Ibn Alƙami, kuma ya karbi kyaututa mai tsoka kan wannan aiki.[11]

Abubuwan Da wannan littafi Ya Keɓanta Da Su

An ambaci abubuwan da wannan littafi na Sharhin Nahjul balga na Ibn Abil Hadid ya keɓanta da su sun hada da:

  • Fa'idantuwa da kuma dogara da madogaran Shi'a da ahlus-sunna: A cikin rubuta bayanin Nahjul Balaga Ibn Abi al-Hadid ya amfana da littafan Shi'a da ahlus-unna,[12] misali, ya kawo wasu daga cikin amsoshin Sayyid Murtada martani ga Alkali Abdul Al-Jabbar al-Mu'tazili kan kare Usman bin Affan,[13] An ambaci cewa Ibn Abil Hadid shi ne ke kula da ɗakin karatu a Bagadaza, don haka yana da iyakoki da dama a kan haka, shi ma ɗakin karatun Ibn Alƙami na hannun shi, don haka ya amfana da litattafai wanda ko a hannun Muhammad bin Jarir ɗabari ma ba shi da su wanda yake shi masanin tarihi ne a ƙarni na uku.[14]
  • Faɗaɗuwa: lallai Sharhin Ibn Abil Hadid wani littafi ne wanda ya ƙunshi ilimomin adabi, akida, fiƙihu, ɗabi'a, da tarihin farkon Muslunci, da ilimin al'adu na halayan Larabawa.[15] Wannan da ya tarjama sharhin Nahjul balaga zuwa Farisanci Mahadawi Damagani yana cewa duk da wannan sharhi ya ƙunshi abubuwa daban-daban,sai dai cewa akwai abubuwa guda uku waɗan da sukafi bayyana fiye da sauran ga su kamar haka, Adabi da tarihi sai ilimin zamtakewa da kuma ilimin aƙida,[16] Haka nan wannan littafi ya kunshi tarihin Musulunci tun daga zamanin Manzon Allah (SAW) har zuwa shekara ta 623 bayan hijira, wato shekaru goma sha uku kafin faduwar Bagadaza a hannun Mogul[16] Kimanin rabin littafin an kebence shi ne da bayanai kan yanayin zamantakewa da al'amuran tarihi na rabin farkon karni na farko bayan hijira.[17] marubucin ya yi amfani da kusan baiti dubu tamanin na waƙa a wajan rubuta sharhi Nahjul balaga,[18] kuma Ibnil Hadid ya yi raddi ga wanda ya ce ko kuma yake da ƙorafi kan Saja'i a cikin Nahjul balaga,[19] kuma bai yarda da wanda yake iƙrari cewa wani ba'ari na littafin Nahjul balaga ko kuma duk littafin bana Imam Ali (A.S) bane.[20] Ibn Abil Al-Hadid ya kamanta magangaun Imam Ali (A.S) da wani jiki wanda dukkaninshi bai ɗaya ne babu banbanci a tare da shi.[21]

• Sharhin bakin kalmomi: Ibn Abil Al-Hadid ya fara aikinshi na bayani ne da gabatar da nassin Nahjul balaga karkashin taken Asali (wato asalin nassin kalmomin Imam), sannan ya gabatar da bayani kan asalin nassi ƙarƙashin sharhi,[22] kuma bayan bayani kan nassi sai bayani kan bakin kalmomi masu wahala waɗanda suka zo a cikin nass.[23]

  • Abubuwa da ci gaban da ya faru a zamanin marubucin: kasancewar Ibn Abil Al-hadid ya yi zamani daya tare da Mogul.[24] bisa haka ne ma ya bada rahoto bullowar Mogul da bayyanarsu da yadda suka mamayi garuruwan da suke bayan kogi da Khurasan, da Iraki, da sauran yankuna da yadda suka kai hari kan garin bagadaza.[25] abna lissafa Sharhu Ibn Abil Al-hadid daga cikin mafi muhimmancin sharihi da aka yi kan littafin Nahjul balaga a stawon tarihi.[26]

Tarihin Sayyid Radiyu: A gabatarwar littafin Ibn Abil Al-Hadid ya ambaci nasabar Imam Ali (A.S) da tsatson Assharif radiyu, wanda ya haɗa Nahjul Balagha, sannan kuma ya kawo tarihinsa a takaice.[27]

Ra'ayoyin Marubucin A Cikin Gabatarwar Littafi

Ibn Abil Al-Hadid ya ambata a muƙaddimar littafinshi Sharhu Nahjul Balaga ra'ayoyin Mu'atazila kan imamanci da kuma fifita Imam Ali (A.S) kan sauran sahabbai, da mutanen suka yi mishi bore da tawaye daga Kawarij.[28]

• fifita Imam Ali (A.S) a kan halifofi uku; Ibn Abil Al-Hadid ya ce, ra'ayoyin Mu'utazila dangane da fifikon halifofi sun kasu kashi uku ne, akwai waɗanda suka yi imani da fifita Imam Ali (A.S), wasu da fifikon Abubakar, da kuma wasu daga cikin waɗanda suka kauracewa al'amarin, suka yi shiru game da shi.[29] Ibn Abil Al-Hadid ya yi imani da fifikon Imam Ali (A.S) kan sauran sahabbai, bisa koyi da malaman Mu'utazilawa a garin Bagadaza, sabo da ladan shi ya fi na kowa yawa kuma ya tarin siffofi nagari wanda sun fi nakowa,[30] amma duk haka Ibn Abil Al-Hadid ya yi imani cewa babu nassi karara daga Annabi (S.A.W) wanda yake nuna cewa Imam Ali(A.S) shi ne halifa bayan manzon Alla (S.A.W)[31]

As'habul Jamal [waɗan da suka yaƙi Imam Ali (A.S)] suna wuta: Ibn Abil Al-Hadid ya yi imani da cewa dukkan ma'abota rakumin suna wuta, in ban da A'isha da ɗalha, da Zubairudomin su sun rigaya sun tuba,[32] kamar yadda sojojin Sham a lokacin yaƙin Siffin da Kawarij duk suma ƴan wuta ne, sabo da dogewarsu kan zalinci.[33]

• Ra'ayin Imam Ali (A.S) shi ne mafi dacewar ra'ayi kuma mafi ingancin mataki: Ibn Abil Al-Hadid ya yi imani da cewa Imam Ali (A.S) ya yiwa Umar bin Khaɗɗab nasiha a lokacin da ya je wurin Rumawa da Iraniyawa[34] sannan kuma ya nuna wa Usman al'amura da ace ya yi aiki da shi, da abin da faru da bai faru ba, da shi ne abin da yafi alheri gare shi.[35]

• lazimtar Imam Ali (A.S) a kan Shari'a: Ibn Abil Hadid ya yi imani da cewa Imam Ali (A.S) ya yi aiki da Shari'a, kuma bai yi aiki da sabanin haka ba, amma sauran halifofi sun yi aiki da maslaharsu, ko sun dace da shari'a ko akasin haka, ya yi imani da cewa duk wanda ya yi aiki tuƙuru da himma, kuma baya bin wasu sharuɗɗa da za su nesanta mutum daga abin da yake dai-dai, yanayin rayuwarsa a duniya zai kasance mai kyauy.[36]

Littattafai

Akwai litattafai da aka rubuta kulasar littafin Sharhu Nahjul Balaga kuma an tarjama shi zuwa yare daban-daban da kuma raddi kanshi, kuma Rida Ustadi ya ƙirga rubuce-rubuce da aka yi kan littafin sharhu Nahjul Balaga inda ya ambace cewa sun kai guda ashirin kafin tarjama da ta'aliƙi da raddi.[37]

Raddi

Haƙiƙa wasu daga cikin malaman shi'a sun rubuta raddodi kan sharhu Nahjul balaga na Ibn Abil Al-Hadid, kuma sun saɓawa da yawa daga cikin abin da Ya zo a cikin shi, sabo da abin da Ya zo a cikinshi ya saɓawa aƙidar shi'a musamman ma abin da ya shafi imamanci da wasu abubuwa da suka faru a tarihi,[38] daga cikin waɗannan raddodi akwai : Salasilil Hadid litaƙyidil Ibn Abil Al-Hadid na Shaik Yusuf Al-baharani wanda ya rasu a shekara ta 1186 hijira wanda ya yi dai-dai da 1772 miladiya,[39] da arruhul fi Naƙadi ma abramahu Ibn Abil Al-Hadid na Ahmad ɗan ɗawos Alhilli wanda ya yi wafati a shekara ta 673 hijira wanda ya yi daidai da 1274 miladiya, sai wani littafin mai suna Arradi ala Ibn Abil Al-Hadid na Ali ɗan Hasan Al-biladi Albahrani wanda ya rasu a shekara ta 1340 hajirar manzon Allah wanda ya yi daidai da 1922 miladiyya, sai Assalasil fir raddi ala Ibn Abil Al-Hadid na Shaik Yusuf Al-kufi, da kuma Annaƙadid Assadid lisharhil Kuɗuba Ashshakshaƙiyya na Ibn Abil Al-Hadid.[40]

Tarjamomi Da Sharhi Nahjul Balaga

An tarjama Sharhu Nahjul balaga zuwa yaran Farisanci ga wasu daga ciki: tarjamatu mulla Shamsud-din ɗan Muhamamad ɗan Murad ya rasu a shekara ta 1013 hijirar Annabi (S.A.W) tare da Nasarullah ɗan Fatahulla addisfuli,[41] da Majmu'itul Jalowe Tariƙ dar Sharhi Nahjulbala na Ibn Abil Al-Hadid wanda yake da Hamishi na Muhammad Mahdi Addamagani mujalladi takwas, da kuma tarjamar Gula Rida liyaƙi mujalladi ashirin 20, kamar yake akwai wannan littafi mai suna Muƙtaba min Nahjul Balaga wanda yake ɗauke da sunan Imam Ali (A.S) a mahangar Ibn Abil Al-Hadid Almu'atazili [wanda shi bayani ne kan Imam Ali (A.S) a mahangar Ibn Abil Al-Hadid Almu'tazili] na Husaini ɗayyibiyan.[42]

Kulasosin Nahjul Balaga

Anyi kulasar littafin Sharhu Nahjul balaga da suna daban-daban:

  • Al'aƙadu An-nadid wanda aka fitar daga littafin Sharh na Ibn Abil Al-Hadid na Fakarurdin Abdullahi Almu'ayyid Billah.[43]
  • Daga cikin waanda ya yi kulasa akwai Sulɗak Mahmud Aɗɗabasi, da kuma kulasa na Shaik Muhammad ƙanbar Ali Alkazumi mai suna Al'iltiƙaɗu Durar Almuntakab.[44]

Ahmad Arrabi'i ya yi magana kan litattafan da Ibn Abil Al-Hadid ya dogara da su a lokacin da ya rubuta littafin shi kuma ya kira littafin shi da suna Alziƙu Annadid Bimasadir Ibn Abil Al-Hadid fi sharhi Nahjul Balaga,[45] a cikin shi marubucin ya ambaci litattafai ɗari biyu da ashirin da biyu waɗanda Ibn Abil Al-Hadid ya yi amfani da su yayin rubuta littafin Sharhi Nahajul balaga.[46]

Buga littafin Sharhi Nahjul Balaga

Littafin Sharhu Nahjul Balaga mujalladi ashirin ne,[47] kuma an buga shi karo daban-daban daga ciki akwai mujalladi biyu da mujalladi huɗu da kuma mujalladi ashirin,[48] kuma wannan littafi ya fito a shekara ta 1270 da 1302 zuwa 1304 hijirar manzon Allah (S.A.W) a Tehran, kuma an buga shi a Alƙahira 1329 hijirar manzon Allah (S.A.W) kazalika an buga shi a shekara ta 1378 hijirar manzon Allah (S.A.W).[49]

A ɗakin karatu na Imam Rida (A.S) akwai wannan littafi na Sharhu Ibn Abil Hadid,[50] kuma daga dukkan alamu an yi amfani da shi tun lokacin da Ibn Abil Al-Hadid ya kasance a raye.[51]

Kuma daga cikin bugu da aka yi na littafin Sharhu Nahjul Balaga akwai wanda Muhammad Abul Fadli Ibrahim ya gyara bisa tsarin da Ibn Abil Al-Hadid ya tsara a cikin mujalladi na ashirin wanda ya ƙunshi shafi dubu shida da ɗari huɗu da sittin.[52] kazalika akwai wanda Abdul-karim Annari ya gyara mai ɗauke da mujalladi sha ɗaya wanda aka buga shi a Darul kutubil Ilmiyya a Berut..</ref> وهناك تصحيح لعبدالكريم النمري في 11 مجلدا صدر عن دار الكتب العلمية في بيروت.[53]

Bayanin kula

  1. Ibn al-Futi, Majma’ al-Adab fi Mu’jam al-Alqab, 1374 AH, juzu’i na 1, shafi na 214.
  2. Ibn Kathir, Al-Bidaya Wal-Nihaya, 1407 Hijira, Juzu'i na 13, shafi na 199.
  3. Mahdavi Damghani, Jalwa Tarikh Dar Sharh Nahj al-Balagha, 1379 AH, fassarar gabatarwa, shafi.
  4. Ibn Khalqan, Wafyat Al-A'yan, 1994, juzu'i na 7, shafi na 342
  5. Fikrat, “Ibn Abi al-Hadid”, shafi na 642-641.
  6. Ibn Khalkan, Wafaytat Al'ayan, 1994, juzu'i na 7, shafi na 342.
  7. Fikret, “Ibn Abi Al-Hadid”, shafi na 641-642.
  8. Mahdavi Damghani, Jalwa Tarikh dar Sharh Nahj al-Balagha, 1379 AH, fassarar gabatarwa, shafi na Dawazdeh.
  9. Ibn Abi Al-Hadid, Sharh Nahj Al-Balagha, 1404H, juzu'i na 20, shafi na 349.
  10. Ibn Abi Al-Hadid, Sharh Nahj Al-Balagha, 1404H, juzu'i na 20, shafi na 349.
  11. Hindushah, Tajarubul Salaf dar Tawarikh Khulafa wa wuzra Ishan, 1357H, shafi na 349.
  12. Mahdavi Damghani, Jalwa Tarikh dar Sharh Nahj al-Balagha, 1379 AH, fassarar gabatarwa, shafi.
  13. Subhaniniya, “ Sharhin Nahj al-Balagha Ibn Abi al-Hadid,” shafi na 59.
  14. Mahdavi Damghani, Jalwa Tarikh dar Sharh Nahj al-Balagha, 1379 AH, fassarar gabatarwa, shafi.
  15. Mahdavi Damghani, Jalwa Tarikh dar Sharh Nahj al-Balagha, 1379 AH, fassarar gabatarwa, shafi.
  16. Mahdavi Damghani, Jalwa Tarikh dar Sharh Nahj al-Balagha, 1379 AH, fassarar gabatarwa, shafi. 14
  17. Mahdavi Damghani, Jalwa Tarikh dar Sharh Nahj al-Balagha, 1379 AH, fassarar gabatarwa, shafi. 14
  18. Mahdavi Damghani, Jalwa Tarikh dar Sharh Nahj al-Balagha, 1379 AH, fassarar gabatarwa, shafi na 18
  19. Ibn Abi Al-Hadid, Sharh Nahj Al-Balagha, 1404 AH, juzu'i na 1, shafi na 126-130
  20. Ibn Abi Al-Hadid, Sharh Nahj Al-Balagha, 1404 AH, juzu'i na 10, shafi na 128 da 129.
  21. Ibn Abi Al-Hadid, Sharh Nahj Al-Balagha, 1404 AH, juzu'i na 10, shafi na 128 da 129.
  22. Ibn Abi Al-Hadid, Sharh Nahj Al-Balagha, 1404 AH, juzu'i na 1, shafi na 57-58.
  23. Hosseini, Masadir Nahj al-Balagha, 1409 AH, juzu'i na 1, shafi na 234.
  24. Hosseini, Masadir Nahj al-Balagha, 1409 AH, juzu'i na 1, shafi na 234.
  25. Ibn Abi Al-Hadid, Sharh Nahj Al-Balagha, 1404 AH, juzu'i na 8, shafi na 219-243.
  26. Fikret, “Ibn Abi Al-Hadid,” shafi na 641.
  27. Ibn Abi Al-Hadid, Sharh Nahj Al-Balagha, 1404 AH, juzu'i na 1, shafi na 11-42
  28. Ibn Abi Al-Hadid, Sharh Nahj Al-Balagha, 1404 AH, juzu'i na 1, shafi na 6-11.
  29. Ibn Abi Al-Hadid, Sharh Nahj Al-Balagha, 1404 AH, juzu'i na 1, shafi na 7-8.
  30. Ibn Abi Al-Hadid, Sharh Nahj Al-Balagha, 1404 AH, juzu'i na 1, shafi na 9.
  31. Ibn Abi Al-Hadid, Sharh Nahj Al-Balagha, 1404 AH, juzu'i na 2, shafi na 59.
  32. Ibn Abi Al-Hadid, Sharh Nahj Al-Balagha, 1404 AH, juzu'i na 1, shafi na 9
  33. Ibn Abi Al-Hadid, Sharh Nahj Al-Balagha, 1404 AH, juzu'i na 1, shafi na 9
  34. Ibn Abi Al-Hadid, Sharh Nahj Al-Balagha, 1404 AH, juzu'i na 1, shafi na 28.
  35. Ibn Abi Al-Hadid, Sharh Nahj Al-Balagha, 1404 AH, juzu'i na 1, shafi na 28.
  36. Ibn Abi Al-Hadid, Sharh Nahj Al-Balagha, 1404 AH, juzu'i na 1, shafi na 28.
  37. Malamina, Kitabnameh Nahj al-Balagha, 1359 AH, shafi na 37-39.
  38. A cikin ra'ayin Namouna Ibn Abi Al-Hadid, Sharh Nahj Al-Balagha, juzu'i na 2, shafi na 59.
  39. Agha Buzurg al-Tehrani, Al-Dhari’ah, 1408 BC, juzu’i na 12, shafi na 210.
  40. Al-Husseini, Masadir Nahj al-Balagha, 1409 AH, juzu'i na 1, shafi na 237-238; Nazari, Kitabname Nahj al-Balagha, 1359 AH, shafi 37-39.
  41. Al-Husseini, Masadir Nahj al-Balagha, 1409 AH, juzu'i na 1, shafi na 238.
  42. «امام علی علیه‌السلام از دیدگاه ابن‌ابی‌الحدید معتزلی/ نگارنده حسین طیبیان.»
  43. Al-Husseini, Masadir Nahj al-Balagha, 1409 AH, juzu'i na 1, shafi na 238.
  44. Al-Husseini, Masadir Nahj al-Balagha, 1409 AH, juzu'i na 1, shafi na 238.
  45. Rabi’i, Al-Udziq al-Nazid bi masadir Ibn Abi al-Hadid Sharhu Nahj al-Balaghah, gabatarwar, 1407H, shafi na 5-6.
  46. Sobhaninia, “Sharhu Nahj al-Balagha Ibn Abi al-Hadid”, shafi na 59
  47. Ibn Kathir, Al-bidaya wa AN-nihaya, 1407 BC, juzu'i na 13, shafi na 199.
  48. Malamina, Kitabname Nahj al-Balagha, 1359 AH, shafi na 37
  49. Fikret, “Ibn Abi Al-Hadid,” shafi na 642.
  50. Astan Quds, Fihrist, juzu'i na 5, shafi na 112-113: I Fikret ne ya ruwaito shi, "Ibn Abi Al-Hadid", shafi na 642.
  51. Fikret, “Ibn Abi Al-Hadid,” shafi na 642.
  52. Mahdavi Damghani, Jalwa Tarikh dar Sharh Nahj al-Balagha, 1379 AH, fassarar gabatarwa, shafi.
  53. «شرح نهج البلاغة 1-11 مع الفهارس »

Nassoshi

  • Hindushah bin Sanjar, Kwarewar Magabata, na Kushsh Abbas Iqbal Ashtiani, Tehran, 1357H.
  • Ibn al-Futi, Abd al-Razzaq bin Ahmad, Majma'ul Adab fi mujam Al-kab,, edited by: Muhammad al-Kadhim, Tehran, Zarat Farhang da Irshad Islami, 1435 BC/1374 AH.
  • Agha Buzurg Al-Tehrani, Muhammad Mohsen, Al-Dhari’a ila Shi’a Classifications, Qom and Tehran, Ismailian Islamic Library, 1408 AH.
  • Husseini, Abd al-Zahra, Masadir Nahj al-Balagha wa Asanadihu, Beirut, Darul-Zahra, 1409 AH/1988 miladiyya.
  • Ibn Abi al-Hadid, Abdul Hamid, Sharh Nahj al-Balagha, bugun: Muhammad Abu al-Fadl Ibrahim, Kum, Ayatullah Marashi Najafi, 1404H.
  • Ibn Kathir al-Dimashqi, Ismail bin Omar, Al-bidaya wal An-nihaya, Beirut, Darul Fikr, 1407H/1986 Miladiyya.
  • Ibn Khalkan, Shams al-Din Ahmad bin Muhammad, Wafyat A'yan wa Anba'u Az-zaman, wanda: Ihsan Abbas, Beirut, Dar Sader, 1994 miladiyya ya buga.
  • Mahdavi Damghani, Mahmoud, Jalwa Tarikh dar Sharh Nahj al-Balagha, Tehran, bugun, 1379 AH.
  • Malam na, Reza, Kitabnameh Nahj al-Balagha, Tehran, Bonyad Nahj al-Balagha, 1359 Sh.
  • Rabi’i, Ahmad, Al-Al-uzeheeq Al-Nadhid Bimasadir Ibn Abi Al-Hadid a Sharh Nahj Al-Balagha, Baghdad, Abdulmajeed Hussein Al-Rubai, 1407 Hijira.
  • Subhaniyya, Muhammad Taqi, "Shafi Nahj al-Balagha Ibn Abi al-Hadid," Dofsnamah Hadith Andishah, Shamarah 6, Bayez and Zamistan 1387 AH.
  • «امام علي عليه‌السلام از ديدگاه ابن‌ابي‌الحديد معتزلي/ نگارنده حسين طيبيان.»، سازمان اسناد وکتابخانه ايران، مشاهده 30 دي 1398 ش.
  • فكرت، محمدآصف، ابن أبي الحديد، دائرة المعارف الإسلامية الكبرى، ج2، طهران، مرکز دائرة المعارف الإسلامية الكبرى، 1374 ش.