Hadis Rayyan Ɗan Shabib
Hadis Rayyan Ɗan Shabib, (Larabci: حديث ريان بن شبيب) wani hadisi ne da Rayyan ya naƙalto daga Imam Rida (A.S) game da watan muharram, da kuma da makoki domin Imam Husaini (A.S). Cikin wannan an yi magana game da ayyukan farkon watan muharram, karya alfarmar watan muharram ta hanyar kashe Imam Husaini (A.S) cikin wannan wata, da kuma wasicci da yin kuka domin Imam Husaini da ziyararsa, tare da tsinewa makasansa da yin farin ciki da farin cikin Ahlul-baiti (A.S) da kuma yin baƙin ciki domin baƙin cikinsu tare da karɓar wilayarasu.
A cikin wata gaɓa daga hadisin, Imam Rida (A.S) ya umarci Rayyan idan har yana son yin kuka kan wani abu, to ya yi kuka domin Husaini (A.S) lallai an yanka shi kama yadda ake yanka Rago, cikin wannan hadisi an yi bayani da cewa ladan kuka domin Husaini (A.S) ziyararsa shi ne za a gafarta zunubai.
Wannan riwaya ta zo cikin littafin Uyunu Akhbar Al-rida (A.S) da Al-amali Shaik Saduƙ da sauran litattafai misalin Al-Iƙbal, Wasa'ilul Al-shi'a da Biharul Al-anwar da suka naƙalto daga litattafai biyun farko.
Malaman shi'a misalin Muhammad Taƙiyyu Majlisi, Sahibul Hada'iƙ da Sayyid Muhammad Sa'id Hakim da Husaini Wahid Khurasani sun tabbatar da ingancin wannan riwaya.
Matsayin Wannan Hadisi Cikin Adabin Ashura
Imam Rida (A.S):
يَا ابْنَ شَبِيبٍ إِنْ كُنْتَ بَاكِياً لِشَيْءٍ فَابْكِ لِلْحُسَيْنِ بْنِ عَلِيِّ بْنِ أَبِي طَالِبٍ فَإِنَّهُ ذُبِحَ كَمَا يُذْبَحُ الْكَبْشُ. Ya dan gidan Shabib! idan kana yi wa wani abu kuka to ka yi kuka domin Husaini bin Abi Talib Lallai an yanka shi kamar yadda ake yanka rago.
Hadisin Rayyan Ɗan Shabib yana daga mafi shaharar hadisai da aka sani game da makoki.[1] hadisi ne da yake magana kan watan muharram, waƙi'ar karbala, ladan kuka domin Husaini Ɗan Abu ɗalib, mafi yawan lokuta masu huɗuba da mawaƙa suna ishara da wannan hadisi kan muhimmancin kuka domin Imam Husaini (A.S), suna karanto wasu ɓangarori daga cikin wannan hadisi. Haka nan ana amfani da gaɓoɓin wannan hadisi a yi rubutun zanensu kan kyallaye da banoni da suke da alaƙa da makokin watan muharram.[akwai buƙatar kawo madogara] haka kuma an rubuta baituka da rera su daga gaɓoɓin wannan hadisi.
Cikin ko wane makoki mai karya zuciya ka yi kuka domin Husaini Cikin ko wace irin musiba da jarrabawa ka yi kuka domin Husaini Gabanin fara ko wace magana ka fara da kuka domin Husaini Cikin tantinunan juyayi da baƙin cikin Ahlul-baiti Cikin makarantar nuna soyayya ta Ibn Shabib tare da kururuwa da Abal Hassan ka yi kuka domin Husaini Idan har ka kasance mai kuka ga wata musiba kamar dai misalin Annabawa cikin ibtila da baƙin ciki ka yi kuka domin Husaini.[2] Ya Ɗan Shabin ka yi kuka daga baƙuntar Husaini A filin karbala an keta alfarmar Husaini Ya Ɗan Shabib an caka tsinin mashi cikin maƙogaro An yanke wuyansa kamar Rago.[3]
Hadisin Rayyan yana sanya fata ga masu Imani da wilayar Ahlul-baiti (A.S) da nuna luɗufi da tausayin Allah dangane ga ƴan shi'a da masu Ahlul-baiti (A.S) sakamakon gwaggwaɓan lada da yake basu daga bisa ƴar ƙaramar ibada da suka yi.[4]
Abin da Yake Cikin Hadisin
Batutuwan da aka bijiro da su cikin hadisin Rayyan Ɗan Shabib[5] su ne kamar haka:
- Ayyuka farkon watan muharram: cikin wannan hadisi an yi ishara game da yin azumi a farkon wanna wata, amsa addu'a a rana kamar misalin amsa addu'ar Zakariyya (A.S)[Tsokaci 1] a cikin wannan rana.[6] Sayyid Ibn ɗawus tare da jingina da wannan riwaya da wasu riwayoyin daban, ya lissafa azumi cikin ayyauka farkon muharram, wannan rana yana ganin ta matsayin ranakun da ake amsa addu'a.[7]
- Keta alfarmar watan muharram: cikin wannan hadisi ya zo cewa ba a kiyaye alfarmar Annabi ba, an kashe masa zuriya, an fursunanta da mata, daidai lokaci da ko a zamanin jahiliyya sun kasance suna kiyaye alfarma watan muharram, basa aikata zalunci ko yaƙi cikin wannan wata na muharram.[8]
- Umarni da yin kuka domin Husaini (A.S): cikin wata gaɓa daga wannan hadisi a maganar da Imam yake yi zuwa ga Rayyan Ɗan Shabib ya zo cewa yana ce masa ya Ɗan Shabib idan ka yi niyyar kuka kan wani abu, to ka yi kuka domin Husaini haƙiƙa sun yanka shi kamar yadda ake yanka Rago, haka nan an ce halittun sama da na ƙasa sun yi kuka kan shahadar Imam Husaini (A.S) sama ta yi ruwan jini da jar ƙasa.[9]
- Falalar kuka kan Imam Husaini (A.S): cikin wannan hadisi an ambaci gafarta dukkanin zunubai, ladan kuka da zubar da hawaye kan Husaini (A.S).[10]
- Wasicci da zuwa ziyarar Imam Husaini (A.S): Imam Rida (A.S) ya umarci Rayyan idan har yana son haɗuwa da Allah yana tsarkake ba tare da zunubi ba to ya je ziyarar Imam Husaini (A.S).[11]
Imam Rida (A.S):
يَا ابْنَ شَبِيبٍ إِنْ سَرَّكَ أَنْ يَكُونَ لَكَ مِنَ الثَّوَابِ مِثْلَ مَا لِمَنِ اسْتُشْهِدَ مَعَ الْحُسَيْنِ بْنِ عَلِيٍّ فَقُلْ مَتَى ذَكَرْتَهُ يا لَيْتَنِي كُنْتُ مَعَهُمْ فَأَفُوزَ فَوْزاً عَظِيماً Ya dan gida Shabib! idan ya faranta maka ace ka samu lada mislain wand aya yi shahada tare da Husaini bin Ali, to duk sand aka tuna da shi ina ma ace na kasance tare da shi na rabauta babbar rabauta.
'
- Tsinewa makasan Imam Husaini (A.S): cikin hadisi ya zo cewa ya kai Ɗan Shabib ! idan har kana so ka kasance tare da Annabi a gidan aljanna, to katsinewa makasan Husaini (A.S).[12]
- Taimakon mala'iku dubu huɗu: kan asasin wannan hadisi, mala'iku dubu huɗu ne suka sauka ƙasa domin taimakawa Imam Husaini sai dai cewa ba a basu izinin shiga yaƙin su taimaka masa ba, bayan haka sai suka shiga matsanancin damuwa da baƙin ciki, waɗannan mala'iku suna nan zaune kusa da ƙabarin Imam Husaini (A.S) sun yi buɗu-buɗu da ƙasa har zuwa miƙewar Imam Mahadi (A.F) suna ta ɗaga murya suna faɗin ya lasaratul Husaini za su kasance cikin mataimakan Imam Mahadi (A.S).[13]
- Umarni da yin farin ciki da farin cikin Ahlul-baiti (A.S) da kuma yin baƙin ciki domin baƙin cikinsu: cikin gaɓoɓin wannan hadisi na ƙarshe an naƙalto cewa ya kai Ɗan Shabib ! idan ka kasance kana samun maɗaukakan darajoji cikin aljanna ka kuma tare da Ahlul-baiti, to ka yi baƙin ciki da baƙin cikin da muke yi mu Ahlul-baiti, haka ka yi murna da farin ciki da muke yi mu Ahlul-baiti, kuma ka karɓi wilayarmu; saboda a ranar ƙiyama ana tashin mutum da wanda yake so a gidan duniya.[14]
Madogarai Da Kuma Inganci
Shaik Saduƙ cikin littafin Uyunu Akhbar Al-rida(A.S)[15] da Al-amali.[16] ya naƙalto wannan hadisi daga Muhammad Ɗan Majilawaihi daga Ali Ɗan Ibrahim ƙummi daga babansa Ibrahim Ɗan Hashim daga Rayyan Ɗan Shabib daga Imam Rida (A.S). sauran litattafai misalin Al-iƙbal na Sayyid Ibn Ɗawus,[17] da Wasa'ilul Al-shi'a na Hurru Amili.[18] Biharul Al-anwar na Allama Majlisi[19] da Awalimul Al-ulumi Wal Al-ma'arif na Abdullahi Baharani Isfahani (Wafati: 148. ƙamari)[20] sun naƙalto wannan hadisi daga littafin Uyun da Al-amali.
Muhammad Taƙiyyu Majlisi[21] ya tabbatar da ingancin wannan riwaya da matsayin hadisi da yake kan matakin "Hadis Hasanun" kuma malamai misalin Sahibul Hada'iƙ da Sayyid Muhammad Sa'id Hakim su ma sun tabbatar da kasancewarsa hadis sahihun.[22] sanadin wannan riwaya a cikin littafin Mausu'atu Ahlul-baiti ya samu matsayin inganci.[23] Husaini Wahid Khurasani[24] da wasu ba'arin masu dandaƙe bincike,[25] suna tafi kan kasancewar marawaitan wannan hadisi matsayin siƙatu (Amintattu) kuma ƴan imamiyya, da wannan dalili ne suka lissafa wannan hadisi matsayin ingantaccen hadisi. Daga sauran dalilin ingancin wannan hadisi akwai kasancewar an same shi cikin littafin Al-nawadir na Ibrahim Ɗan Hashim.[26]
Nazari
- Littafin "Fabki Lil Husaini: Ɗan gajeran bahasi daga wasiyyoyin Imam Rida (A.S) zuwa ga Rayyana Ɗan Shabib" na Sayyid Muhammad Baƙir Hashimi Shaharudi, kamfanin Intisharat Bunyad Fiƙihi Wa Ma'arif Ahlul-baiti (A.S) a shekarar 2018 suka buga shi.
- Littafin "Parishan Muye Wa Khak Alude" na Muhammad Ali Fata Zade, sharhi ne kan riwayar Rayyan Ɗan Shabib wanda kamfanin Kitabistane Marifat suka fitar da shi.
Bayanin Kula
- ↑ Imrani, "Barsi Sanadhi wa Delayli Hadith Rayan bin Shabib Piramun Azadari," shafi na 95.
- ↑ «فابکِ لِلحُسَین»، وبگاه شعر هیأت.
- ↑ «ترکیب بند یابن شبیب. جلوه اول/یابن الشبیب گریه کن از غربت حسین»، وبگاه امام هشت.
- ↑ Mirjahani Tabatabaei, al-Buka Lil Hussein, shafi na 72
- ↑ نگاه کنید به: «بیان جامع امام رضا(ع) در گرامیداشت ایام محرم، عزاداری، ثواب گریه بر امام حسین(ع)»، وبگاه مؤسسه تحقیقاتی حضرت ولیعصر.
- ↑ Sayyid Ibn Tavus, Iqbal al-Amal, 1409H, juzu'i na 2, shafi na 553.
- ↑ Sayyid Ibn Tavus, Iqbal al-Amal, 1409H, juzu'i na 2, shafi na 553.
- ↑ Sheikh Sadouq, Ayoun Akhbar al-Reza, 1378 AH, juzu'i na 1, shafi na 299.
- ↑ Sheikh Sadouq, Ayoun Akhbar al-Reza, Amincin Allah ya tabbata a gare shi, 1378 AH, juzu'i na 1, shafi na 299-300.
- ↑ Sheikh Sadouq, Ayoun Akhbar al-Reza, 1378 AH, juzu'i na 1, shafi na 300.
- ↑ Sheikh Sadouq, Ayoun Akhbar al-Reza, 1378 AH, juzu'i na 1, shafi na 300.
- ↑ Sheikh Sadouq, Ayoun Akhbar al-Reza, 1378 AH, juzu'i na 1, shafi na 300.
- ↑ Sheikh Sadouq, Ayoun Akhbar al-Reza, 1378 AH, juzu'i na 1, shafi na 299.
- ↑ Sheikh Sadouq, Ayoun Akhbar al-Reza, 1378 AH, juzu'i na 1, shafi na 300.
- ↑ Sheikh Sadouq, Ayoun Akhbar al-Reza, amincin Allah ya tabbata a gare shi, 1378 AH, juzu'i na 1, shafi na 299 da 300.
- ↑ Sheikh Sadouq, Al-Amali, 1376, shafi na 129 da 130.
- ↑ Sayyid Ibn Tavus, Iqbal al-Amal, 1409H, juzu'i na 2, shafi na 545.
- ↑ Har Aamili, Al-Shia Tools, 1409 AH, juzu'i na 10, shafi 469, juzu'i na 14, shafi na 502.
- ↑ Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 44, shafi na 285 da juzu'i na 98, shafi na 102.
- ↑ Bahrani Esfahani, Awalam Uloom wa Maarif, 1413 AH, Juzu’i na 17, shafi 538.
- ↑ Majlisi, Al-Mutaqiin, 1406 Hijira, juzu'i na 5, shafi na 383. ↑
- ↑ Bahrani, al-Hadaeq al-Nadrah, 1405 AH, juzu'i na 13, shafi na 376; Hakim, Misbah al-Manhaj, 1425 AH, shafi na 406.
- ↑ Najafi, Maussu'atu Hadiths na Ahlul Baiti (AS), 1423 AH, juzu'i na 2, shafi na 78.
- ↑ «در عظمت مصیبت واقعه عاشورا»، سایت رسمی دفتر آیتالله العظمی وحید خراسانی.
- ↑ Khodamian, Sahih Fi Buka al-Husaini, 1432 AH, shafi na 54-59; Khodamian, Sahih fi Fazl al-Ziyarah al-Husainiyyah, 1432 AH, shafi na 148 da 149; Omrani, “Barsi Sanadi wa dalalai Hadisin Rayan bin Shabib Piramun Azadiri” shafi na 83 da 84.
- ↑ Khodamian, Sahih Fi Buka al-Husaini, 1432 AH, shafi na 59 da 60.
Tsokaci
- ↑ Allah ya amsa addu'ar Zakariyya ta neman zuriya ya umarci mala'iku su saka masa da Yahaya matsayin lada. (Sheikh Sadouq, Ayoun Akhbar al-Reza, 1378H, juzu'i na 1, shafi na 299).
Nassoshi
- Bahrani Isfahani, Abdullah bn Nour Allah, Awalimul Al-ulum wa Al-marif Wal Al-ahwali mianl Al-ayat wal Al-akjbar Wal Akqwali, Mustadrak, Sayyidat al-Nisa ila Imam Al-Jawad, Qum, Mu'assasa Imam Mahdi Al-Mahdi (Allah ya kara masa yarda). ka ba shi zaman lafiya), Babi na ɗaya, 1413 BC.
- Bahrani, Yusuf bin Ahmad, Al-Hada'ek Al-Nadhirah fi Ahkam na Iyali Tsarkaka, editan Muhammad Taqi Irani, Qum, Littafin Rubutun Rubuce-rubucen Musulunci, 1405 BC.
- Hakim, Sayyid Muhammad Saeed, Misbah al-Minhaj (Kitab al-Soom), Qum, Dar al-Hilal, bugu na farko, 1425H.
- Hurru Amili, Muhammad bin Hasan, wasa'il Al-Shi'a , Qum, Al-Bait Institute (A.S.), bugun farko, 1409H.
- Khodamian Arani, Mahdi, Sahih Fi Buka Al-Husseini, Mashhad, Jamal al-Pakhu al-Islami, bugun farko, 1432H/1389.
- Khodamian Arani, Mahdi, Sahih fi Fazl al-Ziyarah al-Husainiyyah, Mashhad, Majma al-Pakhu al-Islami, bugu na farko, 1432H/1389H.
- Majlisi, Mohammad Baqir, Bihar al-Anwar al-Jamaa shugaban Akhbar al-Imam al-Athar (AS), Beirut, Dar Ihya al-Trath al-Arabi, bugu na biyu, 1403H.
- Majlisi, Mohammad Taqi, Ruzda al-Mutaqiin fi Sharh Man la Yahdrah al-Faqih, Kum, Kushanbur Islamic Cultural Institute, 1406 AH.
- Mir Jahani Tabatabai, Seyyed Hasan, Al-Baka Lahussain Amincin Allah ya tabbata a gare shi: kan ladan kuka da makokin Sayyidi Shohda amincin Allah ya tabbata a gare shi da ayyukan tazizidari, binciken Hamed Fadavi Ardestani, Bija, Bina, Bita. .
- Najafi, Hadi, Encyclopaedia of Ahlul Baiti (A.S), Beirut, Dar Ihya al-Trath al-Arabi, bugun farko, 1423H/2002 Miladiyya
- Sayyid Ibn Tavus, Ali Ibn Musa, Iqbal al-Amal, Tehran, Dar al-Kitab al-Islamiya, bugu na biyu, 1409H.
- Sheikh Sadouq, Muhammad bin Ali bin Baboyeh, Al-Mali, Tehran, Kitabchi, bugu na 6, 1376.
- Sheikh Sadouq, Muhammad bin Ali ibn Babouye, nassi da tarjamar Akhbar al-Reza, amincin Allah ya tabbata a gare shi, wanda Hamidreza Mustafid da Ali Akbar Ghafari suka fassara, Tehran, bugun Sadouq, bugun farko, 1372.
- Sheikh Sadouq, Muhammad bn Ali bn Baboyeh, Ayoun Akhbar al-Reza, amincin Allah ya tabbata a gare shi, Mehdi Lajordi, Tehran, Nash Jahan, 1378H.
- «در عظمت مصیبت واقعه عاشورا»، سایت رسمی دفتر آیتالله العظمی وحید خراسانی، تاریخ درج مطلب: ۳ دی ۱۳۸۷ش، تاریخ بازدید: ۲۱ اسفند ۱۴۰۲ش.
- «ترکیببند یابن شبیب. جلوه اول/یابن الشبیب گریه کن از غربت حسین»، وبگاه امام هشت، تاریخ درج مطلب: ۸ مرداد ۱۳۹۷ش، تاریخ بازدید: ۲۴ اسفند ۱۴۰۲ش.
- عمرانی، سید مسعود، «بررسی سندی و دلایلی حدیث ریان بن شبیب پیرامون عزاداری»، فصلنامه آیت بوستان (پژوهشنامه معارف حسینی)، شماره ۲، تابستان ۱۳۹۵ش.
- «فابکِ لِلحُسَین»، وبگاه شعر هیأت، تاریخ بازدید: ۲۴ اسفند ۱۴۰۲ش..