Al-jaru Summad Daru

Daga wikishia
Zanen Fenti na hadisin Al-jaru Summad Daru, fasahar Aki Baharaini

Al-jaru summad daru, (Larabci: الجار ثُمَّ الدّار) ma'ana fara gabatar da maƙoci sannan a tuna da gida, wata jumla ce ta aka ciro ta daga nassin wani sanannen hadisi[1] daga Sayyida Faɗima (S).[2] an rawaito wannan hadisi daga Imam Hassan (A.S) yana cewa babata a daren ranar wata juma'a ta shagaltu da ibada tana ta addu'a ga muminai maza da mata tare da ambaton sunayensu sai na ji ko sau ɗaya ba ta yi wa kanta addu'a ba. Sai na ce: babata! Me ya sanya ban ji kina yi wa kanki addu'a yadda kike yi wa sauran mutane addu'a ? sai ta ce ya ɗana! Da farko ana fara gabatar da maƙoci ne sannan a tuna da gida.[3]

Shaik Saduƙ cikin babi na 145 a cikin littafin Ilalul Ash-shara'i ya kawo hadisai guda biyu, na farko riwaya ce ta Imam Hassan (A.S) na biyu daga Imam Kazim (A.S) ya naƙalto waɗannan hadisai guda biyu daga mahaifinsa sannan babu bambanci mai yawa cikin lafazansu.[4] Shaik Hurru Amili yana ganin fara gabatar da addu'a ga muminai kafi yi wa kai matsayin aiki na mustahabbi a shari'a, a cikin littafin Wasa'ilul Ash-shi'a ya keɓance babi guda kan wannan mas'ala, ya dogara da waɗannan hadisai guda biyu matsayin dalili kan ra'ayinsa.[5]

Sayyid Ali Khan Madani cikin littafin lugga da ya rubuta wannan jumla ta “Al-jaru Summad Daru” tare da wasu abubuwan daga Karin Magana cikin bahasin maƙoci. A cewarsa wannan Karin Magana yana ishara game da sanin mutumin da za kayi maƙotaka da shit un kafin siyan gidan da za ka zauna.[6] cikin litattafan hadisi misalin Al-kafi da Tuhaful Al-uƙul akwai wata Magana daga Imam Ali (A.S) game da zaɓar mutumin da zai kasance maƙocinka tun kafin zaɓar gidan da za ka zauna, wannan Magana tasa ta yi kama da maganar Sayyida Faɗima (S).[7] Mahadi Maharizi, mai nazari, ilimin hadisi, yana larura ayi la'akari da jumlolin farkon hadisin cikin fahima da gane ma'anar lafuzzan misalin waɗannan hadisai da suke ɗauke da lafuzza masu ma'ana guda ɗaya.[8] an ce anyi amfani da wannan jumla cikin adabin farisanci tare da abin da yake cikin hadisai guda biyu da ambatonsu ya gabata..[9] marubucin littafin Al-ikhtisas ya naƙalto rahotan nasihohin Luƙman Hakim ga ɗansa daga Auza'i malamin ahlus-sunna, cikin waɗannan nasihohi an kawo jumlar «الجار ثُمَّ الدّار» (Maƙoci Sannan Gida).[10]

Ana cewa Arifai da Mawaƙa misalin Aɗɗar Naishaburi da Gazali sun danganta jumlar «الجار ثُمَّ الدّار» ga Rabi'atul Adawiyya wata mata mai zuhudu da gudun duniya da ta rayu a ƙarni na biyu hijira ƙamari.[11] ba'arin masu bincike da nazari tare da jingina da madogaran hadisai da bayanan Sayyid Faɗima (S) sun watsi da maganar danganta wannan jumla ga wata mata a ƙarni na biyu.[12] Arifai sun ɗauki ma'anar wannan jumla matsayin rinjayar da Allah da fifita sonsa kan son aljanna da kuma fifita tsarkake niyya cikin ibada.[13]

Bayanin Kula

  1. Jamshidi, “Qawa'id Fahme Hadis,” shafi na 60.
  2. Sheikh Al-Saduq, Illal Al-Shara’i, juzu’i na 1, shafi na 182.
  3. Sheikh Al-Saduq, Illal Al-Shara’i, juzu’i na 1, shafi na 182.
  4. Sheikh Al-Saduq, Illal Al-Shara’i, juzu’i na 1, shafi na 182.
  5. ↑ Sheikh al-Harr Al-Amily, Wasa'il al-Shia, Juzu'i na 7, shafi na 113.
  6. Ibn Masoom al-Madani, al-tarazul al-Awal, juzu'i na 7, shafi na 230.
  7. Al-Kulayni, Al-Kafi, juzu'i na 8, shafi na 24; Ibn Shu`bah al-Harrani, Tuhaf al-Uqul, shafi na 86; Nahj al-Balagha, harafi na 31, shafi na 405.
  8. Mehrizi, HadisPajuhi, juzu'i na 1, shafi na 179.
  9. «تأثیر زبانی و محتوایی روایات شیعی بر ادبیات فارسی»، سایت آیین رحمت.
  10. Sheikh Mufid, Al-Ikhtisas, 1413H, shafi na 337.
  11. Panahi, "Al-Jar Tham Al-Dar wa barsi ma'akiz wa amuzehaye akhlaqiwa irfani an", shafi na 32-34.
  12. Panahi, "Al-Jar Thumma Al-Dar wa barsi ma'akiz wa amuzehaye akhlaqiwa irfani an", shafi na 36-34.
  13. Mulla Sadra, Tafsiri Al-Kur'an al-Karim, 1366, juzu'i na 4, shafi.414; Juzu’i na 7, shafi na 399; Panahi, "Al-Jar Thumma Al-Dar wa barsi ma'akiz wa amuzehaye akhlaqiwa irfani an", shafi na 33.

Nassoshi

Jamshidi, Asadullah, “Qawa'id fahame Hadis,” a cikin Mujallar Ma’rifat, Shamarat 83, Agusta 1383 Hijira.

  • Sheikh Saduq, Muhammad bin Ali, Ilal al-Shara’i’, Qum, Kitab Faroushi Dawari, babin farko, 1385H/1966 Miladiyya.
  • Sheikh Mufid, Muhammad bin Muhammad, Al-Ikhtisas, Qum, taron duniya na karni na Sheikh Al-Mufid, babi na farko, 1413 BC.
  • Kulaini, Muhammad bin Yaqoub, Al-Kafi, wanda Ali Akbar Ghafari da Muhammad Akhunandi suka buga, Tehran, Dar Al-Kutub Al-Islamiyya, Chaharam, 1407H.
  • Madani Shirazi, Ali Khan bin Ahmad, Al-Taraz Al-Awwal da Al-Kanaz saboda yaren Larabci da ya kunsa, Mashhad, Al-Bait (amincin Allah ya tabbata a gare shi) Mu'assasa ta Farko ta Farko, 1384 Hijira. .
  • Mulla sdra, Muhammad, Tafsir Alqur'ani Al-karim, wanda Muhammad Khwajavi ya buga, Qum, Bidar Publications, Chap Dom, 1366 AH.
  • Mawlawi, Jalaluddin Muhammad, Mathnavi Maanavi, Bahkoush Tawfiq Hashimpour Sobhani, Tehran, Zarat Farhang wa Irshad Islami, babin farko, 1373H.
  • Mehrizi, Mahdi, Hadispajuhi, Kum, Darul Hadith, Babi na 1390.
  • Nahj al-Balagha, wanda Subhi Saleh, Qum, Dar al-Hijrah Foundation ya inganta, 1414 BC.