Jump to content

Hassan Da Husaini Su ne Shugabannin Gidan Aljanna

Daga wikishia
Al-Hassan Wal Husaini Sayyida Shabab Ahlil Janna
Rubutun Hadisi na Shuwagabannin Al-Janna a cikin Haramin Imam Husain (A.S).
Rubutun Hadisi na Shuwagabannin Al-Janna a cikin Haramin Imam Husain (A.S).
Maudu'iFifitar Imam Hassan (A.S) da Imam Husaini (A.S)
Ya Fito DagaAnnabi (S.A.W)
MarawaitaSahabbai 25 daga cikinsu akwai Imam Ali (A.S), Abubakar da Umar
Ingancin IsnadiHadisi mutawatiri
Madogaran Shi'aƘurbul Isnad, Man La Yahduruhul Faƙihu, Al-Amali Shaik Mufid, Al-Amali Shaik Ɗusi
Madogaran Ahlus-sunnaSunanu Tirmzi, Sunanu Ibn Maja, Musnad Ahmad, Musannaf Ibn Abi Shaiba
Hadis Silsilatuz ZahabHadis SaƙlainiMaƙbulatu Umar Bin HanzalaHadis Ƙurbu NawafilHadis Mi'irajHadis WilayaHadis WisayaHadis Junud Aƙli Wa JahalHadis Shajara


Hassan Da Husaini Su ne Shugabannin Gidan Aljanna (Larabci:اَلْحَسَنُ و اَلْحُسَینُ سَیِّدَا شَبَابِ أَهْلِ الْجَنَّة) Riwaya ce daga Annabi (S.A.W) game da fifikon Imam Hassan (A.S) da Imam Husaini (A.S) a kan sauran ƴan Aljanna. A fahimtar wasu malaman Shi'a suna ganin abin da wannan hadisin ya ƙunsa shi ne waɗannan Imamai guda biyu a nan duniya ma sunfi kowa daraja a doran ƙasa, in aka ɗauke iyayensu da kakannsu Annabi, don haka dole ne a yi musu biyayya. Idan muka duba riwayoyin wasu daga malaman Ahlus-Sunna sun ce, ruwayoyi sun siffanta `yan Aljanna a matsayin matasa, ma'anar ruwayar ita ce, Hassan da Husaini (A.S) su ne shuwagabannin ƴan Aljanna, sai dai kuma cewa an tigace wasu mutane kamar Annabi (S.A.W) da Imam Ali (A.S)

Wannan hadisin yana cikin litattafai misalin Al-Amali Shaikh Ɗusi, Man La Yahduruhul Faƙihu da Sunanu Tirmizi. Haka kuma an ruwaito daga sahabbai 25, misalin Imam Ali (A.S), da Abubakar da Umar Bin Khaɗɗab, malaman Ahlus-Sunna da Shi'a suna ganin wannan hadisi ya kai matsayin mutawatiri, A cikin wasu madogaran Ahlus-Sunna, akwai wata ruwaya mai kama da wannan hadisi, wace ta gabatar da Abubakar da Umar a matsayin shugabannin dattawan gidan Aljanna, wasu malama Ahlus-Sunna su na ganin wannan hadisi ne mai rauni ne kuma ƙagagge.

Bayaninsu da Sanin Matsayinsu

Hadisin Sayyida Shabab Ahlil al-Janna, shahararriyar ruwayar ce daga Manzon Allah (S.A.W),[1] wace aka yi amfani da ita wajen tabbatar da fifikon Imam Hassan da Imam Husaini (A.S) akan sauran `yan aljanna.[2] Ya zo a cikin littafin Bihar al-Anwar cewa Imam Hussain (A.S) ya kawo wannan hadisi a gaban magauta a lokacin waƙi'ar Karbala domin tabbatar da gaskiyarsa[3]

Nassin hadisin kamar haka: "Al-Hassan da Al-Hussain su ne Shuwagabannin samarin Aljanna".[4] An rawaito wannan ruwayar a wasu litattafan hadisin Shi'a da Ahlus-sunna, daga ciki: "Al-Hassan da Al-Hussain su ne majiɓintan samarin Aljanna kuma mahaifinsu ya fi su biyun daraja"[5] da kuma "Al-Hassan da Husaini su ne shugabannin matasan Aljanna, lallai Fatima ita ce shugabar matan Aljanna".[6]

Fifikon Hasanaini Kan Dukkanin Mutanen Cikin Aljanna

A cikin wasu hadisai an siffanta dukkan `yan aljanna a matsayin samari,[7] Wasu malaman ahlus-sunna bisa dogaro da irin waɗannan hadisan ne yasa suka fassara kalmar Shabab (matasa) ga `yan Aljanna.[8] Wato Hassan da Husaini su ne shuwagabannin ƴan Aljanna bakiɗaya[9] Haƙiƙa an togace Annabi (S.A.W) da Ali (A.S) daga cikin wannan hadisin[10] A wani hadisin kuma. An ambaci cewa Manzon Allah (S.A.W) ya cire Isa da Yahaya daga wannan riwaya[11] Amma Muhammad Hassan Muzaffar ɗaya daga cikin malaman Shi'a ya ce an saka hannu a ruwayar (An canzata) kuma bai yarda da abin da aka ambata ba; Domin akwai Annabawa irin su Ibrahim da Musa (A.S) waɗanda suka fi Yahaya, amma ba a cire su a hadisin ba.[12]

Dalilin Da Yake Tabbatar Da Imamancin Hasanaini

Ali Baharani (Rasuwa: 1340. H), ɗaya daga cikin malaman Shi'a, ya yi nuni da hadisin da ke bayani kan cewa shugabannin ranar Mahshar wato ranar alƙiyama , su ne sarakuna anan duniya,[13] ya yi imani da cewa, kamar yadda hadisin Sayyida Shabab Ahlil Janna ya zo akan Imam Hassan da Imam Husaini (A.S) haka yake a ɗayan hadisin ma su ne shugabanni a nan duniya[14] Don haka ne aka ce wannan hadisi yana daga cikin dalilan tabbatar da imamancin waɗannan Imaman biyu.[15] Ana amfani da kalmar "Sayyid" ga wanda yake da shugabanci da girma da daraja,[16] haka nan wanda ya fi wasu a dukkan kyawawan halaye ana kiransa Sayyid.[17]

Kasancewar Hadisin Mutawatiri

Allama Majlisi malamin hadisi na Shi'a yana ganin hadisin Sayyida Shabab Ahlul-Janna ya kasance mutawatiri a gun malaman Shi'a da Ahlus-Sunna[18] Wasu malaman Ahlus-Sunna da suka haɗa da Suyuɗi da Nasiruddin Albani, su ma sun bayyana tawatirin wannan hadisi.[19] Abu Nu'aimi Isfahani malamin hadisin Ahlus-Sunna a cikin amfani da bayani na kinaya game da karfin isnadin hadisin, an naƙalto daga Ahmad Bin Hanbal cewa da za a karanta wannan ruwaya ga mahaukaci to haukansa zai iya tafiya saboda ƙarfinsa.[20]

Abin da ya fi shahara da aka rawaito wannan hadisi shi ne littafin Al-Amali na Shaikh Ɗusi[21] da Shaik Saduƙ cikin littafin Man La Yahduruhul Faƙihu.[22] Ya zo daga Ahlus-Sunna mislain Tirmizi da Ibn Abi Shaiba[23] Wasu masu bincike sun ruwaito shi da lafazi da ma'ana daban-daban daga sahabban Manzon Allah (S.A.W) guda ashirin da biyar waɗanda suka haɗa da Imam Ali (A.S), da Abubakar da Umar.[24]

Ƙirkirar Kwatankwacin Wannan Hadisi Domin Abubakar Da Umar

A cikin litattafan Ahlus-Sunna, akwai wani rahoto mai kama da hadisin Sayyida Shabab Ahlil-Jinna, na girmama Abubakar da Umar cewa su ne shuwagabannin dattawan Aljanna.[25] Haisami da Ibn Jauzi, daga cikin malaman Ahlus-Sunna sun ɗauki wannan riwaya matsayin riwaya mai rauni kuma wacce aka ƙirɗira.[26]

Ɗabarsi ya ruwaito a cikin littafinsa na Al'ihtijaj a cikin muhawarar da Yahaya Ibn Aksam da ya yi da Imam Jawad (A.S), Ibn Aksam ya tambayi Imam Rida: Mene ne ra'ayinka game da ruwayar da ke cewa "Abubakar da Umar Su ne shuwagabannin Dattawan gidan aljanna"? Imam ya bayyana ƙin fitar irin wannan magana daga bakin Annabi sannan ya ce: Bani Umayya ne suka ƙirƙira. don su yi takara da hadisin "Hassan da Hussaini su ne shuwagabannin ƴan Aljanna".[27]

Bayanin kula

  1. Fathi, “Hadisu Sayyida Shabab Ahlul-Jannah wa Mas'alati Afdaliyat Imam” shafi na 62
  2. Fathi, “Hadisu Sayyida Shabab Ahlul-Jannah wa Mas'alati Afdaliyat Imam” shafi na 82
  3. Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 45, shafi na 6.
  4. Sheikh Tusi, Amali, 1414 AH, shafi 312; Sheikh Sadouq, Man La Yahzara al-Faqih, 1413 AH, Juzu'i na 4, shafi na 179; Tirmizi, Sunan al-Tirmidhi, 1395 AH, juzu'i na 5, shafi na 656; Ibn Abi Shiba, al-Musannaf, 1409, juzu'i na 6, shafi na 378, H. 32176.
  5. Himyari, Qarb al-Isnad, 1413 AH, shafi 111; Ibn Majah, Sunan Ibn Majah, Dar Ihya Al-Katb al-Arabiya, Juzu'i na 1, shafi na 44.
  6. Sheikh Mufid, Amali, 1413 AH, shafi na 23; Ahmad bin Hanbal, Musnad Ahmad, 1421 Hijira, Juzu'i na 38, shafi na 353, Hijira 2329.
  7. Sheikh Mofid, Al-Khissas, 1413 AH, shafi na 358; Tirmizi, Sunan al-Tirmizi, 1395 AH, juzu'i na 4, shafi na 679; Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 43, shafi na 292.
  8. Manavi, Faiz al-Qadeer, 1356 AH, juzu'i na 6, shafi na 151.
  9. Manawi, Al-Taysir bi sharh Al-Jamae al-Saghir, 1408 AH, Mujalladi na 1, shafi na 507; Albani, Silsilatu -Ahadith Sahih, 1415 Hijira, juzu'i na 2, shafi:431.
  10. Muzaffar, Dalai Al-Sidq, 1422 AH, juzu'i na 6, shafi.463; Fathi, "Hadisin Sayyi Shabab na Ahlul-Jannah wa Mas'alati Afdaliyat Imam", shafi na 59.
  11. Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 43, shafi na 316.
  12. Muzaffar, Dalai al-Sidq, 1422 AH, juzu'i na 6, shafi na 461-462.
  13. Ibn Abi al-Hadid, Sharhu Nahj al-Balaghah, 1404 AH, juzu'i na 7, shafi na 64
  14. Bahrani, Manar Al-Huda, 1405H, shafi 582.
  15. بازوند، «بازخوانی سندی و دلالی حدیث سیدا شباب اهل الجنة»، Markaz Haqayiq Islami.
  16. Bahrani, Manar Al-Huda, 1405H, shafi 582.
  17. Samani, Tafsir Alkur'ani, 1418, juzu'i na 1, shafi na 316; Khazan, Labab al-Tawil, 1415 AH, juzu'i na 2, shafi na 242.
  18. Majlesi, Haq al-yaqin, Islamic Publications, shafi na 287.
  19. Manawi, Al-Taysir bi hsarhe Al-Jamae al-Saghir, 1408 AH, Mujalladi na 1, shafi na 507; Albani, Silsilatu Ahadith Sahiha, 1415 Hijira, juzu'i na 2, shafi:431.
  20. Isfahani, Tarikh Isfahan, 1410H, shafi na 73.
  21. Sheikh Tusi, Amali, 1414 AH, shafi na 312.
  22. Sheikh Sadouq, Man La Yahzara al-Faqih, 1413 AH, Juzu'i na 4, shafi na 179.
  23. Tirmizi, Sunan al-Tirmidhi, 1395 AH, juzu'i na 5, shafi na 656; Ibn Abi Shiba, al-Musannaf, 1409, juzu'i na 6, shafi na 378, H. 32176.
  24. Fathi, "Hadisin Sayyida Shabab Ahlul-Jannah wa Mas'alati Afdaliyat Imam", shafi na 62.
  25. Tirmizi, Sunan al-Tirmidhi, 1395 AH, juzu'i na 5, shafi na 611; Ahmad bin Hanbal, Musnad Ahmad, 1421, juzu'i na 2, shafi na 40, H. 602.
  26. Haytami, Majma al-Zawaed, 1414 AH, juzu'i na 9, shafi na 53; Ibn Jozi, al-Ubaat, 1386 Hijira, juzu'i na 1, shafi na 398.
  27. Tabarsi, al-Ihtijaj, 1403 AH, juzu'i na 2, shafi na 447.

Nassoshi

  • Ibn Abi al-Hadid, Abdul Hamid, Sharh Nahj al-Balaghah, Qum, Mazhabar Ayatullahi al-Marashi al-Najafi, bugu na farko, 1404H.
  • Ibn Abi shaibah, Abdullah bin Muhammad, Al-Musannaf fi al-Ahadith and Antiquities, bincike: Kamal Yusuf al-Hout, Riyadh, Al-Rashad School, bugu na farko, 1409 AH.
  • Ibn Jozi, Jamal al-Din, Al-Ubaat, Bincike: Abdur Rahman Muhammad Othman, Madina, Al-Maktab al-Salfiyyah, bugun farko, 1386H.
  • Ibn Majah, Muhammad Ibn Yazid, Sunan Ibn Majah, Bincike: Muhammad Fouad Abdul Baqi, Bija, Dar Ihya Al-Kitab al-Arabiyyah, Bita.
  • Isfahani, Abu Naim, Tarikh Isfahan, wanda Hassan Kasravi ya yi bincike a Beirut, Darul Katb al-Alamiya, 1410H.
  • Tabarsi, Ahmad bin Ali, Al-Ihtijaj Ali Ahl al-Jajj, Mashhad, Morteza Publishing House, bugun farko, 1403H.
  • Ahmed bn Hanbal, Abu Abdullah, Musnad na Ahmad bn Hanbal, bincike: Shuaib Al-Arnaut da Adel Murshid, Bija, Al-Risalah Foundation, bugun farko, 1421H.
  • Albani, Muhammad Nasarul-Din, Silsilatu Hadith al-Sahiha wa shai'ain min fiqihu wa fawa'idiha.
  • Fathi, Ali, "Hadisu Sayyida Shabab Ahl al-Jannah wa Mas'alati Afdaliyat Imam" a cikin Mujallar Kalam ta Musulunci Juzu'i na 21, lamba 82, Qum, Satumba 2011.
  • Haitami, Noor al-Din, Majma al-Zawaed w manba'il Fawa'i, Bincike: Hossam al-Din Al-Qudsi, Alkahira, Mazhabar Qudsi, 1414H.
  • Majlesi, Mohammad Baqer, Bihar Al-Anwar, Beirut, Dar Ihya Al-Trath al-Arabi, bugu na biyu, 1403H.
  • Majlesi, Mohammad Baqer, Haq Alyaqin, Tehran, Islamia Publications, Beta.
  • Manawi, Abdul Raouf bin Taj, Al-Taysir bi sharhe Al-Jamae al-Saghir, Al-Riyadh, Mazhabar Imam Shafi'i, 1408H.
  • Manawi, Abdul Raouf, Faiz al-Qadeer, Sharh al-Jamae al-Saghir, Misr, al-Maktab Tejariyyah al-Kabari, bugu na farko, 1356H.
  • Mozaffar, Mohammad Hasan, Dalai al-Sidq, Qum, Al-Bait (A.S.) Foundation, bugun farko, 1422H.
  • Sheikh Mofid, Muhammad bin Muhammad, Al-Amali, wanda Hossein Ustadwali, Ali Akbar Ghafari, Qom, Sheikh Mofid Congress ya buga, bugun farko, 1413 AH.
  • Sheikh Mofid, Muhammad bin Muhammad, Al-IKhtisas, Ali Akbar Ghafari, Qom, Al-Tomar al-Ilami Lalfiya Al-Sheikh Al-Mofid, bugu na farko, 1413H.
  • Sheikh Sadouq, Muhammad Bin Ali, Man La Yahdrah al-Faqih, Qum, Ofishin Daba'ar Musulunci, bugu na biyu, 1413H.
  • Sheikh Tusi, Muhammad bin Al-Hassan, Al-Amali, Kum, Darul Taqwa, bugun farko, 1414H.
  • Rida, Bazunde «بازخوانی سندی و دلالی حدیث سیدا شباب اهل الجنة»، Cibiyar Haqayiq Islami, ranar ziyara: 20 ga watan Dey, shekara ta 1402 Hijira Shamsiyya

Sendi, Nour al-Din, Hashiya al-Sandi Ali Sunan Ibn Majah, Beirut, Dar al-Jeil, Bita.