Kuka kan Imam Husaini (A.S)

Daga wikishia
Zaman makoki tare da kuka kan shahadar Imam Husaini (A.S)

Kuka Kan Imam Husaini (A.S) (Larabci: البكاء على الحسين(ع)) shi ne yin kuka da zubar da Hawaye kan Zalunci da aka yi kan Imam Husaini (A.S) da Musibun da suka same shi da Sahabbansa, kamar yanda karfafa kan haka ya zo a cikin Hadisan Imamai (A.S) daga cikin Ladan yin Kuka kan Imam Husaini (A.S) akwai misalin Gafarta Zunubai da samun Aljanna, a wasu riwayoyin ya zo cewa suma Mala’iku tare da Annabawa suna yin kuka kan Musibar Imam Husaini (A.S) Malaman Shi’a sun bayyana cewa Illar yin kuka kan Musibar Imam Husaini (A.S) shi ne Hanyar neman `yanci da Gwagwarmaya da Zalunci a kodayaushe za su kasance rayayyu, haka kuma daga cikin Fa’idojin yin kuka kan Musibar Imam Husaini (A.S) akwai bayyana Soyayya zuwa gare shi da sabunta Mubaya’a da haduffa misalin Neman Shahada, hakika ana kidaya wannan aiki sababi na wanzuwar Muslunci. Hakika Ahlil-Baiti (A.S) kari kan kukan da suke yi da kansu hakika sun yi wasicci da sanya Mutane Kuka kan Musibar Imam Husaini (A.S) sun kuma ambaci lada da za a samu kan wannan aiki.

Falalar Yin Kuka Kan Imam Husaini (A.S)

Imam Rida (A.S)

یَا ابْنَ شَبِیبٍ إِنْ کُنْتَ بَاکِیاً لِشَیْءٍ فَابْکِ لِلْحُسَیْنِ بْنِ عَلِیِّ بْنِ أَبِی طَالِبٍ(ع) فَإِنَّهُ ذُبِحَ کَمَا یُذْبَحُ الْکَبْشُ وَ قُتِلَ مَعَهُ مِنْ أَهْلِ بَیْتِهِ ثَمَانِیَةَ عَشَرَ رَجُلًا مَا لَهُمْ فِی الْأَرْضِ شَبِیهُون‏.

Ya kai ɗan Shabib idan har ka kasance kana kuka kan wani abu to ka yi kuka domin Husaini ɗan Ali ɗan Abi ɗalibi (A.S) lallai an yanka shi kamar yanda ake yanka rago, an kashe shi tare da mazaje 18 daga mutanen guidansa waɗanda babu irinsu a dora ƙasa.

Sheikh Saduƙ, Al-Amali, 1376H, shafi na 130.

Yin kuka kan Imam Husaini (A.S) shi ne zubar da Hawaye kan Musibarsa da zaluncin da aka aikata a kansa da Sahabbansa a Waki’ar Karbala, [1] dangane da Falalar wannan aiki akwai riwayoyi masu yawan gaske da aka nakalto daga Annabi (S.A.W) da Ahlil-Baiti (A.S) da suke karfafa Maganar kuka kan Musibar Imam Husaini (A.S) [2] akwai lada mai tarin yawa da ya zo cikin riwayoyi kan yin Kuka kan musibar Imam Husaini (A.S) [3] Shaik Saduk daga Malaman Hadisi na Shi’a ya nakalto daga Rayyanu Bn Shabib cewa ya je wurin Imam Rida (A.S) a farkon watan Muharram, sai Imam Rida (A.S) ya tunatar da shi Musibun da suka samu Kakansa yana cewa: (ya `Dan Shabib idan ka yi kuka kan Husaini Hawayenka ya zuba kan Kumatunka, Allah zai yafe maka dukkanin Zunubin da ka aikata daga Manyansu da kananansu komai yawansu zai yafe maka su. [4] An nakalto daga Imam Sadiƙ (A.S) cewa Ali Bn Husaini (A.S) ya yi shekara Ashirin yana kuka kan Musibar da ta afku kan Mahaifinsa, duk lokacin da aka ajiye abinci a gabansa sai ya fashe da kuka [5] a wasu riwayoyin ya zo cewa Mala’iku da Annabawa Sama da Kasa, Dabbobin Daji, da halittun cikin Ruwa suna Kuka kan Ta’aziyyar Imam Husaini (A.S) [6] Haka kuma a cikin littafin Kamil Az-Ziyarat an nakalto riwaya daga Imam Sadiƙ (A.S) yana cewa Hawayen da aka zubar kan Imam Husaini ko da kuwa bai fi girman Fuffuken Kuda ba hakika ladan da Allah zai bayar kan wannan Hawaye ba zai kasance kasa da gidan Aljanna ba, [7] na’am amma fa da sharadin zubar da Hawayen tare da Imani da kuma sanin Hakkin Imam Husani (A.S) da haduffansa [8] da kuma kiyaye Halal da Haram. [9]

Dalilin Yin Wasicci da Sanya Kuka Kan Imam Husaini (A.S)

Murtada Mutahhari daga Malaman Shi’a, yana ganin karfafawa mai tarin yawa da ta zo daga bakin Imamai (A.S) kan Kuka kan Imam Husaini (A.S) suna so ne a kodayaushe Mikewar Imam Husaini da Hanyar neman `yanci da Gwagwarmaya da Zalunci su wanzu a raye, a cewar Malamin, wannan wasicci da Imamai (A.S) suka yi ya zama sababin raya Gwagarmaya hatta a zamaninsu sunan Imam Husaini (A.S) shi ne Taken Masu Gwagwarmaya da zalunci da kuma neman `Yanci [10] Haka kuma yin Kuka cikin Zaman Makokin Imam Husaini da Shahidan Karbala yana zama matsayin sabunta Muba’aya tare da Sakafar Shahada da shayar da tunani da Ruhi da abin shan wannan hanya, Malamai sun ce shi wannan Kuka wata alama ce ta damfaruwar zuciya da Ahlil-Baiti (A.S) kuma wani nau’in Alkawari ne na soyayyar Imam Husaini (A.S) [11] Imam Khomaini ya bayyana Kuka tare da zaman Makoki domin Imam Husaini (A.S) yana zama sababin kariya ga Muslunci [12]

Sanya yin Kuka

Imaman Shi’a (A.S) kari kan Kuka da suke yi kan Ta’aziyyar Imam Husaini (A.S) sun kasance suna Wasicci da sanya yin Kuka kuma sun yi bayanin irin ladan da za a samu kan wannan aiki, Shaik Saduk ya nakalto daga Imam Rida (A.S): (duk wanda ya tuna da Musibarmu mu Ahlil-Baiti sai ya yi kuka ko ya sa aka yi Kuka, hakika Ranar da Idanu suke kuka (Ranar Alkiyama) shi Idanunsa ba za su yi Kuka ba) [13] haka an nakalto daga Imam Bakir da Imam Sadiƙ (A.S) cewa: duk wanda ya yi kuka cikin Makokin Husaini (A.S) ko kuma ya sanya wasu Kuka ko da kuwa mutum daya ne ya yi kuka lallai mun lamince masa Aljanna, kuma duk wanda bai yi kuka ba sai dai cewa yaji bakin ciki da Makoki shima zai samu wannan lada. [14] A cewar Shaik Abbas Qummi daya daga cikin Malaman Shi’a a karni na Goma sha hudu Sanya kuka baya nufin Aiki Riya, saboda shi Kuka kan Imam Husaini (A.S) ibada ce kuma baya halasta ayi Riya cikin Ibada, [15] sa kai kuka ko kuma Kamanceceniya da Masu Kuka yana nufin kasancewa tare da su, [16] daidai lokacin da ita kuma Riya shi ne Bayyanantar da kyakkyawan aiki domin nuna kai ga wasu. [17]

Bayanin kula

  1. , Guruhi az Tarikh Pajuha, Tarikh KIyam Jame Maktal Sayyid shuhada, 1395, juzu'i na 2, shafi na 323.
  2. Sheikh Sadouq, Al-Amali, 1376H, shafi na 130; Majlesi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 44, shafi na 278.
  3. Hurrul Ameli, Wasa'il Al-Shia, 1409 AH, juzu'i na 14, shafi na 501.
  4. Sheikh Sadouq, Al-Amali, 1376H, shafi na 129 da 130.
  5. Ibn Shahr Ashub, Manaqib Al Abi Talib, 1378, juzu'i na 4, shafi na 165.
  6. Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 45, shafi na 218 da 220.
  7. Ibn Quluyeh, Kamel al-Ziyarat, 1356, shafi na 100, hadisi na 3.
  8. https://makarem.ir/main.aspx?typeinfo=44&lid=0&catid=27752&mid=418549,پایگاه اطلاع‌رسانی دفتر آیت الله مکارم شیرازی.
  9. Makarem Shirazi, Payam Imam Amirul Momineen (AS), 1386, juzu'i na 14, shafi na 334.
  10. Motahari, Majmu'eh Asar, Sadra Publications, juzu'i na 25, shafi na 338.
  11. Muhaddith, Farhang Ashura, 1417H, shafi na 382.
  12. Khumaini, Sahifa Imam, 2009, juzu'i na 8, shafi na 527 da 529.
  13. Sheikh Sadouq, al-Amali, 1376H, shafi na 73
  14. Ibn Nama, Muthir al-Ahzan, 1406H, shafi na 14.
  15. Qomi, Mentehi al-Amal, 1379, juzu'i na 2, shafi.1060.
  16. https://www.karbobala.com/articles/info/2105پایگاه تخصصی امام حسین.
  17. Kamus Al-ur'an, 1371, juzu'i na 3, shafi na 30.

Nassoshi

  • Motahari, Morteza, Majmu'eh Asar Ustad Shahid Motahari, Tehran, Sadra Publishing House, Beta.
  • Guruhi Az Tarikh Fajuhan Zire Nazare Pishawayi, Tarikh Kiyam wa Maktale Sayyid Al-Shohada (AS), Qum, Cibiyar Ilimi da Bincike ta Imam Khumaini, bugu na farko, 1395.
  • Hurril Amili, Muhammad bin Hasan, Wasa'il al-Shia, Qum, Al-Bait Institute (A.S.), bugu na farko, 1409H.
  • Ibn Nama Hilli, Jafar bin Muhammad, Muthirul Ahzan, Madaraseh Imam Mahdi, Qum, bugu na uku, 1406H.
  • Ibn Qolwieh, Jafar bin Muhammad, Kamel al-Ziyarat, bugun Abdul Hossein Amini, Najaf Ashraf, Dar al-Mortazawieh, bugun farko, 1356.
  • Ibn Shahr Ashub Mazandarani, Muhammad Bin Ali, Manaqib Al Abi Talib, Amincin Allah ya tabbata a gare shi, Kum, Allameh Publications, bugun farko, 1378.
  • Khumaini, Sayyid Ruhollah, Sahifa Imam, Tehran, Cibiyar gyara da buga ayyukan Imam Khumaini (a.s), bugu na 5, 1389.
  • Majlesi, Mohammad Baqer, Bihar al-Anwar, Beirut, Dar Ihya al-Trath al-Arabi, bugu na biyu, 1403H.
  • Makaram Shirazi, Nasser, Payam Imam Amirul Momineen (AS), Tehran, Dar Al-Katb al-Islamiya, bugun farko, 1386. Mujalladi na 14, shafi na 334.
  • Mohaddisi, Javad, Farhang Ashura, Qum, shahararren bugu, bugu na biyu, 1417 AH.
  • Qomi, Sheikh Abbas, Mantehi al-Amal, Qom, Dilil Ma, bugun farko, 1379.
  • Qoraishi, Sayyid Ali Akbar, Kamus Quran, Tehran, Dar al-Katb al-Islamiyya, bugu na 6, 1371.
  • Sheikh Sadouq, Mohammad Bin Ali, Al-Amali, Tehran, Kitabchi, bugu na 6, 1376H.
  • «نجات و بهشت رفتن انسان گنهکار به صرف گریه بر امام حسین(ع)»، پایگاه اطلاع‌رسانی دفتر آیت الله مکارم شیرازی، تاریخ بازدید: ۳۰ شهریور ۱۴۰۲ش.
  • wesal Shirazi, Mohammad Shafi, Kulliyat Wesal Shirazi, Mohammad Abbasi edited, Beta, bugun Fakhr Razi bookshop,

«مبانی قرآنی گریه برای امام حسین(ع)»، پایگاه تخصصی امام حسین، تاریخ بازدید: ۲۷ شهریور ۱۴۰۲ش