Daƙiƙa:Majalisar Duniya Ta Kusantar Mazhabobin Musulunci
![]() | |
| Kafawa | 1990M. |
|---|---|
| Waɗanda suka kafa | Sayyid Ali Husaini Khamna'i |
| Salo | Kusanto da Mazhabobin Musulunci |
| Nau'in ayyuka | ilimi, na bincike, da na wa'azi (ko yaɗa saƙo). |
| Faɗaduwar aiki | Duniyar Musulunci |
| Manufofi | Faɗaɗa yaɗa ilimin Musulunci•kare Kur'ani da sunnar Annabi (S.A.W)•Haɗin kai da fahimtar juna tsakanin malamai na addini a duniya ta Musulunci• Kawar da rashin fahimta da shakku tsakanin mabiyan mazhabobin Musulunci. |
| Ayyuka | Shirya taruka da tarurrukan ƙasa‑da‑ƙasa na kusantar juna (Haɗin kai). |
| Babban sakatare | Hamid Shariyari |
| Tsari | Babban Taro na Gaba ɗaya (ko Majalisar Gaba ɗaya). |
| Hali | Tana kan aiki |
| Ayyuka da harshen | Da harsuna daban-daban na duniya |
| Cibiyoyin da suke ƙasanta | Jami'ar Mazhabobin Musulunci•Cibiyar Nazarin Haɗin Kan Mazhabobin Musulunci•Hukumar Labarai ta Taƙrib |
| Rubuce-rubuce | Mujallu kamar Risalat al‑Taƙrib, Risalat al‑Islam, Saƙafat At‑Taƙrib, da sauransu...• |
| Mai alaƙa da | Makon Haɗin Kai•Majalisar Ahlul-Baiti Ta Duniya |
| Adireshin yanar gizo | http://www.taghrib.org |
Majalisar Duniya Ta Kusantar Mazhabobin Musulunci, wata ƙungiya ce mai zaman kanta (ba ta gwamnati ba) wadda ta ƙunshi wasu daga cikin malaman addinin Musulunci daga sassa daban‑daban na duniyar Musulmi, kuma an kafa ta da manufar kusantar da mazhabobin Musulunci da juna.
An kafa wannan ƙungiya a shekarar 1990M, bisa umarnin Ayatullahi Ali Khamna'i, jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Majalisar kusantar mazhabobi yana da ginshiƙai uku: Babbar majalisa, Majalisar Ƙoli, Babban Sakatare Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran ne ke naɗa Membobin Majalisar Ƙoli da Babban Sakatare na wannan Majalisa.
Cibiyar wannan ƙungiya tana a birnin Tehran na ƙasar Iran kuma Hamid Shahriyari ne ya kasance babban sakatare.
Kafawa
A shekarar 1990M, bayan gudanar da Taron Haɗin Kan Musulunci na huɗu, wanda Sashen Yaɗa Addinin Musulunci ya shirya tare da halartar wasu daga cikin masana da masu tunani na duniyar Musulunci a birnin Tehran, bisa umarnin Ayatullahi Khamna'i, Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran, aka kafa Majalisar Duniya ta Kusantar Mazhabobin Musulunci.[1]
Manufofi
A cewar shafin yanar giza-gizo na Majalisar Duniya ta Kusantar Mazhabobin Musulunci, manufofin wannan ƙungiya sun haɗa da:
- Raya da yaɗa al'adu da ilimin Musulunci, da kuma kare martabar Al'ƙur'ani da Sunnar Annabi Muhammad (S.A.W).
- Ƙara fahimtar juna da kusanci tsakanin malamai, masu tunani, da shugabannin addini na duniyar Musulunci a fannoni na aƙida, fiƙihu, zamantakewa, da siyasa.
- Yaɗa ra'ayin kusantar mazhabobi a tsakanin masu ilimi da masu tunani na duniyar Musulunci, da kuma isar da shi ga jama'ar Musulmi tare da faɗakar da su game da makircin da ke haddasa rarrabuwa daga abokan gaban Musulunci.
- Ƙarfafa da yaɗa ka'idar ijtihadi da fitar da hukunci (istinbaṭ) a cikin mazhabobin Musulunci.
- Haɗa kai da samar da gaba ɗaya tsayuwar daka a gaban makircin yaɗa farfaganda da hare‑haren al'adu daga abokan gaban Musulunci, bisa ƙa'idojin Musulunci da aka amince da su.
- Kawar da zargi, rashin yarda, da shakku tsakanin mabiyan mazhabobin Musulunci.[2]
Tsari
Ginshikan Majalisar Kusantar Mazhabobi sun haɗa da:
Babban Taro Na Gaba ɗaya
Membobin Babban Taro na Gaba ɗaya ana zaɓar su ne ta Babbar Majalisar Gudanarwa daga cikin malamai da masu tunani na mazhabobin Musulunci na duniya waɗanda ke goyon bayan kusanto da mazhabobin Musulunci, na tsawon shekaru shida.[3] Babban Taro na Gaba ɗaya yana da kwamitoci kamar: Kwamitin ƙananan al'ummomin Musulmi marasa rinjaye, kwamitin yaɗa saƙo da faɗakarwa, kwamitin ƙalubalen da al'ummar Musulmi ke fuskanta, da kwamitin mata da rawar da suke takawa wajen kusantar mazhabobin Musulunci.[4]
Majalisar Ƙoli Ta Gudanarwa
Membobin Babbar Majalisar Gudanarwa ta Majalisar Duniya ta Kusantar Mazhabobin Musulunci ana naɗa su ne ta Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran, daga cikin malamai, masu tunani, da manyan mutane na mazhabobin Musulunci, na tsawon shekaru shida.[5]
Membobin Majalisar Shura
- Muhsin Araki (Iran)
- Muhammad Is'haƙ Madani (Iran)
- Abdul-Hadi Awang (Malesiya)
- Ahmad Muhammad Al‑Shami (Yaman)
- Abdul-Karim Bi Azar Shirazi (Iran)
- Sayyid Hasasn Rabbani (Iran)
- Ahmad Bin Hamad Al‑Khalili (Oman)
- Abdur-Rahim Ali (Sudan)
- Muhammad Salim Al‑Awa (Masar)
- Muhammad Hassan Akhtari (Iran)
- Mahmoud Muhammadi Araki (Iran)
- Sayyid Sajid Ali Naƙawi (Pakistan)
- Muhammad Al‑Asi (Mataimakin Shugaba) (Amurka)
- Sayyid Musa Musawi (Iran)
- Muhsin Qommi (Iran)
- Muhammad Baƙir Khorramshad (Iran)
- Nazir Ahmad Salami (Iran)
- Abdur-Rahman Khodayi (Iran)[6]
Sai dai kuma wasu daga cikin membobin Babbar Majalisar Gudanarwa ta Majalisar Duniya ta Kusantar Mazhabobin Musulunci, ciki har da Muhammad Ali Taskhiri, Muhammad Wa'iz Zade Khurasani, Muhammad Asif Muhsini, da Abbas Ali Sulaimani, sun riga sun rasu.
Babban Sakatare
Sakataren Janar shi ne mafi girman jami'in gudanarwa na Majalisar Kusantar da Mazhabobin Musulunci. Ana naɗa shi na tsawon shekaru huɗu ta hannun Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran, bisa shawarar Majalisar ƙoli. Muḥammad Wa'iz Zade Khurasani[7](daga 1990M. zuwa 2001M.) Muhammad Ali Taskhiri[8](daga 2001M. zuwa 2012M.), da Muhsin Araki (daga 2012M. zuwa 2019M.) sun kasance manyan Sakatarorin na Majalisar Kusantar da Mazhabobin Musulunci ta Duniya.[9]
Tun daga (15 Disamba 2019M.), Hamid Shahriyari ne ke riƙe da wannan matsayi. [10]
Ayyuka Da Cibiyoyin Da Ke Ƙarƙashinta
Ayyuka da cibiyoyin da ke ƙarƙashinta Majalisar Kusantar Mazhabobin Musulunci tana gudanar da ayyuka a fannoni na ilimi, bincike, da yaɗa bayanai kan batutuwan kusantar mazhabobi. Daga cikin ayyukanta da cibiyoyin da ke ƙarƙashinta akwai:
- Shirya taruka da manyan tarurrukan ƙasa da ƙasa a ƙasashe daban‑daban na duniya.[11] Daga ciki akwai taron ƙasa da ƙasa na haɗin kan Musulunci, wanda ake gudanarwa kowace shekara daga 12 zuwa 17 ga watan Rabi'ul‑Awwal, a lokaci guda da Makon Haɗin Kai. A wannan taro, malamai da masu tunani na Shi'a da Ahlus‑Sunna daga sassa daban‑daban na Iran da sauran ƙasashen duniya suna halarta.[12]
- Jami'ar ƙasa da ƙasa ta mazhabobin Musulunci .An kafa wannan jami'a ne domin koyar da dukkan mazhabobin fikihu da dokokin Musulunci ta hanyar kwatantawa. Babban ginin jami'ar yana Tehran, kuma tana da rassan jami'a a Zahedan, Sanandaj, da Bandar Abbas.[13]
- Cibiyar Binciken Nazarin Kusantar Mazhabobi. Wannan cibiyar tana da sassa uku na bincike:fikihu da doka, tarihi da sanin mazajen riwaya (Rijal),
Al‑ƙur'ani da hadisi. Ginin cibiyar yana Qom.[14]
- Wallafe‑wallafe. Daga cikin mujallun da ake bugawa akwai Risalat al‑Taƙrib, Risalatul al‑Islam, Thaƙafat al‑Taƙrib, Paike Taƙrib, da Andisheye Taƙrib.[15] A cikin manhajar ayyukan Majalisar Kusantar Mazhabobin Musulunci, an gabatar da littattafai 126 daga wallafe‑wallafen majalisar a Larabci da Farisanci.[16]
- Kamafnin dillancin labarai na Taƙrib. Wannan hukuma tana wallafa labarai game da batutuwan kusantar mazhabobi a duniyar Musulunci cikin Farisanci, Larabci, Turanci, Urdu, da Faransanci.[17]
Maƙaloli Masu Alaƙa
Majalisar Ahlul-Baiti Ta Duniya
Bayanin kula
- ↑ «درباره مجمع»، Majma Jahani Taƙrib Mazahib Islami.
- ↑ «درباره مجمع»، Majma Jahani Taƙrib Mazahib Islami.
- ↑ «درباره مجمع»،Majma Jahani Taƙrib Mazahib Islami.isar Duniya ta Kusantar da Mazhabobin Musulunci.
- ↑ «۱۵۰ سال تلاش برای تقریب مذاهب اسلامی بینالملل»، Shafin yanar gizon Mubahathat.
- ↑ «درباره مجمع»، Majma Jahani Taƙrib Mazahib Islami.
- ↑ «مجمع تقریب مذاهب بنا به درخواست شیعیان جهان از رهبری، تشکیل شد»، Kamfanin Dillancin Labarai na Jamhoriye Islami (IRNA).
- ↑ انتصاب شیخ محمد واعظ زاده به سمت دبیرکلی مجمع تقریب بین مذاهب اسلامی, Ofishin Hifze wa Nashre Asare Hazrate Ayatullahi Khamna'i.
- ↑ انتصاب حجتالاسلام والمسلمین تسخیری به سمت دبیرکلی مجمع تقریب مذاهب اسلامی، Ofishin Hifze wa Nashre Asare Hazrate Ayatullahi Khamna'i.
- ↑ انتصاب حجتالاسلام والمسلمین اراکی به سمت دبیرکلی مجمع تقریب مذاهب اسلامی، Ofishin Hifze wa Nashre Asare Hazrate Ayatullahi Khamna'i.
- ↑ انتصاب حجتالاسلام حمید شهریاری به دبیرکلی مجمع تقریب مذاهب اسلامی، Ofishin Hifze wa Nashre Asare Hazrate Ayatullahi Khamna'i.
- ↑ فعالیتهای معاونتهای مجمع جهانی تقریب مذاهب اسلامی-معاونت بینالملل، Majma Jahani Taƙrib Mazahib Islami.
- ↑ «۱۵۰ سال تلاش برای تقریب مذاهب اسلامی بینالملل»، Shafin yanar gizon Mubahathat.
- ↑ «دانشگاه مذاهب اسلامی», Majma Jahani Taƙrib Mazahib Islami.
- ↑ «پژوهشگاه مطالعات تقریبی»، Majma Jahani Taƙrib Mazahib Islami.
- ↑ «انتشارات مجمع جهانی تقریب»، Majma Jahani Taƙrib Mazahib Islami.
- ↑ «مجموعه آثار مجمع جهانی تقریب مذاهب اسلامی»، Cibiyar Tahƙiƙate Kwamfuyari Ulume Islami.
- ↑ «درباره ما»، Kamfanin Dillancin Labarai na Taƙrib.
Nassoshi
- «انتصاب شیخ محمد واعظزاده به سمت دبیرکلی مجمع تقریب بین مذاهب اسلامی»، (Naɗa ShaikMuḥammad Wa'iz zadeh a matsayin Sakataren Gudanarwa na Majalisar Duniya Ta Kusantar Mazhabobin Musulunci (Majma' Taƙrib baina Mazahib Islamiyya), Ofishin Adana da Wallafa Ayyukan Mai Girma Ayatullahi Khamna'i , an duba a ranar 22 Nuwamba 2020M.
- «انتصاب حجتالاسلام والمسلمین تسخیری به سمت دبیرکلی مجمع تقریب مذاهب اسلامی»، (Nada Hujjatul‑Islam wal‑Muslimin Taskhiri a matsayin Sakatare Janar na Majalisar Kusantar Mazhabobin Musulunci), Ofishin Adana da Wallafa Ayyukan Mai Girma Ayatullahi Khamna'i , an wallafa a ranar 22 Satumba 2001, an duba a ranar 22 Nuwamba 2020M.
- «انتصاب حجتالاسلام والمسلمین اراکی به سمت دبیرکلی مجمع تقریب مذاهب اسلامی»، (Naɗa Hujjatul‑Islam wal‑Muslimin Araki a matsayin Sakataren Janar na Majalisar Duniya Ta Kusantar Mazhabobin Musulunci), Ofishin Hifze wa Nashre Asare Hazrate Ayatullahi Khamna'i, an wallafa a ranar 14 Yuli 2012, an duba a ranar 22 Nuwamba 2020M.
- «انتصاب حجتالاسلام حمید شهریاری به دبیرکلی مجمع تقریب مذاهب اسلامی»، (Naɗa Hujjatul‑Islam Hamid Shahriyari a matsayin Sakataren Janar na Majalisar Kusantar Mazhabobin Musulunci),Ofishin Hifze wa Nashre Asare Hazrate Ayatullahi Khamna'i, an wallafa a ranar 15 Disamba 2019, an duba a ranar 22 Nuwamba 2020M.
- «۱۵۰ سال تلاش برای تقریب مذاهب اسلامی بینالملل»، (Shekaru na ƙoƙari domin kusantar da mazhabobin Musulunci a matakin ƙasa da ƙasa), Mubahathat, an wallafa a ranar 15 Disamba 2014, an duba a ranar 22 Nuwamba 2020M.
- «درباره ما»، (Game da mu), Hukumar Labarai ta Taƙrib, an duba a ranar 22 Nuwamba 2020M.
- «جمع تقریب مذاهب بنا به درخواست شیعیان جهان از رهبری، تشکیل شد.»، (Majalisar Duniya Ta Kusantar Mazhabobin Musulunci ta samu kafuwa ne bisa roƙon mabiya mazhabar Shi'a na duniya ga Jagoran Juyin Juya Hali), Hukumar Labarai ta Jamhoriye Islami, an wallafa a ranar 25 Disamba 2019, an duba a ranar 16 Nuwamba 2020M.
- «مجموعه آثار مجمع جهانی تقریب مذاهب اسلامی»، (Taron Ayyukan Majalisar Duniya Ta Kusantar Mazhabobin Musulunci ta Duniya), Markaze Tahƙiƙat Kwamfuyatari Ulume Islami, an wallafa a ranar 22 Disamba 2015, an duba a ranar 22 Nuwamba 2020M.
- «انتشارات مجمع جهانی تقریب.»، (Gidan Buga Littattafai na Majalisar Duniya Ta Kusantar Mazhabobin Musulunci), Majma Jahani Taƙrib Mazahib Islami, an duba a ranar 22 Nuwamba 2020M.
- «دانشگاه مذاهب اسلامی.»، (Jami'ar Mazhabobin Musulunci), Majma Jahani Taƙrib Mazahib Islami, an duba a ranar 22 Nuwamba 2020M.
- « درباره مجمع»، (Game da Majalisa), Majma Jahani Taƙrib Mazahib Islami, an duba a ranar 22 Nuwamba 2020M.
- فعالیتهای معاونتهای مجمع جهانی تقریب مذاهب اسلامی-معاونت بینالملل.، (Ayyukan Mataimakan Sassa na Majalisar Duniya Ta Kusantar Mazhabobin Musulunci – Mataimakin Sashen Harkokin Ƙasashen Waje), Majma Jahani Taƙrib Mazahib Islami, an duba a ranar 22 Nuwamba 2020M.
- .پژوهشگاه مطالعات تقریبی»، (Cibiyar Binciken Nazarin Taƙribi (kusantar mazhabobin Musulunci).), Majma Jahani Taƙrib Mazahib Islami, an duba a ranar 22 Nuwamba 2020M.
