Daƙiƙa:Cibiyar Da'iratul Ma'arif Na Fiƙihun Musulunci Bisa Mazhabar Ahlul‑Baiti (A.S)
(Canja hanya daga Cibiyar Da'iratul Ma'arif Na Fiƙihun Musulunci)
![]() Bajon Wannan Cibiya | |
| Kafawa | 1990M |
|---|---|
| Waɗanda suka kafa | Sayyid Mahmud Hashimi Shahrudi |
| Ƙarƙashin | Ayatullahi Khamna'i |
| Nau'in ayyuka | Koyarwa •Bincike |
| Faɗaduwar aiki | Cikin gida |
| Manufofi | Da'iratul Ma'arif na Fiihun Musulunci • Bincike da wallafa littattafan da suka shafi Shi'a |
| Ayyuka | Shirya Da'iratul Ma'arif na Fiƙhun Musulunci • Wallafa littattafai • Kafa Cibiyar Musulunci ta Binciken Al‑Ghadir • Wallafa Mujallar Fiƙihun Ahlul Baiti (A.S) |
| Wuri | Qum |
| Hali | Tana kan aiki |
| Rubuce-rubuce | Kundin Ilimi Na Rubuce-rubucen Fiƙihun Shi'a • Farhange Fiƙhe Farsi •Muwsu'atul Al‑Fiƙhi Al‑Islami•Muwsu'at al‑Fiƙhi Al‑Islami al‑Muƙaran |
| Adireshin yanar gizo | http://afiqh.ir |
Cibiyar Da'iratul Ma'arif na Fiƙihun Musulunci bisa Mazhabar Ahlul‑Baiti (A.S) wata cibiyar bincike da koyarwa ce a fannonin fiƙihu, usulul fiƙhi da ilmin kalam, wadda take a birnin Qum. An kafa wannan cibiyar ne bisa umarnin Ayatullahi Sayyid Ali Khamna'i, jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran, kuma a ƙarƙashin kulawar Sayyid Mahmud Hashimi Shahrudi a shekarar 1369Sh (1990M).
Manufar wannan cibiyar ita ce shirya Da'iratul Ma'arif na fiƙihun Musulunci (Kundin Ilimomin Fiƙihu Na Musulunci) tare da gudanar da bincike da wallafa littattafan da suka shafi Shi'a. A cikin wannan tsari ta riga ta wallafa Da'iratul Ma'arif na Fiƙihun Musulunci da harsunan Larabci da Farisanci. A halin yanzu, Hasan Nazari Shahroudi ne ke rike da shugabancin wannan cibiyar.
Gabatarwa
Cibiyar Da'iratul Ma'arif na Fiƙhun Musulunci bisa Mazhabar Ahlul‑Baiti (A.S) wata cibiyar ilimi da al'adu ce,[1] wadda ke gudanar da ayyuka a fannonin bincike da koyarwa a bangarorin fiƙihu, usulul fiƙhi da ilmin kalam.[2] An kafa wannan cibiyar a shekarar 1369Sh (1990M) bisa umarnin Sayyid Ali Khamna'i , jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran, kuma tare da jagorancin Sayyid Mahmud Hashimi Shahrudi, wanda malamin fiƙihu ne.[3]
Bayan rasuwar Hashimi Shahroudi, Sayyid Ali Rida Ha'ri, daya daga cikin mambobin Jama'atul Mudarrisin na Hauzar Ilimi ta Qum, ya karɓi shugabancin cibiyar a watan Ordibeheshti na shekara ta 1398Sh (Mayu 2019M). Sai dai ya rasu sakamakon rashin lafiya a 27 ga Tir, 1398Sh (18 Yuli 2019M).[4] Daga baya kuma, a watan Mordad na shekara ta 1398Sh (Agusta 2019M), Hassan Nazari Shahroudi, mamba a Jama'at‑e Mudarrisin na Hauzar Ilmi ta Qum, ya samu nadin shugabancin wannan cibiyar daga Sayyid Ali Khamna'i.[5]
Wannan cibiyar tana a birnin Qum, a kusa da maƙabartar shahidai ta Ali Bin Jafar.[6]
Manufofi
Mafi muhimmancin manufofi da ayyuka na Cibiyar Da'iratul Ma'arif na Fiƙihun Musulunci bisa tsarin kundinta na kafa sun haɗa da:
- Shirya cikakken kundin fiƙihun Musulunci (Da'iratul Ma'arif) a kan dukkan babuka, ra'ayoyi, da rubuce‑rubucen malamai na mazhabar Shi'a.
- Bincike da rubuta batutuwan da suka shafi fiƙihun Shi'a, kamar su tarihin fiƙihun Musulunci, fiƙihun kwatantawa (Fiƙihu na muƙaran), muhawarorin tattalin arziƙin Musulunci, sabbin mas'aloli na zamani, da kuma shirya ƙamus na fiƙihu.
- Bincike, bugu, da wallafa muhimman tushe na fiƙihun Musulunci.
- Wallafa mujallolin ƙwarewa a fannonin fiƙihu, da suka dace da buƙatun yau na al'umma Musulmi.
- Wallafa littattafai da maƙaloli cikin harsunan duniya da ake yawan amfani da su, domin gabatar da mazhabar Shi'a ga duniya.[7]

Ayyuka da Wallafe‑wallafe
An bayyana ayyukan Cibiyar Da'iratul Ma'arif Fiƙhun Musulunci kamar haka:
- Rubuta Da'iratul Ma'arif na Fiƙihun Musulunci bisa mazhabar Ahlul Baiti (A.S). Manufar wannan aiki shi ne tattara bayanan fiƙihu da suke warwatse a wurare daban‑daban, a tsara su ta hanya ta musamman domin sauƙaƙa amfani da su ga masana da kuma waɗanda ba masana ba.
- Kafa Cibiyar Binciken Musulunci ta Al‑Ghadir domin kare akidar Shi'a. Wannan cibiyar ta wallafa ayyuka da dama, daga cikinsu har da gyarawa, tantancewa da buga littafin Al‑Ghadir a cikin juzu'i goma sha biyu.
- Buga mujallar "Fiƙhun Ahlul-Baiti (A.S)" a harsuna biyu: Farisanci da Larabci.
- Gudanar da bincike a harshen Farisanci, wanda ya haɗa da sake wallafa da raya muhimman littattafan Shi'a, da kuma rubuta ƙamus na kalmomin fikihu. Wallafe‑wallafe da Ayyukan da Cibiyar ta Samar.[8]
Wannan cibiyar ta rubuta, ta bincika kuma ta wallafa fiye da littattafai da dama, daga cikinsu akwai:
- Farhange Fiƙh Farsi (juzu'i 6),
- Muwsu'atul Fiƙhil Islami (juzu'i 54),
- Muwsu'atul Fiƙhil Islami Al‑Muƙaran (Fiƙhu na kwatance) (juzu'i 42),
- Muwsu'atul Ghadir (juzu'i 14),
- Al‑Mu'ujam Al-Fiƙhi na littattafan Sheikh Ɗusi(juzu'i 6),
- Kundin Ilimi Na Ayyukan Fiƙihun Shi'a,
- Mu'ujam Fiƙhi Al‑Jawahir,
- Attashayyu: Nasha'atuhu Wa Ma'alimuhu,
- Nasha'atush Tashattu Wash Shi'a,
- Mafhumut Taƙiyya Fil Fikril Islami,
- Mafhumul Bada Fil Fikril Islami,
- Ibn Taimiyya: Hayatuhu Wa Aƙa'iduhu,
- Limaza Ana Shi'i?,
- Ibn Taimiyya Fi Suratihil Haƙiƙiyya,
- Al-Wahabiyya Fi Suratihil Haƙiƙiyya,
- Ala Khuɗa Ahlul-Baiti (A.S),
- Fadak Fit Tarikh,
- Al- Imama Wa Ahlul Baiti (A.S),
- Bahsu Haula Al-Mahdi (A.S),
- Al-Ijtihadi Wat Taƙlid,
- Buhus Fi Ilmil Usul,
- Mazhabul Imamiyya,
- Ide Ghadir Dar Islam,
- Muntakhabu Fada'ilin Nabiyyi Wa Ahlul-Baitihi,
- Dirasatu Fi Siratin Nabawiyya,
- Al-Wajiz Fil Imama Wal Wilaya,[9]
Bayanin kula
- ↑ «Gozareshha: Mu'assese-ye Dayerat al-Ma'aref-e Fiƙhe Islami bar Mazhabe Ahle Baiti (A.S),» Sh. 41.
- ↑ «مؤسسه دایرةالمعارف فقه اسلامی بر مذهب اهل بیت(ع)»، Shafin Intanet na Mataimakiyar Bincike ta Hauzocin Ilimi.
- ↑ «Gozareshha: Mu'assese-ye Dayerat al-Ma'aref-e Fiƙhe Islami bar Mazhabe Ahle Baiti (A.S),» Sh. 38.
- ↑ «مختصری از زندگینامه آیت الله سید علیرضا حائری»، Shafin Intanet na Mataimakiyar Bincike ta Hauzozin Ilimi.
- ↑ «انتصاب رئیس مؤسسه دایرةالمعارف فقه اسلامی بر مذهب اهل بیت(ع)»، Shafin Yaɗa Labarai na Ofishin Ayatullahi Khamna'i..
- ↑ «آدرس مؤسسه»،Shafin Intanet na Cibiyar Kundin Ilimin Fikhun Musulunci Bisa Mazhabar Ahlul Baiti (A.S).
- ↑ «درباره مؤسسه»، Shafin Intanet na Cibiyar Kundin Ilimin Fikhun Musulunci Bisa Mazhabar Ahlul Baiti (A.S).
- ↑ «Gozareshha: Mu'assese-ye Dayerat al-Ma'aref-e Fiƙhe Islami bar Mazhabe Ahle Baiti (A.S),» Sh. 38-40
- ↑ «Gozareshha: Mu'assese-ye Dayerat al-Ma'aref-e Fiƙhe Islami bar Mazhabe Ahle Baiti (A.S),» Sh. 40-41
Nassoshi
- «انتصاب رئیس مؤسسه دایرةالمعارف فقه اسلامی بر مذهب اهل بیت(ع)», (Naɗa Shugaban Cibiyar Kundinn Fiƙihun Musulunci bisa Mazhabin Ahlul Baiti (A.S)), Gidan Yanar Gizon Ofishin Jagoran Maɗaukaki, ranar dubawa: 6 Satumba 2020M.
- «گزارشها: مؤسسه دایرة المعارف فقه اسلامی بر مذهب اهل بیت(ع)»،, (Rahotanni: Cibiyar Da'iratul Ma'arif ta Fiƙhun Musulunci bisa Mazhabar Ahlul Baiti (A.S)), Mujallar Farhang‑e Kauthar, lamba ta 13, Afrilu 1998M.
- «مختصری از زندگینامه آیت الله سید علیرضا حائری»،, (Taƙaitaccen bayani daga tarihin rayuwar Ayatullah Sayyid Ali Rida Ha'iri), Shafin yanar gizo na Jami'ar Malaman Hawzar Ilmiyya ta Qum, ranar da aka ziyarta: 6 Satumba 2020M.
- «مؤسسه دائره المعارف فقه اسلامی بر مذهب اهلبیت(ع), (Cibiyar Da'iratul Ma'arif ta Fiƙhun Musulunci bisa Mazhabar Ahlul Baiti (A.S)), shafin yanar gizo na Mataimakiyar Sashen Bincike na Hawzozin Ilimi (Hauza IlimiyyaRanar da aka ziyarta: 6 Satumba 2020M.
