Jump to content

Ayar Wasila

Daga wikishia
Ayar Wasila
bayanan aya
sunan ayaAyar Wasila
akwai shi cikin suraMa'ida
lambar aya35
juzu’i6
bayanan abin da yake ciki
wurin saukaMadina
maudu’iAƙida
game daTsani da madafa zuwa ga Allah
sauraKira zuwa taƙawa da jihadi


Ayar wasila, (Larabci: الآية الخامسة والثلاثون من سورة المائدة) suratul ma'ida aya ta 35, aya ce da take bayyana samun rabauta ya dogara da sharuɗɗa uku: Taƙawa, neman wasila (Tsani) zuwa ga Allah da jihadi cikin tafarkin Allah.

Abin da ake nufi da wasila shi ne duk wani aiki da yake zama sababi da sanadin samun kusancin bawa zuwa ga Allah. Malaman tafsiri tare da jingina da riwayoyi, sun lissafa adadin abubuwa da suke amsa sunan wasila, daga jumlarsu akwai aiki nagari, tawassuli da Annabi da Ahlul-baiti da kuma rantsuwa da Allah da muƙaminsu da matsayinsu.

Nassi Da Tarjamar Ayar

Aya ta 35 suratul ma'ida wace aka fi sani da ayar wasila.[1] cikin wannan aya an yi amfani da kalmar wasila, kuma domin tabbatar da halascin tawassuli an jigina da wannan aya.[2]

A cikin wannan aya taƙawa, wasila da jihadi cikin tafarkin Allah an bayyana su matsayin hanyoyi uku na samun ceto da rabauta.[3] A ra'ayin ba'arin malaman tafsiri, jihadi a cikin wannan aya ya haɗo da jihadi tare da kafirai da kuma jihadin yaƙar biyewar son zuciya duka suna daga abubuwa da ake kira wasila.[4]

یا أَیهَا الَّذِینَ آمَنُوا اتَّقُوا اللهَ وَابْتَغُوا إِلَیهِ الْوَسِیلَةَ وَجَاهِدُوا فِی سَبِیلِهِ لَعَلَّکمْ تُفْلِحُونَ
Ya ku waɗanda suka yi imani! Ku ji tsoron Allah, ku nemi hanyar kusanci zuwa gare Shi, kuma ku yi jihadi a cikin hanyarSa, domin wataƙila ku rabauta.



(Quran: Ma'ida: Aya ta 35)


Abin da Ake Nufi Da Wasila

Ana kiran duk wani aiki da yake zama sababi da sanadin samun kusanci zuwa ga Allah[5] Allama Ɗabaɗaba'i daga malaman tafisiri na Shi'a, ya fassara wasila da duk wani nau'in alaƙa ta ruhaniyya tsakanin mutum da ubangiji wace take samuwa ta hanyar ibada kuma ilimi da aiki ana lissafa su abubuwan da suke lazimtar wannan alaƙa.[6]

Abubuwa Da Suke Kasancewa Wasila

A cikin riwayoyin Shi'a, Annabi,[7] Imam Ali (A.S),[8] da Ahlul-Baiti[9] an ambace su a matsayin wasila da tsani zuwa ga Allah, a cikin Tafsirin Al-Amsal tare da jingina da wata riwaya daga Imam Ali (A.S),[10] ayyuka misalin sallah, azumi, ciyarwa, sadaka, ambaton Allah, hajji, umara, imani da Allah da Annabi, jihadi da sadar da zumunci ana lissafa su daga wasila.[11] Haka nan ceton Annabawa, Imamai da salihai, biyayya gare su da rantsuwa da Allah albarkacin muƙamansu da matsayinsu (Musamman ma Annabi da Ahlul-Baiti) suma suna daga cikin wasila zuwa ga Allah.[12]

A cewar marubucin Tafsir Aɗyabul Bayan, wasila tana haɗowa da dukkanin aƙidu, kyawawan halaye da ayyuka nagari da Kur'ani, Annabi (S.A.W), Ahlul-Baiti ko muƙamansu da matsayinsu, kuma suna kasancewa mafi cikar abin da yake amsa sunan wasila tsani zuwa ga Allah.[13]

Bayanin kula

  1. Dubi Arefi da Najibi,Barrasi Taɗbiƙi Aye Wasila Az Nazre Manabi Tafsiri Fariƙaini, shafi. 59, taken labarin.
  2. Misali, duba Sobhani, Ayineh Wahabiyyat, Ofishin Daba’ar Musulunci, shafi na. 168.
  3. Makarem Shirazi, Tafsire Namune, 1371, juzu'i. 4, shafi. 364.
  4. Tabataba'i, Al-Mizan, 1390 AH, juzu'i. 5, shafi. 328.
  5. Tabarsi, Majma' al-Bayan, 1372 AH, juzu'i. 3, shafi. 293; Fakhr al-Razi, Al-Tafsir al-Kabir, 1420 AH, juzu'i. 11, shafi. 349.
  6. Tabataba'i, Al-Mizan, 1390 AH, juzu'i. 5, shafi. 328.
  7. Dubi Arefi da Najibi, Barrasi Taɗbiƙi Aye Wasile Az Nazre Manabi Tafsiri Fariƙaini, shafi. 66.
  8. Bahrani, Al-Burhan, 1415 AH, juzu'i. 2, shafi. 292.
  9. Kashani, Tafsir al-Mu'in, Ayatullah Mar'ashi Library, juzu'i. 1, shafi. 290.
  10. Ibn Shu'bah Harrani, Tuhf al-Uqol, 1404 AH, shafi na 149.
  11. Makarem Shirazi, Tafsire-Namune, 1371, juzu'i. 4, shafi. 364.
  12. Makarem Shirazi, Tafsire-Namune, 1371, juzu'i. 4, shafi. 366.
  13. Tayeb, Atyabul Al Bayan, 1378, juzu'i na 4, shafi na 375.

Nassoshi

  • Ibn Shu'bah Harrani, Hassan bn Ali, Tuhaf al-Uqol, Ali Akbar Ghaffari, Qum, Islamic Publications, 1404 H.
  • Bahrani, Sayyid Hashim bn Sulayman, Al-Burhan fi Tafsir al-Quran, Qum, Bissat Foundation, 1415H.
  • Sobhani, Ja'afar, A'yineh al-Wahhabiyyah, Qum, Islamic Publications Office, Beta.
  • Tabataba'i, Muhammad Hussein, Al-Mizan fi Tafsir Qur'an, Beirut, Al'alami Publications Foundation, 1390 AH.
  • Tabarsi, Fadl ibn Hassan, Majma' al-Bayan, Tehran, Nasser Khosrow, 1372H.
  • Tayyib, Abdul Hussein, Atyib al-Bayan fi Tafsir al-Quran, Tehran, Islam, 1378 AH.
  • Arefi, Mohammad Yunus da Mohammad Ali Najibi، «بررسی تطبیقی «آیه وسیله» از نظر منابع تفسیری فریقین»Karatun kwatankwacin Alqur'ani da Hadisi na 23, A lokacin sanyi 1403H
  • Fakhr Razi, Muhammad bn Omar, Al-Tafsir al-Kabir, Beirut, Dar Ihya al-Turat al-Arab, 1420H.
  • Kashani, Muhammad ibn Murtaza, Tafsir al-Mu'in, wanda Hossein Dargahi da Mahmoud Mar'ashi suka yi bincike, Qum, Laburare Ayatullah Mar'ashi Najafi, Beta.
  • Makarem Shirazi, Nasser, Tafsir Namune, Tehran, Darul Kutb al-Islamiya, 1371H.