Hadis Wasiyya
- Kar ku rude da Hadis Wisaya.
Maudu'i | Mahadi Goma Sha Biyu |
---|---|
Ya Fito Daga | Annabi (S.A.W) |
Asalin Marawaici | Imam Ali (A.S), Ibn Abbas, Abu Zar Gifari, |
Ingancin Isnadi | Hadis Da'ifi |
Madogaran Shi'a | Kitabul Al-gaiba Tusi |
Madogaran Ahlus-sunna | Sahihul Bukhari |
Mai ƙarfafawa Na Kur'ani | Babu |
Mai ƙarfafawa Na Riwaya | Babu |
Hadis Silsilatuz Zahab • Hadis Saƙlaini • Maƙbulatu Umar Bin Hanzala • Hadis Ƙurbu Nawafil • Hadis Mi'iraj • Hadis Wilaya • Hadis Wisaya • Hadis Junud Aƙli Wa Jahal • Hadis Shajara |
Hadis Wasiyya, (arabic: حديث الوصية) wata riwaya ce wace cikinta akai Magana kan Mahadi Goma sha biyu wadanda za su kasance magadan Imam Mahadi (A.S) a bayansa wannan riwaya ta zo cikin littafin Algaiba na Shaik Tusi.
Ahmad Alhassan Shugaban Kungiyar Ansarul Mahadi ya jingina da wannan riwaya cikin ayyana kansa matsayin `dan Imam Mahadi amma ta hanyar wasida da tsani, Mabiyansa sun kira shi da Mahadi na farko bayan Imam Mahadi (A.F).
Malaman Shi'a sun yi watsi da wannan gurguwar Fahimta da Ahmad Alhassan ya yi daga wannan riwaya sun kuma bayyana cewa abin da ya fahimata baya dacewa da Mashhur din Riwayoyi da ingatattu, wasu ba'arin Masu zurfafa bincike tare da bincike kan isnadi da abin da hadisin ya tattaro sun yi suka kan hadisin daga cikin sukan su kansa akwai batun raunin isnadi, haka kuma yana cin karo da hadisan da suka takaice magadan annabi (S.A.W) cikin mutane goma sha biyu
Gabatar da hadisin da kuma abin da ya tattaro
Hadis Wasiyya wata riwaya da ta zo cikin littafin Algaiba na Shaik Tusi da aka Nakalto ta daga Annabi[1] cikin hadis Wasiyya Annabin Muslunci (S.A.W) ya baiwa Imam Ali (A.S) labarin samuwar Imamai goma sha biyu bayansa kuma sunayensu iri daya da sunayen Imaman Shi'a goma sha biyu, sannan kuma ya bashi labari kan samuwar wasu Mahadi goma sha biyu daban bayan wafatin Imam Mahadi (A.F) za su kasance magadansa[2] ba'arin Hadisin ya kasance da wannan Maudu'in cikin wannan sharhin na kasa: Bayansu (Imamai goma sha biyu) za a samu Mahadi goma sha biyu, lokacin da Imami na goma sha biyu ya yi wafati, zai mika Halifanci ga `dansa wanda shi ne Makusanci na farko, wannan `dan nasa yana da sunaye uku, daya daga cikin sunansa irin sunana ne, dayan kuma irin sunan Babana ne shi ne Abdullahi da Ahmad, sannan sunansa na uku shi ne Mahadi, kuma shi Mumini ne na farko[3] Wannan hadisi shi ne babbar madogarar Ahmad Alhassan Shugaban Kungiyar Ansarul Mahadi kan tattabatar Mahadi goma sha biyu bayan Imam Mahadi (A.F)[4] hakika wannan mutum tare da jingina da wannan hadisi ya yi da'awar cewa shi ne Mahadi na farko cikin jerin Mahadi sha biyu da za su zo bayan Imam Zaman (A.F)[5] Malaman Shi'a da farko dai ba su ganin ingancin wannan riwaya ta fuskanin isnadi, na biyu kuma ba su karbi abin da ya fahimta daga riwayar ba[6]
Jinginar da Ahmad Alhassan yayi da Riwayar
Ahamd Alhassan tare da jingina da hadisin Wasiyya yana cewa Mahadi Goma sha biyu za su zo bayan Imam Zaman (A.F) kuma shi ne na farkonsu[7] kari kan wannan bisa la'akari da Kalmar Ibnunu (`dansa) da ya zo cikin riwayar sai ya shelanta kansa matsayin `da ga Imam Mahadi amma ta hanyar wasida da tsani[8] Kan wannan asasi ne yayi da'awar rawar da zai taka gabanin Bayyana da kuma lokacin Daular Imam Zaman (A.F) da bayanta[9] Mahangar Malaman Shi'a Malaman Shi'a sun bayyana cewa Hadis Wasiyya ya sabawa shahararrun riwayoyi da ingantattu, daga jumlarsu: Ɗabarasi Malamin tafsiri a karni na biyar, Irbili Malamin Hadisi a karni na bakwai, Allama Majlisi Malamin hadisi a karni na goma sha biyu[10] Ɗabarasi da Irbili sun ce wannan riwaya ta saba da ingatattun riwayoyi da suke bayyana cewa bayan Imam Mahadi (A.F) ba za a sake samun wata Daula ba[11]
Ishkali Da Suka Kan Hadis Wasiyya
Wasu Ba'arin Masu zurfafa bincike sun suka kan wannan hadisi kamar yanda zai zo a kasa:
- Wannan ruwayar, Khabar Wahid ce, kuma khabarul wahid za to ake kan tabbatarsa kuma hadisi ne abin tuhuma. Don haka ba ya yiwuwa a tabbatar da Akidu da shi ba[12]
- kan asasin wannan riwaya ya bayyana cewa Magadan Annabi (S.A.W) Mutum 24 ne wanda haka ya saba da Kadaice Mutum Sha biyu a matsayin Wasiyyai[13]
- Ya ci karo da ruwayoyin da suke bayyana Imam Zaman (AS) a matsayin waliyyi na karshe[14]
- Haka kuma wannan riwaya ta ci karo da riwayoyi masu yawan gaske da suka bada labarin Raja'a, Marawaitansa sun kasance Majhulai ne ba sansu ba , wanda haka na nufi ko cin karo ba zai iya yi da ingantattun hadisai ba[15]
Bayanin kula
- ↑ Sheikh Tusi, Al-Ghaibah, 1411 AH, shafi na 151-150.
- ↑ Sheikh Tusi, Al-Ghaibah, 1411 AH, shafi na 151-150.
- ↑ Sheikh Tusi, Al-Ghaibah, 1411H, shafi na 150.
- ↑ Mujtahid Sistani, Lauhu wal-Kalam, Darul Tafsir, shafi na 13.
- ↑ Mohammadi Hoshiar,Darsenameh Nakadi wa Barasi Juryan Ahmad Al-Hassan, 1396, shafi na 37-39.
- ↑ Misali duba Allameh Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403H, juzu'i na 53.Har Aamili, Al-Iqaz Man Al-Hujaa, 1362, shafi na 368.
- ↑ Ahmad al-Hassan, Al-Juab al-Munir, juzu'i na 1, shafi na 38.
- ↑ Mohammadi Hoshiar, Darsenameh Anakdi wa Barasi Juryan Ahmad Al-Hassan, 1396, shafi na 37-39.
- ↑ Mohammadi Hoshiar, Darsenameh Anakdi wa Barasi Juryan Ahmad Al-Hassan, 1396, shafi na 37-39
- ↑ Tabarsi, Elamul Alwara, 1417 AH, juzu'i na 2, shafi na 295; Erbali, Kashf al-Ghumma fi Marafah al-A'imah, 2001, juzu'i na 2, shafi.467; Alameh Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 53, shafi na 150; Har Ameli, Al-Iqaz Man Al-Hujaa, 1362, shafi na 368; Har Aamili, al-Faadi al-Tawsiyyah, 1403H, shafi na 115.
- ↑ Tabarsi, Elamul Alwara, 1417 AH, juzu'i na 2, shafi na 295; Erbali, Kashf al-Ghumma fi Marafah al-A'imah, 2001, juzu'i na 2, shafi.467; Ameli Nabati, Al-Sarat Al-Mustaqim, Juzu’i na 2, 1384H, shafi na 186.
- ↑ Al Mohsen, Al-Arrad Al-Qasim, 1434H, shafi na 36.
- ↑ Al Mohsen, Al-Arrad Al-Qasim, 1434 AH, shafi na 36; Mujtahid Sistani,Lauhu wal Alkalam, Darul Tafsir, shafi na 129
- ↑ Shahbazian, Mohammad, Rahe Afsaneh, 1396, shafi na 138; Mohammadi Hoshiar,Darsu nameh Nakadi wa Barasi Juryan Ahmad Al-Hassan, 1396, shafi na 150.
- ↑ Mujtahid Sistani, Lauhu wa Kalam
Nassoshi
- Aamili Nabati, Ali Ibn Yunus, Al-Sarat Al-Mustaqim zuwa Al-Maghtire al-Taqadim, bugun Mikhail Ramadan, Najaf, Al-Maktab Al-Haydariyya, bugun farko, 1384H.
- Ahmad al-Hassan, Al-Juab al-Munir Ibr al-Athir, bugun Ansar al-Imam al-Mahdi.
- Al-Mohsen, Ali, Al-Arrad al-Qasim, Najaf, Cibiyar Nazarin Musamman ta Imam Al-Mahdi, 1434H.
- Allameh Majlisi, Muhammad Baqir, Bihar al-Anwar, Beirut, Dar Ahya al-Trath al-Arabi, 1403 AH.
- Erbali, Ali Ibn Isa, Kashf al-Ghumma fi Marafah al-Aima, tare da gabatarwar Jafar Sobhani da Seyyed Hashem Rasouli Mahalati, Tabriz, Bani Hashemi Publishing House, 1381.
- Har Amili, Mohammad Bin Hasan, Al-Iqaz Man Al-Hujjaa Bal Burhan Ali Al-Raj'a, editan Seyyed Hashim Rasouli Mahalati, Ahmad Jannati, ya fassara, Tehran, Navid Publications, 1362.
- Hurrul Amili, Muhammad Bin Hasan, Isbatul Al-Hudat Bin-Nususi wal-Mujizat, wanda Alauddin Al-Alami ya buga, Beirut, Al-Alami Publishing House, 1425H/2004 Miladiyya.
- Mohammadi Hoshiar, Ali, Darsenameh Nakadi wa Barasi Juryan Ahmad al-Hassan al-Basri, Qom, Tuli Publications, 2016.
- Mujtahid Sistani, Mahdi, Louhu wa Qalam: Yin nazarin ruwayar da aka fi sani da Will a cikin littafin Al-Ghaibah na Sheikh Tusi, Qum, Dar al-Tafsir, Bita.
- Shahbazian, Mohammad, Rahe Afsana, Qom, wallafe-wallafen cibiyar kwararrun Mahdavit na Seminary Qum, 2016.
- Sheikh Tusi, Muhammad bin Hassan, Al-Ghaibah, wanda Abdullah Tehrani ya yi bincike da Ali Ahmad Naseh, Qum, Cibiyar Nazarin Musulunci, 1411H.
- Tabarsi, Fazl bin Hasan,Elamul Al-Wara' with Allam Al-Hadi, Qum, Al-Bayt Lahiya Al-Tarath Foundation, 1417 AH.