Jump to content

Daƙiƙa:Musuluntar Da Ilimomin Ɗan Adam

Daga wikishia

Musulmantar da ilimomin ɗan adam wata manufa ce da ke nufin sake tsara da kuma gina waɗannan fannoni na ilimi bisa tushen tunani da ƙa'idojin Musulunci. Manufarta ita ce a daidaita fannoni irin su ilimin halayyar ɗan‑adam da ilimin zamantakewa da fahimtar duniya ta Musulunci.

Wannan tunani ya ƙara samun karɓuwa a Iran bayan juyin juya halin Musulunci a shekarar 1979M, inda aka fara mai da shi wani muhimmin ɓangare na manufofin al'adu da na ilimi. Saboda haka, wasu hukumomi kamar Majalisar Ƙolin Juyin Juya Halin Al'adu an ɗora musu alhakin tsara shirye‑shirye da matakan da za su taimaka wajen aiwatar da wannan buri.

Duk da haka, wannan ra'ayi yana da masu goyon baya da kuma masu adawa da shi. Masu goyon baya,kamar Imam Khomaini, Sayyid Ali Khamna'i, Murtada Muɗahhari da Sayyid Muhammad Baƙir Sadar, suna ganin cewa wannan hanya za ta taimaka wajen tabbatar da ƴancin kai na ilimi da al'adu ga al'ummomin Musulmi. A gefe guda kuma, masu suka kamar Abdul-Karim Sorush da Musɗafa Malekiyan suna ganin cewa ƙoƙarin jingina ilimi da wani tsari na addini ba ya dace da yanayin ilimi na duniya, domin a ganinsu ilimi abu ne da ya kamata ya kasance na kowa kuma ba ya taƙaita ga wata al'ada ko ayyananniyar aƙida ba.

Menene Shi Da Kuma Matsayinsa

Musulmantar da ilimomin ɗan adam a asali ƙoƙari ne na sake fassara da sake gina ilimomin ɗan adam bisa koyarwar Musulunci, domin a daidaita fannoni kamar ilimin halayyar ɗan adam, ilimin zamantakewa, gudanarwa da tattalin arziki da hangen duniya na Musulunci.[1] Ra'ayin musulmantar da ilimi ya ginu ne kan fahimtar cewa ilimi ba ya rabuwa da tasirin hangen duniya, kuma kowane tsarin sani yana dogara ne a kan wasu tushe na falsafa na musamman.[2]

Saboda ilimomin ɗan‑adam na zamani sun samo asali ne a cikin tsarin wayewar Yamma kuma an gina su bisa ra'ayin abu kawai da kuma girmama ɗan adam, ana ganin cewa wajibi ne a sake tsara su a cikin al'ummomin Musulmi domin su dace da tushen addini.[3]

A ra'ayin masu bincike, wannan hanya wadda asalinta ya samo tushe daga tunanin Sayyid Jamaluddin Asad Abadi da Muhammad Abduhu[4] ta ƙara bunƙasa bayan juyin juya halin Musulunci a Iran.[5] Haka kuma haɗa falsafar Girka da koyarwar Musulunci da masana falsafar Musulmi suka yi a tarihi ana ɗaukar sa a matsayin wani misali na irin wannan yunƙuri.[6]

Manufofin Musuluntar Da Ilimi A Iran

A Iran, bayan juyin juya hali, hukumomi da cibiyoyi daban‑daban da suka ɗauki alhakin aiwatar da manufar musuluntar da ilimomin ɗan adam. Majalisar Ƙolin Juyin Juya Halin Al'adu tun daga shekarun 1360 Shamsi (1982m) tana jagorantar wannan fanni, kuma ta ci gaba da bin wannan tsari ta hanyar kafa “Majalisar Ƙwararru ta Sauyi da Inganta Ilimomin Ɗan Adam” a shekarar 1388 Shamsi (2009M).[7]

Jami'o'i da cibiyoyin bincike kamar Cibiyar Kimiyyoyun Musulunci (Farhangistane Ulume Islami), Cibiyar Bincike ta Hauza da Jami'a, Jami'ar Imam Sadiƙ (A.S), Jami'ar Baƙirul Ulum (A.S), da Cibiyar Ilimi da Bincike ta Imam Khomaini su ma an kafa su ne da nufin bunƙasa ilimomin ɗan adam na Musulunci.[8]

Haka kuma, Cibiyar Tsarin Ci gaban Musulunci Ta Iran an ɗora mata alhakin tsara samfurori da tsare‑tsaren tunani na cikin gida a wannan fanni.[9]


Manufar musuluntar da ilimomin ɗan adam ta kuma bayyana a cikin manyan takardun manufofin ƙasa a Iran; daga cikinsu akwai Takardar Babban Sauyi na Asasi a Ilimi da Tarbiyya[10] shirye‑shiryen ci gaban ƙasa na shekaru biyar‑biyar,[11]Takardar Sauyi a Ilimomin ɗan Adam,[12] Taswirar injiniyancin al'adu ta ƙasa, [13]da kuma takardar jami'ar Musulunci.[14]

Matakan da aka ɗauka a aikace sun haɗa da sake duba littattafan da ake kowarwa a makarantu[15] ƙirƙirar sabbin fannoni na karatu kamar tattalin arzikin Musulunci[16] da ilimin halayyar ɗan adam na Musulunci,[17] gudanar da taruka na ilimi,[18] aiwatar da ayyukan bincike, [19] da kuma sanya ranar 12 ga watan De (2 Janairu 1844M) a matsayin ranar ilimomin ɗan adam na Musulunci.[20]

Sai dai duk da haka, wannan ra'ayi har yanzu yana cikin matakin tunani da tsara manufofi.[21] An kuma ambaci wasu dalilai da ke jawo jinkirin ci gaba a wannan fanni, kamar tsawon lokacin da ake buƙata wajen samar da ilimi na addini,[22] da kuma ƙarancin manyan masana.[23]

Masu Adawa Da Masu Goyon Bayan Musuluntar Da Ilimomi

Masu adawa da musuluntar da ilimomin ɗan adam suna ganin cewa ilimi abu ne na duniya baki ɗaya, kuma rarraba shi zuwa na Musulunci da wanda ba na Musulunci ba ba shi da hujja a mahangar ilimin sanin ilimi.[24] A ganinsu, addini yana aiki ne a fannonin aƙida da ɗabi'a,[25] kuma ba shi da ikon ba da amsa ga batutuwan gwaji da na zamantakewa.[26] Abdul-Karim Sorush, Mustafa Malikiyan[27] da Bijan Abdul-Karimi suna daga cikin masu sukar wannan ra'ayi, inda suke ganin haɗa ilimin gwaji da sanin addini abubuwabiyu ne masu warware juna.[28]

A gefe guda kuma, mutane kamar Imam Khomaini, Sayyid Ali Khamna'i, Sayyid Muhammad Baƙir Sadar, Murtada Muɗahhari, Abdullahi Jawadi Amoli, Muhammad Taƙiyyu Misbahu Yazdi, Ali Shari'ati, Sayyid Munirud-dini Husaini , Sayyid Husaini Nasri, Muhammad Mahadi Mir Baƙiri, Ali Akbar Rashad, Ali Rida A'arafi, Hamid Parsaniya da Abdul-Husaini Khosropana suna daga cikin masu goyon bayan wannan ra'ayi. Su na ganin musuluntar da ilimomin ɗan adam wata hanya ce ta samun ƴancin kai na al'adu da tunani ga al'ummomin Musulmi, da kuma kuɓuta daga dogaro da ilimin Yamma.[29][30]

« Muhyiddin Ha'iri Shirazi ya ce:

Ba za mu musanta ƙwarewar da ilimomin ɗan‑adam suke da ita ba. Karanta Alƙur'ani da kuma haddace shi ba tare da mutum yana da ikon yin tadabburi, fahimta mai zurfi da cikakkiyar basira ba, yana iya mayar da mutum mai iklasi kamar robot (Mutummutumi mai motsi). Don haka ba za mu iya zargin Yamma ba mu ce me ya sa suka ci gaba a ilimomin ɗanadam. Su kullum suna gudanar da bincike kuma suna samar da ilimomin ɗan adam. Mu kuma kullum muna fassara ne kawai, muna cin abin da aka riga aka shirya. Ya kamata mu ma mu biya farashin samar da ilimomin ɗan adam. Ba dabara ba ce su riƙa samarwa, mu kuma mu riƙa fassara abin da suka samar ba.

Maƙukar ba mu samar da ilimomin ɗan adam bisa tushen mu ba, kuma muka ci gaba da taƙaita kanmu ga fassara kawai, dole ne mu biya sakamakon hakan.[31]

»


.

Bayanin kula

  1. Ku duba: Khosrowpanah, Falsafe‑ye Olum‑eInsani, s.129; Sharifi, Rawesh‑shenasi‑ye Olum‑Insani‑ye Islami, s.49–50; Alwani, Islamiyyat al‑Ma‘rifa bayna al‑Ams wa al‑Yawm, s.19
  2. Golshani, Olgu‑ye Islami‑Irani‑ye Tose‘e‑ye Elm, s. 96.
  3. Ku duba: Mowahhed Abtahi, Tahlil bar Andishe‑haye Elm‑e Dini dar Jahan‑e Islam, s.12–14.
  4. Mowahhed Abtahi, Tahlil bar Andishe‑haye Elm‑e Dini dar Jahan‑e Islam, s.35–46.
  5. Sanade Tolid‑e Olum‑eInsani‑ye Islami, s.10–12.
  6. Tahiriyan«مدلی برای تحول و اسلامی سازی علوم با اقتباس از شکل گیری فلسفه اسلامی در دوران اوج تمدن اسلامی» Shafin Cibiyar Bincike ta Al'adu da Tunani na Musulunci."
  7. «آیین‌نامه تشکیل شورای تخصصی تحول و ارتقاء علوم انسانی»، Shafin yanar gizon Cibiyar Bincike ta Majalisar Shawarar Musulunci.
  8. Mowahhed Abtahi, Tahlil bar Andishe‑haye Elm‑e Dini dar Jahan‑e Islam, s.48.
  9. «وظایف مرکز»،Shafin yanar gizon Cibiyar Tsarin Ci Gaban Musulunci da Iran..
  10. «مصوبه «سند تحول بنیادین آموزش و پرورش»Cibiyar Bincike ta Majalisar Shawarar Musulunci..
  11. «قانون برنامه پنجساله پنجم توسعه جمهوری اسلامی ایران»،Cibiyar Bincike ta Majalisar Shawarar Musulunci.«قانون برنامه پنج ساله ششم توسعه اقتصادی، اجتماعی و فرهنگی جمهوری اسلامی ایران»،Cibiyar Bincike ta Majalisar Shawarar Musulunci.«قانون برنامه پنج ساله هفتم پیشرفت جمهوری اسلامی ایران»Cibiyar Bincike ta Majalisar Shawarar Musulunci.
  12. «رئیس شورای تحول و ارتقاء علوم انسانی گفت: سند تحول علوم انسانی؛ بستری برای پیشرفت اسلامی-ایرانی و اثرگذاری اجتماعی»،Shafin yanar gizon Babban Majalisar Juyin Juya Halin Al'adu.
  13. Naqše‑ye Mohandesi‑ye Farhangi‑ye Keshwar, 1393sh, s. 39.
  14. «مصوبه «سند دانشگاه اسلامی»،‌ Shafin yanar gizon Cibiyar Bincike ta Majalisar Shawarar Musulunci.
  15. «پژوهشگاه حوزه و دانشگاه در یک نگاه»، Shafin yanar gizon Cibiyar Bincike ta Hōza da Jami'a.
  16. «معرفی رشته اقتصاد اسلامی»، Shafin yanar gizon Jami'ar Khwārizmī.
  17. «سرفصل دوره کارشناسی ارشد روانشناسی اسلامی تصویب شد»، Kamfanin Dillancin Labarai na Mehr.
  18. Mowaḥḥid Abṭaḥī, Taḥlīl bar Andīshehā-ye Elm-e Dīnī dar Jahān-e Eslām shafi na 50–51.«کنگره بین‌المللی علوم انسانی اسلامی»، Shafin Yanar Gizo na Majma‘-e ‘Āli-ye ‘Olum-e Ensāni-ye Eslāmi..
  19. Misali, duba: Ahmadzādah,«واکاوی پژوهشگاه علوم و فرهنگ اسلامی»، Shafin yanar gizon Cibiyar Bincike ta Ilimomin Musulunci da Al'adu; Uliya'i«پروژه علوم انسانی اسلامی و بازخوانی چند رویکرد»،Shafin yanar gizon Jaridar Farhīkhtagān
  20. «بیانیه دبیرخانه شورای عالی انقلاب فرهنگی: علوم انسانی اسلامی؛ محرک اصلی تمدن‌سازی و پیشرفت جامعه»، Shafin yanar gizon Majalisar Ƙoli ta Juyin Juya Halin Al'adu.
  21. Mowahhed Abtahi, Tahlil bar Andishe ha‑ye ‘Elm‑e Dini dar Jahan‑e Islam, s. 15.
  22. Mowahhed Abtahi, Tahlil bar Andishe‑ha‑ye ‘Elm‑e Dini dar Jahan‑e Islam, s. 16; domin misali ku duba: Alwani, Islamiyyat al‑Ma‘rifah bayn al‑Ams wa al‑Yawm, s. 11.
  23. Mowahhed Abtahi, Tahlil bar Andishe‑ha‑ye ‘Elm‑e Dini dar Jahan‑e Islam, s. 16.
  24. Soroush, Islam wa ‘Olum‑e Ejtema‘i: Naqdi bar Dini Kardan‑e ‘Elm, s. 333–334.
  25. Soroush, Din‑e Aqli wa Aksari, s. 4–5; Soroush, Islam wa Olum‑e Ejtema‘i: Naqdi bar Dini Kardan‑e Elm, s. 84–112.
  26. Soroush, Dars‑hayi dar Falsafe‑ye ‘Elm‑e Ejtema‘, s. 17.
  27. Soroush, Din‑e Aqli wa Aksari, s. 4–5; Soroush, Islam wa ‘Olum‑e Ejtema‘i: Naqdi bar Dini Kardan‑e ‘Elm, s. 84–112; Malekian, Emkan wa Chegune‑gi‑ye ‘Elm‑e Dini, s. 11–12.
  28. Abdolkarimi, Payan‑e Te'oloji, j. 1, s. 174–175.
  29. Mowahhed Abtahi, Tahlil bar Andishe‑ha‑ye ‘Elm‑e Dini dar Jahan‑e Islam, s. 47.
  30. Qastalani, al‑Mawahib al‑Ladunniyyah, Qahira, j. 1, s. 442–444.
  31. .ir/others-note?id=8446 ،آماده‌خوری در علوم انسانی، زمینه‌ساز ریزش‌هاست, Ofishin Kiyaye da Yaɗa Ayyuka da Rubuce-rubucen Mai Girma Ayatullahi Al-Uzma Sayyid Ali Khamna'i ..

Nassoshi