Jump to content

Daƙiƙa:Hadis Halal Muhammad Halalun Ila Yaumil Ƙiyama

Daga wikishia
Hadis Halal Muhammad Halalun Ila Yaumil Ƙiyama
Maudu'iKhatamiyyar Annabi (S.A.W) da wanzuwar hukunce-hukuncen Musulunci
Ya Fito DagaAnnabi (S.A.W), Imam Baƙir (A.S) da Imam Sadiƙ (A.S)
Asalin MarawaiciZurara Bin A'ayan da Sama'atu Bin Mihran
Ingancin IsnadiIngancin Isnadinsa a wasu a naƙalin wasu ruwayoyi
Madogaran Shi'aBasa'irud Darajat da Al-Kafi
Madogaran Ahlus-sunnaMusnad Ad-Darimi da...
Hadis Silsilatuz Zahab • Hadis Saƙlaini • Maƙbulatu Umar Bin Hanzala • Hadis Ƙurbu Nawafil • Hadis Mi'iraj • Hadis Wilaya • Hadis Wisaya • Hadis Junud Aƙli Wa Jahal • Hadis Shajara


Hadis Halal Muhammad Halalun Ila Yaumil Ƙiyama magana ce game da adadin wasu ruwayoyi da suke jaddada Khatamiyyar Annabi da wanzuwar addinin Musulunci. bisa wannan hadisi, bayan Annabi Akram (S.A.W) babu wani Annabi ko sabon littafi da zai sake zuwa.

Malamin fiƙihu na Shi'a tare da dogara da waɗannan ruwayoyi sun yi amanna da cewa ba za a taɓa Nasakh ko shafe addinin Musulunci da wani addini daban ba, kuma umarnoninsa har zuwa lokacin da batutuwansu ba su canja ba suna nan tabbace wanzazzu. Haka kuma cikin mas'alolin fiƙihu, daga cikin har da batun taƙlidi da matacce, domin ci gaban hukunce-hukunce Musulunci suna dogara da waɗancan ruwayoyi

Wannan hadisi a cikin litattafan hadisi na Shi'a tun daga ƙarni na uku da bayansa, kamar misalin littafin Al-Kafi da Al-Mahasin, an naƙalto shi da lafuzza daban-daban, kuma wasu daga cikinsu sun kasance ingantattu

Matsayi Da Nazarin Ma'ana

Hadis Halal Muhammad Halalun Ila Yaumil Ƙiyama magana ce game da adadin wasu ruwayoyi da suke jaddada Khatamiyyar Annabi da wanzuwar addinin Musulunci.[1] kuma yana bayani cewa bayan Annabi (S.A.W) ba za aiko da sabon Annabi da sabon littafi ba.[2] Malaman fiƙihun Shi'a ciki har da Shaik Ansari[3] da Mirzayi Na'ini[4] suna ɗaukar wannan ruwaya matsayi wata babbar alama da take tabbatar da rashin nasakh da shafe addinin Musulunci da wani sabon addini. Sayyid Abul Ƙasim Khuyi[5] da Mar'ashi Najafi shima ya tafi kan cewa lallai wannan ruwayoyi alama ce ta wanzuwa da ci gaban shari'a da ci gaban umarnonin Musulunci matuƙar dai maudu'i da batunsu bai canja ba.[6] Allama Hilli, wanzuwa da ci gaban Musulunci ana lissafa su cikin laruran addini.[7]

A cewar Ali Sadrayi Khuyi, masanin kwafin rubuce-rubucen Shi'a, Muhammad Baƙir Bahari Hamadani (ya rasu: 1322 ko dai 1333H), ya rubuta littafi cikin sharhin waɗannan ruwayoyi.[8]

Ingancin Hadisin Da Madogaransa

Jafar Kashiful Giɗa a cikin Kashful Giɗa ya tafi kan kasancewar wannan hadisi mutawatiri ma'anawi.[9] Muhammad Taƙi Majlisi a cikin Raudatul Muttaƙin[10] da Allama Majlisi a cikin Bihar al-Anwar da Mir'atul Uƙul bayan naƙalto waɗannan ruwayoyi, ya inganta wasu daga cikinsu.[11]

ٌWannan hadisai an naƙalto cikin litattafai na Shi'a da yawan gaske a ƙarni na uku Hijira, kamar misalin littafin Al-Mahasin,[12] Basa'irud Darajat,[13] Tafsir Furat Al-Kufi,[14] Al-Kafi,[15] Risalatul Muhkam Wal Mutashabihu,,[16] ta hanyar marawaita misalin Zurara da Sama'atu Bin Mihran daga Annabi (S.A.W), Imam Baƙir (A.S) da Imam Sadiƙ (A.S). haka kuma Shaik Hurru Amlili a cikin Wasa'ilush Shi'a[17] da Al-Fusulul Muhimma[18] shima ya kawo wannan hadisai.

Wannan ruwayoyi sun zo cikin littafin Musnad Ad-Darimi da sauran litattafan Ahlus-Sunna tare da lafuzza daban-daban.[19]

Amfaninsa A Fiƙihu

Da yawan malaman fiƙihun Shi'a na ƙarni na goma zuwa sha biyar Hijira kamar Muƙaddas Ardabili (ya rasu: 993H)[20] Abdullahi Fadil Tuni,[21] Yusuf Bin Ahmad Bahrani,[22] Jafar Kashiful Giɗa,[23] Mirzayi Ƙummi,[24] Sayyid Abul Hassan Isfahani,[25] Sayyid Abul Ƙasim Khuyi,[26] Mar'ashi Najafi, (ya rasu: 1411H) cikin batutuwa daban-daban na fiƙihu misalin wajabcin sallar Juma'a,[27] halacci da rashin halaccin taƙlidi da matacce,[28] yanke hannun ɓarawo,[29] da ƙisasi[30] sun dogara da wannan ruwaya game da ci gaban hukunci har wannan zamani.

Rubutun Hadisin

عَنْ زُرَارَةَ قَالَ: سَأَلْتُ أَبَا عَبْدِ اللَّهِ ع- عَنِ الْحَلَالِ وَ الْحَرَامِ فَقَالَ حَلَالُ مُحَمَّدٍ حَلَالٌ أَبَداً إِلَی یَوْمِ الْقِیَامَةِ وَ حَرَامُهُ حَرَامٌ أَبَداً إِلَی یَوْمِ الْقِیَامَةِ لَا یَکُونُ غَیْرُهُ وَ لَا یَجِیءُ غَیْرُه[31]


Tarjama: Zurara yace: Na tambayi Imam Sadiƙ (A.S) game da halal da haram. Sai ya ce: Halal ɗin Muhammad (S.A.W) halal ne har zuwa ranar alƙiyama, kuma haram ɗinsa haram ne har zuwa ranar alƙiyama. Ba za a sami wani abu dabam da shi ba, kuma ba wani sabon abu dabamda shi da zai zo daga baya.



Bayanin kula

  1. ↑ Astar'abadi, Al-Fawa'idul Madaniyya, shafi na 249, Makarim Shirazi, Tafsir Nauma, juzu'i na 18, shafi na 340-342.
  2. ↑ Barƙi, Al-Mahasin, juzu'i na 1, shafi na 269; Saffar, Basa'irud Darajat, juzu'i na 1, shafi na 148,; Kulaini, Al-Kafi, juzu'i na 2, shafi na 17; Sayyid Murtada, Risalatul Muhkam Wal Mutashabihu, shafi na 55.
  3. ↑ Ansari, Fara'idul Usul, juzu'i na 2, shafi na 573.
  4. ↑ Na'ini, At-Taƙrirat, juzu'i na 2, shafi na 515.
  5. ↑ Khuyi, Siraɗun Najat, juzu'i na 3, shafi na 450.
  6. ↑ Mar'ashi Najafi, As-Sariƙa Ala Dau'il Kur'an Was Sunna, shafi na 315.
  7. ↑ Allama Hilli, Nihayatul Wusul Ila Ilmil Usul, juzu'i na 5, shafi na 79.
  8. ↑ Sadrayi Khuyi, Fehrestegane Nuskhehaye Khaɗɗi Hadis, juzu'i na 3, shafi na 378.
  9. ↑ Kashiful Giɗa, Kashful Giɗa, juzu'i na 1, shafi na 190.
  10. ↑ Majlisi, Raudatul Muttaƙin, juzu'i na 12, shafi na 196.
  11. ↑ Majlisi, Bihar al-Anwar, juzu'i na 16, shafi na 354 da juzu'i na 47, shafi na 35, da juzu'i na 9, shafi na 3; Majlisi Mir'atul Uƙul, juzu'i na 1, shafi na 201.
  12. ↑ Barƙi, Al-Mahasin, juzu'i na 1, shafi na 269.
  13. ↑ Saffar, Basa'irud Darajat, juzu'i na 1, shafi na 148.
  14. ↑ Kufi, Tafsir Furat Al-Kufi, shafi na 93.
  15. ↑ Kulaini, Al-Kafi, juzu'i na 2, shafi na 17.
  16. ↑ Sayyid Murtada, Risalatul Muhkam Wal Mutashabihu, shafi na 55
  17. ↑ Hurru Amili, Wasa'ilush Shi'a, juzu'i na 27, shafi na 169.
  18. ↑ Hurru Amili, Al-Fusulul Muhimma, shafi na 427 da 644.
  19. ↑ Darimi, Musnad Ad-Darimi, juzu'i na 1, shafi na 402; Ibn Ƙutaiba Ad-Dinawari, Ta'awilu Mukhtalaful Hadis, shafi na 271; Baihaƙi, Al-Madkhal Ilas Sunanil Kubra, shafi na 107.
  20. ↑ Muƙaddas Ardabili, Majma'ul Fa'ida Wal Burhan, juzu'i na 1, shafi na 8.
  21. ↑ Fadil Tuni, Al-Ijtihad Wat Taƙlid, shafi na 263.
  22. ↑ Bahrani, Al-Hada'iƙ An-Nadira, juzu'i na 9, shafi na 403 da 424.
  23. ↑ Kashiful Giɗa, Kashful Giɗa, juzu'i na 1, shafi na 190.
  24. ↑ Mirzayi Ƙummi, Manahijul Ahkam, shafi na 21.
  25. ↑ Isfahani, Salatul Musafir, shafi na 98-99.
  26. ↑ Khuyi, Siraɗun Najat, juzu'i na 3, shafi na 450.
  27. ↑ Bahrani, Al-Hada'iƙ An-Nadira, juzu'i na 9, shafi na 424; Mirzayi Ƙummi, Manahijul Ahkam, shafi na 21.
  28. ↑ Bahrani, Sharhu Ar-Risalatis Salatiyya, shafi na 2; Kashiful Giɗa, Kashful Giɗa, juzu'i na 1, shafi na 227.
  29. ↑ Mar'ashi, As-Sariƙa Ala Dau'il Kur'an Was Sunna, shafi na 315.
  30. ↑ Mar'ashi, Al-Ƙisas Ala Dau'il Kur'an Was Sunna, juzu'i na 1, shafi na 30.
  31. ↑ Kulaini, Al-Kafi, juzu'i na 2, shafi na 17.

Nassoshi

  • 27. Mirzayi Ƙummi, Muhammad Bin Haasan, Manahijul Ahkam fi Masa'il al-Halal wa al-Haram, Qom, Ofishin Intisharat Islami, bugu na farko, 1420H.
  • Allama Hilli, Hasan Bin Yusuf, Nihayatul Wusul ila Ilmil Usul, bincike da gyaran rubutu na Ibrahim Bahaduri, Qom, Cibiyar Imam Sadiƙ (A.S), 1425H.
  • Ansari, Murtada, Fara'idul Usul, bincike da gyaran rubutu na Cibiyar Zawil Qurba domin wallafa, Qom, Zawil Qurba, 1437H.
  • Astar'abadi, Muhammad Amin, Al-Fawa'idul Madaniyya, shafi na 249, Makarim Shirazi, Tafsir, binciken Rahmatullah Rahmati Araki, Qom, Cibiyar Annashr al-Islami, bugu na uku, 1426H.
  • Bahrani, Yusuf Bin Ahmad, Al-Hada'iƙ An-Nadira fi Ahkam Al-Itra Aɗ-Ɗahira, bincike da gyaran rubutu na Muhammad Taƙi Irwani da Sayyid Abdur-Razzaƙ Muƙarram, Qom, Ofishin Intisharat Islami, bugu na farko, 1405H.
  • Bahrani, Yusuf Bin Ahmad, Sharhu Ar-Risalatis Salatiyya, gyaran rubutu na Adil Bin Ahmad Bahrani, Bushehr, Muhammad bin Shaik Abdul-Hamid, bugu na farko, 1403H.
  • Baihaƙi, Ahmad Bin Husain, Al-Madkhal Ilas Sunanil Kubra, bincike da gyaran rubutu na Muhammad Diya Ar-Rahman Al-A'zami, Kuwait, Dar al-Khulafa lil-Kitab al-Islami, ba tare da shekarar bugawa ba.
  • Barƙi, Ahmad Bin Muhammad, Al-Mahasin, gyaran rubutu na Jalalud-Din Muhaddis Urmawi, Qom, Dar al-Kutub al-Islamiyya, ba tare da shekarar bugawa ba.
  • Darimi, Abdullah Bin Abdur-Rahman, Musnad Ad-Darimi, Saudi Arabia, Dar al-Mughni, bugu na farko, 1421H.
  • Fadil Tuni, Abdullah Bin Muhammad, Al-Ijtihad Wat Taƙlid (al-Wafiya fi al-Usul), Qom, Majma al-Fikr al-Islami, bugu na biyu, 1415H.
  • Faizul Kashani, Muhsin, Dah Risala, gyaran rubutu na Rasul Jafariyan, Isfahan, Kitabkunaye Amir al-Mu'minin, bugu na farko, 1371Sh.
  • Ibn Ƙutaiba Ad-Dinawari, Abdullah Bin Muslim, Ta'awilu Mukhtalaful Hadis, binciken Muhammad Muhuyid-Din Al-Asfar, al-Maktab al-Islami – Cibiyar al-Ishraq, bugu na biyu, 1419H.
  • Isfahani, Sayyid Abul Hassan, Salatul Musafir, Taƙririn Sayyid Husain Alawi Khunsari, Qom, Ofishin Intisharat Islami, bugu na farko, 1415H.
  • Ismaili Zadeh, Abbas,«بررسی سندی روایت حَلَالُ مُحَمَّدٍ حَلَالٌ أَبَداً إِلَی یَوْمِ الْقِیَامَةِ و...»، (Binciken isnadin ruwayar: “Halal ɗin Muhammad halal ne har abada, har zuwa ranar Alƙiyama, kuma), Mujallar Ulum al-Qur'an wa al-Hadis, lamba ta 109, lokacin kaka da hunturu na shekarar 2022–2023M, ranar dubawa: 21 ga Oktoba 2026M.
  • Karajaki, Muhammad bin Ali, Kanzul-Fawa'id, Qom, Dar Az-Zakha'ir, 1369Sh.
  • Kashiful Giɗa, Jafar, Kashful Giɗa An Mubhamat Ash-Shari'a Al-Garra, Qom, Ofishin Tablighat Islami Hauzeye Ilmiyya-ye Qom, bugu na farko, 1422H.
  • Khuyi, Sayyid Abul Ƙasim, Siraɗun Najat (al-Muhashsha), bincike da gyaran rubutu na Musa Mufid Ad-Din Asi Amili, Qom, Maktab Nashr al-Muntakhab, bugu na farko, 1416H.
  • Kufi, Furat Bin Ibrahim, Tafsir Furat Al-Kufi, bincike da gyaran rubutu na Muhammad Kazim, Tehran, Cibiyar Aɗ-Ɗab wan Nashr fi Wizarat al-Irshad al-Islami, 1410H.
  • Kulaini, Muhammad Bin Yaƙub, Al-Kafi, Tehran, Dar al-Kutub al-Islamiyya, 1363Sh.
  • Majlisi, Muhammad Baƙir, Bihar al-Anwar al-Jami'a li-Durar Akhbar al-A'imma Al-Aɗhar, Beirut, Dar Ihya al-Turas al-Arabi, bugu na biyu, 1403H.
  • Majlisi, Muhammad Baƙir, Mir'atul Uƙul Fi Sharhi Akhbari Ali Ar-Rasul, bincike da gyaran rubutu na Sayyid Hashim Rasuli Mahallati, Tehran, Dar al-Kutub al-Islamiyya, bugu na biyu, 1404H.
  • Majlisi, Muhammad Taƙi, Raudatul Muttaƙin Fi Sharhi Man la Yahduruhul Faƙihu, gyaran rubutu na Husain Musawi Kermani da Ali Panah Ishtihardi, Qom, Cibyar Farhangi Islami Kushanbur, bugu na biyu, 1406H.
  • Makarim Shirazi, Nasir, Tafsir Namuna, Tehran, Dar al-Kutub al-Islamiyya, 1374Sh.
  • Mar'ashi Najafi, Sayyid Shihabud-Din, Al-Ƙisas Ala Dau'il Kur'an Was Sunna, Taƙririn Sayyid Adil Alawi, Qom, Kitabkhuna wa Chapkhanaye Ayatullah Marashi Najafi, bugu na farko, 1415H.
  • Mar'ashi Najafi, Sayyid Shihabud-Din, As-Sariƙa Ala Dau'il Kur'an Was Sunna, Taƙririn Sayyid Adil Alawi, Qom, Kitabkhuna wa Chapkhunaye Ayatullah Mar'ashi Najafi, bugu na farko, 1424H.
  • Muƙaddas Ardabili, Ahmad Bin Muhammad, Majma'ul Fa'ida Wal Burhan Fi Sharh Irshad Al-Azhan, bincike da gyaran rubutu na Agha Mujtaba Iraqi, Ali Panah Ishtihardi da Agha Husain Yazdi Isfahani, Qom, Ofishin Intisharat Islami, bugu na farko, 1403H.
  • Na'ini, Muhammad Husaini, Ajwadu Taƙrirat (Taƙrirat Ayatullah Na'ini), taƙririn Sayyid Abul Ƙasim Khuyi, Qom, Kitabfurushiye Mustafawi, 1368Sh.
  • Sadrayi Khubi, Ali, Fehrestegane Nuskhehaye Khaɗɗi Hadis Wa Ulum Al-Hadis Shi'a, Qom, Dar al-Hadis, 1382Sh.
  • Saffar, Muhammad Bin Hasan, Basa'irud Darajat Fi Fada'il Ali Muhammad (S.A.W), Qom, Kitabkhunaye Umumiye Hazrat Ayatullah Mar'ashi Najafi, 1363Sh.
  • Sayyid Murtada, Ali Bin Husain, Risalatul Muhkam Wal Mutashabihu, Mashhad, Astan Quds Razawi, Gidauniyar Pajuhishha-ye Islami, Mashhad, 1386Sh.
  • Shaik Hurru Amili, Muhammad Bin Hassan, Al-Fusulul Muhimma Fi Usulil A'imma (Takmilat al-Wasa'il), gyaran rubutu na Muhammad Bin Muhammad Husain Ƙa'ini, Qom, Cibiyar Ma'arif Islami Imam Rida, bugu na farko, 1418H.