Annazafatu Minal Iman
| Maudu'i | Tsabta |
|---|---|
| Ya Fito Daga | Annabi Muhammad (S.A.W) |
| Asalin Marawaici | Babu |
| Ingancin Isnadi | Mursal |
| Madogaran Shi'a | Ɗibbun Nabiyyi (S.A.W) |
| Mai ƙarfafawa Na Kur'ani | Suratul Baƙara aya ta 125 |
| Mai ƙarfafawa Na Riwaya | Aɗɗuhru Nisful Iman (Tsarki (tsabta) rabin imani ne) |
| Hadis Silsilatuz Zahab • Hadis Saƙlaini • Maƙbulatu Umar Bin Hanzala • Hadis Ƙurbu Nawafil • Hadis Mi'iraj • Hadis Wilaya • Hadis Wisaya • Hadis Junud Aƙli Wa Jahal • Hadis Shajara | |
Annazafatu Minal Iman Tsafta tana daga imani (النظافة من الإيمان) wani hadisi ne da aka danganta ga Annabi Muhammad (S.A.W), wanda ke nufin cewa tsafta na daga alamomin imani.
An kawo wannan hadisi a cikin littafin Ɗibbun Nabiyyi wanda aka danganta ga Abul Abbas Mustagfiri (ya rasu 422H).[1] Wannan littafi kuma yana daga cikin madogara da Allama Majlisi ya dogara da shi a cikin Bihar Al-Anwar.[2]
Wannan hadisi yana cikin wani dogon ruwaya mai kama da haka: Ku yi amfani da khilal (tsinken tsabtace haƙora), domin yana daga tsafta, kuma tsafta tana daga imani, kuma imani yana tare da mai shi a Aljanna.[3]
Dukkan ruwayoyin da suke cikin littafin Ɗibbun Nabiyyi (S.A.W) da suka shafi lafiya da magani, kuma aka danganta su ga Annabi (S.A.W), ana kawo su ne ba tare da cikakken isnadi ba.[4] Wannan ya haifar da muhawara a tsakanin masana hadisi da masu bincike.[5]
Duk da haka, ma’anar wannan hadisi an ɗauke ta a matsayin abin karɓa, saboda dalilai kamar haka:[6] Na farko, akwai ƙarfafawa a cikin Kur’ani kan tsarki da kauce wa najasa, kamar a Suratul Ahzab aya ta 33 da Suratul Baƙara aya ta 125.[7]
Na biyu, akwai hadisai masu yawa da ke ƙarfafa tsafta da kiwon lafiya, kamar: Tsarki rabin imani ne,[8] umarni da tsaftace tufafi,[9] kula da tsaftar gida,[10] da kuma nisantar abubuwan da ba tsafta ba (kamar rashin wanke kwanoni da rashin share gida).[11]
Na uku, akwai wani hadisi makamancin wannan a cikin tsoffin littattafan Ahlus-Sunna, wanda ke cewa:
“Ku yi amfani da khilal (tsinken tsabtace haƙora), domin yana daga tsafta; kuma tsafta tana kiran imani; kuma imani yana tare da mai shi a Aljanna.[12]

Allama Majlisi ya danganta littafin Ɗibbun Nabiyyi (S.A.W) ga Mustaghfiri.[13] Amma duk da haka, ya amince da wannan hadisi da littafin, har ya nakalto dukkan littafin a cikin Bihar Al-Anwar.[14]
Bayan Majlisi da Bihar al-Anwar, wannan hadisi kuma ya sami karɓuwa a wurin Muhaddith Nuri, har ya shiga cikin Mustadrakul Wasa'il.[15]
Tun da dadewa, a wasu littattafai da kasidu da ke magana kan kiwon lafiya daga fuskar fikihu ko ta gaba ɗaya, hadisin “Annazafatu Minal Iman” shi ne hadisi na farko da ake ambata.[16]
Haka kuma, a ƙasashen Musulmi, ana amfani da wannan hadisi a matsayin rubutun bango ko alluna domin yaɗa tsafta da kiwon lafiya.[17]
Bayanin kula
- ↑ Mustaghfiri, Tibb al-Nabi (S.A.W), shafi na 21.
- ↑ Majlisi, Bihar al-Anwar, juzu’i na 59, shafi na 290–301.
- ↑ Mustaghfiri, Tibb al-Nabi (S.A.W), shafi na 21.
- ↑ Mahmudi, Abbas, «Barrasi taḥlili-ye e'tebar wa jaygah-e Ketab-e Tebb al-Nabi (S.A.W)», shafi na 111–142.
- ↑ Hoseini Karnami, «E'tebar-sanji-ye maḥtava’i wa sanadi-ye aḥadith-e Tibbi-ye Ketab-e Tibb al-Nabi (S.A.W) Mustaghfiri», shafi na 27–40. Mahmudi, Abbas, «Barrasi taḥlili-ye e'tebar wa jaygah-e Ketab-e Tebb al-Nabi (S.A.W)», shafi na 111–142.
- ↑ Hoseini Karnami, «E'tebar-sanji-ye maḥtava’i wa sanadi-ye aḥadith-e Tibbi-ye Ketab-e Tibb al-Nabi (S.A.W) Mustaghfiri», shafi na 27–40.
- ↑ Husaini Shirazi, Al-Fiqh al-Nazafa, Qum, juzu’i na 1, shafi na 12.
- ↑ Tamimi al-Maghribi, Nu'man bn Muḥammad, Da'aʾim al-Islam, juzu’i na 1, shafi na 100.
- ↑ Kulaini, Al-Kafi, juzu’i na 6, shafi na 441.
- ↑ Kulaini, Al-Kafi, juzu’i na 6, shafi na 531.
- ↑ Shu'ayri, Jami' al-Akhbar, shafi na 124.
- ↑ Tabarani, Al-Mu'jam al-Awsat, Dar al-Ḥaramayn, juzu’i na 7, shafi na 215.
- ↑ Majlisi, Bihar al-Anwar, juzu’i na 59, shafi na 290.
- ↑ Majlisi, Bihar al-Anwar, juzu’i na 59, shafi na 290–301.
- ↑ Nuri, Mustadrak al-Wasaʾil, juzu’i na 16, shafi na 319.
- ↑ Husaini Shirazi, Al-Fiqh al-Nazafa, Qum, juzu’i na 1, shafi na 16; marubuci wanda ba a san shi ba, shafi na 20–26, «Nazafa».
- ↑ «زیباسازی مدارس محروم توسط جهادگران دانشجو»، Ƙungiyar ‘Yan Jarida na Dalibai ta Iran«موضوع تعبیر عن النظافه من الایمان»، shafin yanar gizo na al-Jawab; Bayt al-Ma'lumah Online..
Nassoshi
- Husaini Karnami, Sayyid Ḥusain, «E'tebar-sanji-ye maḥtava’i wa sanadi-ye aḥadith-e Tibbi-ye Ketab-e Tibb al-Nabi (S.A.W) Mustaghfiri», (Binciken ingancin abun ciki da sanadodin hadisai na likitanci na littafin Tibb al-Nabi na Mustaghfiri.), a cikin mujallar Islam wa Salamat, lamba ta 4, hunturu 1393Sh/2014M.
- Husaini Shirazi, Sayyid Muḥammad, Al-Fiqh al-Nazafa, Qum, Ofishin Ayatullah Sayyid Muḥammad Ḥusaini Shirazi, ba buga shekara.
- Kulaini, Muḥammad bn Yaƙub, Al-Kafi, Tehran, Dar Kutub Islamiyya, 1365Sh.
- Mahmudi, Abbas, «Barrasi taḥlili-ye e'tebar wa jaygah-e Ketab-e Tebb al-Nabi (S.A.W)», (Binciken nazari kan inganci da matsayi na littafin Tibb al-Nabi (S.A.W.).), a cikin mujallar Hadith-e Ḥawze, lamba ta 7, kaka da hunturu 1392Sh/2015M.
- Majlisi, Muḥammad Baƙir, Bihar al-Anwar, Beirut, al-Wafa, 1404H.
- Mustaghfiri, Abu al-Abbas, Tibb al-Nabi, Qum, Mawallafar Raḍi, 1362SH.
- Nuri, Ḥusain, Mustadrak al-Wasaʾil, Qum, Cibiyar Ahlul Baiti (A.S.), 1408 H.
- Shu'ayri, Taj al-Din, Jami' al-Akhbar, Qum, Mawallafar Raḍi, 1363Sh.
- Tabarani, Abu al-Qasim Sulayman bn Aḥmad bn Ayyub bn Mutayr al-Lakhmi al-Shami, Al-Mu'jam al-Awsat, mai bincike: Tariƙ Bin Awaḍ Allah Bin Muhammad, Abd al-Muḥsin Bin Ibrahim al-Ḥusaini, al-Qahira, Dar al-Ḥaramayn, ba buga shekara.
- Tamimi al-Maghribi, Nu'man bn Muḥammad, Da'aʾim al-Islam, Masar, Dar al-Ma'arif, 1385 H.
- «موضوع تعبیر عن النظافه من الایمان»، (Maudu'i: Tsabta da muhimmancinta a Musulunci.), Sayt al-Jawab; Bayt al-Ma'lumah Online, ranar wallafa: 21 Nuwamba 2020, ranar duba: 25 Satumba 2024M.
- «زیباسازی مدارس محروم توسط جهادگران دانشجو»، (Kawata Makarantun Yankunan Marasa Galihu ta Hannun Dalibai Masu Ayyukan Jihadi.), Sayit Ƙungiyar ‘Yan Jarida na Dalibai ta Iran (IRANS), ranar wallafa: 1 Janairu 2020, ranar duba: 16 Satumba 2024M.