Jump to content

Hukuncin Aurar Mata Biyu Ƴan uwan Juna

Daga wikishia

Aurar mata biyu ƴan uwan juna, (Larabci: الزواج من الشقيقتين) cikin surar da namiji guda ɗaya bya haɗa mata biyu da suka kasance ƴan uwan juna, hakan ya haramta a addinin muslunci.[1] dalilin da malaman fiƙihu suka dogara da shi kan haramta auren mata biyu ƴan uwan juna shi ne aya ta 23 suratul nisa'i da riwayoyi.[2] da suka zo da bayani ƙarari kan haramta haɗa mata biyu ƴan uwan juna cikin inuwar auren da'imi da ko muwaƙƙati (Mutu'a).[3] kan wannan asasi idan mutum ya saki matarsa ko kuma ya yafe mata sauran lokacin da ya rage cikin aure muwaƙƙati , bayan ƙarewar idda, zai iya aurar ƴar uwar matarsa da suka rabu da ita.[4]

A bisa imanin malaman fiƙihu dangantakar ƴan uwantaka cikin wannan hukunci ta tattaro da ƴar uwa wace suke uba ɗaya ko uwa ɗaya haka kuma wace suka sha mama wuri ɗaya.[5] ba'arin malaman fiƙihu na shi'a sun tafi kan cewa idan aka aurar da mata biyu ƴan uwan juna a lokaci guda ga namiji guda ɗaya to duka auren biyu ya gurɓata.[6] haka nan idan aka fara ɗaura auren ɗaya daga baya aka ƙara da ɗayar to na biyun bai ɗauru ba bai kuma inganta ba.[7] a cewar Jawadi Amoli (Haihuwa: 1312 hijira shamsi.] daga malaman fiƙihu na shi'a, idan har mutum ya san cewa hukunci auren mata biyu ƴan uwa sannan tare da haka ya aikata shi, ƙari kan gurɓatar auren, lallai ya aikata babban zunubi.[8]

Bisa riwayoyin shi'a, an yi hani kan wannan aik; a cikin littafin Wasa'ilul Als-shi'a akwai riwayoyi guda 23 da suka zo game da haramcin haɗa mata biyu ƴan uwan juna ƙarƙashin inuwar miji ɗaya.[9] Sahibul Jawahir tare da bayanin riwayoyi daga waɗannan riwayoyi ya tafi kan cewa a wasu lokutan sakamakon larurar taƙiyya Imamai (A.S) ba su yi bayyana haramcin haklan ba ƙarara.[10]

Nasir Makarim Shirazi, marja'in taƙlidi na shi'a, ya kawo tsammanin dalilin haramcin auren mata biyun ƴan uwa a lokaci guda ya faru sakamakon kaucewa kishiyantar juna da gasa a tsakaninsu, daga ƙarshe hukuncin haramcin ya lamintar da dawwama dangantaka da soyayya tsakanin ƴan uwan juna.[11] a cikin aya ta 23 suratul nisa'i bayan sanar da hukuncin haramcin auren mata biyu ƴan uwan juna a lokaci guda, sai aka togace auren da aka rigaya a ka ƙulla shi gabanin sauka wannan ayar.[12] bisa abin da malaman tafsiri suka naƙalto misalin Shaik Ɗusi cikin Al-tibyan da Ɗabarsi cikin Majma'ul Al-bayan, abin da ake nufi daga kau da kai daga aure da aka ƙulla kafin saukar wannan aya, shi ne auren Annabi Yaƙub (A.S) da ya yi da mata biyu ƴan uwa, watau Rahila da Liya.[13]

Ana cewa kafin saukar wannan aya, aurar yan uwan juna wata ala'ada ce da ta yi matuƙar yaɗuwa, amma bayan saukar wannan aya waɗanda suka rigaya suka yi wannan aure kafi saukar ayar , ya zama dole su rabu da ɗaya daga cikinsu su zauna da ɗaya , duk da cewa babu uƙuba kan abin da suka aikata gabanin saukar ayar, kuma ƴaƴan da aka samu ƴa ƴa ne na halal.[14]

Bayanin Kula

  1. Shahid Thani, Masalak al-Afham, 1413 AH, juzu'i na 7, shafi 289; Najafi, Jawahir al-Kalam, 1404 AH, juzu'i na 29, shafi na 356; Tabatabaei, Riyad al-Masa'il, 1418, juzu'i na 11, shafi 180.
  2. ↑ Ameli, Wasa’il al-Shi’ah, 1412 AH, juzu’i na 20, shafi na 476-486.
  3. Shahid Thani, Masalik Al-Afham, 1413 BC, juzu'i na 7, shafi na 289.
  4. Tabatabai, Riyad al-Mas’il, 1418 AH, juzu’i na 11, shafi 181; Hakim, Minhaj al-Salihin, 1415 BC, juzu'i na 3, shafi na 27.
  5. Hili, Qawad al-Ahkam, 1413 BC, juzu'i na 3, shafi na 34; Ruhani, Fiqhun Al-Sadiq, Amincin Allah ya tabbata a gare shi, 1412 Q, juzu'i na 21, shafi na 244.
  6. Shahidi Thani, Al-Rawdah Al-Bahiyya, 1410 BC, juzu'i na 5, shafi na 187.
  7. Sistani, Minhaj al-Salihin, 1417 AH, juzu'i na 3, shafi na 60; Ruhani, Fiqhu Al-Sadiq, Amincin Allah ya tabbata a gare shi, 1412 Q, juzu'i na 21, shafi na 249.
  8. "Darasi kharijul Fikihi Ayatullah Javadi Amoli mabhasi jam'i baina uktaini", gidan yanar gizon makarantar fikihu.
  9. Ameli, Wasa’il Al-Shi’a, 1409 AH, juzu’i na 20, shafi na 476-486.
  10. Najafi, Jawahir al-Kalam, 1404 BC, juzu'i na 29, shafi na 356.
  11. Makarem Shirazi, Tafsir Namuna, 1371 AH, juzu'i na 3, shafi na 331.
  12. Suratul Nisa’i, aya ta 23.
  13. Tabarsi, Majma Al Bayan, 1372, juzu'i na 3, shafi.49; Tusi, Al-Tabyan fi Tafsir Al-Qur'an, Dar Ihya Al-Trath Al-Arabi, juzu'i na 3, shafi na 160
  14. Makarem Shirazi, Tafsir Namuna, 1371 AH, juzu'i na 3, shafi na 331.

Nassoshi

  • Alqur'ani mai girma.
  • Ameli, Muhammad bin Hasan, Wasa'il al-Shia, Cibiyar Al-Bait, Qum, bugun farko, 1409H.
  • Hakim, Sayyid Muhammad Saeed, Minhaj al-Salehin, Beirut, Darul-Safwa, bugu na farko, 1415H.
  • Hali, Hasan bin Yusuf, Qawa'idul Al-Ahkam, Qum, Jamia Madrasin, bugu na farko, 1413H.
  • Makarem Shirazi, Nasser, Tafsir Namune, Tehran, Darul-e-Kitab al-Islamiyya, bugu na 10, 1371.
  • Najafi, Mohammad Hasan, Jawaher al-Kalam fi Sharh Shar'i al-Islam, Dar Al-Ahiya Letrat al-Arabi, Beirut, bugu na 7, 1404H.
  • Rouhani, Sayyid Sadik, Fiqh al-Sadiq (a.s.), Kum, Darul Katab- Madrasah Imam Sadik (a.s.), bugu na farko, 1412H.
  • Shaheed Thani, Zain al-Din bin Ali, Masalak al-Afham ili Tankih Shari'i al-Islam, Islamic Encyclopaedia Foundation, Qum, bugu na farko, 1413H.
  • Shahidi Thani, Zain al-Din bin Ali, al-Rawda al-Bahiya fi Sharh al-Lama' al-Damashqiya (Mohshi Kalanter), Davari, Qom, bugun farko, 1410H.
  • Sistani, Sayyid Ali, Minhaj al-Salehin, Qum, bugun littafin Sayyidina Ayatullah Sistani, bugu na biyar, shekara ta 1417 bayan hijira.
  • Tabarsi, Fazl bin Hassan, Majma al-Bayan fi Tafsir al-Qur'an, Iran, Nasser Khosrow, bugu na uku, 1372.
  • Tabatabai, Sayyid Ali, Riaz al-Masail, Qum, Cibiyar Al-Bait, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, bugun farko, 1418H.
  • Tusi, Muhammad bin Hassan, Al-Tabyan fi Tafsir Al-Qur'an, Beirut, Dar Ihya Al-Tarath Al-Arabi, bugun farko, Bita.
  • «درس خارج فقه آیت الله جوادی آملی مبحث جمع بین اختین»، سایت مدرسه فقاهت، تارخ بازدید: ۹خرداد۱۴۰۳ش.