Juz'i (Alkur'ani)

Daga wikishia

Juz’i (Larabci: الجزء (قرآن)) yana daga cikin ma’aunan rarraba Alkur’ani, kowanne juz’i guda ɗaya yana daidai da kaso ɗaya bisa talatin na Alkur’ani, kusan shafuka ashirin kenan cikin rubutun Usman ɗaha, duk juzu’i guda ɗaya yana matsayin hizbi biyu juzu’i talatin ya ƙunshi surorin 37 wanda shi ne ya ƙunshi mafi yawan surori, cikin ba’arin al’adu, ana karanta juzu’an Alkur’ani cikin ƙarƙashin ambaton lamba ko Kalmar farkon juz’in.

Sanin Mafhumi

Juz’i, yana cikin tsarin Alkur’ani, Musulmai sun kasa Alkur’ani zuwa juz’i talatin, ma’ana ɓangarori talatin. [1] a wasu al’adu ana karanta juz’an Alkur’ani cikin hanyar amfani da lambar da take kansu ko kuma Kalmar take a farkon juz’in, misalin juz’in Amma, wanda yake da ma’anar juz’i na talatin wanda yake farawa da (Amma yatasa’alun) [2] kowanne juz’i yana kasuwa zuwa hizbi biyu sannan a Alkur’ani rubutun Usman ɗaha kowanne juz’i yana da shafi ashirin. [3]

Takaitaccen Tarihin Juz’in Kur’ani

Juzu'i na tara na Alkur'ani

Wasu ba’arin Malamai suna ganin asalin amfani da tsarin juz’i a Kur’ani ya samu daga wata riwaya daga Annabi (S.A.W) wanda cikinsa aka yi ishara kan karanta Alkur’ani a kowanne wata cikin watannin Muslunci. [4] amma game da wanne zamani ne aka fara kasa Kur’ani zuwa tsarin Juz’i-juz’i zuwa juz’ai talatin, akwai mabambantan ra’ayoyi, an ce hakan ya faru ne a lokacin Hajjaju Bn Yusuf Saƙafi wanda ya mutu shekara ta 95 h ƙamari, [5] a kowacce rana cikin watan Ramadan ana karanta juzu’ ɗaya. [6] wasu ba’ari kuma sun ce Sarki Mamun Abbasi wanda ya yi mulki tsakanin shekaru 198-218, shi ne wanda ya bada umarnin karkasa Kur’ani cikin tsarin Juz’I, [7] Zarkashi daga Malaman tafsiri a ƙarni na takwas yana ganin yaɗuwar tsarin juz’antar Kur’ani zuwa juz’i talatin ya samu ne daga makarantun addini. [8]

Karatun Juz’-juz’i

Majalisin Karatun Kur'ani a Haramin Imam Husaini (A.S)
Asalin Maƙala: Karatun Juz’i

A ƙasar Iran da ba’arin wasu ƙasashen Muslunci, a cikin watan Ramadan Musulami suna taruwa su karanta Kur’ani tun daga farko har ƙarshensa (Khatma), da wannan ne ya kasance suke karanta juz’i ɗaya a kowacce rana, ana kiran wannan al’ada da sunan karatun juzu’i, a ƙasar Iran karatun juzu’i da ake yi a wurare masu tsarki Tashoshin Talabishin suna ɗaukowa suna watsa wannan karatu kai tsaye. [9] Cikin ba’arin ƙasashen Musulmi misalin Iran, ana buga juz’an Kur’ani a ware daga cikin Alkur’ani, zai zama kenan kammalallensa cikin yanki guda talatin ana karantawa kan wannan tsarin a taron addu’ar zaman makoki. [10] na’am Sayyid Muhammad Husaini Tehrani wanda ya mutu shekara 1416 h shamsi,yana da sa ɓani da wannan al’ada, yana ganin wannan tsari na rarraba Kur’’ani da junansa a khatma ya fara yaɗuwa ne a zamanin Mulkin Yazidu Bn Mu’awiya, Malamin yana ganin ya kamata ne ayi amfani da kammalallen Alkur’ani a lokacin Khatamarsa bawai wanda aka rarraba shi zuwa juz’i-juz’i ba. [11]

Fihirisar Karatun Juzu'in Kur'ani

Juzu'an Kur'ani
Juzu'i Ayar farkon juzu'i Surorin da ya tattaro
1 Aya ta 1 Suratul Fatiha: "Bismillahi..." Suratul Fatiha da Suratul Baƙara (farkon aya ta 141)
2 Aya ta 142 Suratul Baƙara:"sayaƙulu Alsufaha'u..." Baƙara (Ayoyi 142-253)
3 Aya ta 253 Suratul Baƙara: "tilkar Ar-rusulu..." Baƙara (Aya 253 zuwa ƙarshen sura) da kuma Alu Imran (farkon aya ta 92)
4 Aya ta 93 Suratul Alu Imran: "kullu ɗa'ami..." Alu Imran(Aya 93 zuwa ƙarshen sura) da kuma Nisa'i (farko aya ta 23)
5 Aya ta 24 Suratul Nisa'i:"Wal-muhsanat..." Nisa'i(Aya 24-148)
6 Aya ta 148 Suratul Nisa'i:"La yuhibbulahu..." Nisa'i(Aya 148 zuwa ƙarshen sura)
7 Aya ta 82 Suratul Ma'ida: " Latajidanna..." Ma'ida (Aya 82 zuwa ƙarshen sura)
8 Aya ta 112 Suratul An'am: "wa lau anna nazzalna..." An'am (Aya 112 zuwa ƙarshen sura)
9 Aya ta 89 Suratul A'araf "ƙalal Al-Mala'u..." A'araf (Aya 90 zuwa ƙarshen sura) da kuma Anfal (farkon Aya ta 40)
10 Aya ta 41 Suratul Anfal: "Wa'alamu..." Anfal (Aya ta 41 zuwa ƙarshen sura) da kuma Tauba (farkon aya ta 92)
11 Aya ta 93 Suratul Tauba"Innamas As-Sabil..." Tauba (Aya ata 93 zuwa ƙarshen sura)
12 Aya ta 6 Suratul Hudu: "wama min da'batin..." Hudu (Aya ta 6 zuwa ƙarshen sura) da Yusuf (farkon aya ta 53)
13 Aya ta 54 Suratul Yusuf: Yusuf (Aya ta 54 zuwa ƙarshen sura) Ra'ad da Ibrahim
14 Aya ta 1 Suratul Hujurati: "ALif lamra" Hijri da Nahali
15 Aya ta 1 Suratul Isra'i: "Subhanallahi..." Isra'i da Kahafi (farkon Aya ta 74 zuwa ƙarshen sura)
16 Aya ta 75 Suratul Kahafi: "ƙala alam..." Kahafi, Maryam da Ɗaha
17 Aya ta 1 Suratul Anbiya: "Iƙtaraba lilnasi..." Anbiya da Hajji
1 Aya ta 1 Suratul Muminun: "ƙad Aflaha..." Muminun, Nur da Furƙan (farkon aya ta 20)
19 Aya ta 21 Suratul Furƙan: "Wa ƙala Allazina..." Furƙan, (Aya ta 21 zuwa ƙarsehn sura)
20 Aya ta 56 Suratul Namli: "Fama kana..." Namli, ƙasas da Ankabut (farkon aya ta 45)
21 Aya ta 46 Suratul Ankabut: "Wa latujadilu..." Ankabut (Aya ta 46 zuwa ƙarshen sura) Rum, Luƙman, Sajada da Ahzab (ayoyi na 30 na farko)
22 Aya ta 31 Suratul Ahzab: "wa man yaƙnut..." Ahzab (Aya ta 31 zuwa ƙarshe), Saba'i, Faɗir da Yasin (farkon aya ta 27)
23 Aya ta 28 Suratul Yasin: "Wama Anzalna..." Yasin, Sa'fat, Sa'd da Zumar (farkon Aya ta 31)
24 Aya ta 32 Suratul Zumar: "Faman Azlama" Zumar, (Aya ta 32 zuwa ƙarshe), Gafir da Fussilat (farkon aya ta 46)
25 Aya ta 47 Suratul Fussilat: "Ilaihi yaruddu..." Fussilat, (Aya ta 47 zuwa ƙarshe), Shura, Zukhruf, Dukhan da Jasiya
26 Aya ta 1 Suratul Ahƙaf: "Hemim...) Ahƙaf, Muhammad, Fathu, ƙaf, Zariyat, (farkon aya ta 30)
27 Aya ta 31 Suratul Zariyat: "ƙala Fama Khaɗbukum..." Zariyat, (Aya ta 31 zuwa ƙarshe), ɗur, Najmu, ƙamaru Ar-Rahman, Waƙi'a da Hadid
28 Aya ta Suratul Mujadala: "ƙad Sami'a..." Hashar, Mumtahana, Saffi, Juma'a, Munafiƙun, Tagabun, Ɗalaƙ da Tahrim
29 Aya ta 1 Suratul Mulki: "Tabaral Allazi..." ƙalam, Ha'ƙati, Ma'arij, Nuhu, Jinni, Muzammil, Mudassir, Insan da Mursalat
29 Aya ta 1 Suratul Naba'i: "Amma yatasa'alun...' Nazi'at, Abasa, Takwir, Infiɗar, Muɗaffifin, Inshiƙaƙ, Buruji, ɗariƙ, A'ala, Gashiya, Fajar, Balad, Shamsu, Laili, Dhuha, Sharhu, Tinu, Alaƙ, ƙadar, Bayyina, Zalzala, A'diyat, ƙari'atu, Takasur, Asri, Humazatu, Filu, ƙuraishi, Ma'un, Kausar, Kafirun, Nasar, Masad, Iklasi, Falaƙi, Nasi

Bayanin kula

  1. Moini, "Juz'u", shafi na 836.
  2. Moini, "Juz'u", shafi na 836.
  3. رضاپورa class="external text" href="http://irandaveh.blogfa.com/post/130">دانستنی‌های قرآن
  4. Ahmad bin Ahmad bin Muhammad Abdullah Al-Tawil, Fannun Al-Tartil wa Ulumehi, 1420 AH, shafi na 65.
  5. Faiz Kashani, Mahajjah Al-Bayda, 1428H, shafi na 224.
  6. Moini, "Juz'u", shafi na 836.
  7. Marfat, Tamhid, 1412 AH, juzu'i na 1, shafi na 364.
  8. Zarakshi, Al-Burhan, 1408H, Mujalladi na 1, shafi na 250.
  9. class="external text" href="http://www.tavoosebehesht.ir/news/1572">برنامه جزءخوانی صدا و سیما طاووس بهشت
  10. Dehkhoda, Luggat Nameh Dehkhoda, ƙarƙashin kalmar Si pareh.
  11. class="external text" href="https://maktabevahy.org/Document/Article/Details/97/%D8%AF%DB%8C%D8%AF%DA%AF%D8%A7%D9%87-%D8%B9%D9%84%D8%A7%D9%85%D9%87-%D8%B7%D9%87%D8%B1%D8%A7%D9%86%DB%8C-%D9%86%D8%B3%D8%A8%D8%AA-%D8%A8%D9%87-%D8%A8%D8%B1%DA%AF%D8%B2%D8%A7%D8%B1%DB%8C-%D9%85%D8%AD%D8%A">«دیدگاه علاّمه طهرانی نسبت به برگزاری محافل جشن و عروسی و ترحیم»

Nassoshi