Sabawa Iyaye

Daga wikishia

Saɓawa Iyaye, (Larabci: عقوق الوالدين) ko cutaway Iyaye yana daga Manya-manyan Zunubai kuma ana ƙirga shi cikin layin miyagun halaye, saɓawa iyaye shi ne baƙanta musu daga kowanne irin nau’in aiki babu banbanci kalma ce aka faɗa musu ko kuma wata mu’amala mara kyau, kamar yanda ya zo cikin riwayoyi, saɓawa umarni, kallon da yake cuɗanye da fushi, rashin girmamawa da da furta kalmomin ƙosawa misalin Uf da kai duka ana ƙirga su cikin misdaƙan saɓawa Iyaye, ya zo cewa idan da akwai wani abu da yake ƙasa da furta musu Kalmar Uf shima haramun ne furta shia kansu, daga cikin illoli na saɓawa iyaye akwai haramtuwa daga samun shiga Aljanna, za kuma a wurga mai saɓawa iyaye cikin wuta, da azabar ƙabari, rashin karɓar sallarsa da rashin amsa addu’arsa dukkanin suna daga cikin natijoji da sakamakon saɓawa Iyaye da aka yi bayaninsu cikin riwaya kan ilollin da suke samun mai saɓawa iyaye, ba’arin Malaman Akhlaƙ suna ganin gajercewar rayuwa, tsanani a lokacin fitar rai da matsananciyar mutuwa suma duka suna cikin sakamako daga saɓawa iyaye

Mafhumi

saɓawa Iyaye, shi ne Mutum ya dinga cutawa Babansa da babarsa ta hanyar harshe ko mu’amala. [1] na’am Kalmar Uƙuƙ a harshen Larabaci ta zo da ma’anar yankewa, saboda haa anan wurin anyi amfani da ita cikin ma’anar yanke zumunci da su, [2] Mulla Mahadi Naraƙi yana ganin saɓawa iyaye yafi munana daga yanke zumunci, ya tafi kan cewa duk da cewa Kalmar tana da ma’anar yanke zumunci haka zalika tana shiryarwa kan tawayar saɓawa iyaye, haka kuma saɓawa iyaye tana cikin miyagun halaye da suke da alaƙa da ɓangaren fushi da sha’awa da suke ɓuɓɓugowa daga ƙiyayya da fushi ko rowa da son duniya. [3]

Misdaƙai

Saɓawa iyaye shi ne duk wani nau’in cutarwa ga Uba da Uwa ko kuma ɗaya daga cikinsu, a cikin riwaya ya zo cewa kallo da yake cuɗanye da fushi [4] tozartar haƙƙoƙi [5] rashin biyan buƙata, rashin bin umarni, rashin girmamawa [6] suna daga misdaƙan saɓawa iyaye, Mulla Ahmad Naraƙi ya ce kowanne irin abu da yake zama sababin cutawa Iyaye ana ƙirga shi cikin layin saɓawa iyaye [7] a cikin wata riwaya daga Imam Sadiƙ (A.S) furta Uf ga Uwa ko Uba ana kirga shi mafi ƙanƙantar saɓawa iyaye, an ce idan da akwai wata kalma ƙasa da Uf itama baya halasta a furtata ga Mahaifa. [8]

Saƙonni

Saɓawa Iyaye yana cikin miyagun halaye waɗanda riwaya ta lissafa su cikin layin Manya-manyan zunubai, [9] kuma akwai saƙonni da suke biye da aikata hakan da aka yi bayaninsu cikin riwaya:

  • Haramtuwa daga shiga Aljanna da jin ƙanshinta, [10] kan asasin wata riwaya daga Imam Sadiƙ (A.S) ranar Alƙiyama za a cire labule daga labulayen Aljanna ƙamshinta zai bazu dukkanin halittu za su ji wannan ƙamshi zai yaɗu nisan tafiyar shekaru ɗari biyar kowa da kowa zai isa zuwa gare shi amma banda masu saɓawa Iyaye [11] haka kuma akwai riwayoyi masu tarin yawa da suka zo da jumlar
«لایَدْخُلُ الْجَنّه»
  • Mai saɓawa Iyayensa ba zai shiga Aljanna ba. [12]
  • za kuma a tura shi cikin Jahannama. [13]
  • ba a karɓar sallarsa 14 a cikin wata riwaya ya zo cewa wanda ya yi kallo na ƙiyayya ga Iyayensa matsayin wanda suke zaluntarsa Allah ba zai karɓi sallarsa ba. [14]
  • rashin amsa addu’a. [15]
  • Azabar a duniya; a wata riwaya daga Annabi (S.A.W) haƙiƙa saɓawa Iyaye yana cikin Manya-manyan zunubai wanda tun a duniya mutum yake fara ganin sakamakonsa [16] Mulla Ahmad Naraƙi ya ce tajriba ta tabbatar da cewa saɓawa Iyaye yana haifar da gajercewar rayuwa, ɗacin rayuwa da tsanani, talauci, tsananin lokacin fitar rai da tsanantar mutuwa. [17]
  • Azabar ƙabari; a cewar Mulla Mahadi Naraƙi duk wanda mahaifiyarsa ta yi fushi da shi zai fuskanci tsananin fitar rai da azabar ƙabari mai tsanani. [18]

Saɓawa Iyaye Bayan Mutuwarsu

Kan asasin ba’arin riwayoyi, saɓawa Iyaye bai keɓantu da zamanin da suke raye ba ya tataro har bayan mutuwarsu, kamar yanda kyautata musu bai iyakantu da lokacin da suke raye ba, zai iya yiwuwa mutum ya kasance mai tausayi da kyautatawa Iyayensa a lokacin da suke raye amma kuma bayan mutuwarsu ya zama mai saɓa musu, kamar dai misalin wanda ya ƙi biya musu bashi bayan mutuwarsu, kuma baya nema musu gafarar Ubangiji, haka kuma za iya yiwuwa mutum ya kasance mai saɓawa iyayensa a duniya amma kuma bayan mutuwarsu ya zama mai kyautata musu. [19] Mulla Ahmad Naraƙi domin nesanta daga saɓawa iyaye: yace a dinga tunawa da irin wahalhalun da suka sha da rashin bacci da tsananin ƙaunarsu ga ɗan da suka Haifa da kuma karbar la’anar da suke kan ɗan da suka Haifa. [20]

Bayanin kula

  1. Naraghi, Meraj Al-Sa'ada, 1378, shafi na 532.
  2. Farahidi, Al-Ainu, 1409 Hijira, juzu'i na 1, shafi na 63
  3. Naraghi, Jame Al-Sa'adat, 2003, juzu'i na 2, shafi na 262.
  4. Kulaini, Al-Kafi, 1407 Hijira, juzu'i na 2, shafi na 349.
  5. Tamimi Amadi, Ghurarul Al-Hekam, 1410 AH, shafi na 671.
  6. Noori, Mostadrak Al-Wasa'il, 1408 AH, juzu'i na 15, shafi na 194.
  7. Naraghi, Meraj al-Sa'ada, 1378, shafi na 532.
  8. Kulaini, Al-Kafi, 1407 Hijira, juzu'i na 2, shafi na 349.
  9. Kulaini, Al-Kafi, 1407 Hijira, juzu'i na 2, shafi na 276.
  10. Kulaini, Al-Kafi, 1407 Hijira, juzu'i na 2, shafi na 349.
  11. Kulaini, Al-Kafi, 1407 Hijira, juzu'i na 2, shafi na 349.
  12. Himyari, Qurbul Al-Asnad, 1413H, shafi na 82.
  13. Kulaini, Al-Kafi, 1407 Hijira, juzu'i na 2, shafi na 348.
  14. Kulaini, Al-Kafi, 1407 Hijira, juzu'i na 2, shafi na 349.
  15. Kulaini, Al-Kafi, 1407 Hijira, juzu'i na 2, shafi na 448.
  16. Payandeh, Nahj al-Fasaha, 1382, shafi na 165.
  17. Naraghi, Meraj al-Sa'ade, 1378, shafi na 532.
  18. Naraghi, Jame Al-Sa'adati, 2013, juzu'i na 2, shafi na 263.
  19. Kulaini, Al-Kafi, 1407 Hijira, juzu'i na 2, shafi na 163.
  20. Naraghi, Meraj al-Sa'ada, 1378, shafi na 532.

Nassoshi

  • Payandeh, Abolqasem, Nahj al-Fasaha, Tehran, Danesh, 2002.
  • Tamimi Amadi, Ghurarul Al-Hekam da Darr al-Kalam, editan Seyyed Mahdi Rajaee, Qum, Dar al-Kitab al-Islami, 1410H.
  • Himyari, Abdullahi bin Jafar, Qorbul Al-Asnad, Qum, Mu’assasa Al-Baiti, 1413H.
  • Farahidi, Khalil bin Ahmad, Qum, bugun Hijira, 1409H.
  • Kuliani, Muhammad bin Yaqub, Al-Kafi, wanda: Ali Akbar Ghafari da Muhammad Akhundi suka yi masa bita, Tehran, Darul Kitab al-Islamiya, 1407H.
  • Naraghi, Ahmed bin Mohammad Mahdi, Meraj al-Saadah, Hijrat Publications Institute, 1378.
  • Naraghi, Mohammad Mahdi, Jame al-Saadat, Qum, Iranian Press Institute, 1963 AD/1383 AH.
  • Nouri, Hossein bin Mohammad Taqi, Mustadrak al-Wasail da Mustanbat al-Masal, Kum, Mu'assasa Al-Baiti, 1408H.