Farin Aure

Daga wikishia
Risala Ilmiyya

Farin Aure, (Larbaci:الزواج الأبيض) wani nau’in alaƙa ce ta Motsin rai (emotional relationship) da kuma rayuwar jima’i wacce ta kasance a wajen igiyar aure tsakanin mace da namiji wacce a al’adar yammacin turai suke kira da suna “zaman tare”, a ra’ayin malaman fiƙihu na Shi’a, wannan wata haramtacciyar alaƙa ce, kuma ba a ƙidayata cikin layin halastaccen aure, sakamakon rashin kiyaye sharuɗɗan aure na larura a cikinta misalin karanta sigar ɗaura aure daga ɓangare biyu da kuma rashin lazimcin kufaifayin shari’a daga fuskanin gado, ciyarwa da kuma yin idda. Illolin da Farin aure yake haifarwa, daga cikin akwai misalin yawaitar ha’inci, yawaita ɗaukar cikin da ba a shirya masa ba, zubar da ciki da barazanar rusa katangar dangi, sababin samuwar waɗannan sabbin miyagun al’adu na yammacin turai sun faru ne sakamakon sakacin iyaye cikin tarbiyar ƴaƴansu da kuma tsawaita shekarun aure, haka kuma malamai sun fitar da hanyoyin da za ƙalubalancin wannan matsala; daga jumlarsu akwai samar da yanayi da dandalin auratayya, samar da aikin yi da kuma ƙarfafa saƙafar auren mutu’a

Farin Aure Ko Zaman Tare

Farin Aure wani nau’in ɗamfaruwa da juna ne na rayuwar soyayya da jima’i tsakanin mace da namiji wanda yake kasancewa ba tare da kiyaye dokokin aure na shari’a ba kamar misalin karanta sigar ɗaurin aure tsakanin ɓangarori biyu, wannan nau’in alaƙa da ake kira da zaman tare, haka zalika ana kiranta rayuwar tarayya a gida da makwanci tsakanin mace da namiji. [1] dalilin kiran wannan alaƙa da suna farin aure ya faru ne sakamakon wanzuwar takardar haihuwar a fara. [2] wannan isɗilahi babu shi a al’adun turawan yamma ba, wannan wata sannaniyar alaƙa ce da aka santa da taken zaman tare (cohabitation). [3]

Bambancinsa Da Aure Na Shari’a

Farin aure yana da bambanci da aure na shari’a ta fuskoki da daman gaske. Alal misali cikin karanta sigar ɗaura aure, ayyana sadaki, kiyaye idda da iznin waliyyi yarinyar da za a aurar idan ta kasance budurwa, su na daga sharuɗɗa da babu cikin farin aure. [4] haka kuma kufaifayin aure misalin gado tsakanin mata da miji, sadaki da ciyarwa duka babu su a farin aure. [5] hakan nan kuma hatta cikin Nikahu Mu’aɗati wanda shi ma cikinsa babu karanta sigar ɗaura amma duk da haka yana kasancewa ne ƙarƙashin shelar yarda da ƙulla aure ta wasu hanyoyi misalin ishara ko rubutu. [6]

Taƙaitaccen Tarihinsa

Ana ganin yaɗuwar mummunar al’adar farin aure cikin al’ummun musulmai ta faru ne sakamakon tasirantuwa da al’adun turawa. [7] masana suna cewa a ƙarshen shekarar 1960 ne a ƙasar Amerika da ƙasashen Turai aka fara samun sauyi cikin rayuwar jinsi wanda ake kira da sunan (juyin juya halin jinsi) sanannan abu ne a wancan lokacin ƙarƙashin uzurin ƴancin jinsi an samu yaɗuwar karkacewa mai yawan gaske kuma ya yaɗu sosan gaske, zaman tare ɗaya ne daga cikin abubuwan da suka samu yaɗuwa sosan gaske, bayan wani lokaci a hankula hankula sai ya dinga tsallakawa cikin sauran al’ummu yana watsuwa. [8] Hukuncin Fiƙihu Game Da Farin Aure a ra’ayin malaman fiƙihun Shi’a farin aure ya haramta kuma suna ƙirga shi ciki zina. [9] kan asasin fatawar maraji’an taƙlidi a shekarar 2017 daga jumlarsu Khamna’i, Makarim Shirazi Nuri Hamdani, Subhani, Shubairi Zanjani da Safi Gulfaigani, cikin wannan fatawa sun haramta farin aure. [10] wasu ba’ari tare da jingina da doka mai lamba 1062 daga dokokin farar hula ta jamhuriyar muslunci ta Iran wacce ta ƙunshi kasancewar karanta siga sharaɗi a aure, sun bayyana cewa farin aure ya saɓawa dokokin ƙasar Iran. [11]

Sabubba, Sakamako Da Mafita

Buƙatu na motsin rai (emotional needs), sakacin iyaye kan sa ido cikin mu’amalolin ƴaƴansu da korarsu daga gida, tsawaita shekarun aurar da ƴan mata su na daga sabubban da suka haifar da yaɗuwar farin aure. [12] haka nan kuma an yi bayanin wasu saƙonni da sakamako da yake biye da farin aure.

  • Barazanar Rusa Katangar Dangi. [13]
  • ƙaruwar yaɗuwar haramtattun alaƙoƙi, ɗaukar cikin da ba a shirya masa ba, yawaitar zubar da ciki. [14]
  • Raguwar haihuwa, rashin yarda da ƴaƴan da aka samu daga wannan hanya a hukumance, da rashin makoma gare su. [15]
  • ƙaruwar sakin aure. [16]
  • Cutuwar hankali misalin al’adantuwa da shaye-shaye (Mental injuries such as addiction) [17]

Hanyoyin magance wannan matsala misalin samar da dandalin aure, samar da sana’a , samar da saƙafar ɗaukar nau’yin iyali, ƙarfafa saƙafar auren mutu’a hanyoyi ne da zasu rage yaɗuwar wannan muguwar al’ada a cikin zamantakewa. [18]

Bayanin kula

  1. Bostan, Jami'eh Shinasi Khanuwadeh Ba Negahi be Manabi Islami, 1392shafi na 63; Mohammadi Asl, "Jinsiyat wa Izdiwaje Safid", shafi na 20.
  2. Rahmat Abadi wa Karizi; “Izdiwaje Safid; Payamadha wa Khaɗirat", shafi na 79.
  3. Nosrati wa Digaran, “ Izdiwaje Safid Az Manzare Fiƙihi Huƙuƙi” shafi na 92.
  4. Jafarzadeh Kouchaki wa Siddiƙi, “Barasi Tafawutwa wa Hamsuyiha Izdiwaje Safid Ba Nikahe Mu'aɗati aza manzare fiƙh Imamiyyeh” shafi na 15; Rashidinejad wa Vahad Yarijan, “ Wujuhu Tafawut wa tashabuhi Izdiwaje Mu'aƙƙat ba padide "Izdiwaje Safid" shafi na 84.
  5. Arjamand Danesh wa Digaran, " Mahiyat, wa Mashru'iyyat wa Asare Izdiwaje Safid", shafi na 15.
  6. Hedayatnia, "Nikahu Mu'aɗati az manzarer fiƙkh", shafi na 205; Sadeghi Tehrani,Risaleh Tauzihul Al-Masa'il, 2007, shafi na 281.
  7. Maghribi Kete Shamshiri wa digaran, " Asare wa Payamadhaye Huƙuƙi Izdiwaje Safid dar Iran", shafi na 46; Rahmat Abadi wa Karizi; “Izdiwaje Safid; Payamadha wa Khaɗirat", shafi na 81-82.
  8. Maghribi Kete Shamshiri wa digaran, " Asare wa Payamadhaye Huƙuƙi Izdiwaje Safid dar Iran", shafi na 46; Rahmat Abadi wa Karizi; “Izdiwaje Safid; Payamadha wa Khaɗirat", shafi na 81-82.Nosrati wa Digaran, “ Izdiwaje Safid az Manzare fiƙihi wa huƙuƙi” shafi na 90; Shekar Begi et al., “ Barsakt Ijtima'i Izdiwaje shafi na 69
  9. class="eɗternal teɗt" href="http://ijtihadnet.ir/همباشی-یا-ازدواج-سفید-همان-زنا-است-نظر/">«همباشی یا ازدواج سفید همان زنا است/ نظر آیت‌الله شبیری زنجانی درباره معاطات»سایت شبکه اجتهاد
  10. Arjamand Danesh wa Digaran, "Mahiyat, Mashru'iyyat wa Asar Izdiwaj Safid", shafi na 20
  11. Maghribi Kete Shamshiri wa digaran, " Asare wa Payamadhaye Huƙuƙi Izdiwaje Safid dar Iran", shafi na 50
  12. Shekar Begi et al., “ Barsakt Ijtima'i Izdiwaje shafi na 95
  13. Maghribi Kete Shamshiri wa digaran, " Asare wa Payamadhaye Huƙuƙi Izdiwaje Safid dar Iran", shafi na 57-58Afraz, "Izdiwaje Safid wa Payamadhaye an", shafi na 121
  14. Maghribi Kete Shamshiri wa digaran, " Asare wa Payamadhaye Huƙuƙi Izdiwaje Safid dar Iran", shafi na 55-57. Afraz, "Izdiwaje Safid wa Payamadhaye an", shafi na 121
  15. Afraz, "Izdiwaje Safid wa Payamadhaye an", shafi na 122
  16. Afraz, "Izdiwaje Safid wa Payamadhaye an", shafi na 122
  17. Afraz, "Izdiwaje Safid wa Payamadhaye an", shafi na 122
  18. Maghribi Kete Shamshiri wa digaran, " Asare wa Payamadhaye Huƙuƙi Izdiwaje Safid dar Iran", shafi na 60-63 آتش افروز<a class="eɗternal teɗt" href="http://vasael.ir/fa/news/6759">«راه‌کارهای فقه شیعه در مواجهه با پدیده ازدواج سفید»</a>پایگاه تخصصی فقه حکومتی وسائل

Nassoshi