Istimna'i

Daga wikishia
Wannan wata ƙasida ce ta siffantawa game da mafhumi na fikihu kuma ba za ta iya zama ma'auni na ayyukan addini ba. domin samun cikaken bayani dole a koma zuwa madogaran ayyukan addini na daban.
Risala Ilmiyya

Istimna’i (Larabci: الاستمناء) ko gamsar da kai, wata al’ada ce ta gamsar da kai ta hanyar wasa da al’aurar da fitar da maniyyi, malaman fiƙihu sun bada fatawa kan haramcin istimna’i kuma yana cikin manya-manyan zunubai, hukuncin shari’a kan aikata wannan al’ada idan ta kai ga fitar da maniyyi shi ne ta’aziri kan wanda aka samu da ita wanda ayyana miƙdarin ladabtarwar yana hannun Hakimul Shar’i. Aikata istimna’i ya na janyo wasu hukunce-hukunce daga cikinsu akwai yin wankan janaba, karya azumi, da sauransu…

Sanin Mafhumi

Istimna’i ko gamsar da kai ko kuma ta hanyar wani, wani aiki ne da yake faruwa sakamakon motsin sha’awa da ake wasa da al’aura har ta kai ga fitar da maniyyi [1] a fiƙihu ana amfani da kalmar istimna’i a kan maza a a kan mata kuma ana amfani da kalmar istish’ha [2] an yi maganar istimna’i a cikin babukan azumi [3] Itikafi, [4] Hajji, [5] da Hudud. [6] cikin riwayoyi ma hani ya zo kan wannan mummunar al’ada, sannan babi tahrim istimna’a babi ne da ya keɓantu da riwayoyi kan wannan al’ada. [7] bisa riwaya duk wanda yake aikata istimna’i Allah ba zai kalle shi ba. [8]

Haramcin Istimna’i

A mahangar fiƙihu istimna’i haramun ne, wasu ba’arin malamai suna ganinsa cikin layin manya-manya zunubai. [9] madogararsu kan haramcinsa ta kasance ayoyin Alkur’ani da riwayoyi. [10] cikin tabbatar da haramci a kansa sun kafa hujja da aya ta 6 suratul Muminun [11] kan asasin wannan aya an haramta duk wani nau’in jima’i da ya kasance ba tare da matarka ba ko baiwa, wasu ba’ari sun halasta istimna’i a halin larurara misalin ɗibar maniyyi domin gwaje-gwajen lafiya da suka dogara da wannan hanya. [12] hakan nan kuma bisa fatawar wasu ba’ari daga malaman Shi’a istimna’i da hannun matarka ko baiwarka [13] ya halasta. [14] na’am Allama Hilli hatta wannan wurin ma ya haramta istimna’i.

Hukunce-hukuncen Fiƙihu

Cikin masadir ɗin fiƙihu an yi bayani wasu hukunce-hukunce kan istimna’i a halin da ya kai ga fitar da maniyyi:

  • Janaba: mutumin da ya yi janaba, dole ne ya fara wanka kafin yin sallah, shiga masallaci da kuma wasu ayyukan addini. [15]
  • Karya azumi: istimna’i yana karya azumi kuma waji a bada kaffara kan aikata hakan cikin azumi, bisa fatawar malaman fiƙihun Shi’a, karya azumi ta hanyar aikin haramun yana sabbaba bada kaffarar jam’u (`yantar da bawa, azumin wata biyu, ciyar da talawa guda sittin).[16] tare da haka wasu maraji’an taƙalidi sun tafi kan cewa zai bada kaffarar jam’u ne bisa ihtiyaɗi istihbabi ba wujubi ba. [17]
  • lalata Itikafi: aikata istimna’i yana lalata azumi da itikafi. [18] wasu ba’ari sun tafi kan ra’ayin cewa istimna’i a kankin kansa yana lalata itikafi, saboda ko da a daddare ne aka aikata istimna’i itikafi ya lalace. [19]
  • Aikata Istimna’i a halin Ihrami wajibi a bada kaffara, [20] kuma kaffararsa shi ne raƙumi guda ɗaya [21] haka nan kuma aksarin malaman fiƙihu sun tafi kan ra’ayin cewa aikata istimana’i a halin Ihrami yana ɓata aikin hajji. [22]

Hukuncin Aikata Istimna’i Ana ta’aziri (ladabtarwa) kan wanda aka samu ya aikata istimna’i, sannan ayyana miƙdarin ta’aziri yana hannun Hakimul shar’i. [23] idan aka samu mutum ya maimaita aikata wannan mummunar al’adar za ayi masa hukunci mai mafi tsanani daga na baya. [24] a cewar marubucin littafin Jawahirul Al-Ma’ani, hukuncin istimna’i yana tabbata da shaida maza adalai guda biyu ko kuma iƙrari sau ɗaya daga wanda ya aikata istimna’in. [25]

Illolin Da Aikata Istimna’i Yake Haifarwa

Wasu malamai sun yi bayanin irin illolin da istimna’i yake haifarwa ga gangar jiki da ma ruhi da hankali.

  • Illoli na gangar jiki: raunana idanu, raunana ƙarfin jiki, hana haihuwa, Raunin mahaɗan gwiwowi da girgizar hannu,
  • Illolin Ruhi da Hankali: raunana kwakwalwa da rashin nutsuwa, rarrawa, kaɗaita, yawan damuwa, rashin nishaɗi, rashin danne fushi, yawan kasala da raunanar irada.
  • illoli na zamantakewa: rashin daidatuwar iyali, rashin jin sha’awar matarka da rashin sha’awar aure, raunin mazakuta. [26] da jinkirin aure.

Bayanin kula

  1. Abd al-Moneim, Mujam Almusɗalahat wa Al-Alfazu Al-Fiƙhiyyah, Dar Al-Fadilah, Mujalladi na 1, shafi na 161.
  2. Sohrabpour, Khalwat Shaiɗani, 1390, shafi na 15.
  3. Seyed Morteza, Al-Intisar, 1415 AH, shafi na 178; Mohagheƙ Hilli, Shara’i Al-Islam, 1408H, juzu’i na 1, shafi na 172.
  4. Alameh Hali, Tazkiratul Al-Fuƙaha, 1414 AH, juzu'i na 6, shafi na 257.
  5. Ibn Hamza, Al-Wasila, 1408H, shafi na 159; Allameh Hali, Tazkira Al-Fuƙaha, 1414 AH, juzu'i na 7, shafi na 381.
  6. Ibn Hamza, Al-Wasila, 1408H, shafi na 159; Shaikh Mofid, Al-Muƙna, 1410H, shafi na 791.
  7. Hurru Ameli, Wasa'il Al-Shia, 1416 AH, juzu'i na 20, shafi na 352-355.
  8. Hurru Ameli, Wasa'il Al-Shia, 1416 AH, juzu'i na 20, shafi na 354-355.
  9. Duba: Najafi, Jawahirul Al-Kalam, 1362, juzu'i na 41, shafi.647.
  10. Mu'assaseh Da'iratul Al-Marif Fiƙh islami, Mausu'atu Al-fiƙh Al-islami, 1423 AH, juzu'i na 12, shafi na 219 da 220.
  11. Shaikh ɗusi, Al-Mabusuɗ, 1388H, juzu'i na 4, shafi na 242; ƙutbuddin Rawandi, Fiƙhul ƙur'an, 1405 Hijira, juzu'i na 2, shafi na 144.
  12. Bani Hashemi Khomeini, Risaleh Tauzihul Al-Masa'il Al-Maraji'ah, Ofishin Yada Labarai na Musulunci, juzu'i na 1, shafi na 978.
  13. Mu'assaseh Dayiratul Al-Marif Fiƙhi Islami, Mausu'atu Al-Fiƙhi Al-Islami, 1423 AH, juzu'i na 12, shafi na 219 da 221.
  14. Allama Hilli, Tazkirah Al-Fuƙaha, 1388H, shafi na 577.
  15. ɗabaɗaba'i Yazdi, Al-Urwa Al-Withghati, Mujalladi na 1, shafi na 507-508.
  16. Sheikh Baha'i, Jame Abbasi, 1429H, shafi na 462.
  17. Bani Hashemi Khomeini, Risaleh Tauzihul Al-Masa'il (Maraji), Ofishin Daba’ar Musulunci, juzu’i na 1, shafi na 978.
  18. Duba Najafi, Jawahirul Al-Kalam, 1362, juzu'i na 17, shafi na 207.
  19. Khoei, Minhaj Al-Salehin, juzu'i na 1, shafi na 292.
  20. Ibn Hamza, Al-Wasila, 1408H, shafi na 159; Allama Hilli, Tazkira Al-Fuƙaha, 1414 AH, juzu'i na 7, shafi na 381.
  21. Najm Al-Din Hilli, Izah Al-Taraddudat Al-Sharia, 1428 AH, juzu'i na 1, shafi na 231
  22. Duba Najafi, Jawaher Al-Kalam, 1362, juzu'i na 20, shafi na 367-368.
  23. Najafi, Jawahirul Al-Kalam, 1362, juzu'i na 41, shafi na 647, 649; Sheikh Mufid, Al-Muƙni'a, 1410 AH, shafi na 791; Ibn Idris Hali, Kitab As-sara'ir, 1410H, juzu'i na 3, shafi na 536.
  24. Duba: Ibn Hamzah ɗusi, Al-Wasila, 1408H, shafi na 415.
  25. Najafi, Jawahirul Al-Kalam, 1362, juzu'i na 41, shafi na 649.
  26. <a class="eɗternal teɗt" href="http://fa.parsiteb.com/news.php?nid=9128">تاثیرات استمنا بر زندگی زناشویی</a>

Nassoshi

  • Abdul Moneim, Mahmoud Abdul Rahman, Mujam Almusɗalahat The Dictionary of Al-Tirmidhom and Al-Alfaz al-Fiƙhiyyah, Cairo, Dar Al-Fadilah, Bita.
  • Allama Hilli, Hasan Bn Yusuf, Tadzkirah Al-Fuƙaha, wanda Kungiyar Bincike ta Cibiyar Al-Baiti ta ƙom, Cibiyar Al-Baiti, 1414H.
  • Allama Hilli, Hasan bin Yusuf, Tazkira Al-Fuƙaha, ƙum, Al-Bait Institute, 1388H.
  • Bani Hashemi Khomeini, Mohammad Hasan, Risaleh Tauzihul Al-Masa'l (References), ƙom Seminary Madrasin Society, Islamic Publications Office, Beta.
  • Hurru Amili, Muhammad Bin Hassan, Wasa'ilul Al-Shia' Litahsilul Ahkam Al-Shari'a, ƙum, Al-Bayt Lahiya Al-Trath Foundation, bugu na uku, 1416H.
  • Ibn Hamzah ɗusi, Muhammad Bin Ali, Al-Wasila El-Nil Al-Fadilah, ƙum, Publications of Ayatullah Marashi Library, 1408H.
  • Ibn Idris Hilli, Muhammad Ibn Ahmad, Al-Saraer Al-Hawi li Tahrir al-Fatawi, ƙum, Islamic Publications Office, 1410 AH.
  • Khoi, Sayyid Abul ƙasim, Minhaj Al-Salehin, ƙum, Madinar Kimiyya, 1410H.
  • Mohaghegh Hilli, Jafar bin Hassan, Shara'e Al-Islam fi Al-Halal wa Haram, ƙum, Isma'il Press Institute, bugu na biyu, 1408H.
  • Muassaseh Dayirat, Farhang Fiƙh Muɗabiƙ Mazhab Ahlul-Baiti Alaihim Salam, ƙum, Institute of Encyclopedia of Islamic Fiƙhu, 1423H.
  • Muassaseh Dayirat, Farhang Fiƙh Muɗabiƙ Mazhab Ahlul-Baiti Alaihim Salam, ƙum, Institute of Islamic Fikihu Encyclopaedia, 1385.
  • Najafi, Mohammad Hasan, Jawaher Al-Kalam fi Sharh Shariah Al-Islam, bincike ta Mahmoud ƙochani, Beirut, Dar Ahya Al-Trath al-Arabi, bugu na 7, 1362.
  • Najm Al-Din Hilli, Izahu Taraddudatul Al-Shara'i, Sayyid Mahdi Rajaee, ƙum, Ayatullahi Murashi Najafi Publications Library, 1428H.
  • Seyyed Morteza, Al-Intisar fi Infradat Al-Imamiyah, edita daga: Sashen Bincike na Ofishin Daba'ar Musulunci, ƙum, Ofishin Daba'ar Musulunci, 1415H.
  • Sheikh Baha'i, Baha'ul-Din, Jame Abbasi wa Takmili An Mohashi, sabon bugu, ƙum, ofishin wallafe-wallafen Musulunci, 1429H.
  • Sheikh Mufid, Muhammad bin Muhammad, Al-Muƙna'a, ƙum, Jama'at al-Madrasin, 1410H.
  • Sheikh Tusi, Muhammad bin Hassan, al-Massut fi fiƙhu al-Umamiyah, bincike na Mohammad Baƙir Behboodi, Tehran, al-Muktaba al-Mortazawieh, bugu na uku, 1388H.
  • Sohrabpour, Ali, Khalwat Shaiɗani:, ƙom, Gidan Bugawa Maarif, 1390.
  • ƙutb Al-Din Rawandi, Sa'eed bin Hebatullah, Fiƙh Al-ƙur'an, ƙum, Ayatullah Marashi Library Publications, 1405 AH.