Maɗigo

Daga wikishia

Maɗigo, (Larabci المساحقة) ma’ana mace ta goga farjinta kan farjin ƴar’uwarta mace cikin wani yanayi na neman jin daɗi da biyan buƙata, cikin riwaya an yi bayani tanadin azabar mai tsanani ga masu yin wannan mummunar al’ada, cikin riwayoyin shi’a an bayyana maɗigo matsayin babbar zina tare da tsinuwa kan masu yin maɗigo. Malaman fiƙihu na Shi’a bisa dogara da riwayoyin Ma’sumai, sun yi fatawa kan haramcin maɗigo da kuma bulala ɗara ga wanda aka samu sun aikata wannan mummunar al’ada, bisa fatawar aksarin Malaman Shi’a, hanyoyi tabbatar da maɗigo shi ne shaidar maza huɗu adalai ko kuma wacce ake tuhuma da akaita wannan aiki ta yi iƙrarin aikatawa har sau huɗu, na’am idan mai lefin ta tuba kafin tabbatar da lefin da ta aikata ba za a tsayar da hukunci a kanta ba, bisa fatawar galibin Malamai, idan aka tsayar da haddin aikata maɗigo kan mace har karo uku to na huɗu za a jefeta.

Mafhumin Maɗigo da Matsayinsa A Shari’a

Malaman fiƙihu na Shi’a sun bayyana cewa maɗigo shi ne mace ta goga farjinta kan farjin wata mace. [1] Maɗigo wata hanya ce ta neman jin daɗi na jinsi (Lesbian) ɗaya daga hanyoyi jinsi ce da mata ƴan maɗigo [2] suke amfani da ita. [3]

Tarihi Da Matsayi

Cikin riwayoyi an ƙirga maɗigo matsayin babbar zina, [4] tare da tsinewa masu maɗigo, [5] an kuma yi bayanin azabar mai tsanani a kansu ranar alƙiyama, [6] kan asasin wata riwaya daga Imam Sadiƙ (A.S) mata na farko da suka fara aikata maɗigo sune mutanen Annabi Luɗ (A.S) saboda cikin waɗannan mutane aka samu maza suna lalata da maza mata suna lalata da mata, da wannan dalili mata suka rasa mazaje, sai ya zamana mata suna aikata irin abin da maza suke aikatawa da ƴan’uwansu maza, [7] a cikin wata riwaya [8] abin da ake nufi da As’habul Rassi cikin aya 12 suratul ƙaf shi ne masu aikata maɗigo.

Maɗigo A Mahangar Fiƙhu

Cikin fiƙihun Shi’a, hukuncin taklifi dangane da maɗigo shi ne Haramci, sannan an yi bayanin hanyoyin tabbatar da shi da kuma uƙubar da shari’a ta tanada a kansa.

Kasancewarsa Haramun

A cewar Allama Hilli, babban Malamin fiƙihun Shi’a a ƙarni na takwas h ƙamari, ya tafi kan haramcin Maɗigo, [9] cikin wata riwaya daga Imam Rida (A.S) a cikinta ya yi bayani illa da dalilin haramta jima’i da jinsi ɗaya wanda ya haɗa har da maɗigo cikin mata, ya kasance bisa tsarin halittar mata da karkartar hallittar sha’awar maza zuwa ga mata. [10] haka kuma cikin wannan riwaya karkata zuwa ga sha’awar jinsi ɗaya daidai yake da ƙarar da tsatson ɗan Adam, lalata tsari da gudanarwar al’umma da halaka duniya. [11]

Hanyoyi Tabbatar Da Maɗigo

Kan asasin fatawar aksarin Malaman Shi’a, maɗigo yana tabbatuwa ta hanyar shaidar maza huɗu adalai ko kuma wacce ta aikata maɗigo ta yi iƙrari sau huɗu, [12] kishiyar wannan ra’ayi, Ayatullahi Ardabili Malamin fiƙihu a ƙarni na goma h ƙamari, ya tafi kan cewa shaidar maza biyu adalai ko kuma mace ta yi iƙrari sau biyu kaɗai yana wadatarwa, [13] kan asasin doka mai lamba 172 da 199 daga dokokin uƙuba na jamhuriyar muslunci ta Iran [14] maɗigo yana tabbata ne ta hanyar shaidar maza huɗu ko iƙrarin matar da ta aikata maɗigon.

Uƙubar Aikata Maɗigo

Gabaɗayan Malamai fiƙihu na shi’a sun tafi kan cewa akwai haddi na shari’a kan aikata maɗigo, [15] a fatawarsu za a yi bulala ɗari-ɗari kan kowacce ɗaya daga cikin matan da suka aikata maɗigo kuma babu banbanci tsakanin musulma da kafira, [16] haka kuma a cewar marubucin littafin Jawahir Al-Kalam Malamin fiƙihu na shi’a a ƙarni na goma sha uku h ƙamari, haƙiƙa cikin wannan hukunci babu banbanci tsakanin matar aure da wacce ba ta da aure, [17] kishiyarsa, Shaik ɗusi, [18] Ibn Barraj [19] da Ibn Hamza ɗusi [20] daga Malaman fiƙhu a ƙarni na biyar h ƙamari, sun tafi kan cewa haddin uƙuba kan aikata maɗigo daga mace mai aure shi ne a jefeta. Kan asasin doka mai lamba 239 da 240 dokar uƙuba ta muslunci ta jamhuriyar muslunci ta Iran, uƙubar aikata maɗigo shi ne bulala ɗari, [21] babu bambanci tsakanin Musulma da Kafira, mai aure da mara aure. [22] A fatawar Malaman fiƙihun Shi’a, idan mace ta tuba to ba za a mata haddi ba, a cewar marubucin littafin Riyad, Malamin fiƙihu na Shi’a a ƙarni na goma sha biyu h ƙamari,, aksarin Malaman fiƙihun Shi’a sun yi fatawa idan maɗigon mace ya tabbata har karo uku kowanne ɗaya za a mata bulala ɗari, idan ta ƙara aikata a karo na huɗu sai a kasheta kawai, [23] Ibn Idris Hilli Malamin fiƙihun Shi’a a ƙarni na shida h ƙamari, [24] ya tafi kan cewa za a zartar da kisa a kanta a idan aka ƙara tabbatar da ta aikata maɗigo a karo na uku.

Bayanin kula

  1. Misali, duba Allama Hilli, Tahrir Al-Ahkam, 1420 AH, juzu'i na 5, shafi na 333; Shahid Sani, Al-Rawda Al-Bahiya, 1412 AH, juzu'i na 2, shafi.361; Tabatabai Hae'ri, Riyadh Al-Masa'il, 1418 AH, juzu'i na 16, shafi na 5.
  2. Kimmel, Gay, Bise ɗual, and Transgender Aging: Research and Clinical Perspectives, pp. 73–79.
  3. Dehkhoda, Luggatnameh Dehkhoda, Zaile wajehr " ɗaba ƙ Zani".
  4. Kulaini, Al-Kafi, 1429 Hijira, juzu'i na 11, shafi na 274.
  5. Kulaini, Al-Kafi, 1429 Hijira, juzu'i na 11, shafi na 267 da shafi na 274.
  6. Kulaini, Al-Kafi, 1429 Hijira, juzu'i na 5, shafi na 257 da juzu'i na 11, shafi na 273.
  7. Kulaini, Al-Kafi, 1429 AH, juzu'i na 11, shafi na 273.
  8. Kulaini, Al-Kafi, 1429 Hijira, juzu'i na 14, shafi na 83.
  9. Allama Hilli, Tahrir Al-Ahkam, 1420 AH, juzu'i na 5, shafi na 333.
  10. Shaikh Sadu ƙ, Ilalul Ash-Shara'i, Maztabat Al-Davari, juzu'i na 2, shafi na 547.
  11. Shaikh Sadu ƙ, Ilalul Ash-Shara'i, Maztabat Al-Davari, juzu'i na 2, shafi na 547.
  12. Misali, duba Shaikh ɗusi, Al-Nihaya, 1400H, shafi na 706; Shahidi na Farko, Al-Lam'atu Al-Damash ƙiya, 1410H, shafi na 257.
  13. Mu ƙaddis Ardabili, Majma Al-Fa'edat, Jami'at Al-Mudarrisin, juzu'i na 13, shafi na 127.
  14. <a class="e ɗternal te ɗt" href="https://rc.majlis.ir/fa/law/show/845048">قانون مجازات اسلامی</a>مرکز پژوهش‌های مجلس شورای اسلامی ایران.
  15. Misali, duba Shaikh ɗusi, Al-Nihaya, 1400H, shafi na 706; Mu ƙaddis Ardabili, Jama Al-Fa'edat, Jamaat Al-Muddarisin, juzu'i na 13, shafi na 120; Sheikh Mufid, al-Mu ƙni'a, 1410 AH, shafi na 787.
  16. Misali, duba Shaikh ɗusi, Al-Nihaya, 1400H, shafi na 706; Mu ƙaddis Ardabili, Jama Al-Fa'edat, Jamaat Al-Muddarisin, juzu'i na 13, shafi na 120; Sheikh Mufid, al-Mu ƙni'a, 1410 AH, shafi na 787.
  17. Sahib Jawaher, Jawaher Al-Kalam, 1362, juzu'i na 41, shafi na 388.
  18. Sheikh ɗusi, Al-Nihaya, 1400H, shafi na 706.
  19. Misali, duba Ibn Baraj, Al-Muhazzab, 1406H, juzu’i na 2, shafi na 531; Sheikh ɗusi, Al-Nihaya, 1400H, shafi na 706.
  20. Ibn Hamzah ɗusi, Al-Wasila, 1408H, shafi na 414.
  21. <a class="e ɗternal te ɗt" href="https://rc.majlis.ir/fa/law/show/845048">قانون مجازات اسلامی</a>مرکز پژوهش‌های مجلس شورای اسلامی ایران
  22. Misali, duba Shaikh ɗusi, Al-Nihaya, 1400H, shafi na 708; Sahib Jawaher, Jawaher Al-Kalam, 1432 AH, juzu'i na 41, shafi na 390.
  23. Sahib Riyad, Riyad Al-Masa'il, 1404 AH, juzu'i na 2, shafi na 477.
  24. Bin Idris, Al-Sara'iru, 1410 AH, Mujalladi na 3, shafi na 467.

Nassoshi

  • Allama Hilli, Hasan bin Yusuf, Tahrir Al-Ahkam, ƙum, Imam Al-Sadi ƙ (A.S), 1420 H.
  • Ibn Baraj, Abd al-Aziz bin Nahrir, al-Muhazzab, ƙum, Jamaat al-Muddarisin fi Al-Hawza Al-Ilamiya in ƙum, Al-Nashar Al-Islami Foundation, 1406 AH.
  • Ibn Idris, Hali, al-Sara'iru Al-Hawi Litahrir Al-fatawi, ƙum, Al-Nashar Al-Islami Foundation of Jama’ah al-Madrasin, 1410 H.
  • Sahib Riyad, Ali bin Muhammad Ali, Riyad Al-Masa'il, ƙum, Al-Bait (a.s.) Lahiya al-Tarath, 1404H.
  • Shahidi Awwal, Muhammad bin Makki, Al-Lam'a Al-Damash ƙiyyah fi fi ƙhu Al-Imamiya, Muhammad Ta ƙi Marwarid da Ali Asghar Marwarid suka yi bincike a Beirut, Darul-Tarath, 1410H.
  • Sheikh Mufid, Muhammad bin Muhammad, Al-Mu ƙni'a, Kum, Jama'atul Muddarisin fi Al-Hawza Al-Ilimiya a ƙum, 1410H.
  • Tabatabai Ha'eri, Sayyid Ali, Riyad Al-Masa'il, ƙum, Al-Bait (A.S.) Foundation, 1418H.
  • «قانون مجازات اسلامی»، مرکز پژوهش‌های مجلس شورای اسلامی ایران، تاریخ بازدید: ۱۸ مهر ۱۴۰۲ش.
  • ابن حمزه طوسی، محمد بن علی، الوسیلة الی نیل الفضیلة، تحقیق محمد الحسون، قم، منشورات مکتبة المرعشی النجفی، ۱۴۰۸ق.
  • دهخدا، علی‌اکبر و گروهی از نویسندگان، لغت‌نامه دهخدا، تهران، روزنه، ۱۳۷۲-۱۳۷۳ش.
  • شهید ثانی، زین‌الدین بن علی عاملی، الروضة البهیة فی شرح اللمعة الدمشقیة، شرح حسن بن محمد سلطان العماء، قم، دفتر تبلیغات اسلامی حوزه علمیه قم، ۱۴۱۲ق.
  • شیخ صدوق، محمد بن علی، علل الشرائع، مقدمه و شرح محمدصادق بحرالعلوم، قم، مکتبة الداوری، بی‌تا.* Shaikh ɗusi, Muhammad bin Hasan, Al-Nihaya fi majard fi ƙh wa Al-fatawi, Beirut, Dar al-Kitab al-Arabi, 1400 AD.
  • صاحب جواهر، محمدحسن بن باقر،‌ جواهر الکلام فی شرح شرائع الاسلام، بیروت، دار احیاء التراث العربی، ۱۳۶۲ش.
  • کلینی، محمد بن یعقوب، الکافی، تحقیق و تصحیح دارالحدیث، قم، دارالحدیث، ۱۴۲۹ق.
  • مقدس اردبیلی، احمد بن محمد، مجمع الفائدة و البرهان فی شرح ارشاد الاذهان، تحقیق مجتبی عراقی، علی اشتهاردی، حسین یزدی، قم، جامعة المدرسین فی الحوزة العلمیة فی قم، بی‌تا.