Khalilullahi (Laƙabi)

Daga wikishia


Khalilullahi (Larabci: خليل الله) ma’ana Badaɗin Allah.[1] sunan Annabi Ibrahim ne.[2] kasancewarsa Khalilullahi ya kasance abin yabo ga Ibrahim.[3] wanda ya fi matsayin Annabci da Manzonci.[4] a wata ruwaya. daga Imam Sadiƙ (A.S) an ce da farko Allah ya ɗauki Ibrahim a matsayin bawa, sannan annabi, sannan kuma manzo, sannan ya ɗauke shi a matsayin badaɗinsa (Khalil).[5]

A cikin aya ta 125 a cikin suratul Nisa'i ya zo cewa: و اتَّخَذَ اللَّهُ إِبْراهیمَ خَلیلاً؛ Kuma Allah ya zaɓi Ibrahim a matsayin badaɗayinsa.[6] kalmar "ttikaza" ta zo da ma'anar zaɓa.[7] a farkon wannan aya an yi wasicci da biyayya da addinin Ibrahim.[8] bayan nan domin kwaɗaitar da sauran mutane zuwa ga addinin Ibrahim, an ce da saboda haka ne Allah ya zaɓe shi badaɗayi.[9] Zamakhshari malamin Ahlus-Sunna kuma mai sharhi da tafsiri ya ɗauki ma'anar badaɗayi matsayin misali, wanda hakan alama ce ta zaɓar Ibrahim da aikin da ya yi a kan siffa da ke tsakanin badaɗayi biyu.[10]

A cikin Ruwayoyi ana amfani da kalmar Khalilullahi ga Annabi Ibrahim.[11] Shi ma Ibrahim (a.s) ya kira kansa Khalilullah,[12] musulman garin ƙasar palasɗinu da aka mamaye wannan ƙasa da Ibrahim ya rayu a cikinta.[13] saboda abin da aya ta 125 ta Nisa’i suna kiransa Khalil.[14] tare da wannan laƙabi ya keɓantu da Annabi Ibrahim, sai dai a wasu ruwayoyi da addu’o’i cikin siffanta Annabi Muhammad (s.a.w), Imam Ali (A.S).[15] Imam Husaini (A.S).[16] nan ma haka an yi amfani da wannan kalma da khalil.

cikin Adabin farisanci nan ma an yi amfani da kalmar khalil kan Annabi Ibrahim (A.S). Mulla Ahmad Naraƙi cikin zubin waƙar Masnawi ɗaƙidis ya rere baituƙan waka kamar haka:

برگزید او را خداوند جلیل خواند او را از برای خود خلیل

خلعت خُلَّت رسید او را ز رب آمد او را هم خلیل الله لقب

Allah ne ya zaɓe shi ya kira shi da sunan khalil.

wanda ya zaɓe shi shi ne Allah mai girma. Khulat Khullat ya isa gare shi daga ubangijinsa aka ce masa Khalilullah.[17]

wani Mawaki kuma ya rera:

بنای خانه کعبه خلیل الله نهاد اما علی در کعبه ظاهر گشت و صاحبخانه پیدا شد

Khalilullah ya gina gidan Ka’aba, amma Ali ya bayyana a ɗakin ka’aba, aka samu mai [18]

Hadisai sun ambato abubuwa daban-daban a matsayin falalar Ibrahim, wanda ya sa Allah ya ba shi wannan matsayi.[19] A cikin Littafin Ilalush-shara'i, akwai wani sashi mai suna “Abubuwan suka janyo Allah ya sanya Ibrahim ya zama abokinsa”[20] A cikin wannan ɓangare an hadisai da dama.[21] An ce akwai : yawan sujjada, ciyar da mabuƙata, sallar dare, ƙin korar mabuƙaci, da karɓar baƙi[22] da rashin neman wani abu face Allah.[23] Wasu malaman tafsiri kuma sun ambaci watsi da gumaka da bautar Allah.[24]

Ma'anar Khalil

An yi la'akari da ma'anoni biyu masu yiwuwa ga kalmar Khalil

Khalil yana nufin aboki; Kalmar Khalil ta samo asali ne daga al-Khullah, ma’ana badaɗayi ko aboki[25] Fassarar Majma al-Bayan na tafsirin ƴan Shi’a da aka rubuta a ƙarni na shida ya ambaci wannan ma’anar Khalilullah da ma'anar abota,[26] makarim shirazi daga masu tafsirin shi'a shi ma yace: lokacin da Allah ya zaɓi Annabi Ibrahim kuma ya bashi wannan sunan yana nufin wannan ma'anar ta abota, kuma babu wata ma’ana da ta dace.[27] sauran malaman tafsiri ma suna ganin wannan ma’anar daidai ce.[28]

Khalil kalma ce wacce take nufin talauci; An samo Khalil daga al-khala, ma’ana talauci.[29] Wasu suna ganin Khalil ga Annabi Ibrahim yana nufin shi talaka ne mabukaci a wajen Allah,[30] Allama ɗabaɗaba'i ya ce: Khalil yana nufin talauci. A mahangarsa ma’anar gaskiya ita ce, ɗaukar Khalilullah a matsayin mutum ne mai kai buƙatunsa ga Allah kawai kuma yana roƙonsa ya biya masa buƙatunsa wato baya nema gun wanda ba Allah ba.[31]

Bayanin kula

 1. Makarem Shirazi, Tafsir Namuneh, 1374 AH, juzu'i na 4, shafi na 145.
 2. Mughniyah, Tafsir al-Kashif, 1424 AH, juzu'i na 2, shafi 448.
 3. Abu al-Futuh Razi, Rawd al-jinan wa Ruh al-jinan fi Tafsir al-ƙur’an, 1408 AH, juzu’i na 6, shafi na 129.
 4. Mughniyah, Tafsir al-Kashif, 1424 AH, juzu'i na 2, shafi 448.
 5. Kulayni, Al-Kafi, 1407 AH, juzu'i na 1, shafi na 175.
 6. Suratul Nisa’i, aya ta 125.
 7. Kashani, Zabadat al-Tafsir, 1423 BC, juzu'i na 2, shafi na 160.
 8. Hosseini Shirazi, Tabyin Al-ƙur’an, 1423 AH, shafi na 109.
 9. Ibn Kathir Dimashƙi, Tafsir Alƙur’an Al-azeem, 1419 Hijira, juzu’i na 2, shafi na 374.
 10. Zamakhshari, Al-Kashf fi Haƙaiƙ gawamiz At-tanzil, 1407 AH, juzu'i na 1, shafi 569.
 11. Kulayni, Al-Kafi, 1407 AH, juzu'i na 1, shafi 473
 12. Kulayni, Al-Kafi, 1407 AH, juzu'i na 4, shafi na 205.
 13. Lahuti, “Khalil”, shafi na 91.
 14. Lahuti, “Khalil”, shafi na 91.
 15. Ibn ƙolwieh, Kamel al-Ziyarat, 1356, nassi, shafi na 44.
 16. Sheikh Tusi, Tahzeeb al-Ahkam, 1407 AH, juzu'i na 6, shafi na 113.
 17. نراقی، مثنوی طاقدیس، بخش ۱۳۵، «سبوح قدوس رب الملائکة والروح» گفتن جبرئیل و بیهوش شدن ابراهیم خلیل، سایت گنجور.
 18. صغیر اصفهانی، دیوان اشعار، قصاید، شمارهٔ ۱۷ «در تهنیت عید مولود مسعود امیرالمؤمنین علی علیه‌السلام»
 19. Makarem Shirazi, Tafsir Namuneh, 1374, juzu'i na 4, shafi na 146.
 20. Sheikh Saduƙ, Ilal al-Shara’i’, 1385H, juzu’i na 1, shafi na 34
 21. Sheikh Saduƙ, Ilal al-Shara’i’, 1385H, juzu’i na 1, shafi na 34-37.
 22. Kira'ati, Tafsir Nour, 1383 AH, juzu'i na 2, shafi na 395.
 23. Tabatabai, Al-Mizan fi Tafsir Al-ƙur’an, 1417 AH, juzu’i na 5, shafi na 96.
 24. Madrasi, Min Hadayi al-ƙur’an, 1419 AH, juzu’i na 2, shafi na 201.
 25. Sheikh Tusi, Al-Tibyan fi Tafsir Al-ƙur’an, Beirut, juzu’i na 3, shafi na 340.
 26. Tabarsi, Majma’ al-Bayan fi Tafsir al-ƙur’an, 1372 AH, juzu’i na 3, shafi na 178.
 27. Makarem Shirazi, Tafsir Namuneh, 1374 AH, juzu'i na 4, shafi na 145.
 28. Talƙani, Partwa Az-ƙur’an, 1362 AH, juzu’i na 6, shafi 195; Tayyab, Atyab Al-Bayan fi Tafsir Al-ƙur’an, 1378 AH, juzu’i na 4, shafi na 221
 29. Sheikh Tusi, Al-Tibyan fi Tafsiri Al-ƙur’an, Beirut, juzu’i na 3, shafi na 340.
 30. Najafi Khumaini, Tafsir Asan, 1398H, juzu'i na 6, shafi na 253.
 31. Tabatabai, Al-Mizan fi Tafsir Al-ƙur’an, 1417 AH, juzu’i na 5, shafi na 96.

Nassoshi

 • Abol Fattouh Razi, Hossein bin Ali, Ruz al-Jinnan da Ruh al-Jinnan fi Tafsir al-ƙur'an, bincike na Mohammad Jaafar Yahaghi, Mohammad Mahdi Naseh, Mashhad, Astan ƙuds Razaɓi Islamic Research Foundation, 1408 AH.
 • Hosseini Shirazi, Sayyid Muhammad, Tabayin al-ƙur'an, Beirut, Darul Uloom, bugu na biyu, 1423H.
 • Ibn Kathir Damaschi, Ismail bin Amr, Tafsir al-ƙur'an al-Azeem, bincike na Muhammad Hossein Shams al-Din, Beirut, Dar al-Kitab al-Alamiya, Muhammad Ali Bizoun, bugu na farko, 1419H.
 • Ibn ƙolwieh, Jafar bin Muhammad, Kamel al-Ziyarat, mai bincike kuma mai bincike Abdul Hossein Amini, Najaf, Dar al-Mortazawieh, bugun farko, 1356.
 • Kashani, Mulla Fathullah, Zubda al-Tafaseer, ƙum, Islamic Studies Foundation, bugun farko, 1423H.
 • Kulaini, Muhammad bin Yaƙub, al-Kafi, mai bincike kuma mai karantawa Ali Akbar Ghafari, Muhammad Akhundi, Tehran, Dar al-Kitab al-Islamiyya, bugu na 4, 1407H.
 • Lahoti, Behzad, "Al-Khalil", Encyclopaedia of Islamic World, Juzu'i na 16, Tehran, Islamic Encyclopaedia Foundation, 1390.
 • Madrasi, Sayyid Muhammad Taƙi, Man Hadayi al-ƙur'an, Tehran, Darmhabi Al-Hussein, bugu na farko, 1419H.
 • Makarem Shirazi, Nasser, Tafsir Namuneh, Tehran, Darul-e-Kitab al-Islamiyya, bugun farko, 1374.
 • Mughniyeh, Mohammad Jaɓad, Tafsir al-Kashif, Tehran, Darul-e-Kitab al-Islamiyya, bugun farko, 1424H.
 • Najafi Khomeini, Mohammad Jaɓad, Tafsir Asan, Tehran, Islamic Publications, bugun farko, 1398H.
 • ƙaraati, Mohsen, Tafsir Noor, Tehran, Cibiyar Al'adu ta Al'kur'ani, bugun 11, 2003.
 • Sheikh Sadouƙ, Dokokin Shari'a, Kum, Kasuwar Littattafai Daɓari, bugun farko, 1385.
 • Sheikh Sadouƙ, Man La Yahdara al-Faƙihu, mai bincike kuma mai karantawa: Ali Akbar Ghafari, ƙum, ofishin wallafe-wallafen Musulunci, bugu na biyu, 1413 AH.
 • Sheikh Tusi, Muhammad bin Hasan, Al-Tabyan fi Tafsir al-ƙur'an, gabatarwa: Sheikh Agha Bozur Tehrani, bincike: Ahmad ƙusayr Aamili, Beirut, Dar Ahya Al-Trath al-Arabi, Beirut, Bita.
 • Sheikh Tusi, Muhammad bin Hassan, Tahdhib al-Ahkam, Hasan al-Musawi, Khurasan, Tehran, Dar al-Kutub al-Islamiyyah, ya buga, 1407 BC.
 • Tabarsi, Fazl bin Hassan, Majma al-Bayan fi Tafsir al-ƙur'an, gabatarwa: Mohammad Jaɓad Balaghi, Tehran, Nasser Khosrow, bugu na uku, 1372.
 • Tabatabai, Seyyed Mohammad Hossein, Al-Mizan fi Tafsir Al-ƙur'an, ƙum, Islamic Publications Office, bugu na biyar, 1417H.
 • Tayeb, Seyyed Abdul Hossein, Atyeb al-Bayan fi Tafsir al-ƙur'an, Tehran, Islam Publications, bugu na biyu, 1378.
 • Zamakhshari, Mahmoud, Al-Kashaf akan haƙiƙanin Ghwamaz al-Tanzil, Beirut, Darul Kitab al-Arabi, bugu na uku, 1407H.
 • صغیر اصفهانی، محمدحسین، دیوان اشعار، قصاید، شمارهٔ ۱۷ «در تهنیت عید مولود مسعود امیرالمؤمنین علی علیه‌السلام، سایت گنجور، تاریخ بازدید: ۱۳ اسفند ۱۴۰۲ش.
 • نراقی، ملا احمد، مثنوی طاقدیس، بخش ۱۳۵، «سبوح قدوس رب الملائکة والروح» گفتن جبرئیل و بیهوش شدن ابراهیم خلیل، سایت گنجور، تاریخ بازدید: ۱۳ اسفند ۱۴۰۲ش.
 • Taleghani, Seyyed Mahmoud, Partoɓi az Alƙur'ani, Tehran, kamfanin buga littattafai, bugu na 4, 1362.