Daƙiƙa:Wilaya Takwniyya
Wilaya takwiniyya ko wilaya kan halitta (Larabci: الولاية التكوينية), magana ce game da ƙudura da iko da ya wuce ɗabi'a da zahiri kan ikon tasiri da sarrafa halitta, wilaya takwiniyya ta Allah tana da ma'anar cikakken ikonSa cikin tasiri da sarrafa dukkanin halittu da kuma tafiyar dukkanin al'amuransu. Mas'alar wilaya takwiniyya a mazhabar Shi'a mas'ala ce da aka bijira kanta tare da tattaunawa musamman dangane da Annabi (S.AW) da Imamai. Haka kuma tana cikin shahararrun mas'aloli a ilimin irfanin Muslunci. A cikin adabi malaman Shi'a sun yarda da tushen samuwar wannan wilaya ga Annabi da Imamai; Sannan game da iyakokin wannan wilaya ga Annabi da Imamai akwai mahanga guda biyu:
Bisa mahanga ta farko, wilaya takwiniyyar Annabi da Imamai iyakantacciya ce cikin keɓantattu wasu al'amura , kamar sanin abin da yake ɓoye cikin zukatansu wasu mutane da ikon shiga da sarrafawa wace ta wuce abin da aka al'adantu kansa cikin abubuwa. Kan asasin mahanga ta biyu baki ɗayan al'amuran halittu, daga jumla rayawa da kashewa dukkansu suna ƙarƙashin wilayar Annabi da Imamai, kuma ta hanyarsu ne Allah yake kwarara failar falalar samuwa ga talikai da duniya.
Gabatarwa
Wilaya takwiniyya na nufin ƙarfi da iko da ya wuce abin da aka al'adantu kansa, wanda yake sarrafa halittu da abubuwa a duniya. Ma'ana Allah yana da cikakken ikon sarrafawa cikin dukkanin halittu.[1] Ko kuma wani mutum da ya kai ga cimma kamalar ruhaniya, wanda da izinin Allah yana iya samar da canji wanda ya saɓa da al'ada a cikin halittu.[2] Murtada Muɗahhari malamin aƙida a Shi'a (Rasuwa:1980M) yana bayyana cewa wilaya takwiniyya da ma'ana iko da Allah ya sallama zuwa ga hannun wani mutum domin ya sarrafa halitta gaba ɗaya, matsayin wani abu ne da ba zai taɓa yiwuwa ba, kuma yana ɗaukar taku na farko na wannan wilaya (Wanda shi ne dai ƙudura da iko) matsayin ibada ta gaskiya ga Allah, wace take farawa da iko kan mutum da gaɓoɓinsa,sha'awe-sha'awensa, tunaninsa da zuciyarsa, bayan nan tana kaiwa ga tasiri da makka a cikin sassan halittun duniya.[3] Wasu misalai daga samfura na wilaya takwiniyya sune: Mu'ujizozi da karamomi na Annabawa da Imamai, abubuwa da suka saɓawa al'ada kamar naɗe ƙasa[4] tafiya kan ruwa.[5] sanin baɗinin mutane[6] magana da dabbobi,[7] raba gangar jiki da ruhi[8] sarrafa ɗabi'a ta hanyar ƙudura da ƙarfin wahayi.[9]
Mece Ce Mas'alar Wilaya Takwiniyya
A cikin litattafai na Muslunci, mafi yawan lokuta ana tattauna mas'alar wilaya takwiniyya game da mutum. Tambayoyi da ake bijirowa da su cikin wannan batu shi ne cewa shin mutum zai iya kasance tare da wilaya takwiniyya ko kuma a a, idan zai iya zama yana da ita, to mene ne zurfi da iyakokin wannan wilaya da yake da ita.[10]
Wilaya takwniyya ba ta da ma'anar mutum ya yi addu'a, Allah ya zartar da al'amuran da suka saɓa da al'ada cikin amsa masa addu'a;[11] Ma'anarta shi ne mutum saboda cikakkiyar bauta ga Allah zai iya kaiwa ga wani matsayi na ruhaniya wanda da shi ne zai zai iya yin tasiri na kai tsaye a cikin halittu, na'am wannan tasiri da sarrafawa yana kasancewa ne ƙarƙashin izinin Allah..[12]
Tushen Wannan Mas'ala
A cewar Murtada Muɗahhari (Rayuwa: 1920-1980M) a mahangar Shi'a ita mas'ala wilaya takwiniyya mas'ala ta irfani da kuma addini; amma shaidu na tarihi suna cewa shi'anci shi ne tushen irfanin Muslunci.[13] An naƙalto hadisai daga Imaman Shi'a wanda a cikinsu aka yi magana game da fawwala da miƙa al'amarin gudanar da al'amuran halittu da Allah ya yi zuwa hannun Annabi (S.A.W) da Imamai. Cikin ba'arin waɗannan hadisai, an tabbatar da Tafwiz (Fawwala al'amarin halittu)[14] cikin wasu ba'ari kuma an yi watsi da shi.[15]
Kan asasin bincike, mas'alar wilaya takwiniyya, a karon farko a ƙarni na uku hijira ƙamari, aka fara tattaunawa kanta ƙarƙashin taken "Wilaya" kuma a cikin irfanin Muslunci. Bayan nan, aka ci gaba da bijiro da ita cikin irfanin Muslunci har zuwa bayyanar Muhuyid-dini Ibn Arabi (Rayuwa: 560-638H) wanda ya faifaice sharhi kan wannan mas'ala.[16] Wannan bincike ya kuma nuna cewa haɗaɗɗiyar kalmar (Wilaya takwiniyya) a matsayin isɗilahi ta fara bayyana ne a ƙarnoni na zamani, musammam ma a cikin rubuce-rubucen malaman Shi'a.[17]
Wilaya Takwiniyyar Annabi (S.A.W) Da Imamai (A.S) Malaman Shi'a sun yi imani da cewa Annabi (S.A.W) da Imamai (A.S) suna da wilaya takwiniyya; amma sun yi saɓani cikin zurfi da iyakar wilayarsu:
Wasu jama'a sun tafi kan cewa Ma'asumai za su iya tasiri da sarrafa ɗabi'a; amma wannan tasiri da sarrafawa bai shafi komai da komai, kaɗai yana kasancewa cikin wasu keɓantattun wurare, Murtada Muɗahhari, Safi Gulfaigani da Jafar Subhani suna kan wannan ra'ayi.[18] A fahimtarsu, wilaya takwniniyya ba ta nufin an fawwala komai da koma a hannun ma'asumai kuma sune suke gudanarwa cikin halitta a duniya, kuma su ne suke halitta da izinin Allah, suna rayawa suna kashewa.[19] Shaik Saduƙ da Shaik Mufid suma sun yi watsi da maganar fawwala halitta a hannun ma'asumai kuma sun tafi kan cewa wannan magana ce kawai ta masu guluwi da wuce gona da iri.[20]
Akasin haka, Muhammad Husaini Garawi Isfahani da Sayyid Muhammad Husain Husaini Tehrani sun tafi kan cewa Annabi da Imamai suna da wilaya takwiniyya kan baki ɗayan al'amuran halitta, kuma sune tsanin falalolin Allah zuwa ga halitta.[21]
Maƙaloli Masu Alaƙa
Bayanin kula
- ↑ Alama Tabataba’i, Al‑Mizan, 1417 H., juzu’i na 6, shafi na 12.
- ↑ Subhani, Wilayatul Takwiniyya Wa Tashri’iyye Az Didgahe ilime Wa falsafe, 1385 H.S., shafi na 26.
- ↑ Mutahhari, ’Azadi Ma’anawi, shafi na 71; Majmu'eh Asar, 1389 H.S., juzu’i na 23, shafi na 495.
- ↑ Rahimi, “Barrasi Tadawwur Tariki Welayate Takwini Az Hakim Tirmidhi Ta Ibn ‘Arabi Dar Mutunen Irfan,” shafi na 82.
- ↑ Rahimi, “Barrasi Tadawwur Tariki Welayate Takwini Az Hakim Tirmidhi Ta Ibn ‘Arabi Dar Mutunen Irfan,” shafi na 82.
- ↑ Majmu'eh Asar, 1389 H.S., juzu’i na 3, shafi na 286.
- ↑ Rahimi, “Barrasi Tadawwur Tariki Welayate Takwini Az Hakim Tirmidhi Ta Ibn ‘Arabi Dar Mutunen Irfan,” shafi na 82.
- ↑ Subhani, Wilayatul Takwiniyya Wa Tashri’iyye Az Didgahe ilime Wa falsafe, 1385 H.S., shafi na 49-50.
- ↑ Subhani, Wilayatul Takwiniyya Wa Tashri’iyye Az Didgahe ilime Wa falsafe, 1385 H.S., shafi na 49-50.
- ↑ Don misali, duba Mutahhari, Majmu'eh Asar, 1375 H.S., juzu’i na 3, shafuka 285–286; Safi Gulpaigani, Wilayatul Takwiniyya Wa Wilayatul Tashri’iyya, 1393 H.S., shafuka 82, 99–100; Subhani, Wilayatul Takwiniyya Wa Tashri’iyya Az Didgahe ilime Wa falsafe, 1385 H.S., shafi na 26.
- ↑ Safi Gulpaigani, Salsale Mabahise Imamat Wa Mahdawiyat, 1391 H.S., juzu’i na 1, shafi na 43.
- ↑ Don misali, duba Mutahhari, majmueh Asar, 1375 H.S., juzu’i na 3, shafi na 285; Subhani, Wilayatul Takwini Wa Tashri’i Az Didgahe ilime wa falsafe, 1385 H.S., shafi na 26.
- ↑ Mutahhari, Majmueh Asar, 1375 H.S., juzu’i na 3, shafi na 289.
- ↑ Rabbani Gulpaigani, Ali, “Naƙshe Fa'ii Imam Dar Nizame Afarinesh,” shafuka 20–25.
- ↑ Don misali, duba Shaykh Sadouq, al‑I‘tiqadat, 1414 H., juzu’i na 1, shafi na 100.
- ↑ Rahimi, “Barrasi Tadawwuri Tarikhi Wilayate Takwini Az Hakim Tirmidhi Ta Ibn ‘Arabi Dar Mutune Mansur Irafni ,” shafi na 75.
- ↑ Rahimi, “Barrasi Tadawwuri Tarikhi Wilayate Takwini Az Hakim Tirmidhi Ta Ibn ‘Arabi Dar Mutune Mansur Irafni ,” shafi na 73.
- ↑ Mutahhari, Majmu'eh Asar, 1375 H.S., juzu’i na 3, shafuka 285–286; Safi Gulpaigani, Wilayate Takwini wa Wilayatul Tashri’i, 1393 H.S., shafuka 99–100; Subhani, Wilayatul Takwini Wa Tashri’iyya Az Disgahe ilime Wa falsafe, 1385 H.S., shafi na 51.
- ↑ Mutahhari, Majmu'eh Asar, 1375 H.S., juzu’i na 3, shafuka 286; Safi Gulpaigani, Wilayate Takwini wa Wilayatul Tashri’i, 1393 H.S., shafuka 98–100; Subhani, Wilayatul Takwini Wa Tashri’iyya Az Disgahe ilime Wa falsafe, 1385 H.S., shafi na 51.
- ↑ Shaykh Sadouq, al‑I‘tiqadat, 1414 H., juzu’i na 1, shafuka 97, 100; Shaykh Mufid, Silsilatu Muallifati Shaykh Mufid, 1414 H., juzu’i na 5, shafi na 134.
- ↑ Gharawi Isfahani, Hashiya Kitabi al‑Makasib, 1427 H., juzu’i na 2, shafi na 379; Husayni Tehrani, Imam Shinasi, juzu’i na 5, 1418 H., shafi na 114.
Nassoshi
- Muṭahhari, Murtaza, Majmu‘a‑ye athar-e Ustad Shahid Muṭahhari, Tehran, Ṣadra, 1375 SH.
- Gharawi Isfahani, Muhammad Husayn, Hashiyat al‑Makasib, Qum, Zhawi al‑Qurba, 1427 AH.
- Husayni Tehrani, Sayyid Muhammad Husayn, Imam‑Shinasi, Mashhad, Intisharat-e ‘Allameh Tabataba’i, 1418 AH.
- Muṭahhari, Majmu‘a‑ye athar, Nashir Ṣadra, 1389 SH, ba a bayyana wuri ba.
- Rabani Gulpayigani, Ali, "Rawar Aiki ta Imam a Tsarin Halitta", a cikin Entizar-e Mow‘ud lamba 29, 1388 SH.
- Rahimi, Ja‘far, “Binciken Sauyin Tarihi na Wilaya Takwini daga Hakim Tirmidhi zuwa Ibn ‘Arabi a cikin rubuce‑rubucen sufi na zube”, a cikin Mutala‘at-e ‘Irfani, lamba 20, 1393 SH.
- Shaykh Mufid, Muhammad bin Muhammad, Silsilat Mu’allafat al‑Shaykh al‑Mufid, Beirut, Dar al‑Mufid, 1414 AH.
- Shaykh Ṣaduq, Muhammad bin Ali, al‑I‘tiqadat, Qum, Kongareh‑ye Shaykh Mufid, bugu na biyu, 1414 AH.
- Subhani, Ja‘far, Wilaya Takwini da Tashri‘i daga hangen ilimi da falsafa, Qum, Mu’assasar Imam Sadiq, 1385 SH.
- Ṣafi Gulpayigani, Luṭf‑Allah, Silsilat‑e Mabaḥith Imamat wa Mahdawiyyat, Qum, Ofishin Shirya da Buga Ayyukan Ayatollah al‑‘Uzma Ṣafi Gulpayigani, 1391 SH.
- Ṣafi Gulpayigani, Luṭf‑Allah, Wilaya Takwini da Wilaya Tashri‘i, Qum, Ofishin Shirya da Buga Ayyukan Ayatollah al‑‘Uzma Ṣafi Gulpayigani, 1393 SH.
- Ṭabaṭaba’i, Sayyid Muhammad Husayn, al‑Mizan fi Tafsir al‑Qur’an, Qum, Daftar Intisharat-e Islami, bugu na biyar, 1417 AH.