Jump to content

Daƙiƙa:Wasiyyoyin Sayyida Faɗima (S)

Daga wikishia
Rubutun zane na kira (calligraphy) na wani ɓangare daga wasiyyar Sayyida Faɗima (S) da rubutun Kufi

Wasiyyoyin Sayyida Faɗima (S) ta ƙunshi wasiyyoyinta rubutattu da kuma na baka waɗanda ta yi wa Imam Ali (A.S) da sauran mutane. A cikin wasiyyoyinta rubutattu, ta naɗa Imam Ali (A.S), sa'an nan Imam Hassan (A.S), sannan Imam Husaini (A.S) a matsayin waɗanda za su kula da aiwatar wa da kuma tafiyar da dukiyarta. Haka nan, ta ware rabo na musamman ga matan Manzon Allah (S.A.W), da ƴar Abu Zar Gifari, da kuma wasu gungun mabuƙata.

A wasu littattafan tarihi, an ruwaito cewa a cikin wasiyyoyinta na baka, ta buƙaci a taƙaita adadin mutanen da za su halarci jana'izarta, kuma ta yi umurni da a ɓoye wurin da za a binne ta. Haka nan, akwai ruwayoyin da suka bayyana ƙarara cewa ta hana wasu mutane halartar jana'izarta. Waɗannan bayanai sun zo a cikin littattafan Shi'a da kuma wasu daga na Ahlus-Sunna.

An ɗauki wasiyyar Nana Faɗima (A.S) da ta yi da cewa a binne ta da daddare a ɓoye a matsayin wata hanya ta nuna rashin amincewa da kuma nuna rashin jin daɗi da kwace halifanci, da kuma yaƙi da waɗanda suka zalunce ta bisa aƙidar Shi'a.

Nau'ukan Wasiyyoyin Nana Faɗima (A.S)

Dangane da ruwayoyin da ke cikin littattafan tarihi na Shi'a da Ahlus-Sunna, an ce Nana Faɗima (A.S) ta yi wasiyya da dama, rubutattu ko na baka. Daga cikinsu akwai wasiyya guda wadda ta shafi yadda za a tafiyar da dukiyarta, da kuma wasiyyoyi guda biyu waɗanda ta yi wa Imam Ali (A.S) da Asma'u Bint Umaisi game da yadda za a yi mata sallah, likkafani, da kuma jana'iza.[1]

Wasiyyar Nana Faɗima (A.S) rubutacciyya ta keɓanta ne ga batutuwan dukiya da abubuwan da suka shafi hakan. Bisa ga ruwayoyi, ko dai da hannunta ta rubuta wasiyyoyin, ko kuma dai Imam Ali (A.S) ne ya rubuta ta bisa umarninta.[2]

Wasiyya Game da Yadda Za A yi Sallah da Likkafani Da Binnewa

A kwanakinta na ƙarshe a duniya, Nana Faɗima (A.S) ta yi wasiyya guda biyu ga Imam Ali (A.S) game da yadda za a yi mata sallah, likkafani, da kuma jana'iza: ɗaya rubutacce, ɗaya kuma na baka.[3] A cikin waɗannan wasiyyoyin, ta bayyana Imam Ali (A.S) a matsayin bawa mafi sani kuma mafi tsoron Allah a cikin bayin Allah, sannan ta ba shi wasu shawarwari. Baya ga umarnin a binne ta da daddare, ta kuma buƙaci bayan mutuwarta, ya auri Umama Ƴar Abul Asi Bin Rabi, domin ita (Umama) tana jin ƙan ƴaƴan Nana Faɗima (A.S) kamar yadda ita ma take ji.[4]

Binnewa Da Daddare Da Hana Wasu Mutane Halartar Jana'iza

Dangane da rahotannin da suka zo a littattafan hadisi, Nana Faɗima (A.S) ta yi wa Imam Ali (A.S) wasiyya cewa, waɗanda suka zalunce ta kada su halarci jana'izarta.[5] Ta rantsar da Ali (A.S) cewa Abubakar da Umar[6] da mabiyansu kada su yi mata sallah.[7] Mutane ƙalilan ne kawai aka umarci su sani su kuma halarci jana'izar, su ne: Ummu Salama, Ummu Aiman, Fidda, Hassanaini, Abdullahi Bin Abbas, Salmanul Farisi, Ammar Bin Yasir, Miƙdad, Abu Zar, da Huzaifa.[8] Ɗaya daga cikin wasiyyoyin Nana Faɗima (A.S) shi ne a binne ta da daddare[9] kuma a ɓoye wurin kabarinta.[10]

Haka nan, ta yi wasiyya cewa Ali (A.S) shi ne zai zama mai kula da wankan gawa, likkafani, sallah, da kuma binnewa. Sannan ta buƙaci bayan mutuwarta, ya zauna kusa da gawar ta yana karatun Alƙur'ani da addu'a domin hakan ya kawo mata kwanciyar hankali. A ƙarshe, ta damƙa amanar Imam Ali (A.S) ga Allah, sannan ta ba shi shawarar ya kyautata wa yaranta.[11]

Me Ya Sa Nana Faɗima (A.S) Ta Yi Wasiyyar A Binne Ta Da Daddare Kuma A Ɓoye?

Wasiyyar Nana Faɗima (A.S) na a binne ta da daddare kuma a ɓoye kabarin, ana ɗaukar ta a matsayin wata alama ta nuna rashin amincewa da waɗanda bisa aƙidar Shi'a suka kwace halifanci suka kuma zalunce ta. An ce bayan Nana Faɗima (A.S) ta yanke ƙauna daga samun taimakon musulmi wajen dawo da haƙƙinta da na Imam Ali (A.S), ta so kabarin nata ya kasance a ɓoye, kuma halifan musulmi kada ya halarci sallar jana'izarta, domin wannan tambaya ta tarihi ta ci gaba da kasancewa har abada.[12] A cikin ruwayoyin Ahlul-baiti (A.S) ma, an jaddada rashin jin daɗinta ga "Shaikhaini" (Abubakar da Umar); kamar yadda Imam Ali (A.S) ya bayyana cewa dalilin binne ta da daddare shi ne fushin da take yi da wasu mutane.[13] Ibn Abil Hadid, wani masanin tarihi daga Ahlus-Sunna, shi ma ya ruwaito cewa ta yi wasiyyar a binne ta da daddare a matsayin alamar nuna rashin amincewa da halayen wasu daga cikin sahabbai, kuma ta hana su halartar sallarta da jana'izarta.[14] Michel Kadi, marubuci kirista, ya bayyana wannan wasiyyar a matsayin ƙololuwar nuna adawa da nuna rashin amincewa daga Nana Faɗima (A.S) .[15] Haka nan, ana kallon wannan wasiyyar a matsayin hujja ta zaluncin da aka yi mata,[16] kuma ana ambatonta a matsayin babban darasi a cikin wa'azozi, rubuce-rubucen juyayi, waƙen juyayi kuma jawabai a lokutan tunawa da ita.

Wasiyya Ga Asma'uu Bint Umaisi

Dangane da ruwayoyin tarihi, Nana Faɗima (A.S) ta bayyana damuwarta ga Asma'uu bint Umaisi dangane da yadda za a ɗauki gawarta a kan wani abin ɗauka bayan mutuwarta, har mutane su iya hango siffar jikinta. Asma'u ta shirya mata wani akwatin ɗaukar gawa (tabut) wanda take gani a ƙasar Habasha, wanda yake rufe dukkan jiki.[17] Sa'ad da Nana Faɗima (A.S) ta gan shi, sai ta yi wa Asma'uu addu'a.[18] Wasu masana suna ganin wannan akwatin ɗaukar gawa shi ne na farko da aka ƙera a Musulunci.[19]

Haka nan, an ruwaito cewa Nana Faɗima (A.S) ta yi wasiyyar cewa bayan rasuwarta, Asma'uu da Ali (A.S) ne kawai za su yi mata wanka, kuma kada wani ya shiga. Bisa wannan umarni, a lokacin da Nana Faɗima (A.S) ta rasu, sai A'isha ta yi ƙoƙarin shiga, amma Asma'u ta hana ta. A'isha ta je ta yi ƙara ga Abubakar, inda ta nuna cewa Asma'u ta hana ta shiga kuma ta shirya wani ɗakin ɗaukar gawa (Haudaj) don jana'izar Faɗima. Abubakar ya tsaya a ƙofar gidan, ya kuma tsawatar wa Asma'u kan hana A'isha shiga da kuma ƙera wannan ɗakin ɗaukar gawan. Asma'u ta amsa da cewa Nana Faɗima (A.S) ce ta ba ta umarnin cewa bayan mutuwarta kada a bar kowa ya shiga, kuma ita ce ta ba ta umarnin ƙera akwatin ɗaukar gawan. Daga nan sai Abubakar ya janye kuma ya ce a aiwatar da duk abin da aka yi wasiyya da shi.[20] A wani ruwayar kuma, an ce Salma, kuyangar Manzon Allah (S.A.W), ita ma ta kasance tare da Asma'u a lokacin wankan Nana Faɗima (A.S) kuma ta taimaka wa Imam Ali (A.S).[21]

Wasiyyar Nana Faɗima (S) Game da Dukiyarta

Dangane da abin da ya zo a wasiyyar Nana Faɗima (A.S) ta rubutacce game da dukiyarta, ta ware wasu rabo daga cikinta ga matan Manzon Allah (S.A.W) da kuma mabuƙatan Bani Hashim. Ta kuma naɗa Imam Ali (A.S), sa'an nan Imam Hassan (A.S), sannan Imam Husaini (A.S) a matsayin manyan ƴaƴanta maza a matsayin waɗanda za su kula da aiwatar da wannan wasiyya.[22] Bisa ga wannan wasiyya, an sadaka da oƙiya tamanin[Tsokaci 1] daga gonakinta a matsayin waƙafi, don a riƙa rarraba ribar da aka samu duk shekara a watan Rajab (Bayan an cire kuɗin kula da gonar) ga waɗannan gurfan da aka ambata: oƙiya 45 ga matan Manzon Allah (S.A.W), sauran kuma ga mabuƙata.[23]

A cikin wannan wasiyya, an kuma ware wa ƴar Abu Zar Gifari rabo, inda aka ba ta wani ɓangare na dukiya da kayan ɗaki. Bugu da ƙari, an tsara cewa tufafin Nana Faɗima (A.S) su koma ga ɗaya daga cikin ƴaƴanta mata guda biyu.[24] Haka nan, an damƙa wa Imam Ali (A.S) ikon yanke hukunci kan yanayin gonakin idan wani abu ya faru. A ƙarshe, an ambaci Allah, Miƙdad, Zubair, da Ali (A.S) a matsayin shaidun wannan wasiyya, kuma an bayyana cewa an rubuta wasiyyar ne a lokacin da take cikin ƙoshin lafiya.[25]

Hiɗanul Saba'a (Gonaki Bakwai)

"Hitan Sab'ah" su ne gonaki bakwai waɗanda suka kasance mallakin wani Bayahude mai suna Mukhairiƙ, wanda ya ba su kyauta ga Manzon Allah (S.A.W),[26] shi kuma Manzon Allah (S.A.W) ya mayar da su waƙafi ga Nana Faɗima (A.S).[27] Bisa ga wata ruwaya daga Imam Baƙir (A.S) ana amfani da kuɗin shigar waɗannan gonaki don ayyukan alheri da kuma taimaka wa addinin Musulunci, inda aka damƙa amsar su ga Imam Ali (A.S), sannan Imam Hassan (A.S), sannan Imam Husaini [28](A.S), kuma bayan su, sai ya koma hannun manyan ƴaƴan Nana Faɗima (A.S).

Ummul Iyyal

Ummul Iyyal wani ƙauye ne da ke tsakanin Makka da Madina,[29] wanda yake da wani maɓuɓɓugar ruwa da ke ɓallewa, kuma ruwan yana shayar da dabino fiye da dubu ashirin. An kiyasta cewa kudin shigar wannan ƙauye a kowace shekara ya kai kimanin dinari dubu tamanin.[30] Ummul Iyyal mallakin Nana Faɗima (A.S) ne, kuma ta yi wasiyyar cewa a riƙa amfani da kudin shigarsa a matsayin sadaka.[31]

Bayanin kula

  1. ↑ Zamani, «Wasayaye Hazrat Faɗima (S),» shafi na 70. Ashuri Langarudi, «Mururi bar Wasiyat‑nameye Hazrat Faɗima Zahra (Alayha al‑salam),» shafi na 68.
  2. ↑ Majlisi, Bihar al‑Anwar, juzu'i na 100, shafi na 184. Nuri, Mustadrakul Wasa'il, juzu'i na 14, shafi na 54. Mu'izziye Malayeri, Jami'ul Ahadis Ash‑Shi'a, juzu'i na 19, shafi na 106.
  3. ↑ Majlisi, Bihar al-Anwar, juzu'i na 43, shafi na 178.
  4. ↑ Fattal Nishaburi, Raudaul Wa'izin, juzu'i na 1, shafi na 151.
  5. ↑ Fattal Nishaburi, Raudatul Wa'izin, juzu'i na 1, shafi na 151.
  6. ↑ Majlisi, Bihar al‑Anwar, juzu'i na 29, shafi na 112; kuma juzu'i na 31, shafi na 619. Amili, As‑Sahihu Min Siratil Imam Ali, juzu'i na 10, shafi na 296.
  7. ↑ Fattal Nishaburi, Rawdat al‑Wa'izin, juzu'i na 1, shafi na 151.
  8. ↑ Ɗabari, Dala'ilul Imama, shafi na 133. Majlisi, Bihar al‑Anwar, juzu'i na 43, shafi na 208.
  9. ↑ Fattal Nishaburi, Raudatul Wa'izin, juzu'i na 1, shafi na 151. Majlisi, Bihar al‑Anwar, juzu'i na 31, shafi na 619.
  10. ↑ Ɗabari, Dala'ilul Imama, shafi na 133. Majlisi, Bihar al‑Anwar, juzu'i na 43, shafi na 208.
  11. ↑ Majlisi, Bihar al‑Anwar, juzu'i na 79, shafi na 27. Nuri, Mustadrakul Wasa'il, juzu'i na 2, shafi na 316.
  12. ↑ Ƙa'imi, Dar Maktabe Faɗima (Alayha al‑salam), shafi na 313–314. Zamani, «Wasayaye Hazrat Faɗima (S),» shafi na 72.
  13. ↑ Majlisi, Bihar al‑Anwar, juzu'i na 43, shafi na 209.
  14. ↑ Ibn Abil Hadid, Sharhu Nahjil Balaga, juzu'i na 16, shafi na 214.
  15. ↑ «Katib al‑Masihi: Az‑Zahra arazat al‑zulm wa Intafadat li‑Himayat Siyasat al‑Haƙƙi al‑Ilahi,» Shafin yanar gizo na tashar Al‑Kausar.
  16. ↑ «Ustad Andelibe Hamadani dar Gofte‑Gu ba Shafaqna: Dafne Makhfiyane Wa Shabaneh‑ye Hazrat Zahra (S) Bozorgtarin Sanade «Mazlumiyyat Wa I'tiraz» Ast,» Kamfanin dillancin labarai na Shafaqna.
  17. ↑ Majlisi, Bihar al‑Anwar, juzu'i na 43, shafi na 189.
  18. ↑ Shaik Ɗusi, Tahzibul Ahkam, juzu'i na 1, shafi na 469. Hurru Amili, Wasa'ilush Shi'a, juzu'i na 3, shafi na 220.
  19. ↑ Nu'uman Magribi, Da'a'imul Islam, juzu'i na 1, shafi na 233. Shaik Ɗusi, Tahzibul Ahkam, juzu'i na 1, shafi na 469.
  20. ↑ Baihaƙi, As‑Sunanul Kubra, juzu'i na 4, shafi na 35. Dulabi, Az‑Zurriya Aɗ‑Ɗahira An‑Nabawiyya, shafi na 154. Ibn Abdul‑Barr, Al‑Isti'ab, juzu'i na 4, shafi na 1898. Muttaƙi Hindi, Kanzul Ummal, juzu'i na 13, shafi na 687.
  21. ↑ Ibn Abdul-Barr, Al-Isti'ab, juzu'i na 4, shafi na 1862. Ibn Asir, Usdul Ghaba, juzu'i na 5, shafi na 478. Mizzi, Tahzibul Kamal, juzu'i na 35, shafi na 197. Safadi, Al-Wafi Bi al-Wafayat, juzu'i na 15, shafi na 190.
  22. ↑ Majlisi, Bihar al-Anwa, juzu'i na 100, shafi na 184.
  23. ↑ Nuri, Mustadrakul Wasa'il, juzu'i na 14, shafi na 54. Mi'azziye Malayeri, Jami'ul Ahadis Ash‑Shi'a juzu'i na 19, shafi na 106.
  24. ↑ Nuri, Mustadrakul Wasa'il, juzu'i na 14, shafi na 54.
  25. ↑ Majlisi, Bihar al-Anwar, juzu'i na 100, shafi na 184. Nuri, Mustadrakul Wasa'il, juzu'i na 14, shafi na 54. Mu'izzi Malayeri, Jami'ul Ahadis Ash‑Shi'a juzu'i na 19, shafi na 106.
  26. ↑ Ibn Is'haƙ, Tarakatun Nabi, shafi na 78. Hamawi, Mu'ujam Al-Buldan, juzu'i na 5, shafi na 241. Azim-abadi, Aunul Ma'abud, juzu'i na 8, shafi na 137.
  27. ↑ Himyari Ƙummi, Ƙurb Al-Isnad, shafi na 363.Kulaini, Usulul Kafi, juzu'i na 7, shafi na 47.
  28. ↑ Kulaini, Usulul Kafi, juzu'i na 7, shafi na 48. Nu'uman Magribi, Da'a'imul Islam, juzu'i na 2, shafi na 344.
  29. ↑ Hamawi, Mu'ujam Al-Buldan, juzu'i na 1, shafi na 254.
  30. ↑ Ibn Hazm, Jamharat Ansabil Arab, shafi na 140.
  31. ↑ Hamawi, Mu'ujam Al-Buldan, juzu'i na 1, shafi na 254. Ibn Jauzi, Al-Muntazam, juzu'i na 1, shafi na 145.

Tsokaci

  1. ↑ A cikin ma'auni na gargajiya, kowane ukiya (Uƙiyya) yana daidai da kusan misƙali 7 (misƙal 7).

Nassoshi

  • Baihaƙi, Ahmad Bin Husain, As-Sunanul Kubra, Ba a bayyana wurin bugawa ba: Dar al-Fikr; ba a bayyana shekarar bugawa ba.
  • Fattal Nishaburi, Muhammad Bin Ahmad, Raudatul Wa'izin wa Basirat al-Muta'azzin, Qom: Mawallafar Radi, bugu na farko. 1375Sh.
  • Himyari, Abdullah Ibn Jafar, Ƙurb Al-Isnad, gyara: Cibiyar Alul-Bait, Qom: Cibiyar Alul-Bait, 1413H.
  • Hurru Amili, Muhammad, Wasa'ilush Shi'a ila Tahsil Masa'il al-Shari'a, gyara: Cibiyar Alul-Bait, Qom: Cibiyar Alul-Bait, 1414H.
  • Ibn Abdul-Barr, Yusuf Bin Abdullah, Al-Isti'ab fi Ma'arifat Al-As'hab, gyara: Ali Muhammad. Beirut: Dar al-Jil, 1412H.
  • Ibn Abil Hadid, Abdul-Hamid Bin Hibatullah, Sharhu Nahijl Balaga, Beirut: Dar Ihyail Turasil Arabi. 1385H.
  • Ibn Hazm, Ali Bin Ahmad, Jamharat Ansabil Arab, gyara. Kwamitin Malamai, Beirut: Darul Kutubil Ilmiyya. 1403H.
  • Ibn Is'haƙ, Hammad, Tarakatun Nabi, gyara: Akram Diya Al-Umari; ba a bayyana wuri ba; ba a bayyana mawallafa ba, 1404H.
  • Ibn Asir, Ali Bin Muhammad, Usdul Ghaba, Beirut: Darul Kutubil Arabi; ba a bayyana shekarar bugawa ba.
  • Ibn Ahmad Dulabi, Muhammad, Az‑Zurriya Aɗ‑Ɗahira An‑Nabawiyya, gyara. Sa'ad al-Mubarak al-Hasan, Kuwait: Maktabatus Salafiyya. 1407H.
  • Ibn Jauzi, Abdur-Rahman Bin Ali, Al-Muntazam fi Tarikh al-Umam wa al-Muluk, gyara: Muhammad Abdul-Ƙadir da Mustafa Abdul-Ƙadir; Beirut:Darul Kutubil Ilimiyya. 1412H.
  • Kulaini, Muhammad Bin Yaƙub, Usulul Kafi, ta'liƙin: Ali Akbar Gaffari, Ba a bayyana wurin bugawa ba: Darul Kutubil Islamiyya.1367Sh.
  • Majlisi, Muhammad Baƙir, Bihar al-Anwar, Beirut: Cibiyar al-Wafa', 1403H.
  • Mizzi, Yusuf, Tahzibul Kamal fi Asma' al-Rijal, gyara. Bashshar Awwad, Beirut: al-Risalah, Bugu na huɗu., 1413H.
  • Mu'izzi Malayeri, Isma'il, Jami'ul Ahadis Ash‑Shi'a fi Ahkam al-Shari'a, a ƙarƙashin kulawar Ayatullahi al-Uzma Burujerdi. Qom: Mu'allif, 1412H.
  • Murtada Amili, Sayyid Jafar, As-Sahihu Min Siratil Imam Ali, Qom: Wila' al-Murtada, 1430H.
  • Muttaƙi Hindi, Ala'ud-Din, Kanzul Ummal, gyara: Bakri Hayyan Sakhwah al-Safa, Beirut: Cibiyar al-Risalah, 1409H.
  • Nu'aman Mahribi, Da'a'imul Islam, gyara. Asif Bin 'Ali, Qahira: Mawallafar Ma'arif, 1383H.
  • Nuri, Husain, Mustadrakul Wasa'il wa Mustanbaɗ al-Masa'il, gyara.Cibiyar Alul-Bait, Beirut: Cibiyar Alul-Bait, Bugu na biyu.1408H.
  • Ƙa'imi, Ali, Dar Maktabe Faɗima (Alayha al‑salam), Majmu'ah-i az Maƙalat wa Sukhanraniha, Tehran: mawallafar Amiri.1377Sh.
  • Safadi, Salah al-Din, Al-Wafi Bi al-Wafayat, gyara. Ahmad Arna'ut da Turki Mustafa, Beirut: Dar Ihya' Turas. 1420H.
  • Siddiƙi Azim-abadi, Muhammad Ashraf, Aunul Ma'abud: Sharhu Sunan Abi Dawud wa huwa Ghayat al-Maƙṣud fi Hall Sunan Abi Dawud, Beirut: Darul Kutubil Ilimiyya; bugu na uku. 1415H.
  • Ɗusi, Muhammad, Tahzibul Ahkam fi Sharhi Al-Muƙni'a lil-Shaik Al-Mufid, Mai gyara: Hassan Musawi; Tehran: Darul Kutubil Islamiyya; bugu na huɗu. 1364Sh.
  • Yaƙut Hamawi, Mu'ujam Al-Buldan, Beirut: Dar Ihya'i Turasil Arabi. 1399H.
  • «استاد عندلیب همدانی در گفت وگو با شفقنا: دفن مخفیانه و شبانه حضرت زهرا(س) بزرگترین سند «مظلومیت و اعتراض» است»، (Ustad Andalib Hamadani a cikin tattaunawa da Shafaqna: Binnewar Sirri da dare ta Sayyida Faɗima (S) ita ce babbar hujja ta zalunci da kuma nuna adawa), Kamfanin dillancin labarai na Shafaqna, ranar wallafa: 24 Nuwamba 2025M, ranar ziyara: 1 Disamba 2025M.
  • «کاتب المسیحی: الزهراء عارضت الظلم وانتفضت لحمایة سیاسة الحق الإلهی»، (Marubuci Kirista: Faɗima ta yi adawa da zalunci kuma ta tashi domin kare siyasar gaskiyar Allah), Shafin yanar gizo na Al-Kausar Network, ranar ziyara: 30 Nuwamba 2025M.
  • Ɗabari, Muhammad, Dala'ilul Imama, gyara: Sashen Nazarin Musulunci; Qom: Cibiyar Al-Bi'isa.1413H.
  • Ashuri Langarudi, Hassan، «مروری بر وصیت‌نامه حضرت فاطمه زهرا(س)»، (Dubawa kan wasiyyar Sayyida Faṭima al-Zahra (A.S)), A cikin mujallar wata uku-uku ta mai suna Rahe Tusha, lamba ta 11, shekara ta 202M.
  • Zamani, Rajab Ali، «وصایای حضرت فاطمه(س)»، (Wasiyyoyin Sayyida Faɗima (S)), A cikin mujallar Farhang-e Kausar, lamba ta 69, shekara ta 2007M.