Nuwwabul Arba'a

Daga wikishia

Nuwwabul Arba'a. (Larabci: النواب الأربعة) ma'ana na'ibai ko keɓantattun wakilan Imam Mahadi (A.S) a lokacin daurar gaiba sugra waɗanda suka kasance hanyar sadarwa tsakanin Imam Mahadi (A.S) da ƴan shi'a. Usman ɗan Sa'id, Muhammad ɗan Usman, Husaini ɗan Ruhu da Ali ɗan Muhammad Samari. Nuwwabul Arba'a sun kasance daga amintattu yardaddun sahabban Imamai, sun kasance sanannu ta hanyar ayyanawar Imam ko ta hanyar na'ibin da ya gabata, waɗannan mutane guda huɗu sun na'ibanci Imam Mahadi (A.F) tsawon shekaru 70, ta hanyar wakilansu a garuru na kusa da na nesa sun kasance sun sadar da sa ƙonni, tambayoyi da bu ƙatun ƴan shi'a zuwa ga Imam, haka kuma suna sadar da amsoshi da sa ƙonnin Imam zuwa ga ƴan shi'a, daga cikin ayyukan waɗannan keɓantattun jakadu guda huɗu, akwai kawar da duk wata shakka da kokwanto game da Imam Mahadi, sun kuma kiyaye amanar ɓoye shi da mahallin da yake rayuwa.

Keɓantaccen Na'ibanci

Tushen ƙasida: Keɓantaccen Na'ibanci

Kalmar niyaba wani isɗilahi ne da yake ba da ma'anar halifancin wani daga ɓangaren Imam (A.S) domin tabbatar da sadarwa tsakaninsa da mutane, a wurare da ba za a iya samun sadarwa kai tsaye ba, Imam yana zaɓar wasu keɓantattun mutane domin su kasance jakadunsa cikin mutane, a ci gaba sai ya zamana na'ibi na farko d aya fara zaɓa kafin mutuwarsa zai gabatarwa da mutane sabon na'ibin Imam da zai ɗora daga inda ya tsaya.[1]

Na'ibai Da Tsawon Muddar Na'ibancinsu

Ayyukan keɓantattun na'iban Imam Zaman (A.F) ya fara daga shekara ta 260 bayan hijira zuwa 329 (Kusan shekaru 70) ma'ana ya kasance daga lokacin daura gaiba sugra. Cikin waɗannan shekaru mutane huɗu daga ƴan shi'a waɗanda suka kasance daga sahabban Imami na goma da Imami na sha ɗaya kuma sanannu fitattun mutane tsakankanin ƴan shi'a, su ne suka ɗauki alhakin ayyukan jakadanci da wakilci tsakanin Imam Mahadi (A.F) da ƴan shi'a, tsawon waɗannan shekaru waɗannan wakilai sun zaɓi mutane da za su wakilci a garuruwan muslunci masu nisa.[2]

  • Usman ɗan Sa'id Amri (Wafati:267.h. ƙ) ya kasance farkon keɓantaccen na'ibin Imam Mahadi (A.F). ya zo a riwaya cewa Imam Askari (A.S) ya nunawa mutane huɗu daga sahabbansa ɗansa Imam Mahadi (A.F) yace musu a tsawon gaiba sugra ku yi ɗa'a ga Usman ɗan Sa'id Amri,[3] haka nan kuma cikin ganawa Imam Zaman (A.S) da mutanen garin ƙum ya yi ishara zuwa ga na'ibancin Usman ɗan Sa'id Amri ya kuma umarce su da komawa zuwa gare shi.[4] Usman ɗan Sa'id har zuwa ƙarshen rayuwa ya na'ibanci Imam Zaman (A.S) tsawon shekaru shida.
  • Muhammad ɗan Usman ɗan Sa'id Amri (Wafati:305.h. ƙ) ya kasance ɗa ga na'ibi na fark, kuma shi ne na'ibi na biyu daga keɓantattun na'iban Imam Zaman (A.F), lokacin da na'ibi na farko ya rasu, Imam Zaman (A.F) ya rubuta wasiƙa zuwa ɗansa Muhammad ɗan Usman cikin wannan wasiƙa bayan yi masa ta'aziyya sai ya naɗa shi a matsayin keɓantaccen na'ibinsu na biyu.[5] kafin nan Imam Askari (A.S) ya riga ya gabatar da Muhammad ɗan Sa'id a matsayin wakilin Imam Zaman (A.F),[6]Muhammad ɗan Usman Amri ya yi na'ibanci kusan tsawon shekaru huɗu.[7]
  • Husaini ɗan Ruhu Naubekti (Wafati:326.h. ƙ) na'ibi na uku daga keɓantattun na'iban Imam Zaman (A.F) , ya kasance daga amintattu yardaddun mutane a wurin Muhammad ɗan Usman a garin bagdad. Muhammad ɗan Usman a ƙarshen kwanakin rayuwarsa ya ayyana magajinsa bisa umarnin Imam Mahadi (A.F).[8] a farko ya kasance yana da ƙima da matsayi da girmamawa a hukumar Abbasiyawa, amma daga baya ya samu matsala da su ta ƙai ga sai da ya ɓoye kansa tsawon wani lokaci, bayan nan suka kama shi suka ɗaure shi shekaru biyar a kurkuk.[9] ya yi jakadanci da na'ibanci kusan tsawon shekaru 21.

Tauƙi'in Imamul Asri Ga Samari:
“Kai da `yan'uwanka Allah ya baku ladansa da kulawarsa. lallai na da kwanaki uku masu zuwa Allah zaka yi bankwana da wannan duniya, saboda haka ka yi kokarin kammala ayyukanka, ka kumak anada kowa matsayin magajinka, saboda yanzu haka an shiga gaiba da biyu, gaiba ce da zata yi tsayi sosai, matuƙar dai Allah bai bada izinin bayyana da fitowa ba zamu fito, har zuwa lokacin da zukata za su bushe su, duniya za ta cika da rashin adalci, za a samu wasu makaryata za su dinga zuwa wurin `yan shi'armu da masoyanmu suna gaya musu cewa sun ganmu ido da ido, saboda haka ku fadaka, duk wanda gabanin miƙewar Sufyani da karajin sama ya zo ya yi muku da'awar ganinmu, lallai wannan mutum maƙaryaci ne.

Source: Tarikh Baygani, Saduq, Kamal al-Din da Tammam al-Nimah, 1395 BC, juzu'i na 2, shafi na 516.

  • Ali ɗan Muhammad Samari (Wafati:329.h. ƙ) na'ibi na huɗu wanda ya na'ibanci Imam Mahadi (A.F) tsawon shekara uku, daga shekara 326-329, a lokacin na'ibancinsa ya yi fuskanci ƙuntatawa da tsanantawa daga ɓabngaren hukumar Abbasiyawa, da wannan dalili ne bai samu damar faɗaɗa ayyukan wakilanci ba yadda ya kamata.[10] tauƙi'in Imam Zaman zuwa Ali ɗan Muhammad Samari game da labarin mutuwarsa da ƙarshen daurar keaɓantaccen na'ibanci da shiga daurar gaiba kubra, suna daga mafi muhimmancin abubuwan da suka faru a ƙarshen rayuwarsa.[11]

Matakai Da Ayyuka

Dukkanin matakan da na'ibobi huɗu suka ɗau sun kasance bisa umarnin Imam Zaman (A.F).[12] waɗannan ayyuka suna kasancewwa cikin wasu adadin rukunai:

Gudanar Da Ayyuka A Sirrance

Tare da shahadar Ima Askari (A.S) da gaibar Imami na sha biyu, nuwwabul arba'a su ne kaɗai makomar ƴan shi'a cikin lamurran addininsu. Sakamakon kasancewa a zamanin gwamnatin Abbasiyawa, aiki da ta ƙiyya ya kai ƙololuwar inda zai kai musamma ma a zamanin na'ibi na uku.[13] akwai lokacin sai da takai ga Husaini ɗan Ruhu na'aibi na uku yana rayuwa a ɓoye. A cewar rasul Jafariyan, ya ɗauki wannan mataki saboda ƴan shi'a su kiyaye samuwarsu a a cibiyoyin gwamnatin Abbasiyawa, kuma su rayu matsayin marasa rinjaye a hukumance da kuma kasancewa sanannu, da kuma shi kansa ya kiyaye kansa daga sharrin ahlus-sunna masu tsaurin ra'ayi da wuce gona da iri a a garin bagdad.[14]

Dangantaka Da Gidan Sarauta

ɗaya daga cikin siyasosi na musammam a wancan zamani, wasu ba'ari ƴan shi'a a keɓance sun kasance sun kasance a gaba-gaban gidan sarauta kuma sun yi hakan ne da goyan bayan Imamai Ma'asumai, sun kutsa gidan sarautar Abbasiyawa ta kai ga wasunsu sun kasance ri ƙe da manya mu ƙamai a gidan sarauta.[15] Husaini ɗan Ruhu Naubekti a farkon na'ibancisa wanda ya zo lokaci ɗaya da halifa Muƙtadir abbasi, sakamakon tasirin da dangin naubekti da dangin ibn furat a gidan sarauta waɗanda suke ri ƙe da mu ƙaman ma'aikatun masarautar Mu ƙtadir Abbasi kuma masu nuna goyan baya ga shi'a, hakan ya baiwa na'ibu na uku damar yin tasiri cikin gidan sarauta tare da samun girmamawa daga gare su.[16]

Fito Na Fito Da Gullatu

Mas'alar guluwi ɗaya ce daga muhimman mas'aloli a zamanin nuwwabul arba'a, ta kai ga ba'arin ƴaƴan Imamai misalin Jafar ɗan Imam Hadi (A.S) wanda ake yiwa laƙabi da Jafarul kazzab ya haɗa ya kasance tare da gullatu, ba'arin wasu fitattun mutane daga ƴan siyasar shi'a sun kasance suna goyan bayan gullatu.[17] ɗaya daga cikin ayyukan nuwwabul arba'a shi ne tonawa waɗannan ɓatattun mutane kuma ma ƙarya masu da'awar ƙarya asiri, tare da isar da sa ƙon Imam Zaman (A.S) zuwa ga ƴan shi'a cikin tsinuwar da ya yi kan waɗannan ɓatattu da kuma barranta daga gare su.[18] alal misali Muhammad ɗan Nusairu wanda ya assasa firƙa Nusairiyya ya kasance daga Gullatu kuma yana da a ƙidar ubangijintar da Imamai (A.S) da yaɗa halasta aure muharramai, Muhammad ɗan Usman ya tsine masa tare da barranta daga gare shi.[19] Shalmagani ɗaya ne daga wakilan Imamai duk da cewa ya kasance tare da mu ƙami a lokacin Husaini ɗan Ruhu, amma saboda dalili neman babban matsayi da kwaɗayi kansa sai ya dinga munana amfani da mu ƙaminsa daga ƙarshe ya koma wurin Gullatu, Husaini ɗan Ruhu da kansa ya koreshi, kuma sa hannu ya fito daga wurin Imam Mahadi (A.F) yana tsinuwa a kansa.[20]

Kawar Da Shakka Da Kokwanto Game da Imam Mahadi (A.F)

Kan asasin na ƙali daga Shaik ɗusi, an samu afkuwar bahasi tsakanin Ibn Abi Ganinm da wasu jama'a daga ƴan shi'a game da rashin kasancewar Imam Hassan Askari (A.S) yana da ɗa ko baya da shi, da wannan dalili sai ƴan shi'a suka rubuta wasiƙa zuwa ga Imam Mahadi (A.F) suka nemi ya kawo ƙarshen wannan jayayya da suke ta yi da masu saɓani da su, Imam cikin amsar ya tabbbatar da cewa bayan Imami na goma sha ɗaya Allah bai gurɓata addininsa kuma bai yanke dangantakarsa da mutane ba, kuma har zuwa tashin al ƙiyama hakan ba zai taɓa faruwa ba.[21]

Cikin wani tauƙi'i (Sa hannu) daga Imam Mahadi (A.F) ya zo a riwaya cewa daidai lokacin da wannan tauƙi'i ya fito a lokacin ne Jafarul Kazzab ya kasance yana da'awar halifancin Imam Askari (A.S), a wannan tauƙi'i cikin ishararsa kan imamanci Imamai da ismarsu, ya yi ishara kan rashin faɗaka da tsinkayar Jafarul Kazzab kan haramun da halal da kuma rashin iya tantance gaskiya daga ƙarya.. cikin wannan tauƙi'i Imam yana sanya alamar tambaya da cewa ya za ai mutumin da yake haka zai yi da'awar imamanci.[22]

Kokwanton Muhammad ɗan Ibrahim ɗan Mahziyar wanda babansa ya kasance daga wakilan Imam Hassan Askari (A.F), bayan samun wasiƙa daga Imam Mahadi (A.F) ya fita daga cikin wannan kokwanto.[23] haka nan kuma cikin wani tauƙi'i daga Imam Mahadi (A.F) an naƙalto cewa cikin wannan tauƙi'i Imam cikin tabbatar da samuwarsa gaban masu shakku da kokwanto, ya bada amsar wasu mas'alolin fiƙihu.[24]

Jagorantar Wakilai

Tushen ƙasida: Hukumar Wakilai

Ayyana wakili da manufar gudanar da al'amuran nahiyoyi daban-daban da kuma samar da alaƙar sadarwa tsakanin ƴan shi'a da Imamai, wani abu ne dya fara yaɗuwa sosai daga zamanin Imam Kazim (A.S) da bayansa, bayan shiga gaiba alaƙar sadarwa ta kai tsaye tsakanin wakilai da Imam Mahadi (A.F) ta yanke, Naibansa guda huɗu sune su zama tsani na sadarwa tsakanin Imam Mahadi (A.F) da wakilan haƙƙoƙin shari'a, waɗanda suke tattaro khumusi da zakka daga hannun mutane zuwa gare shi, bayan gaiba sai ya zamana su komawa ne zuwa ga na'ibinsa na bagdad, shi kuma yana sarrafa waɗannan ha ƙ ƙo ƙi kan asasin umarnin Imam Mahadi. (A.F).[25]

Akwai wakilansa da garuruwan Ahwaz, Samarra, Hijaz, Yaman da kuma yankunan ƙasar Iran misalin Khurasan, ƙum, Rayyu, da ƙum zaka samu labaransu cikin matanan riwayoyi.[26]

Ɓoye Imam Mahadi (A.F)

Ɓoye Imam yana ɗaya daga cikin wazifofi da ayyuka na asasi a wurin na'ibansa, rahotanni tarhi da riwaya sun labarta cewa Imam ya kasance a Iraƙi, Makka da Madina yana rayuwa a sirrance babu masu iya gane shi sai na'ibansa da suke ganawa da shi.[27] yayin da Husaini ɗan Ruhu ya zama na'ibi, Abu Sahal naubekti game da mu ƙamin Husaini ɗan Ruhu yana cewa: da ace ni ne nake da masaniya game da mahallin Imam Mahadi (A.F) kamar yadda Husaini ɗan Ruhu yake da masaniya, ta yiwu lokacin da na samu kaina cikin takura a yayin bahasi da jidali da waɗanda muke da saɓanin akida da su da tuni takura ta sani na faɗi mahallin da yake ɓoye, kai ta kai ga da ace yana ɓoye da shi ƙar ƙashin abayarsa , da ba zai taɓa nuna Imam ga wani mutum ba, kai ko da ma za a yi gunduwa gunduwa da namansa ba zai taɓa nuna shi ba.[28] Duk da cewa keɓantattun na'ibai sun nace kan tabbatar da samuwar Imami na goma sha biyu, amma tare da haka sun bu ƙaci kada ƴan shi'a su yi naci da dagiya kan sanin yanayi da yaya Imam Mahadi (A.F) yake. Sun yi hakan ne domin kariya ga Imam Mahadi (A.F).[29]

Amsa Tambayoyi Na fiƙihu Da A ƙida

Nuwwabul arba'a (Na'ibai huɗu) suna yiwa Imam Mahadi (A.F) bayanin tambayoyin da mutane suka aiko, bayan karɓo amsa daga wurinsa su kawo mutane waɗannan amsoshi, wannan ayyuka ba su iyakantu da mas'alolin fiƙihu ba kaɗai, ha ƙi ƙa sun kasance suna tarayya cikin warware matsalolin ilimi da a ƙida da nusantar da mutane cikin bahasosi da munazarori.[30]tauƙi'in Is'haƙ ɗan Yaƙub.[31] da kuma tauƙi'in Muhammad ɗan Jafar Asadi,[32] da suka tattaro mas'alolin fiƙihu da halartar Husaini ɗan Ruhu cikin munazarorin ilimi da a ƙida, abubuwa ne da suke nuni kan ayyukan nuwwabul arba'a a waɗannan gurabe.[33]

Ziyarar Na'ibai

Sayyid Ibn ɗawus cikin littafin Misbahul Az-za'ir, ya naƙalto wasu ziyarori da ake karantawa kowanne ɗaya daga cikin nuwwabul arba'a, ya danganta matanin wannan ziyara zuwa ga baban Husaini ɗan Ruhu Naubekti.[34] [Tsokaci 1] haka kuma Allama majlisi cikin Biharul Al-anwar ya naƙalto ziyara ga Usman ɗan Sa'id yana cewa ya sameta ne daga wani daɗaɗɗen kwafi daga wani malamin shi'a.[35][Tsokaci 2]

Nazari

"Pajuheshi piramun zindigani nuwwab khas Imam Zaman (A.F)"wanda Ali Gaffarzadeh wani rubutu ne mai cin gashin kansa a fagen sanin na'ibai huɗu wanda Ayatullahi Jafar Subhani ya rubuta masa mu ƙaddima, kuma kamfanin intisharat nubug suka fara buga shi a shekarar 1375 hijira shamsi.[36]

Bayanin kula

  1. Ahmadi, Nawab Arbaa wa shaksiyat ijtima'i Anan, 1390.
  2. Ahmadi, Nawab Arbaa a zamantakewarsu, 1390.
  3. Tusi, Al-Ghaibah, 1411 AH, shafi na 232-231, Sadouq, Kamal al-Din da Tammam Al-Naimah, 1395 AH, Mujalladi na 2, shafi na 435.
  4. Sadouq, Kamaluddin, 1395 AH, juzu'i na 2, shafi na 476.
  5. Sadouq, Kamaluddin, 1395 AH, juzu'i na 2, shafi na 510.
  6. Tusi, Al-Ghaibah, 1411H, shafi na 356.
  7. Sadr, Tarikh al-Ghaibah, 1412 AH, juzu'i na 1, shafi na 404.
  8. Tusi, Al-Ghaibah, 1411H, shafi na 371.
  9. Jafarian, Hayate Fikri wa Siyasi Imamane Shi'a, 1381H, shafi 583.
  10. Jabbari, Sazman Wakalat, 1382 AH, juzu'i na 2, shafi 480.
  11. Saduq, Kamal al-Din, 1395 BC, juzu'i na 2, shafi na 516.
  12. Ghaffarzadeh, Peramun Zandghani Nawab Khas Imam Zaman, shafi na 85.
  13. Tusi, Al-Ghaybah, 1411 AH, shafi 112; Ghafarzadeh, Zandaghani Nawab Khas Imam Zaman, 1375 AH, shafi na 304.
  14. Jafar, Hayate Fikri wa siyasi Imaman Shi'a, 2013, juzu'i na 1, shafi na 580.
  15. Tusi, Al-Ghaibah, 1411 AH, shafi na 109.
  16. Tusi, Al-Ghaibah, 1411 AH, shafi na 109.
  17. Jafar, Hayate Fikri wa Siyasi Imaman shi'a, 2013, shafi na 585.
  18. Jabbari, Sazman Wakalat, 1382 AH, juzu'i na 2, shafi na 688.
  19. Tusi, Al-Ghaybah, 1411 AH, shafi na 398.
  20. Tusi, Al-Ghaybah, 1411 BC, shafi na 187, 252 da 253.
  21. Tusi, Al-Ghaybah, 1411 AH, shafi na 285 da 286.
  22. Tusi, Al-Ghaybah, 1411 BC, shafi na 287-289.
  23. Kulayni, Kafi, 1362 AH, juzu'i na 1, shafi 518.
  24. Kulayni, Kafi, 1362 AH, juzu'i na 1, shafi na 176
  25. Jafar, Hayate Fikri wa Siyasi Imaman Shi'a, 1381H, shafi 588.
  26. Jafar, Hayate Fikri wa Siyasi Imaman Shi'a, 1381H, shafi 588.
  27. Jassim Hussein, Tarikh Siyasi Gaibat Imam Dawazdahom, 1385H, shafi na 166.
  28. Tusi, Al-Ghaybah, 1411 AH, shafi na 391.
  29. Jafar, Hayate Fikri wa Siyasi Imaman Shi'a, 1381H, shafi 588
  30. Ghaffarzadeh, Zandaghani Nawab Khas Imam Zaman, 1379 AH, shafi 86-87.
  31. Tusi, Al-Ghaybah, 1411 AH, shafi na 290.
  32. Saduq, Kamal al-Din, 1395 BC, juzu'i na 2, shafi na 520.
  33. Tusi, Al-Ghaybah, 1411 BC, shafi na 324, 373, 378, 388, 390; Saduq, Kamal al-Din, 1395 BC, 1403 BC, juzu'i na 2, shafi na 519; Majlisi, Bihar Al-Anwar, 1403, juzu'i na 53, shafi na 192.
  34. Ibn Tawus, Misbah al-Zahir, 1416 BC, shafi na 514.
  35. Majlisi, Bihar Al-Anwar, 1403 BC, juzu'i na 99, shafi na 293.
  36. پژوهشى پيرامون زندگانى نواب خاص امام زمان(عج)، کتابخانه دیجیتال نور.

Tsokaci

  1. اخْتَصَّكَ بِنُورِهِ حَتَّى عَايَنْتَ الشَّخْصَ فَأَدَّيْتَ عَنْهُ وَ أَدَّيْتَ إِلَيْهِ ثُمَّ تَرْجِعُ فَتَبْتَدِئُ بِالسَّلَامِ عَلَى رَسُولِ اللَّهِ ص إِلَى صَاحِبِ الزَّمَانِ وَ تَقُولُ بَعْدَ ذَلِكَ جِئْتُكَ مُخْلِصاً بِتَوْحِيدِ اللَّهِ وَ مُوَالاةِ أَوْلِيَائِهِ وَ الْبَرَاءَةِ مِنْ أَعْدَائِهِمْ وَ مِنَ الَّذِينَ خَالَفُوكَ يَا حُجَّةَ الْمَوْلَى وَ بِكَ اللَّهُمَّ تَوَجُّهِي وَ بِهِمْ إِلَيْكَ تَوَسُّلِي ثُمَّ تَدْعُو وَ تَسْأَلُ اللَّهَ مَا تُحِبُّ تَجِبُ إِنْ شَاءَ اللَّهُ تَعَالَى
  2. السَّلَامُ عَلَیک أَیهَا الْعَبْدُ الصَّالِحُ النَّاصِحُ لِلَّهِ وَ لِرَسُولِهِ وَ لِأَوْلِیائِهِ الْمُجِدُّ فِی خِدْمَةِ مُلُوک الْخَلَائِقِ أُمَنَاءِ اللَّهِ وَ أَصْفِیائِهِ السَّلَامُ عَلَیک أَیهَا الْبَابُ الْأَعْظَمُ وَ الصِّرَاطُ الْأَقْوَمُ وَ الْوَلِی الْأَکرَمُ السَّلَامُ عَلَیک أَیهَا الْمُتَوَّجُ بِالْأَنْوَارِ الْإِمَامِیةِ الْمُتَسَرْبِلُ بِالْجَلَابِیبِ الْمَهْدِیةِ الْمَخْصُوصُ بِالْأَسْرَارِ الْأَحْمَدِیةِ وَ الشُّهُبِ الْعَلَوِیةِ وَ الْمَوَالِیدِ الْفَاطِمِیةِ السَّلَامُ عَلَیک یا قُرَّةَ الْعُیونِ وَ السِّرَّ الْمَکنُونَ السَّلَامُ عَلَیک یا فَرَجَ الْقُلُوبِ وَ نِهَایةَ الْمَطْلُوبِ السَّلَامُ عَلَیک یا شَمْسَ الْمُؤْمِنِینَ وَ رُکنَ الْأَشْیاعِ الْمُنْقَطِعِینَ السَّلَامُ عَلَی وَلِی الْأَیتَامِ وَ عَمِیدِ الْجَحَاجِحَةِ الْکرَامِ السَّلَامُ عَلَی الْوَسِیلَةِ إِلَی سِرِّ اللَّهِ فِی الْخَلَائِقِ وَ خَلِیفَةِ وَلِی اللَّهِ الْفَاتِقِ الرَّاتِقِ السَّلَامُ عَلَیک یا نَائِبَ قُوَّامِ الْإِسْلَامِ وَ بَهَاءِ الْأَیامِ وَ حُجَّةَ اللَّهِ الْمَلِک الْعَلَّامِ عَلَی الْخَاصِّ وَ الْعَامِّ الْفَارُوقَ بَینَ الْحَلَالِ وَ الْحَرَامِ وَ النُّورَ الزَّاهِرَ وَ الْمَجْدَ الْبَاهِرَ فِی کلِّ مَوْقِفٍ وَ مَقَامٍ السَّلَامُ عَلَیک یا وَلِی بَقِیةِ الْأَنْبِیاءِ وَ خِیرَةَ إِلَهِ السَّمَاءِ الْمُخْتَصَّ بِأَعْلَی مَرَاتِبِ الْمَلِک الْعَظِیمِ الْمُنْجِی مِنْ مَتَالِفِ الْعَطَبِ الْعَمِیمِ ذی [ذَا اللِّوَاءِ الْمَنْصُورِ وَ الْعَلَمِ الْمَنْشُورِ وَ الْعِلْمِ الْمَسْتُورِ الْمَحَجَّةَ الْعُظْمَی وَ الْحُجَّةَ الْکبْرَی سُلَالَةَ الْمُقَدَّسِینَ وَ ذُرِّیةَ الْمُرْسَلِینَ وَ ابْنَ خَاتِمِ النَّبِیینَ وَ بَهْجَةَ الْعَابِدِینَ وَ رُکنَ الْمُوَحِّدِینَ وَ وَارِثَ الْخِیرَةِ الطَّاهِرِینَ صَلَّی اللَّهُ عَلَیهِمْ صَلَاةً لَا تَنْفَدُ وَ إِنْ نَفِدَ الدَّهْرُ وَ لَا تَحُولُ وَ إِنْ حَالَ الزَّمَنُ وَ الْعَصْرُ اللَّهُمَّ إِنِّی أُقَدِّمُ بَینَ یدَی سُؤَالِی الِاعْتِرَافَ لَک بِالْوَحْدَانِیةِ وَ لِمُحَمَّدٍ بِالنُّبُوَّةِ وَ لِعَلِی بِالْإِمَامَةِ وَ لِذُرِّیتِهِمَا بِالْعِصْمَةِ وَ فَرْضِ الطَّاعَةِ وَ بِهَذَا الْوَلِی الرَّشِیدِ وَ الْمَوْلَی السَّدِیدِ أَبِی مُحَمَّدٍ عُثْمَانَ بْنِ سَعِیدٍ أَتَوَسَّلُ إِلَی اللَّهِ بِالشَّفَاعَةِ إِلَیهِ لِیشْفَعَ إِلَی شُفَعَائِهِ وَ أَهْلِ مَوَدَّتِهِ وَ خُلَصَائِهِ أَنْ یسْتَنْقِذُونِی مِنْ مَکارِهِ الدُّنْیا وَ الْآخِرَةِ اللَّهُمَّ إِنِّی أَتَوَسَّلُ إِلَیک بِعَبْدِک عُثْمَانَ بْنِ سَعِیدٍ وَ أُقَدِّمُهُ بَینَ یدَی حَوَائِجِی أَنْ تُصَلِّی عَلَی مُحَمَّدٍ وَ آلِ مُحَمَّدٍ وَ شِیعَتِهِ وَ أَوْلِیائِهِ وَ أَنْ تَغْفِرَ لِی الْحُوبَ وَ الْخَطَایا وَ تَسْتُرَ عَلَی الزَّلَلَ وَ السَّیئَاتِ وَ تَرْزُقَنِی السَّلَامَةَ مِنَ الرَّزَایا فَکنْ لِی یا وَلِی اللَّهِ شَافِعاً نَافِعاً وَ رُکناً مَنِیعاً دَافِعاً فَقَدْ أَلْقَیتُ إِلَیک بِالْآمَالِ وَ وَثِقْتُ مِنْک بِتَخْفِیفِ الْأَثْقَالِ وَ قَرَعْتُ بِک یا سَیدِی بَابَ الْحَاجَةِ وَ رَجَوْتُ مِنْک جَمِیلَ سِفَارَتِک وَ حُصُولَ الْفَلَاحِ بِمَقَامِ غِیاثٍ أَعْتَمِدُ عَلَیهِ وَ أَقْصِدُ إِلَیهِ وَ أَطْرَحُ نَفْسِی بَینَ یدَیهِ وَ السَّلَامُ عَلَیک وَ رَحْمَةُ اللَّهِ وَ بَرَکاتُهُ ثُمَّ صَلِّ صَلَاةَ الزِّیارَةِ وَ أَهْدِهَا لَهُ وَ لِشُرَکائِهِ فِی النِّیابَةِ صَلَّی اللَّهُ عَلَیهِمْ أَجْمَعِینَ ثُمَّ وَدِّعْهُ مُسْتَقْبِلًا لَهُ إِنْ شَاءَ اللَّهُ تَعَالَی.

Nassoshi

  • Ahmadi, Muhammad Hussein, “Nuwwabul Arba'a Shaksiyat Ijtima'i Anan,” Mujallar Simai Tarikh, Tabistan 1390 - Shamara 4.
  • Ghaffarzadeh, Ali, Zindgani, Nawab Khas Imam of the Zaman, Qom, Nabugh Publications, 1379 AH.
  • Hussaini, Jassim, Tarikh Siyasi Fakuwar Imam Dawazdahom (A.F), Sayyid Muhammad Taqi Ayatullah, Tehran Emirkabir, 1385H.
  • Jabbari, Muhammad Reza, Sazman, WeKalat, wa Naqsh-an Asre A'Immeh, Qum, wanda ya kafa Amozesh Pazhoushi Imam Khumaini, 1382H.
  • Jafarian, Rasul, Hayate Fikri wa siyasi limamane Shi'a, Qum, Ansar, 1381H.
  • Kulaini, Muhammad bin Yaqoub, Usul Kafi, bugun Ali Akbar Ghafari, Tehran, Dar Al-Kutub Al-Islamiyyah, 1388H.
  • Majlisi, Muhammad Baqir, Bihar Al-Anwar Al-Jami'ah Lidurr Akhbar Al-Akhbar Al-Pure Imams, Tehran, Islamic, 1363H.
  • Pazhoushi Peramun Zindgani, Nawab Khas Imam Zaman (Mai Amincin Allah ya tabbata a gare shi), littafinsa, Digital Noor.
  • Sadr, Sayyid Muhammad, Tarikh Gaiba, Beirut, Dar Al-Ta’arif, 1412 BC.
  • Saduq, Muhammad bin Ali, Kamal al-Din wa Tammam al-Nim`ah, Tehran, Islamiya, 1395 BC.
  • Tusi, Muhammad bin Hassan, Al-Ghaybah, Qum, Dar Al-Ma’arif Al-Islamiyyah, 1411 BC.

Ibn Tawus, Ali bin Musa, Misbah al-Za’ir, Kum, Al-Bait, 1375H.