Jump to content

Shalmagani

Daga wikishia

Muhammad Bin Ali Shalmagani (Larabci:الشلمغاني) wanda aka kashe shekara ta 323 h ƙamari, wanda aka fi sani da suna Al'azaƙiri daga cikin jumlar masu da'awar na'ibancin Imam Mahadi (A.F) da wannan dalili ne ma wasiƙa da sa hannun Imam Mahadi (A.F) ta fito kan raddi a kansa. da farko dai shi Shalmagani ya kasance daga Sahabban Imam Hassan Askari (A.S) kuma daga malaman fiƙihun shi'a a zamanin gaiba sugra. a rahotannin malaman ilimin Rijal daga baya Shalmagani ya canja ya karkata zuwa ga guluwi, ya karkace daga ingantacciyar aƙidar da ya kasance a kai a baya, tare da haka kuma ya samu mabiya waɗanda suka shahara da sunan shalmaganiyya, Husaini Bin Ruhi ya kori shalmagani, cikin wani sa hannu daga Imam Mahadi (A.F) da ya fito kan yi masa raddi, an umarci ƴan shi'a su barranta daga Shalmagani.

”Al-Taklif” ɗaya ne daga rubuce-rubucen Shalmagani wanda aka bayyana cewa in banda mas'aloli biyu zuwa uku littafin ya samu goyan bayan Husaini Bn Ruhu, a cewar shaik ɗusi wasu ba'ari daban daga rubuce-rubucen Shalmagani gabanin gullanci da karkacewa haƙiƙa sun kasance ingantattu kuma ana aiki da su, an kama Shalmagani da umarnin Halifa Razi billahi Abbasi, sannan an kashe shi a shekara 323 hijira ƙamari.

Gabatarwa

Shalmagani ya kasance daga Sahabban Imam Hassan Askari (A.S) kuma ɗaya daga malaman fiƙihu da hadisi a lokacin gaiba sugra.[1] shaik ɗusi wanda ya rasu shekarar 460 cikin littafin Al-Gaiba ya naƙalto matsaya biyu game da Shalmagani a wurin Husaini Bin Ruhu Naubekti na'ibi na uku daga Na'ibai guda huɗu.[2] bisa dogara wani naƙali shalmagani yana da matsayi na musammam wurin Husaini Bn Ruhu, ya kuma kasance tsani tsakaninsa da mutane ya na tattaro buƙatun ƴan shi'a ya ɗauka ya kai masa.[3] a wani naƙalin kuma an bada rahoto cewa Husaini Bin Ruhu bai bashi wannan matsayi ba, kaɗai dai Shalmagani ya kasance ɗaya daga masana fiƙihun shi'a abin dogara.[4]

Shalmgani wanda aka fi sani Al'azaƙiri an haife shi a wani ƙauye kusa da garin Wasiɗ da take ƙasar Iraƙi.[5] ana masa alkunya da Abu Jafar.[6] an kama shi ƙarƙashin umarnin Halifa Razi billahi Abbasi halifa na 20 cikin jerin halifofin Abbasiyawa, da kuma umarninsa ne a kashe shi a shekara 323 h ƙamari.[7]

Wani Sashen Sa Hannun Imam Mahadi (A.S) Barranta Da La'antar Shalmagani
Shalmagani yana cikin mutanen da Allah ya gaggauta azaba kansu ya ƙi jinkirta mus, mutum ne da ya karkace daga muslunci, ya fitar da kansa ya yi ridda... Allah ya dawwamar da tsinuwa a kansa, a bayyane da ɓoye cikin kowanne wuri da kowanne lokaci, Allah ya tsinewa masu dacewa da ra'ayinsa da mabiyansa, da duk waɗanda suke kan tafarkinsa a kowanne zamani.[8]

'

Karkata Zuwa Guluwi Da Kuma Da'awar Na'ibancin Imam Mahadi (A.S)

Ance shalmagani ya kasance yana buri da fatan samun na'ibancin Imam Mahadi (A.S),[9] da wannan dalili bayan an naɗa Husaini Bn Ruhu muƙamin na'ibi sai ya shiga suka da saɓani da ƙirƙirar karya yana danganta masa.[10] A rahotan Ibn Asir wanda ya rasu shekarar 630 h ƙamari marubucin tarihi daga ɓangaren Ahlus-sunna, haƙiƙa karkacewar shalmagani wani abu ne da ya bayyana kuma ya karkata zuwa ga guluwi. [11] ya yi imani da cewa ruhin Allah ya shiga cikin Hazrat Adam bayansa kuma ya cirata zuwa sauran Annabawa da wasiyyai har zuwa kan Imam Hassan Askari (A.S) bayansa sai ya shiga shalmagani ma'ana shi kankin kansa.[12] Shalmagani ƙari kan haka ya yi da'awar na'ibancin Imam Mahadi (A.S) ya kuma bayyana kansa matsayin wanda aka umarce shi da bayyana wannan muƙami.[13] ya samu mabiya wanda aka fi saninsu da shalmaganiyya.[14]

Sa Hannun Imam Mahadi Cikin Raddi Kan Shalmagani

Bayan Husaini Bn Ruhu ya yi tsinkaye kan aƙidun Shalmagani, sai ya barranta daga gare shi tare da la'antarsa ya kuma umarci ƴan shi'a su nesance shi.[15] haka nan kuma sa hannun ya fito daga hazrat Mahadi (A.S) zuwa ga hannun Husaini Bn Ruhu kan raddi kan Shalmagani, cikin wannan sa hannu Imam ya barranta daga gare shi da siffanta mutum maƙaryaci da ya karkace daga muslunci kuma ya yi ridda, tare da umartar ƴan shi'a su nesance shi da barranta daga gare shi.[16]

Matsayin Shalmagani A Mahangar ilimin Rijal

Amincewa Da Inganci

A cewar Abbas Iƙbal Ashtiyani wand aya rasu shekarar 1324 cikin littafin ”Khandane Naubekti” haƙiƙa rubuce-rubucen Shalmagani fuskanin kusancinsa da muƙaminsa na ilimi da kusancinsa da Husaini Bn Ruhu gabanin karkacewarsa da gullancinsa sun kasance ingantattu ababen dogara a wurin ƴan shi'a kuma suna komawa zuwa gare su, bayan karkacewarsa sai ƴan shi'a suka tambayi Husaini Bn Ruhu game da litattafan Shalmagani, sai ya basu amsa da cewa abin da shalmagani ya naƙalto daga A'imma (A.S) ku ɗauka. Abin da kuma ya kasance daga ra'ayinsa ku yi watsi da su; [17] da wannan dalili ne wasu suke cewa shalmagani ya kasance amintacce gabanin karkata da gullanci,[18] Shaik ɗusi shima cikin littafin Al-Fihirisat ya ce ƴan shi'a sun kasance suna aiki da litattafan shalmagani gabanin karkatarsa da gullancinsa.[19]

Rubuce-rubucen Shalmagani

Najashi, marubucin ilimin Rijal a ƙarni na biyar h ƙamari, cikin littafinsa mai taken Fihirisat Asma'i Musannifi Al-Shi'a. Ya ambaci littafi goma sha bakwai na Shalmagani.[20] littafin ”Al-Taklif” ɗaya ne daga cikin waɗannan litattafai 21 littafi,[21] ne da ya tattaro riwayoyin Imaman shi'a gabanin karkacewarsa da guluwi. Kuma ƴan shi'a sun kasance suna aiki da shi,[22] a rahotan shaik ɗusi wanda ya rasu shekara ta 460 h ƙamari cikin littafin Al-Gaiba, wasu jama'a daga ƴan shi'a sun kai wannan littafi wurin Husaini Bin Ruhu ya karɓa ya yi nazarin bakiɗayan littafin daga ƙarshe ya goyi bayan abinda ya ƙunsa in banda wurare biyu zuwa uku. Sauran abin da suke cikin daga A'imma (A.S) ya naƙalto babu kuma wani abu da ya saɓawa shari'a a cikinsa.[23] Muhammad Taƙiyyu Shushtari wanda ya rasu shekara 1415 h ƙamari, cikin littafin ƙamus Al-Rijal, ya kawo tsammanin cewa littafin nan mai suna Fiƙhu Al-Rida da aka samu kwafinsa a zamanin Allama majlisi shi ne dai littafin ”Al-Taklif” na Shalmagani.[24]

Bayanin kula

  1. Safari Forushani, Ghalian (Jaryanha wa Bar'Ayandeha), 1378, shafi 136.
  2. Sheikh Tusi, Kitab al-Ghaibah, 1411 AH, shafi na 303 da shafi na 408.
  3. Sheikh Tusi, Kitab al-Ghaibah, 1411H, shafi na 303.
  4. Sheikh Tusi, Kitab al-Ghaibah, 1411 AH, shafi na 408.
  5. Ibn Athir, al-kamal fi al-tarikh, 1385 AH, juzu'i na 8, shafi na 290.
  6. Khoyi, Mujam Rijal Al-Hadis, Islamic Khoyi Foundation, juzu'i na 18, shafi.
  7. Sheikh Tusi, Al-Ghaibah, 1411 AH, shafi na 406 da 412.
  8. Sheikh Tusi, Al-Ghaibah, 1411 AH, shafi na 406 da 411.
  9. Safari Forushani, Ghalian (Jaryanha wa Bar'Ayandeha), 1378, shafi 136.
  10. Khoyi,Mujam Rijal Al-Hadis, Islamic Khoyi Foundation, juzu'i na 18, shafi.
  11. Ibn Athir, al-kamal fi al-tarikh, 1385 AH, juzu'i na 8, shafi na 290.
  12. Iƙbal Ashtiani, Khandane Nobakhti, 1345 AH, shafi na 224-227.
  13. Mashkoor, Farhang Feraƙ Islami, 1375, shafi na 258.
  14. Mashkoor, Farhang Feraƙ Islami, 1375, shafi na 259.
  15. Sheikh Tusi, Kitab al-Ghaibah, 1411 AH, shafi na 406.
  16. Sheikh Tusi, Kitab al-Ghaibah, 1411 AH, shafi na 411-410.
  17. Iƙbal Ashtiani, Khandane Nobakhti, 1345, shafi na 231-232.
  18. Khoyi, Mujam Rijal Al-Hadith, Islamic Khoyi Foundation, juzu'i na 18, shafi.
  19. Sheikh Tusi, Al-Fahrisat, 1417H, shafi na 224.
  20. Najashi, Rizal Al-Najashi, 1365, shafi na 378-379.
  21. Najashi, Rizal Al-Najashi, 1365, shafi na 378.
  22. Safari Forushani, Ghalian (Jarynaha wa Bar'Ayandeha), 1378, shafi 137.
  23. Sheikh Tusi, Kitabut Tauhid 1411H, shafi na 409.
  24. Sheikh Tusi, Kitab al-Ghaibah, 1411 AH, shafi na 409.

Nassoshi

  • Allameh Majlisi, Mohammad Bagher, Bihar Al-Anwar, Beirut, Al-Wafa Foundation, bugu na biyu, 1403 AH.
  • Hurru Ameli, Muhammad bin Hassan, Wasa'il Al-Shia, ƙum, Al-Bayt Institute, 1416H.
  • Ibn Athir, Ali Ibn Muhammad, Al-Kamal fi al-Tarikh, Beirut, Dar al-Asaƙ, bugun farko, 1385H.
  • Iƙbal Ashtiani, Abbas, Khandane Nobakhti, Tehran, Tahuri Library, 1345.
  • Khoi, Sayyid Abulƙasem, Mujam Rijal Al-Hadith, ƙum, Al-Khoei Islamic Foundation, Bita.
  • Mashkoor, Mohammad Javad, Feraƙ Islamic, Mashhad, Astan ƙuds Razavi, 1375.
  • Najashi, Ahmed bin Ali, Rizal al-Najashi, bincike na Sayyid Musa Shabiri Zanjani, ƙum, Al-Nashar al-Islami Est., 1365.
  • Safari Forushani, Nematollah, Ghalian (Jaryanha wa Bar'Ayandeha), Mashhad, Astan ƙuds Razavi, 1378.
  • Sheikh Tusi, Muhammad bin Hassan, Al-Fahrest, ƙum, Al-Fiƙahah Publishing House, bugun farko, 1417H.
  • Sheikh Tusi, Muhammad bin Hassan, Kitab al-Ghaibah, ƙum, Dar al-Maarif al-Islamiyya, bugun farko, 1411H.
  • Tustari, Mohammad Taƙi, ƙamus Al-Rijal, ƙum, Islamic Publications Office, bugun farko, 1419 AH.