Karajin Sama

Daga wikishia

Karajin Sama (Larabci: الصيحة) wata Tsawa ko kuma ace Kira ne da zai fito daga Samaniya yana daya daga cikin yankakkun Alamomin Bayyanar Imam Mahadi (A.F) za a ji wannan Sauti daga Sama, wata Bushara ce kan bayyanar Imam Mahadi (A.F) bayani ne kan Imam Mahadi (A.F) da gaskatuwar Mazhabar Shi’anci, a karshen wannan rana dai kuma za aji wani Karaji daga Shaidan yana bada gaskiya zuwa ga Usman Bn Affan da Mabiyansa, hakan zai sanya kokwanto ga wasu ba’ari. An ambaci wasu hususiya ga wannan sauti a riwayoyi daga ciki shine dukkanin mutane zasu ji wannan sauti da yarensu da suke Magana da shi, bayan nan kuma sai sunan Imam Mahadi (A.S) ya fada kan harsuna, dangane da yaya wannan al’amari zai afaku akwai ra’ayoyi guda biyu, wasu Jama’a sun tafi kan cewa wannan alama ta Karaji za ta zo da surar Mu’ujiza, amma wasu ba’ari kuma suna cewa zai iya yiwuwa ya faru ta hanyar taimakon kayayyakin sadarwa zamani.

Karaji wata Tabbatacciyar Allama ce Yankkakiya kan Zuhuri

Imam Sadiƙ (A.S):

قَبْلَ قِيَامِ الْقَائِمِ خَمْسُ عَلَامَاتٍ مَحْتُومَاتٍ الْيَمَانِيُّ وَ السُّفْيَانِيُّ وَ الصَّيْحَةُ وَ قَتْلُ النَّفْسِ الزَّكِيَّةِ وَ الْخَسْفُ بِالْبَيْدَاءِ؛

Kafin miƙewar ƙa'im akwai wasu tabbatattun alamomi guda biyar: Yamani, Sufyani, karajin sama, Kashe Nafsuz Zakiyya da kisfewar ƙasa a baida'u

Tarikh Bayigani, Sadouq, Kamaluddin, 2014, juzu'i na 2, shafi na 650, H7.

Saihatu Asimani (Karaji daga Samaniya) da labaraci ana kiranta da (Assaihatu) ishara ce zuwa ga wani sauti lokacin da Imam Mahadi (A.S) ya kusa bayyana za aji wannan sauti ne daga Sama [1] kan asasin riwayoyi wannan sauti wata shela ce da Mala’ika Jibrilu zai samar da ita [2] kuma dana daya daga cikin Alamomin bayyanar Imam Mahadi (A.S) [3] wasu ba’ari sun Imani da cewa akwai Tawatiri Ma’anawi kan wannan batu [4] an ce akwai kusan hadisai daidai har guda 68 da aka kawo su cikin littafin Al-Gaibatul Numani sannan kuma akwai hadisi 30 da yake Magana kan wadannan Alamomi na bayyana [5] Dangane da Karajin Sama akwai riwaya da ta zo da lafazin (Annida’u) Kira [6] haka kuma a ba’arin waus riwayoyin ayar

«إِنْ نَشَأْ نُنَزِّلْ عَلَيْهِمْ مِنَ السَّماءِ آيَةً فَظَلَّتْ أَعْناقُهُمْ لَها خاضِعِينَ؛

Idan muka ga dama zamu saukar musu da aya daga Sama wuyoyinsu zasu kaskanta gaban wannan aya [7]-[8] Haka kuma ayar

«َّ فَإِذا نُقِرَ فِي النَّاقُور؛

A lokacin da aka yi busa cikin Kaho. Wannan aya anyi tawilinta da ishara ne kan Karaji daga Sama. [9]- [10]

Kasacewarta Tabbatacciyar Alama

Kan asasin riwayar da Shaik Saduk ya nakalto daga Imam Sadiƙ (A.S) hakika Karajin Sama tare da Fitowar Sufyani, Fitowar Yamani, Kusufu Baida'u da kashe Nafsuz Zakiyya Alamomi ne da suke tabbatar da kusantowar bayyana Imam Mahadi (A.S) [11] a wata riwayar ya zo cewa farko kira daga Sama zai faru ne a Watan Ramadan [12]

Abin da ta Kunsa da Kuma Siffofi

Abinda ke kunshe cikin Kira na Sama da yake bayanin Imam Mahadi (A.S) zai kasance tare da sunansa da Siffofinsa [13] kan bayanin ba’arin wasu riwayoyi, wannan Karaji zai bayani kan gaskiyar da cancantuwar Imam Ali (A.S) da gaskiyar `Yan Shi’arsa [14] haka kuma an kawo riwaya cewa Karajir Sama na nufin kawo karshen Hukumar Azzalumai `Yan danniya, da kuwa zuwan mafi ingancin mutum cikin al’umma, Annabi ya bada labari cewa za a kira Mutane a Makka domin risker tafiyar Imam Mahadi (A.F) [15]

Hususiyya

An kawo hususiya da siffofin Karaji a cikin riwayoyi:

  • baki dayan mutane za su ji ta su fahimceta da yarensu da suke Magana. [16]
  • Za aji wani Kira daga Sama. [17]
  • Na kusa da na Nesa duk da yanayi guda daya za su ji ta. [18]
  • Za ta tashi wanda suke cikin bacci zasu firgita kowa da kowa [19]
  • Rahama ce ga Muminai kuma Azaba ce ga Kafirai. [20]
  • Bayan kira sai sunan Imam Mahadi (A.F) ya fada kan harsuna. [21]

Lokacin da Abun Zai Faru

Akwai riwayoyi mabambanta game da Kiran Sama, bida dogara da wasu ba’arin riwayoyi sun bayyana cewa zai faru gabanin bayyanar Imam (A.S) [22] wasu ba’ari kuma sun nuna cewa zai faru a lokacin bayyanar [23] wasu kuma suka ce bayan bayyanar [24] gabanin mikewarsa haka kuma kan asasin wasu riwayoyi wannan karaji zata faru ne a watan Ramadan [25] amma kuma wasu sun bayyana cewa a watan Rajab [26] wani nakalin kuma a Ranar Ashura [27] Akwai wadanda suka tafi kan cewa cikin Marhalolin zuhuri da Mikewar Imam Mahadi (A.F) zuwa samun tabbatuwar hukumarsa za aji Karaji da kira daban daban a wannan duniya [28]

Karajin Shaidan

Cikin wasu ba’arin hadisai yazo cewa a karshen wannan Rana shima Shaidan zai yi Karaji da niyyar haiar da shakku da kokwanto ga Mabiya Mahadi (A.F) [29] wannan Karaji zata fito tana bayyana cewa Usman Bn Affan da Mabiyansa sune suke kan gaskiya, hakika an kashe shi bisa zalunci, saboda haka ku mike ku nemi fansar jininsa [30] da wannan kira wasu Jama’a zasu fada cikin shakku [31] A wasu riwayoyi sun bayyana cewa abinda kiran Shaidan ya kunsa shine Kiran mutne zuwa addinin Kiristanci [32] wasu sun tafi kan cewa babu cin karo da juna tsakanin riwayoyin saboda ta iya yiwuwa a samu kira daban-daban daga mutane daban daban da suke aiki da yakar mikewar Imam Mahadi [33] sannan akwai tsammanin danganta kiran zuwa ga Iblis saboda kiran ya faru ne da zugarsa [34] Cikin banbancin kiran sama da kiran Shaidan Malamai sunce shi Kiran Sama daga Sama zai zo kuma zai zo ne ta hanyar da ba sa ba da ita ba da yanayin na Mu’ujiza, sabanin Kiran Shaidan da shi zai faru ta hanyar amfani da kayayyakin zamani [35]

Yaya Zai Faru

A cewar Sayyid Muhammad Sadar cikin littafin Tarikh Algaiba Alkubra, hakika wasu ba’arin AlamominBayyana misalin Kiran Sama za su faru ne da yanayi na Mu’ujiza [36] a cewar Kodamurad Sulamiyan Mai bincike kan Sha’anin Mahadawiyya, hakika a zahirin riwayoyin za a fahimci cewa wannan kira ba zai zo da yanayi da aka saba ji ba [37] Sabanin wadanda suka tafi kan cewa wannan Karaji daga Sama za ta faru ne ta hanyar kayayyakin sadarwa na zamani misalin Satelite (Tauraron dan Adam), ta yiwu kan wannan asasi da bayani ya zama bai kamata mu yi gaggawa fitar da Natija ba kan cewa wannan abubuwa za su faru da yanayi na Mu’ujiza [38]

Bayanin kula

  1. Salimian, ّFarhang Nameh Mahdaviyat, 2008, shafi na 441.
  2. Duba Nomani, Al-Ghaibah, 1397 AH, shafi na 290, h6.
  3. Duba Nomani, Al-Ghaibah, 1397 AH, shafi na 290, h6.
  4. Mahori, "Saiha asimani Nashaneh Zuhuri", shafi na 67.
  5. Mohammadi Rishahri, Daneshnameh Imam Mahdi, 2013, juzu'i na 7, shafi na 441.
  6. Misali, duba Nu'mani, Al-Ghaibah, 1397H, shafi na 274, h6.
  7. Suratul Shaara, aya ta 4.
  8. Tusi, Al-Ghaibah, 1411 AH, shafi na 177.
  9. Suratul Mudassir, aya ta 8.
  10. Estrabadi, Taweel Al-Ayat Al-Zahira, 1409 AH, shafi na 708.
  11. Sheikh Sadouq, Kamaluddin, 1412 AH, juzu'i na 2, shafi na 650.
  12. Nomani, Al-Ghaibah, 1397 AH, shafi na 289, h6.
  13. Misali, duba Sheikh Sadouq, Kamal al-Din, 1412 AH, juzu'i na 2, shafi.372.
  14. Kulaini, Al-Kafi, 1401 Hijira, juzu'i na 8, shafi na 310.
  15. Mofid, Al-Ekhtasas, 1413 AH, shafi na 208.
  16. Nomani, Al-Ghaibah, 1397 AH, shafi na 274, h. 54.
  17. Kulaini, Al-Kafi, 1401 Hijira, juzu'i na 8, shafi na 310.
  18. Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 51, shafi na 109, h42.
  19. Duba Nomani, Al-Ghaibah, 1397 AH, shafi na 254.
  20. Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 51, shafi na 109, h42.
  21. Kurani, Mujamu Ahadis Al-Imam al-Mahdi, 1411 AH, juzu'i na 3, shafi na 35, AH 589.
  22. Nomani, Al-Ghaibah, 1397 AH, shafi na 254.
  23. Nomani, Al-Ghaibah, 1397 AH, shafi na 263, h. 22; Sheikh Sadouq, Kamal al-Din, 1412 AH, Juzu'i na 1, shafi na 330, H. 16.
  24. Kurani, Mujamu Ahadis Imam Al-Mahdi, 1411 Hijira, Mujalladi na 3, shafi na 489, H. 1060.
  25. Nomani, Al-Ghaibah, 1397 AH, shafi na 254 da 290.
  26. Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 51, shafi na 109, h42.
  27. Kurani, Mujamu Ahadis Imam Al-Mahdi, 1411 Hijira, Mujalladi na 3, shafi na 489, H. 1060.
  28. Mehori, "Saiha Asimani Nashaneh Zuhur Imam Mahadi", shafi na 75.
  29. Nomani, Al-Ghaibah, 1397 AH, shafi na 265, h. 29.
  30. No'mani, Al-Ghaibah, 1397 AH, shafi na 261, H. 19 da 20.
  31. No'mani, Al-Ghaibah, 1397 AH, shafi na 261, H. 19 da 20.
  32. Ibn Tavus, Al-Tashrif, 1416H, shafi na 133.
  33. Mehori, "Saiha Asimani Nashaneh Zuhur", shafi na 70-71.
  34. Mehori, "Saiha Asimani Nashaneh Zuhur", shafi na 71
  35. Mehori, "Saiha Asimani Nashaneh Zuhur", shafi na 71
  36. Sadr, Tarikh al-Ghaibah Al-Kubra, 1412 AH, shafi na 480.
  37. Salimian, Farhanga Nameh Mahdaviyat, 2008, shafi 442-443
  38. Esmaili, "Saiha Asimani Nashaneh Zuhur", 2008, shafi 261-260.

Nassoshi

  • Ibn Tavus, Ali Ibn Musa, Al-tashrif balmanan fi al-tarif balftan, Qom, Sahib al-Amr Institute (AJ), 1416 AH.
  • Astarabadi, Ali, Tawheel Al-Ayat Al-Zahira fi Fadael al-Utrah al-Tahirah, edited by Hossein Wali, Qum, Al-Nashar al-Islami Foundation, 1409 AH.
  • Ismail, Ismail,بررسی نشانه‌های ظهور»، A cikin mujallar Hauzah, lambobi 4 da 5, 1374.
  • Salimian, Khodamorad, Farhanga Nameh Mahdawiyat, Qum, Hazrat Mahdi Mououd Cultural Foundation, bugu na biyu, 2008.
  • Sadr, Seyyed Muhammad, Tarikh al-Ghaibah al-Kubari, Beirut, Dar al-Taraif don bugawa, 1412H.
  • Sadouq, Muhammad bin Ali, Kamal al-Din wa Tamamul Al-Naimah, Beirut, Al-Alami Foundation, bugu na farko, 1412H.
  • Tusi, Muhammad bin Hasan, Kitab al-Ghaibah al-Hajjah, edita na Ebadullah Tehrani da Ali Ahmad Naseh, Qum, Darul Maarif al-Islamiya, 1411H.
  • Kulaini, Muhammad Ibn Yaqub, Al-Kafi, ta kokarin Ali Akbar Ghafari, Beirut, Dar Taqran, bugu na uku, 1401
  • Korani, Ali,معجم احادیث الامام المهدی علیه‌السلام،Qum, Islamic Encyclopedia Foundation, bugu na farko, 1411H.
  • Majlesi, Mohammad Baqer, Bihar Al-Anwar, Beirut, Al-Wafa Foundation, bugu na biyu, 1403H.
  • Mohammadi Rishahri, Mohammad,Daneshnaeh Imam Mahdi (Aj), Kum, Darul Hadith, 2013.
  • Mufid, Muhammad bin Muhammad, Al-Ekhtasas, Ali Akbar Ghaffari da Mahmoud Moharrami, Qum, Al-Anqar Al-Alami Lalfiya Al-Sheikh Al-Mufid, 1413H.
  • Mahmouri, Muhammad Hussaini, «ندای آسمانی نشانه ظهور»Rowaq Andisheh, Mujalladi 17, Mayu 2013.
  • Nomani, Muhammad bin Ibrahim, Al-Ghaibah, bugun Ali Akbar Ghafari, Tehran, Publishing Sadouq, 1397H.