Tauki’n Imam Mahadi (A.F)

Daga wikishia

Tauki’in Imam Mahadi (A.F) (Larabci: توقيعات الإمام المهدي (ع)) ba wani abu bane face wasikun Imami na goma sha biyu ga `yan Shi’a da ya aiko su a lokacin Gaiba Sugra, hakika sun kasance amsoshin tambayoyin da `yan Shi’arsa suka yi masa, ya zo a hadisi cewa adadin Tauki'i sun kai guda 100 kan batutuwan da suka shafi fikihu da akida, ya bada amsar su ne da hannunsa ko kuma shiftawa zuwa ga kebantattun Na’ibai guda hudu, Malaman fikihun shi’a a wurare da dama suna istinbadin hukunce-hukuncen shari’a daga wadannan wasiku. Ya zo cikin littafan Algaiba Shaik Tusi da Kamalud-Addini wa-Tamam An-Ni'ima na Shaik Saduk sun ware fasali na musammam da suka tattaro wasikun Imam Mahadi (A.F) haka zalika akwai littafi sukutum da aka rubuta shi kan batun wasikun Imam Mahadi (A.F)

Sanin Mafhumi

Tauki’in Imam Mahadi (A.F) kan tsinewa Shalmaganiwacce ya aikowa da Husaini Bn Ruhu Naubekti: ku sanar da mutane cewa hakika mu muna kauracewa Shalmagani; kamar yanda muka kauracewa ire-irensa gabaninsa, hakama ma mun kauracewa Shari’i da Namiri da Hilali da Bilali.

Littafin Ihitijaju na Dabarasi j 2 sh 290.

Ana kiran wasiku da rubutun Imamul Hujja da sunan Tauki’i [1] a lokacin Gaiba sugra Imamul Mahadi (A.F) yana basa amsar wasikun da aka aika gareshi ta hannun Na’ibai guda hudu.[2] Tauki’in Imam Mahadi (A.F) wani lokaci yana kasancewa da rubutunsa wani lokacin kuma shifta ma Na’ibansa yake su rubutu, dogaro da bayanan da tarihi ya kawo a cikin Tauki’insa akan samu tambarinsa a kai [3] a karshen wasu wasikun kuma yak an yi rubutu da hannunsa [4] an karbo daga Abdullahi Bn Jafar Himyari: Lokacin da Abu Amru (Na’ibi na farko ga Imam Mahadi) ya mutu mun samu wasu wasiku dangane da halifancin Abu Jafar (Na’ibi na biyu ga Imam Mahadi) sai muka ga wannan rubutu dai da muke aika wasiku ake aiko mana da amsa a cikinsu [5] haka zalika an samu wani Tauki’I daga Imam Mahadi (A.F) da rubutun Ahmad Bn Ibrahim Naubakti da kuma shiftawar Husaini Bn Ruhu Naubakti (Na’ibi na uku ga Imam Mahadi (A.F) [6]

Wata Ma’anar Daban

Kalmar Tauki’i kalma ce ta zo cikin hadisan da suke ba rubutattu ba daga Imami na goma sha biyu cikin jerin Imaman Shi’a [7] haka kuma Shaik Saduk ya kawo ba’arin zantukan Imam Mahadi [8] da kuma wasu ba’arin zantukan kebatattun Na’ibansa guda hudu misalin labarurrukan na bayyane da na boye dangane da mas’alolin addini da suka kasance cikin iyakokin tauki’i [9] ance ana tsammanin dalilin yin hakan ya kasance daga Husaini Bn Ruhu Naubakti ya kasance bai zantarwa daga zancen kankin kansa[10] dukkanin abinda ya kawo daga Imam Mahadi (A.F) ya ji. [11]

Adadin Tauki’i

Tauki’in Imam Mahadi (A.F) na karshe zuwa ga Na’ibinsa na hudu: Hakika nan da kwanaki uku masu zuwa zaka bar wannan duniyar, saboda haka sai ka shirya, sannan kada kayi wasiccin wanda zai gajeka bayanka, domin Gaiba ta biyu ta fara aiki, ni kam ba zan kara bayyana ba sai dai idan Allah ya bani izini bayan wani zamani mai tsayi bayan tsanani ya cika zukata da zalunci da danniya, da wuri wani a cikin shi’anmu zai zo yayi da’awar ganina, ku fada ku bude idanuwanku hakika dukkanin wanda ya zo yayi da’awar ganina gabanin fitowar Sufyani da tsawa to wannan mutumi Makaryaci ne karya yake kirkira.

Daga littafin Kamaluddini Saduk j 2 sh 51

Ya zo cikin litattafan hadisi cewa adadin tauki’in ya kai guda 100 daga wanda aka samu [12] yawancinsu suna danganewa da lokacin Gaiba Sugra ya zo cikin littafan Kamaluddini na Shaik Saduk kusan tauki guda 49 da kuma addu’a daya aka nakalto, cikin littafin Algaiba an kawo Tauki’I 43 amma 12 daga ciki daga littafin Kamaluddini aka rawaito su.[13] Haka kuma cikin littafin Al’ihtijaj na Ɗabarasi wanda aka rubutu a karni na shida hijira kamariya an samu tauki’i daga Imam Mahadi (A.F) har zuwa ga Shaik Mufid wanda ya mutu hijira na shekara 413 a tauki’in yana danganewa ga Gaiba Kubra [14] sannan Ayatullahi Kuyi cikin la’akari da wannan tauki’i yayi shakka kansa kamar yanda yake fadi cewa hakika ta hanyar da wannan tauki’i ya gangaro zuwa ga Shaik Mufid da kuma hanyar da ya gangaro zuwa Dabarasi ba sananniyar hanya bace. [15] Wata nukta abar lura shine cewa cikin rubuce rubucen Shaik Mufid da kuma littafin Algaiba da na Shaik Dusi almajirin Shaik Mufid wanda ya wallafa littafi guda kan Gaiba babu wata ishara da ta zo cikin littafin kan wannan tauki’i [16] sai dia cewa kuma idan aka jingina da karshen jumlar da ta zo cikin Tauki’in kamar haka (ku boye shi daga barin kowa da kowa) [17] akwai tsammanin cewa Shaik Mufid ya biye wannan tauki’in ne yana sane da wannan dalili ne yasa bai iso zuwa hannun Shaik Dusi ba. [18] [19]

Maudu’in Tauki’i

Tauki’in da suka zo daga Imamul Mahadi (A.F) sun tattaro maudu’ai mabanbanta daga Akida.fikihu,nadi da kwabe wakilai, karbar hakkokin shari’a, karyata masu karyar da’awa na’ibanci, amsa bukatun shi’a 19, hakika a cikin wasikun Imam Mahadi (A.F) a kashi na hudu baki dayansa Magana ne kan mas’alolin Akida, hukunce-hukuncen fikihu, karamomi da addu’o’i da kuma wasu batutuwa daban daban [20]

Akida

Wani bangare daga Tauki’in Imam Mahadi (A.F) Magana zuwa ga Is’hak Bn Yakub:

«وَ أَمَّا الْحَوَادِثُ‌ الْوَاقِعَةُ فَارْجِعُوا فِيهَا إِلَى رُوَاةِ حَدِيثِنَا فَإِنَّهُمْ حُجَّتِي عَلَيْكُمْ وَ أَنَا حُجَّةُ اللَّهِ عَلَيْهِم

Amma gameda abubuwan da suke faruwa hakika sai ku koma zuwa ga Marawaitan hadisanmu hakika su hujjata ne a kanku ni kuma hujjar Allah ne.

Saduk, Kamaluddin, 1395 AH, juzu'i na 2, shafi na 484.

Wani adadi daga Tauki’i da ya zo daga Imamul Mahadi (A.F) sun kasance amsa ga tambayoyin akida misalin siffofin Allah, Annabta da Imamanci, Hazrat Mahadi (A.F) cikin amsarsa ga tambayoyin da suka shafi Imamanci tareda ishara zuwa ga cewa lallai babu wani lokaci da kasa zata wofinta daga barin hujja hakika wannan sunna ce ta Ubangiji kuma za ta cigaba har zuwa tashin Alkiyama, hakika Imam (A.S) yana sauke nauyinsa cikin ayyana wane ne zai kasance Imami bayansa, Imam Hassan Askari (A.S) ya ayyana Imam Mahadi (A.S) a matsayin Imami magajinsa da zai kasance a bayansa, sannan kuma karyata mai da’awar gadarsa da karya wato Jafarul Kazzab sannan kuma ya hani yan shi’a kan bincike da ayyana lokacin bayyanar Imam Mahadi (A.F). [21]

Masu da’awa na karya

Wani bangare na Tauki’i da ya zo daga Imam Mahadi (A.F) cikin la’anta da karyata masu da’awar na’ibanci na karya, daga ciki akwai wani tauki da ya zo kan Abu Muhammad Hassan Shari’ati mutum na farko da ya fara yin shelar karya cewa yana da dangantaka da Imamul Mahadi (A.F) a zamanin Gaiba Sugra, sai Imam Mahadi (A.S) ya tsine masu a cikin tauki’in da ya zo. [22]

Tauki’in da ya kunshi bayanan fikihu

Wnai bangare daga Tauki’in Imam Mahadi (A.F) yana kunshe da amsa ne ga tambayoyi na fikihu, ya tattaro tambayoyin da `yan Shi’a suka yi game da hukuncin alwala, sallah, azumi, hajji, shahada, alkalanci, wakafi, mu’amaloli, khumusi, sadaka,aure,abubuwa masu bugar da hankali,ziyartar kaburbura A’imma (A.S) da aka bada amsoshinsu. [23]

Karamomi da addu’a

Wani bangare daga tauki’in ya kunshi abubuwa da suke Magana kan karamomi na Imam Mahadi (A.F) daga cikinsu addu’o’in Imam Mahadi (A.F) bayan bukatar hakan daga `yan shi’arsa da kuma ba da labarinsa game da ba’arion wasu hakkoki na kudi a boye [24] daga cikinsu akwai tauki’insa gameda tabbatar da cancantuwa da kuma Imamancinsa (A.F). [25]

Ingancin tauki’insa

Malaman fikihu a wurare masu yawa domin ciro hukuncin shari’a suna jingina da wannan tauki’I [26] alal misali Malaman fikihu na shi’a tareda dogaro da tauki’insa sun bada fatawar haramci ko karhanci cikin amsa tambayar Muhammad bn Abdullah Himyari kan hukuncin yin salla gefan Kabarin Imamai, sai dai cewa ana iya yin sallar a bayan Kabarburan nasu. [27] Haka dangane da tauki’in Imam Mahadi (AF) wanda ya kunshi wasicci da komawa zuwa ga Marawaita hadisai, [28] ana amfani da wannan magana tasa domin tabbatar da nazariyar wilayat fakihi, hakika Imam Khomaini dogaro da wannan tauki’i ya tafi kan cewa dole a mika ragamar lamurra zuwa ga Malaman fikihu.[29]

Sanin tushe

Wasikar Imam Mahadi (A.F) cikin goyan bayan Husaini Bn Ruhu: Mu mun san shi, Allah ya tabbatar masa da dukkanin alherinsa da farin cikinsa, ya kuma sanya shi farin ciki da falalarsa. Muna sane da wasiƙarsa kuma mun amince da shi. Yana da matsayi a wurinmu wanda zai faranta masa rai. Allah ya kara masa falala

Tusi, Al-Gaiba bugun shekara 1411,h.k. shafi 372

Kamar yanda ya zo cikin littafin Daneshnameh Imam Mahadi (A.F) mafi muhimmancin tushen tauki’in Imam Mahadi (A.F) shine littafin Kamalu-Addini wa-Tamam An-Ni'ima na Shaik Saduk da kuma littafin Algaiba na Shaik Tusi [30] kowwane daya cikinsu ya ware bangare guda mai cin gashin kansa da ya tattaro Magana kan tauki’i. [31] Sai dai cewa akwai tauki’in da suka zo a sauran litattafan hadisi kamar misalin littafin Alkafi,Al’ihtijaj, Ma’adinul Hikma, Bihar-Anwar, sannan sun zo a Makatibul A"imma cikin yarjeneniyar A’imma a wurare daban daban, [32] haka zalika cikin littafin da aka rubuta kan Wakilai Na’ibai guda hudu misalin littafin Al’akbarul Wukala’il Arba’ati wallafar Ahmad Bn Muhammad wanda ya rasu a shekara 401 h, littafin ya kunshi batun tauki’Ii. [33] Saboda haka akwai rubuce-rubuce masu zaman kansu dangane da tauki’in Imam Mahadi (A.F) sun kunshi tattaro tauki’I, misalin: 1-Kurbul Isnad ila Sahibul Amri, wallafar Abdullahi Jafar Himyari daya daga cikin manyan mutane a birnin Qom a rabin karni na uku hijira Kamari. 2- Tauki Mukaddase, wallafar Jafar Wujdani. 3- Majmu’eh Suknani wa Taukiha wa Ada’iyya Hazrat Bakiyatulla, wallafar Kadimi Shirazi. [34] 4- Mausu’eh Tauki’at Imam Mahadi, wallafar Muhammad Taki Akbar Nejad, Qom Masjidul Jamkaran, 1427 kamari. 5- Tauki’at Nahiya Mukadda, wallafar Allama Majlisi.

Bayanin kula

  1. Mohammadi Rishahri, Daneshnameh Imam Mahdi, 2014, juzu'i na 4, shafi na 115.
  2. Duba Tusi, Al-Ghaibah, 1411H, shafi na 356.
  3. Misali, duba Kulaini, al-Kafi, 1407 AH, juzu'i na 7, shafi na 163.
  4. Misali, duba Kashshi, Rizal al-Kasshhi, 1409 AH, shafi na 513, 551.
  5. Tusi, Al-Ghaibah, 1411H, shafi na 362.
  6. Sadouq, Kamaluddin, 1395 AH, juzu'i na 2, shafi na 508-509.
  7. Shabiri, "Tawqee", shafi na 577.
  8. Sadouq, Kamaluddin, 1395 AH, juzu'i na 2, shafi na 505.
  9. Sadouq, Kamaluddin, 1395 AH, juzu'i na 2, shafi na 502-504; Tusi, Al-Ghaibah, 1411 AH, shafi na 294, 298, 307, 308, 321.
  10. Shabiri, "Tauqee", shafi na 577.
  11. Sadouq, Kamaluddin, 1395 AH, juzu'i na 2, shafi na 508-509.
  12. Mohammadi Rishahri, Daneshnameh Imam Mahdi, 2014, juzu'i na 4, shafi na 117.
  13. Mohammadi Rishahri, Daneshnameh Imam Mahdi, 2014, juzu’i na 4, shafi na 117, qafa na 2.
  14. Tabarsi, al-Ihtjaj, 1403 AH, juzu'i na 2, shafi na 500-497.
  15. Khoi, Mujam Rijal al-Hadith, 1372, juzu'i na 18, shafi na 220.
  16. Mohammadi Rishahri, Daneshnameh Imam Mahdi, 2014, juzu'i na 4, shafi na 445.
  17. Tabarsi, al-Ihtjaj, 1403 AH, juzu'i na 2, shafi na 499.
  18. Mohammadi Rishahri, Daneshnameh Imam Mahdi, 2014, juzu'i na 4, shafi na 445.
  19. Shabiri, "Tauqee", shafi na 582.
  20. Mohammadi Rishahri, Daneshnameh Imam Mahdi, 1393, juzu'i na 4, shafi na 117-120.
  21. Don ganin waɗannan Tauki'at, duba Mohammadi Raishahri, Daneshnameh Imam Mahdi, 1393, juzu'i na 4, shafi 130-165.
  22. Tusi, Al-Ghaibah, juzu'i na 1, shafi na 397.
  23. Don ganin wadannan Tauki'at, duba Mohammadi Rishahri, Daneshnameh Imam Mahdi, 1393, juzu'i na 4, shafi na 180-239.
  24. Don ganin waɗannan Tauki'at, duba Mohammadi Rishahri, Daneshnameh Imam Mahdi, 2013, juzu'i na 4, shafi na 322-425
  25. Mohammadi Rishahri, Tauki'at Imam Mahdi, 1393, juzu'i na 4, shafi na 119.
  26. Don ganin Tauki'at, duba Mohammadi Rishahri, Daneshnameh Imam Mahdi, 2014, juzu'i na 4, shafi na 255-320.
  27. Ameli, Miftah al-Karamah, 1419 AH, juzu'i na 6, shafi na 212-214.
  28. Sadouq, Kamaluddin, 1395 AH, juzu'i na 2, shafi na 484.
  29. Duba Imam Khumaini, Kitab al-Bai, 1421H, juzu'i na 2, shafi na 635; Imam Khomaini Velayat Faqih, 1374, shafi na 78-82
  30. Mohammadi Rishahri, Daneshnameh Imam Mahdi, 2014, juzu'i na 4, shafi na 124.
  31. Sadouq, Kamaluddin, 1395 AH, juzu'i na 2, shafi na 532-482; Tusi, Al-Ghaibah, 1411 AH, shafi na 281 zuwa gaba.
  32. Mohammadi Rishahri, Daneshnameh Imam Mahdi, 2014, juzu'i na 4, shafi na 124.
  33. Mohammadi Rishahri, Daneshnameh Imam Mahdi, 2014, juzu'i na 4, shafi na 123.
  34. Mohammadi Rishahri, Daneshnameh Imam Mahdi, 2014, juzu'i na 4, shafi na 122-124.

Nassoshi

  • Sayyid Ruhollah, Kitab al-Bi, Qum, Ismailian Publications, 1363. [Imam Komaini]،
  • Imam Khomeini, Sayyid Ruhollah, Velayat Faqih, Tehran, Imam Khomeini's Editing and Publishing Institute, 1373.
  • Kuyi Sayyid Abu Kaseem, [Mujamu Rijalil Hadis]Qum, Al-Thaqa al-Islami fi al-Alam printing center, 1372.
  • Shubairi Muhammad Jawad, «توقیع»،Encyclopaedia of Islamic World (Juzu'i na 8), Tehran, 2003.
  • [Shaik Saouk]Muhammad bin Ali, Kamal al-Din da Tammam al-Naimah, Ali Akbar Ghafari, Tehran, Islamia, 1395 H.
  • Tabarsi, Ahmad bin Ali, Al-Ihtjaj Ali Ahl al-Jajj, Mohammad Baqer Khorsan, Mashhad, Mawallafin Morteza, 1403 H.
  • Dusi Muhammad Bn Hassan [Dusi Kitabul Gaiba]Qum, Ebadullah Tehrani da Ali Ahmad Naseh suka buga, Qum, Darul Maarif al-Islamiya, 1411H.
  • Aamili, Seyyed Javad bin Muhammad, Miftah al-Karamah fi Sharh al-Qasas al-Allamah, editan Muhammad Baqir Khalsi, Qum, ofishin wallafe-wallafen Musulunci mai alaka da kungiyar malamai ta Qum Seminary Society, 1419 AH.
  • Kashi, Muhammad bin Omar, Rijal al-Kashi (Okhtiyar Marafah al-Rijal), Muhammad bin Hassan Tousi ya gyara, Hassan Mostafavi, Mashhad, Mashhad University Publishing House, 1409 AH.