Fitowar Sufyani

Daga wikishia

Fitowar Sufyani, (arabic: السفياني) yana daya daga cikin abubuwa guda biyar da za su faru a lokacin kusantowar bayyanar Imam Mahadi (A.F) fitowar ta sa zata kasance a garin Sham, riwaya ta zo daga Imam Rida (A.S) hakika Imam Mahadi (A.F) ba zai bayyana gabanin fitowar Sufyani, a wata riwayar kuma: bayan Sufyani ya yi hukuma tsahon watanni tara a garin Sham zai tunkari garin Madina tare da sojoin sa a wani wuri da ake kira Baida'u sai kasa ta hadiye shi a can. Sufyani a riwayar shi'a da sunna, yana daga jikokin Abu Sufyan da yake mummunan tarihi cikin zubar da jini da rashin tausayi mutane su na firgita da ganin sa, yana da sunaye daban-daban dga ciki akwai Anbasatu Bin Murra.

Tarihi Rayuwarsa Da Halayensa

Cikin litattafan `Yan Shi'a da Ahlus-Sunna an kawo sunaye daban-daban nasa; daga cikin su akwai abin da ya zo a riwaya daga Imam Ali (A.S) cewa sunan sa Anbasatu Bin Murra[1] da kuma Harbu Bin Anbasatu[2] Usmanu Bin Anbasa[3] yana daga jikokin Abu Sufyan[4] haka kuma ya zo cikin litattafan sunna da sunan Harbu Bin Anbasa Moghdisi, Ikdul Al-Darar, 1428 AH, shafi na 128. Mu'awiyatu Bin Utbatu.[5] Hakika riwayoyi sun siffanta shi a matsayin mutum mai yawan zubar da jini, mai kashe mutane, mara tausayi da jin kai,[6] haka ya zo cikin riwayar daga abin da aka nakalto daga Imam Ali (A.S) mutum mai kafadu hudu, da ka gan shi kaga Wawa, Mai ido daya mutane suna firgita da ganin sa,[7] a wata riwaya daga Imam Sadiƙ (A.S) da ta zo cikin littafin Bihar-Anwar: hakika Sufyani Makiyin shi'a ne mai shelar sa zai shela cikin garin Kufa cewa duk wanda ya sare kan dan shi'a za a biya shi lada da dirhami dubu daya.[8]

Tabbacin fitowar Sufyani

Fitowar Sufyani wani tabbataccen lamari ne da zai faru kamar yanda ya zo cikin riwaya daga Imam Sadiƙ (A.S)[9] tare da fitowar akwai Tsawa ta sama da za aji daga sama, da kuma Kashe Nafsuz Zakiyya, Kusufu Baida'u, alamomi ne biyar da za su zo gabanin bayyanar Ka'imu.[10] Haka kuma an nakalto riwaya daga Imam Rida (A.S) bayyanar Ka'imu wani tabbatacen lamari daga Allah, fitowar Sufyani shi ma tabbatacce ne, Ka'imu ba zai taba bayyana ba[11] har sai Sufyani ya fito, ya zo cikin wata riwaya daga Imam Sadiƙ (A.S) ya bayyana cewa: Sufyani tabbas zai bayyana a watan Rajab,[12] a wata riwaya daga Imam Baƙir (A.S) tana hakaito cewa fitowar Sufyan da Sayyid Yamani da Sayyid Khurasani duka zai faru cikin shekara daya ba zai faru a wata guda ba ko rana daya ba.[13]

Kusufin Baida'u: halakar Sufyani

Asalin Makala: Kusufu Baida'u

Ya zo cikin riwaya daga Annabi (S.A.W) daya daga cikin alamomin bayyanar Imam (A.F) akwai fitowar runduna daga garin Sham zuwa Makka da kuma hadiyewar da kasa zata yi musu a Baida'u (wata sahara ce tsakanin Makka da Madina) kamar yanda bayanin haka ya zo a litattafan riwaya ya shahara da Kusufi Baida,[14] saboda haka a wata riwayar Imam Ali (A.S) dangane da yanki daga aya ta 51 cikin suratul Saba'i

(وَ لَوْ تَرىٰ‌ إِذْ فَزِعُوا فَلاٰ فَوْتَ‌ وَ أُخِذُوا مِنْ‌ مَكٰانٍ‌ قَرِيبٍ)

Kuma da ace ka gani yayin da suka firgita kuma babu kubuta kuma aka kama su daga wuri makusanci. Ya bayyana cewa wannan aya tana ishara kan Sufyani, ya kuma kara bayyana cewa zai yi hukuma tsahon watanni tara a garin Sham bayan nan sai ya ja rundunar sa ya nufi Madina, sai ubangiji ya halaka shi a saharar Baida inda kasa zata hadiye shi.[15]

Alamomin na gaskiya na hakika ko kuma ramzi ne?

Sayyid Muhammad Sadar wanda ya rayu tsakanin shekara (1322-1377 sh) daya daga cikin Maraji'an taklidi a karni na sha hudu shamsi a ikin littafin Tarikul Al-Gaiba Al-kubra, ya bayyana cewa Sufyani wata alama ce ta karkacewa cikin al'ummar musulmi,[16] sai dai cewa cikin amsar da ya bayar yace: daukar alomomin bayyana matsayin ramzi wani abu ne da ya sabawa hadisai,[17] kuma zai iya zama sababin wazifar sanin alamomin bayyana da sanin Imam Mahadi (A.S) ya zama daga Masu da'awa ta karya,[18] ya zama mana an soke su[19]

Bayanin kula

  1. Ibn Tavus, al-Tashrif Balmenan, 1416 AH, shafi na 296; Fatlawi, Alamat Al-Mahdi Al-Munthazar, 1421H, shafi na 279.
  2. Shushtri, Ahqaq al-Haq, 1409 AH, shafi na 567; Fatlawi, Alamat Al-Mahdi Al-Munthazar, 1421H, shafi na 337.
  3. Taj al-Din, Majalis Mahdi, 1437 BC, shafi na 223.
  4. Shushtri, Ahqaq al-Haq, 1409 AH, shafi na 567; Fatlawi, Alamot Al-Mahdi al-Muntazhar, 1421H, shafi na 337; Taj al-Din, Majlis al-Mahdawiyyah, 1437 AH, shafi na 223.
  5. Moghdisi, Ikdul Al-Darar, 1428 AH, shafi na 116
  6. Misali, duba: Ibn Tavus, al-Tashrif Balmenan, 1416 AH, shafi na 115-117; Moghdisi,Akdul Al-Darar, 1428 AH, shafi na 76.
  7. Duba: Allameh Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 52, shafi na 205
  8. Alameh Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 52, shafi na 215.
  9. Sheikh Sadouq, Kamal al-Din, 1429 AH, juzu'i na 2, shafi.678, h5; P.680, H14 da 15.
  10. Sheikh Sadouq, Kamal al-Din, 1429 AH, juzu'i na 2, shafi na 678, h5.
  11. Himyari, Qarb al-Isnad, shafi na 374, 1329 bayan hijira
  12. Nomani, Al-Ghaibah, [1397 AH], shafi na 302.
  13. Nomani, Al-Ghaibah, [1397 AH], shafi na 369.
  14. Ibn Tavus, Al-Tashrif Balmanan, 1416 Hijira, shafi na 158, H. 205 da 206.
  15. Nomani, Al-Ghaibah, [1397 AH], shafi na 305.
  16. Sadr, Tarikh al-Ghaibah al-Kubra, 1412 AH, shafi na 484.
  17. Mohammadi Rishahri, Encyclopaedia na Imam Mahdi, 2013, juzu'i na 7, shafi na 460.
  18. Mohammadi Rishahri, Encyclopaedia na Imam Mahdi, 2013, juzu'i na 7, shafi na 414-415.
  19. Mohammadi Rishahri, Encyclopaedia na Imam Mahdi, 2013, juzu'i na 7, shafi na 460.

Nassoshi

  • (Juzu'i na 7), Hadisi da Tarihi, Kum, Cibiyar Kimiyya da Al'adu ta Darul-Hadith, 2013.
  • 8CBeirut, Al-Wafaa Foundation, 1403 BC / 1983 AD.
  • Fatlawi, Mahdi Hamad, Alamot Al-Mahdi al-Muntazhar (amincin Allah ya tabbata a gare shi) fi kudab Imam Ali (a.s) wa Rasail wa ahadis, Beirut, Darul-Hadi, 1421H/2001 Miladiyya.
  • Himyari, Abdullahi bin Jafar, ƙorb Al-Isnad, ƙum, Mu’assasa Al-Baiti, 1413H.
  • Ibn Tawus, Ali Ibn Musa, Al-Tashrif Balmanan Fi Al-Tafrif Balfatn: Ya Al-Malham Walfatn, Isfahan, Golbahar, 1416 AH.
  • Muƙdisi Shafi Salmi, Yusuf bin Yahya, Ekd Al-Darr Fi Akhbar al-Mantazhar, Abdul Fattah Mohammad Halo ya yi bincike, edita na Ali Nazari Monfard, ƙum, Masallacin Jamkaran, 1428H.
  • Numani Muhammad Bn IBrahim Algaiba
  • Sadr, Seyyed Muhammad, Tarikh al-Ghaibah al-Kubra, Beirut, Dar al-Taarif don wallafe-wallafe, 1412H.
  • Shoshtari Nurullahi Bn Sherif.Tare da gabatarwar Shahab al-Din Murashi Najafi, ƙum, Makarantar Ayatullah al-Azmi Murashi al-Najafi, 1409H. bn Aliyu Bincike Ali Akbar Ghafari, ƙum, Islamic Publishing House, 1429ƙ.
  • Taj al-Din, Mahdi, Majlis al-Mahdawiyyah, ƙum, al-Haydariyya Institute, 1437H.