Husaini Bn Ruhu Naubekti

Daga wikishia
Makwancin Husaini Bn Ruhu

Husaini Bn Ruhu Naubekti (arabic: الحسين بن روح النوبختي) wanda ya bar duniya 326 kamari, daya daga cikin Na’ibai guda hudu na Imam Mahadi (A.F), ya yi Na’ibanci tsawon Shekaru 21 sannan kuma ya kasance daga Sahabban Imam Hassan Askari (A.S) kuma ya kasance daga Mataimakan Na’ibi na biyu a garin Bagdad, Muhammad Bn Usman a karshe-karshen rayuwarsa karkashin Umarnin Imam Mahadi (A.F) ya ayyana Husaini Bn Ruhu Matsayin Magajinsa a Na’ibancin Imam bayan 6 ga Watan Shawwal shekara ta 305 Tauki’i Na farko ya fito daga Imam Mahadi (A.F) dangane goyan bayan Na’ibancin Husaini Bn Ruhu, a farko-farkon Na’ibancin Husaini Bn Ruhu ya kasance yana samun Girmamawa daga Fadar Abbasiyawa amma daga baya sai ya samu matsala da su hakan ya tilasta yin rayuwa a boye tsawon lokaci, kai daga karshe ma suka kama shi suka wurga shi Kurkuku tsawon shekaru biyar, daga cikin Muhimman abubuwa da suka faru a lokacin Na’ibancinsa akwai Waki’ar Shalmagani wanda ya a da kasance yardajje wakilin Husaini Bn Ruhu daga baya sai ya karkace daga hanyar Akidar gaskiya, Tauki’i daga Imam Mahadi (A.F) ya fito yana Tsinuwa kan Shalmagani. Hakika Husaini Bn Ruhu bayan rubuta littafi na Fikhu da sa idanu cikin Munzarorin Ilimi ya samu fifita da daukakar a fagen ilimi, a cikin Masadir na Riwayoyi an nakalto Karamomi daga gareshi

Tarihin Rayuwarsa

Babu cikakken Bayani kan shekarar da aka haife shi, ana masa Alkunya da Abu Kasim amma cikin Masadir ya shahara da Lakubban Naubekti, [1] Ruhi, Qummi, [2] danganta shi da Qum ya samo asalin ne daga Magana da ya yi da Mutanen garin Abeh kusa Sawa da harshen Farisanci da kuma tsammanin [3] Munasabar Kusancinsa [4] tare da da mutanen wannan garin [5] amma a galibin Masadir yafi shahara da Lakabin Naubekti, ana masa lakabi da wannan lakabi sakamakon danganewarsa da Dangin Naubekti, daga bangaren Mahaifiyarsa [6] wasu kuma sun ce reshen Dangin Naubekti daga Qum ya fito a zamanin Na’ibi na farko yayi Hijira zuwa Bagdad [7]

abarin Husaini Bn Ruhu Naubekti

Dangantakarsa Tare da Imam Hassan Askari

cewar Husaini Bn Ruhu yana daga Sahabban Imam Hassan Askari (A.S) akwai sabani ra’ayin Malamai akai, Ibn ShahruAshub cikin Almanakib ya bayyana cewa yana cikin Sahabbansa kuma Mataimakan Imam Hassan Askari (A.S) na musammam [8] amma wasu Malaman Ilimin Rijal basu ce komai ba kan wannan batu, wasu kuma sun tafi kan cewa wannan hadisi yana da matsala saboda Imam Askari (A.S) a shekaru ta 260 hijiri Kamari yayi wafati shi kuma Naubekti ya mutu ne a shekara ta 326 hijiri Kamari [9]

Hususiyoyi

Shaik Tusi cikin littafin Algaiba yace Husaini Bn Ruhu ya kasance mutum mafi hankalin mutanen zamaninsa ya kasance yana Takiyya cikin Mu’amala Ahlus-sunna [10] ta kai Haddin da lokacin da wani Korar daya daga Masu masa hidima saboda zagin Mu’awiya [11] A cewar Jasim Husaini a cikin littafin Tarikh Siyasi Gaibat, kyawawan siffofinsa suka kaishi wannan Mukami [12] Ummu Kulsum `diyar Muhammad Bn Usman dangane da alakarsa da Babanta tana cewa hakika Husaini Bn Ruhu ya kasance daga kebantattun Makusantar Mahaifina ya kasance yana gaya masa kebantattun sirrikansa daga rayuwarsa [13] Abu Sahal Naubekti dangane kiyaye amanar sirrin Husaini Bn Ruhu yana cewa da ace zai boye Imaminsa a Kama shi a dinga yanka shi gunduwa gunduwa kan ya fadi inda Imam yake ba zai fada [14]

Wafati

Husaini Bn Ruhu ya mutu a 18 ga watan Sha'aban a shekara ta 326, Kabarinsa yana Unguwar Naubektiyya a cikin Kasuwar Addaran ko kuma Shurje a garin Bagdad a wannan zamani wurin ya shahara da sunan Mukamu Husaini Bn Ruhu wuri ne na ziyarar `Yan Shi’a [15]

Na’ibanci

Asalin Makala: Na’ibanci na musammam Bayan mutuwar Na’ibin Imam Zaman na biyu a shekara ta 305 an nada Husaini Bn Ruhu Na’ibanci, gabanin nada shi ya kasance Ma’aikaci kula da kudade kuma makusanci na musammam ga Muhammad Bn Usman [16] [17] kuma Muhammad Bn Usman ya sanya wakilinsa tsakaninsa ga sauran Wakilai a Bagdad [18] tare da kasancewa Wakilan Na’ibi na biyu sun kai mutum Goma a garin Bagdad amma Muhammad Bn Usman a lokacin rashin lafiyarsa sai ya ajiye Husaini Bn Ruhu a matsayinsa kuma da jakadanci Sahibul Amri ya kuma nemi `Yan Shi’a su koma gareshi bayan mutuwarsa [19]kamar yanda Allama Majlisi ya rubuta a ranar da Na’ibi na biyu ya rasu Husaini Bn Ruhu ya zauna a gidansa sai Hadimin Muhammad Bn Usman ya tattaro dukanin ajiya da amana da akwatun da ake ajiye ajiyoyin Imamanci ya mika gare shi [20] bayan wani lokaci a 6 ga watan Shawwal shekara 305 sai tauki’in Imam Mahadi (A.F) na farko ya fito kan goyan bayan Na’ibancin Husaini Bn Ruhu [21]

Wasiƙar Imam da take tabbatar da Husaini Bn Ruhu
“Mun san shi (Hussein bin Rooh), Allah ya nuna masa dukkan alherinsa da jin dadinsa, ya kuma sanya shi farin ciki da falalarsa. Muna sane da wasiƙarsa kuma muna da tabbaci kan alhakin da aka damƙa masa. Yana da matsayi a wurinmu wanda zai faranta masa rai. Allah ya kara masa falala”.

Tarikh Bayigani

A ba’arin wasu Nakalin ya zo cewa Matsayin Husaini Bn Ruhu ya kasance sabanin na Na’ibi na farko da na biyu shin a nasa al’amarin ya kasance a bayyane da wannan dalili ne ya sanya wasu adadi daga `Yan Shi’a suka dinga alaka da shi kai tsaye babu shamaki su ka mantar da Wakilan Yanki-Yanki da garuruwansu [22]

Wakilai da Ma’aikata

Husaini Bn Ruhu tare da samun Hadin kai da Wakilai goma a Bagdad da sauran Wakilan garuruwan Muslunci ya bude fara ayyukansa, sunayen Wakilansa da da Ma’aikatansa ya kasance kamar haka: Muhammad Bn Nafis a Ahwaz farkon tauki’in Imam Zaman (A.F) a lokacin Husaini Ruhu ta hannunsa ya yadu.

Matsayi a Fadar Sarki

Husaini Bn Ruhu a lokacin Muhammad Bn Usman yana raye ya samu shiga sosai a fadar Sarkin Abbasiyawa ta kai ga suna aiko masa taimako daga hukuma [24] amma bayan ya karbi Wakilcin Na’ibanci a lokacin halifancin Muktadir har wan nan lokaci yana da matsayi sosai a fada suna kuma bashi girma, dalili samun wannan matsayi ya samo asali albarkacin dangin Naubekti da yake danganewa gare su a kuma gefe guda akwai wazircin Abu Hassan Muhammad Bn Alu Furat wanda ya kasance daga Masoyan [25] `Yan Shi’a [26] a cewar Ummu Kulsum diyar Muhammad Bn Usman a tsawon wannan lokaci kudaden Alu Furat suna isowa wurin Husaini Bn Ruhu [27] daga wasu dalilan kuma na daban da ya samu girma a fada akwai taa tsantsan da ya dinga a wurare daban daban daga cikin nesanta kansa daga tawayen da aka dinga yi a wancan zamani daga cikin tawayen Karamidawa [28] Amma bayan zuwan Hamid Bn Abbasi Wazirci wanda ya kasance yana kiyayya da `Yan Shi’a, sai ya zamana Husaini Bn Ruhu ya fara samun matsala a Fadar Sarki [29]

Buya

Wasu Masadir sun bada Rahotan buyan Husaini Bn Ruhu tsawon wani lokaci bayan ayyana shi Na’ibi sai dai cewa babu cikakken rahoto kan hakikanin lokacin amma akwai tsammanin a shekaru 306-311 a lokacin wazircin Hamid Bn Abbas [30] bisa dogara da abinda Shaik Tusi ya rubuta a wannan daurar ne Muhammad Bn Ali Shalmagani ya kasance Wasida tsani kuma Jakadansa tsakaninsa da al’umma [31] babu wadataccen bayani da rahoto daga wannan daura.

Daure shi a Kurkuku

Husaini Bn Ruhu Naubekti ya zauna a Kurkuku daga shekara 312 zuwa 317 hijiri Kamari a Kurkuku din Muktadir, sai dai cewa a Masadir din Shi’a ba ambaci dalilin daure shi ba, amma ba’arin wasu Masu zurfafa bincike kan asasin Nakalin Ahlus-sunna sun kawo dalilai biyu: 1.kin aikawa da kudade zuwa ga Diwanin Masarauta. 2-alaka da Karamidawa da a wancan zamani sukai nasarar samun iko a Bahrain [32] Wasu ba’arin Masu zurfafa bincike sun bayyana cewa sababin daure shi ya kasance shaharar da yayi a Mukamin Na’ibanci, da kuma alakar da yake da `Yan Shi’a da karbuwar da ya samu cikin daidaita yanayinsu da tattaro wasiku da Hakkokin shari’a da mika su zuwa Hazrat Mahadi (A.S) [33] amma kuma wasu sun tafi kan cewa dalilin kama shi ba wani abu bane sai gabar da yake da Shalmagani da kuma sa hannun Muhsin Bn ALi Bn Furat (`Dan Ali Bn Furat wazirin da yake dasawa da Shalmagani) an daure shi ne a lokacin wazircin Aliyu Bn Furat daga shekara 311 zuwa 312 ya zauna a Kurkuku [34] Bayan an sake shi saboda alfarmar samuwar wasu Manyan mutane daga dangin Naubekti a cikin Hukuma ba a kuma kara samun wani ya takura masa ba [35]

Waki’ar Shalmagani

Asalin Makala: Shalmagani Hakika Shalmagani ya kasance daga Malaman Shi’a a Bagdad kuma yana daga Makusantan Husaini Bn Ruhu, sannan bayan Ayyana Husaini Bn Ruhu Mukamin Na’ibanci sai ya nada Shalmagani wakilinsa ya mika gudanar da al’amuran `Yan Shi’a zuwa hannunsa [36] sai dai cewa lokacin da Husaini Bn Ruhu yake tsare a Kurkuku yayi amfani da matsayinsa kan cimma miyagun muradunsa, da farko sai ya fara bayyana kansa Matsayin Na’ibin Imamul Hujja (A.F) maimakon Wakilin Husaini Bn Ruhu, daga karshe ma sai yayi ridda ya karkacewa Akidar Gaskiya, bayan bayyana karkacewar Shalmagani, Husaini Bn Ruhu bai yi kasa a gwiwa cikin fadakar da `Yan Shi’a wannan al’amari ya kuma haramta musu duk wata mu’amala da shi har zuwa shekara ta 312 lokacin da Tauki’in Imam Mahadi (A.F) ya fito yana mai tsinewa Shalmagani [37]

Mukamin Ilimi da Karamomi

Husaini Bn Ruhu yana da wani littafi na fikihu me suna Atta-Adib ya wallafa shi ne kan bincike da kuma bayyana ra’ayi kan Makarantar Hadisi ta garin Qum ya kuma aika littafin can ya nemi Malaman Qum su karanta su kuma tunasar da shi wurare da suke da sabanin ra’ayi da shi, bayan sun yi mudala’ar littafin sun nuna dukkanin goyan bayansu kan wata gaba sannan suka mayar masa da littafinsa [38] A lokacin Na’ibancinsa yayi munazarori wanda bayaninsu dalla-dalla ya zo cikin litattafan Riwaya,[39] .[40], [41]amsoshin Husaini Bn ruhu kan Tambayoyin da aka bijiro masa da su ya nuna kwarewar kan mas’alolin addini da kuma daukakar a Ilimi [42] hakika ya nakalto riwaya sannan Shaik Tusi [43]ya nakalto Ziyaratu Rajabiyya ta hanyar Husaini Bn Ruhu Naubekti [44]

Karamomi

A ba’arin wasu masadir,an nakalto Karamomi daga Husaini Bn Ruhu, hakika wasu lokuta yak an bayyana wasu Sirruka da wasu Alamomi saboda kawar da kokwanto ga masu kishiyantarsa wani lokacin kuma domin karfafar kansa, wasikar Ali Bn Babawaihi Mahaifin Shaik Saduk zuwa ga Na’ibi na uku domin neman samun haihuwa da kuma neman addu’a daga Hazrat Mahadi (A.S) [45] ko kuma wata wasika daga `dan Babawaihi Mahaifin Saduk kan ayyana masa taklifinsa dangane da tafiya aikin Hajji [46] da kuma labarin mutuwar Ahmad Bn Is’hak Qummi [47]

Bayanin kula

  1. Tusi, Al-Ghaibah, 1411 AH, shafi na 225.
  2. Kashshi, Rizal Kashshi, 1348, shafi na 557.
  3. Sadouq, Kamaluddin, 1395 AH, juzu'i na 2, shafi na 503-504.
  4. Tusi, Al-Ghaibah, 1411 AH, shafi na 195.
  5. Iqbal Ashtiani, Khandani Nobakhti, 1345, shafi na 214.
  6. Iqbal Ashtiani, Khandani Nobakhti, 1345, shafi na 214.
  7. Jassim Hossein, Tarikh Siyasi Gaibat Imam Dawazdahom , 2005, shafi na 192.
  8. Ibn Shahr Ashub, al-Manaqib, 1379H, juzu'i na 4, 423.
  9. Jassim Hossein, Tarikh Siyasi Gaibat Imam Dawzdahom, 2005, shafi na 192.
  10. Tusi, Al-Ghaibah, 1411 AH, shafi na 112.
  11. Tusi, Al-Ghaibah, 1411H, shafi na 386.
  12. Jassim Hossein, Tarikh Siyasi Gaibat Imam Dawazdahom, 2005, shafi na 193 da 194.
  13. Tusi, Al-Ghaibah, 1411H, shafi na 372.
  14. Tusi, Al-Ghaibah, 1411H, shafi na 391.
  15. Tusi, Al-Ghaibah, 1411 AH, shafi na 238
  16. Jassim Hossein, Tarikh Siyasi Gaibat Imam Dawazdahom, 2005, shafi na 192.
  17. Dhahabi, "Siyar A-alam An-Nubala", 1413 AH, juzu'i na 15, shafi na 222.
  18. Sadouq, Kamaluddin, 1395 AH, juzu'i na 2, shafi na 501 da na 502.
  19. Tusi, Al-Ghaibah, 1411H, shafi na 371.
  20. Majlesi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 85, shafi na 211.
  21. Tusi, Al-Ghaibah, 1411H, shafi na 372.
  22. Jassim Hossein, Tarikh Siyasi Gaibat Imam Dawazdahom, 2005, shafi na 198.
  23. Jassim Hossein, Tarikh Siyasi Gaibat Imam Dawazdahom, 2005, shafi na 196
  24. Ghafarzadeh, Zindagi Nawab Khas Imam Zaman, 1375, shafi na 237.
  25. Jassim Hossein, Tarikh Siyasi Gaibat Imam Dawazdahom, 2005, shafi na 198
  26. Jafar,Hayat Fikri Wa siyasi A'immeh, 2013, shafi na 583.
  27. Tusi, Al-Ghaibah, 1411H, shafi na 372.
  28. Azimzadeh Tehrani, Ilalu Dastigiri Hossein bin Ruhu Nobakhti, 1382.
  29. Jafar,Hayat Fikri Wa siyasi A'immeh, 2013, shafi na 583.
  30. Azimzadeh Tehrani, Ilalu Dastigiri Hossein bin Ruhu Nobakhti, 1382 shafina 303-304
  31. Tusi, Al-Ghaibah, 1411 AH, shafi na 303 da 304.
  32. Azimzadeh Tehrani, Ilalu Dastigiri Hossein bin Ruhu Nobakhti, 1382 shafina Dhahabi ya ruwaito a cikin Tarikhul Islam.
  33. Vasoi, Kasai, Fajuhi Piramuni Zindagi Siyasi Farhan Nawab Arbaeh, 1378.
  34. Azimzadeh Tehrani, Ilalu Dastigiri Hossein bin Ruhu Nobakhti, 1382
  35. Vasoi, Kasai, Fajuhi Piramuni Zindagi Siyasi Farhan Nawab Arbaeh, 1378.
  36. Tusi, Al-Ghaibah, 1411 AH, shafi na 228, 239, 251 da 252
  37. Tusi, Al-Ghaibah, 1411 AH, shafi na 187, 252 da 253.
  38. Tusi, Al-Ghaibah, 1411 AH, shafi na 228, 239, 251 da 252
  39. Amin, A-ayan al-Shia, 1421 AH, juzu'i na 6, shafi na 22.
  40. Sadouq, Kamaluddin, 1395 AH, 1403 AH, Juzu'i na 2, shafi na 519.
  41. Majlesi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 53, shafi na 192.
  42. Sadr, Tarikh al-Ghaibah, 1412 AH, juzu'i na 1, shafi na 483.
  43. Khoui, Mujam Rijal Al-Hadith, 1403 AH, juzu'i na 5, shafi na 236.
  44. Tusi, Misbah Al-Mutahajjid, 1411H, shafi na 821.
  45. Najashi, Rijal Najashi, 1407 AH, shafi na 261.
  46. Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 51, shafi na 293.
  47. Sadouq, Kamaluddin, 1395 AH, juzu'i na 2, shafi na 518 da 519.

Nassoshi

  • Amin Ameli, Seyyed Mohsen, A-ayan al-Shi'a, Beirut, Dar al-Taarif, 1421H.
  • Sadouq, Muhammad bin Ali, Kamal al-Din da Tamam Al-Neema, Tehran, Islamia, 1395H.
  • Najashi, Ahmed bin Ali, Rizal al-Najashi, bugun Musa Shabiri Zanjani, Qum, 1407H.
  • Ibn Shahr Ashub Mazandarani, Muhammad Bin Ali, Menaqib Al Abi Talib, Kum, Allameh, 1379H.
  • Tusi, Mohammad bin Hassan, Rijal al-Kashshi (Okhtiar Marafah al-Rijal), Mashhad, Jami'ar Mashhad, 1348.
  • Tusi, Muhammad bin Hassan, Al-Ghaibah, Qum, Mu'assasa Al-Maarif al-Islami, 1411H.
  • Tusi, Muhammad bin Hassan, Misbah al-Mutahjad, Beirut, Institute of Fiqh al-Shia, 1411 AH.
  • Zahabi, Sir Alam al-Nabila, Ishraf da Takhrij: Shoaib al-Arnaut, bincike: Ibrahim al-Zibaq, Beirut, Al-Risalah Foundation, 1413 AH.
  • Khoei, Sidabul al-Qasim, Majam Rizal al-Hadith, Beirut, Dar al-Zahra, 1403H.
  • Sadr, Sayyid Muhammad, Tarikh al-Ghaibah, Beirut, Dar al-Tagharf, 1412H.
  • Iqbal Ashtiani, Abbas, Khanad Nobakhti, Tehran, 1345.
  • Jaafarian, Rasulu,Hayatu Fikri wa siyasi Imaman Shi'a, Qum, Ansari, 2001.
  • Jassim Mohammad Hossein, Tarikh Siyasi Gaibat Imam Dawazdahom, Mohammad Taghi Ayatollahi, Tehran, Amir Kabir, 2005 ya fassara.
  • Ghaffarzadeh, Ali, Zindagi Nawab Khas Imam Zaman, Kum, Nabogh Publications, 1379.
  • Azimzadeh Tehrani, Tahereh, Ilalu Dastigiri Hossein bin Roh Nobakhti, Tarihin Musulunci, spring 2002 - lamba 13.
  • Mousavi, Sayyid Hassan; Kesai, Nouraleh,Fajuheshi Piramuni Zinadagi siayasi Nawab Arbaeh, Faculty of Literature and Humanities, Jami'ar Tehran, bazara 2018 - lamba 150.