Jump to content

Nassi Kan Imami

Daga wikishia

Wannan wani rubutu ne da aka yi shi game da "Nassin imamanci" domin sanin imamanci tare da fayyace Imami ta hanyar nassi, ku duba Imamanci Na Nassi.

Rubutun kaligirafi da salon khaɗɗu Mu'aalla, mai ɗauke da nassin Manzon Allah (SAW) kan wilayar Imam Ali (A.S) a matsayin magajinsa

Nassi kan imami, matani ne na Kur'ani ko hadisi da yake ishara zuwa ga imamancin wani mutum ko wasu jama'a wanda zai iya kasancewa daga Allah, Annabi (S.A.W) ko Imamin da ya gabata, a ra'ayin imamiyya, ayyana Imami dole ne ya kasance a bayyane a fili ƙarara, ko wane Imami yana gabatar da magajinsa ƙarƙashin nassi.

Nassoshin imamanci sun rabu zuwa rukuni biyu: bayyanannen nassi wanda cikinsa imamanci ke kasancewa ƙarara, kamar Hadis Ghadir, da ɓoyayyen nassi wanda cikinsa imamanci bai zo ƙarara kai tsaye ba kaɗai ana fitar da imamanci ne cikin ma'anar da taƙe ƙunshe cikinsa, kamar Hadis Manzilat. Cikin Kur'ani an yi ishara ga imamancin Imamai amma ba kai tsaye ba, kuma ba a ambaci sunayen Imamai ba domin kare Kur'ani daga hannun masu son jirkita shi.

An yi rubuce-rubuce masu yawa game da nassoshin imamanci da suka haɗa da tattara dukkanin nassoshi game da Imamai, binciken keɓantattun nassoshi kamar Hadis Ghadir da warware da'awowin sauran ƙungiyoyi, ba'arin ƙungiyoyi sun yi da'awa cewa akwai nassoshi da suka zo daga Annabi ko Imamai game da wasu ɗaiɗaikun mutane kamar Abubakar, Isma'il ɗan Imam Sadiƙ (A.S) da Abdullahi Afɗahu, sai dai cewa malaman imamiyya sun watsi da wannan magana. Ba'arin Ahlus-Sunna sun yi imani bayan Annabi babu nassi kan ayyana Imami ko shugaba, zaɓen Imami da shugaba yana kasancewa ne kan asasin zaɓi ko galaba.

Matsayi Da Nazarin Ma'ana

A cewar Shaikh Mufid, malamin aƙida a Shi'a (Rasuwa: 413H) nassi daga dalilin kur'ani da sunnar annabi suna ishara da shiryarwa kan imamancin Imami.[1] A ra'ayin malamin samuwar nassin kan imamanci bayan Annabi batu ne da ake saɓani tsakanin Shi'a da Ahlus-Sunna, malaman imamiyya sun yi bakin ƙoƙarinsu cikin tattaro duk wani nassi da yake da alaƙa da Imamancin Ali (A.S).[2]

Fadil Miƙdad malamin aƙida a ƙarni na 9 hijira, ya yi imani da cewa nassi na iya kasancewa daga Allah, da surar magana ko wani aiki da ya shallake abin da aka saba da shi wanda yake shiryarwa kan imamancin wani mutum.[3] Ibn Maisam Bahrani (Rasuwa:679 ko 699H) shima ya yi bayani cewa nassi zai iya kasancewa daga Annabi ko Imamin da ya gabata cikin surar lafazi ko aiki da yake nuni da imamanci wani.[4]

Bayyanannen Nassi Da Ɓoyayyen Nassi

Nassoshi da suke da alaƙa da imamanci sun kasu zuwa bayyananne da ɓoyayye, bayyanannen nassi dalili ne wanda cikinsa ma'anar imamanci ta kasance zahiri a bayyane babu buƙatar ko wane irin ijtihadi don fito da wannan ma'ana, kamar Hadis Ghadir.[5] Kishiyar haka, ɓoyayyen nassi wanda ya ƙunshi ma'anar imamanci amma ba a bayyane ba, kamar Hadis Manzilat.[6] Kan asasin mahangar imamiyya, nassi kan imamanci wajibi ne ya kasance bayyananne, zallan bayanin siffofi da halayen Imami ba ya wadatarwa, saboda gano halaye da siffofi misalin isma ba abu bane mai yiwuwa ga kowa da kowa.[7]

Sayyid Murtada (Rasuwa: 436H) yana da wani rabe-raben daban da ya gabatar daga bayyanannen nassi da ɓoyayye. Kan asasin wannan bayyanarwa, riwayar da aka naƙalto ta a iya litattafan Shi'a yana ɗaukar ta matsayin "Bayyanannen nassi". Riwayar da ƙari kan naƙalto ta a litattafan Shi'a an naƙalto ta a rubuce-rubucen wanda suka saɓa da su kuma sun yarda da ita, yana la'akari da ita matsayin "Ɓoyayyen nassi".[8]

Ra'ayoyi Game da Nassi Kan Imamanci Bayan Annabi

Asalin ayyana Imami ta hanyar nassi abu ne da ya samu karɓuwa gurin dukkanin Musulmi;[9] Amma tare da haka, mafi yawan Ahlus-Sunna sun yi imani da cewa babu wani nassi da ya zo daga Annabi (S.A.W) game da imamanci da shugabanci.[10] Abul Hassan Ash'ari cikin kore samuwar nassi ya dogara da bai'ar da Umar ya yi wa Abubakar a Saƙifa yana mai cewa da ace naɗa Abubakar ya kasance bisa nassi daga Annabi (S.A.W), to da bai'ar da Umar ya yi masa tare da sanin cewa akwai nassi kan shugabancinsa da ta zama aiki mara ma'ana da amfani.[11] Sayyid Murtada cikin suka kan wannan fahimta da mahanga ta Ahlus-Sunna, a wannan karon ya yi ishara zuwa ga gayyar nassoshi daga Ahlus-Sunna wanda a fahimtarsa a bayyane ko ƙarƙashin ishara suna shiryarwa ne kan imamancin Imam Ali (A.S).[12] Cikin Zaidiyya, Yahaya Bin Hamza Alawi wanda aka fi sani da Al-Mu'ayyad Billahi (Rasuwa: 749H) ya yi imani da cewa yarda da bayyanannen nassi kan imamancin Imam Ali (A.S) ya kasance daga aƙidu da suka keɓanta da imamiyya, ya kuma yi imani kaɗai ɓoyayyen nassi kaɗai ya zo game da imamanci.[13]

Sayyidina Muhammad (S.A.W):
Jawabi ga danginsa da ƙabilarsa: "Wane ne zai taimake ni a cikin al'amarin Musulunci, domin ya zama ɗan uwana, wasiyyina kuma halifana daga cikin ku?”

Sai Imam Ali (A.S) ya nuna goyon bayansa, Annabi (SAW) ya yi nuni zuwa gare Ali ya ce: wannan ɗan uwana ne halifana wasiyyina daga cikinku, ku saurare shi ku bi shi.

Ɗabari, Tarikh Ɗabari, 1387ƙ. j 2 s 320-321

Nassoshi Na Imamancin Imaman Shi'a (A.S)

Nassoshi na Kur'ani

Nassoshi na Kur'ani da suke da alaƙa da imamanci sun kasu zuwa kashi uku: Ishara zuwa ga Imamai tsawon tarihi, ayyana wasu Imamai daga tsatson Annabi Ibrahim (A.S) da kuma ayyana Imamai daga iyalan gidan Annabi (S.A.W), kamar ayoyin wilaya, taɗhir, muwadda da tablig, a cewar Muhsin Araki ba a ambaci sunayen Imamai ba a Kur'ani domin kariya ga mataninsa da hana jirkita shi.[14] Bisa riwayar da aka naƙalto daga Imam Sadiƙ (A.S) a cikin littafin Al-Kafi, Kur'ani ya yi bayanin asalai da siffofin Imamai kuma ayyana misalai ya kasance a wuyan Annabi.[15]

Nassoshi Na Riwaya

Cikin riwayoyi daga Annabi (S.A.W) da Imamai an yi ishara game da halifofi. Litattafan Shi'a ƙari kan kawo adadin Imamai sun naƙalto sunayensu, daidai lokacin da litattafan Ahlus-Sunna galibi sun naƙalto iya adadin halifofi kaɗai.[16] Cikin madogaran Shi'a daɗi kan adadi, an yi bayanin sunayen halifofin Annabi, cikin ba'arin naƙali an kawo sunan Imami na farko[17] cikin wasu kuma misalin Hadis Lauhi an ambaci sunayen dukkan Imamai.[18]

Tushen aƙidun imamiyya, ana gabatar da duk Imami ta hannun Imamin da ya gabace shi da nassin Annabi.[19] Da wannan tsarin Imam Ali (A.S) da nassin Annabi (S.A.W),[20] Imam Hassan (A.S) da nassin Annabi (A.S) da Imam Ali (A.S), Imam Husaini (A.S)[21] da nassin Annabi (S.A.W) da Imam Hassan (A.S)[22] suka kai ga imamanci. Imamai tara da suka zo daga zuriyara Husaini suma ko wane ɗaya ya kai ga imamanci da nassin Imamin da ya gabace shi.[23]

Talifofi Masu Alaƙa Tare da Nassosin Imamancin Imaman Shi'a (A.S)

Littafin Isbatul Hudari Bin Nususi Wal Mu'ujizat na Shaik Hurrul Amili (Rasuwa:1104H) cikin batun nassoshi game da Imamancin Imaman Shi'a

Domin tabbatar da samuwar nassi kan imamancin Imamai (A.S) an wallafa litattafai waɗanda za a iya kasa su zuwa kashi biyu:

Nassoshi Da'awa Na Sauran Ƙungiyoyi

Abubakar

Bakariyya wata ƙungiya ce daga Hanbalawa da Khawarijawa, da suka yi imani cewa wai Annabi (S.A.W) a bayyane ya naɗa Abubakar matsayin halifansa.[25] Wata ƙungiyar kuma, daga jumla Baihaƙi, sun tafi kan ra'ayin cewa Annabi (S.A.W) ba kai tsaye ba, ta hanyar ayyana Abubakar limamin jam'i, ya yi nuni zuwa ga imamancinsa.[26] Mafi yawan Ahlus-Sunna ba su yarda da wannan ra'ayi ba, sun yi imani babu wani nassi da ya zo daga Annabi game da ayyana halifansa bayansa.[27] Sayyid Murtada tare da dogara da raunin marawaitan wannan riwaya, da rashin bayani ƙarara cikinta da kuma samun wasu shaidu daga waje, ya yi watsi da wannan da'awa ta Baihaƙi.[28]

Rawandiyya suma sun yi imani Annabi a kaikaice ya naɗa baffansa Abbas matsayin halifansa a bayansa, wannan ra'ayi ya fito ne a farko-farkon daurar mulkin Abbasiyawa.[29]

Isma'il Bin Jafar

Cikin mazhabar Isma'iliyya, Isma'il ɗan Imam Sadiƙ (A.S) ana ɗaukarsa matsayin Imami bayan mahaifinsa, kuma a wurinsu nassi ne kaɗai ma'aunin tabbatar da imamanci;[30] Tare da haka, cikin litattafan Isma'iliyya, babu bayyanannen nassi da aka naƙalto game da imamancin Isma'il.[31][31] ya naƙalto wata riwaya mara sanadi.[32] kuma ruwaya ce da su kansu suke ɗaukar ta matsayin wace ba ta shahara ba.[33] Malaman aƙida na imamiyya sun yi watsi da duk wani nau'in nassi kan imamancin Isma'il, kuma mutuwarsa a lokacin rayuwar Imam Sadiƙ (A.S) dalili ne kan rashin kasancewarsa Imami.[34]

Abdullahi Afɗahu

Abdullahi Afaɗahu ɗan Imam Sadiƙ (A.S) bayan shahadar mahaifinsa ya yi da'awar imamanci kuma an samu wasu tsirarun ƴanshi'a da suka yi imani da imamancinsa.[35] An ce ɗaya daga cikin dalilan da'awarsa, akwai wasiyyar Imam Sadiƙ (A.S)[36] da ya yi da mutane biyar daga jumla har da shi Afɗahu a matsayin wasiyyansa bayansa.[37] Allama Majlisi tare da ishara da raunin sanadin wannan riwaya, ayyana ba'arin mutane kamar Mansur Dawaniƙi da Humaida matar Imam Saɗiƙ a matsayin wasiyyai yana ganin hakan ya faru ne saboda taƙiyya.[38] A ra'ayin malamin kasancewa Humaida a mace, ya hana ta zama Imami, kuma idan babban ɗa shi ke da cancantuwar imamanci to babu buƙatar ambaton suna ɗan ƙarami ɗa, saboda haka ambaton sunan ƴaƴa biyu cikin wannan wasiyya alama ce da take tabbatar da imamancin Musa Bin Jafar (A.S).[39]

Bayanin kula

  1. Shaikh Mufid, Mas'alatan fin naṣṣi ʿala ʿAli (A.S), 1414ƙ., juzu’i na 2, shafi na 3.
  2. Shaikh Mufid, Mas’alatan fi al‑naṣṣ ʿala ʿAli (A.S), 1414 H., juzu’i na 2, shafi na 3.
  3. Faḍil Miƙdad, al‑Anwar al‑Jalaliyya, 1378SH, shafi na 160.
  4. Faḍil Miƙdad, al‑Anwar al‑Jalaliyya, 1378SH, shafi na 160.
  5. Sayyid Murtada, al‑Shafi fi al‑Imamah, 1407ƙ., juzu’i na 2, shafi na 67; Tawagar marubuta, Sharḥ al‑Muṣṭalaḥat al‑Kalamiyya, 1415ƙ., shafi na 366
  6. Sayyid Murtada, al‑Shafi fi al‑Imamah, 1407ƙ., juzu’i 2, shafi 67; Tawagar marubuta, Sharḥ al‑Muṣṭalaḥat al‑Kalamiyya, 1415ƙ., shafi 367
  7. Shaikh Ṭusi, al‑Iƙtiṣad, 1406ƙ., shafuka 314–315; Amirkhani, “Naṣṣ”, shafi 338.
  8. Sayyid Murtada, al‑Shafi fi al‑Imamah, 1407ƙ., juzu’i 2, shafuka 67–68.
  9. Malik‑Makan, “Imamah a hangen Ahlus‑Sunnah”, shafi 234.
  10. Don misali, duba:Taftazani, Sharḥ al‑Maƙaṣid, 1412ƙ., shafuka 258–263; Juwaini, Lumaʿ al‑Adillah, 1407ƙ., shafi 128; Shahrastani, Nihayat al‑Iƙdam, 1425 H., shafi 395; Ƙaḍi ʿAbd al‑Jabbar, al‑Mughni, tahkikin Ƙasim Maḥmud Muḥammad, juzu’i 20, ɓangare na 1, shafuka 112–129
  11. Ashʿari, al‑Lumaʿ, al‑Maktabah al‑Azhariyah li‑l‑Turath, shafuka 133–134.
  12. Sayyid Murtada, al‑Shafi fi al‑Imamah, 1407ƙ., juzu’i 2, shafuka 179–184.
  13. al‑Mu’ayyad bi‑llah, ʿAƙd al‑Laʾali, 1422ƙ., shafi 73.
  14. Araki, Naẓariyyat al‑Naṣṣ ʿala al‑Imamah, 1428ƙ., shafi 111.
  15. Kulayni, al‑Kafi, 1407ƙ., juzu’i 1, shafuka 286–288.
  16. Bukhari, Ṣaḥiḥ al‑Bukhari, 1422ƙ., juzu’i 9, shafi 81, hadisi 7222; Ƙushayri Naysaburi, Ṣaḥiḥ Muslim, Dar Iḥya’ al‑Turath, juzu’i 3, shafi 1452, hadisi 1821; Abu Dawud Sijistani, Sunan, Dar Iḥya’ al‑Sunnah, juzu’i 4, shafi 106; Tirmidhi, Sunan, 1357ƙ., juzu’i 4, shafi 501; Ibn Ḥanbal, Aḥmad, Musnad, 1313 H., juzu’i 1, shafi 398; Ḥakim Naysaburi, al‑Mustadrak, 1411ƙ., juzu’i 3, shafi 715.
  17. Shaikh Ṣaduƙ, Man la yaḥḍuruhu al‑Faƙih, 1413ƙ., juzu’i 4, shafi 180.
  18. Don misali, duba:Kulayni, al‑Kafi, 1407ƙ., juzu’i 1, shafi 527; Nuʿmani, al‑Ghaybah, 1397 H., shafi 62; Shaikh Ṣaduƙ, Kamal al‑Din, 1395ƙ., juzu’i 1, shafi 308; Shaikh Ṭusi, al‑Ghaybah, 1411ƙ., shafi 143; Ṭabarsi, al‑Iḥtijaj, 1386ƙ., juzu’i 1, shafi 85; Shadhan Ƙummi, al‑Faḍa’il li‑Ibn Shadhan, 1363, juzu’i 1, shafi 113; Ibn Shahrashub, Manaƙib al Abi Ṭalib, 1376ƙ., juzu’i 1, shafi 256; Nabaṭi ʿamili, al‑Ṣiraṭ al‑Mustaƙim, 1384ƙ., juzu’i 2, shafi 131; Shaikh Mufid, al‑Irshad, 1413 H., juzu’i 2, shafi 346
  19. Saddabadi, al‑Muƙniʿ fi al‑Imamah, 1414ƙ., shafi 145.
  20. Kulayni, al‑Kafi, 1407ƙ., juzu’i 1, shafuka 292–297; Sayyid Murtada, al‑Shafi fi al‑Imamah, 1407ƙ., juzu’i 2, shafuka 179–184; Ṭabari, Tarikh Ṭabari, 1387 H., juzu’i 2, shafi 321; Suyuṭi, Jamiʿ al‑Aḥadith, bugu na Ḥasan ʿAbbas Zaki, juzu’i 31, shafi 154; Abu al‑Fida’, al‑Mukhtaṣar, al‑Maṭbaʿah al‑Ḥusayniyah, juzu’i 1, shafi 117
  21. Kulayni, al‑Kafi, 1407ƙ., juzu’i 1, shafuka 297–300.
  22. Kulayni, al‑Kafi, 1407ƙ., juzu’i 1, shafuka 300–303.
  23. Saddabadi, al‑Muƙniʿ fi al‑Imamah, 1414ƙ., shafi 145.
  24. Kulayni, al‑Kafi, 1407ƙ., juzu’i 1, shafuka 292–328; Majlisi, Biḥar al‑Anwar, 1403ƙ., juzu’i 23, shafi 104 da gaba.
  25. Ashʿari, Maƙalat al‑Islamiyyin, 1400ƙ., shafi 455;Sayyid Murtada, al‑Shafi fi al‑Imamah, 1407ƙ., juzu’i 1, shafi 7.
  26. Beyhaƙi, al‑I'tiƙad, 1423ƙ., sh. 464.
  27. Don misali ku duba: Ash'ari, al‑Luma', al‑Maktaba al‑Azhariyya li al‑Turath, sh. 133–134; ƙaḍi 'Abd al‑Jabbar, al‑Mughni, tahkikin ƙasim Maḥmud Muḥammad, j. 20, k. 1, sh. 112–129;Taftazani, Sharḥ al‑Maƙaṣid, 1412ƙ., sh. 258–263;Juwayni, Luma' al‑Adilla, 1407ƙ., sh. 128; Shahrastani, Nihayat al‑Iƙdam, 1425ƙ., sh. 395.
  28. Sayyid Murtaḍa, al‑Shafi fi al‑Imama, 1407ƙ., j. 2, sh. 107–201.
  29. Ḥusayni Khaṭib, Muƙaddimat al‑Shafi fi al‑Imama, 1407ƙ., j. 1, sh. 7.
  30. Abu Ya'ƙub Sijistani, al‑Iftikhar, 2000M., sh. 168–169; Kirmani, al‑Maṣabiḥ fi Ithbat al‑Imama, 1429ƙ., sh. 111; Naṣiri, “Imama daga mahangar Isma'iliyya”, sh. 219.
  31. Habibi Muẓahiri, “Isma'il bin Ja'far”, j. 11, sh. 269.
  32. Ja'far bin Manṣur al‑Yaman, Sara’ir wa Asrar al‑Nuṭaƙa’, 1404ƙ., sh. 256.
  33. Habibi Muẓahiri, “Isma'il bin Ja'far”, j. 11, sh. 269.
  34. Don misali ku duba: Sayyid Murtaḍa, al‑Fuṣul al‑Mukhtara, Maṭba'at Ḥaydariyya, sh. 101–102; Shaikh Ṣaduƙ, Kamal al‑Din, 1395 H., sh. 70–71.
  35. Shahrastani, al‑Milal wa al‑Niḥal, 1415ƙ., j. 1, sh. 195–196.
  36. Kulayni, al‑Kafi, 1407ƙ., j. 1, sh. 310.
  37. Kalantari da Jadidi, “Taḥlil wa Tabiyin iddi'a‑ye Imamat‑e 'Abdullah Afṭaḥ wa Dalayil‑e Radd‑e Imamat‑e Vi”, sh. 143.
  38. Majlisi, Mir’at al‑'Uƙul, 1404ƙ., j. 3, sh. 337–338.
  39. Majlisi, Mir’at al‑'Uƙul, 1404ƙ., j. 3, sh. 337–338.

Nassoshi

  • Abul-Fida, Ismail bin Ali, Al-Mukhtasar fi Akhbar il-Bashar, Misra, Mabugar Husainiyya, ba tare da kwanan wata ba.
  • Abu Ya'kub Sijistani, Is'haƙ bin Ahmad, Al-Iftikhar, Beirut, Wallafar Gidan Bugawa na Gharibil Islami, 2000M.
  • Ibn Babawaihi, Ali bin Husain, Al-Imamatu wa at-Tabsiratu min al-Hairati, Qom, Makarantar Imamul-Mahadi, 1363SH.
  • Ibn Hanbal, Ahmad, Musnad, Al-ƙahirah, ba tare da sunan mawallafi ba, 1313ƙ.
  • Ibn Shahrashub, Muhammad bin Ali, Manakibu Ali Abi Talib, Najaf,Gidan Littattafan Haidariyya, 1376ƙ.
  • Ibn Maitham al-Bahrani, Maitham bin Ali, An-Najatu fi al-ƙiyamati fi Binkice Amr il-Imamati, Qom, Majalisar Tunani ta Musulunci, 1417ƙ.
  • Ibn Maitham al-Bahrani, Maitham bin Ali, ƙawa'id al-Maram fi Ilm il-Kalam, Qom, Laburaren Ayatullah al-Mar'ashi an-Najafi, 1406ƙ.
  • Arak'i, Muhsin, Nazariyyat un-Nass ala al-Imamati fi al-ƙur'an al-Karim, Qom, Ƙungiyar Duniya ta Ahlul‑Baiti.” Ko cikin salo mafi mawallafa:, 1428ƙ.
  • Ash'ari, Ali bin Isma'il, Al-Luma' fi ar-Raddi ala Ahl iz-Zayghi wa al-Bida', Al-ƙahirah, Laburaren Azhar don Litattafan Tarihi , ba tare da kwanan wata ba.
  • Ash'ari, Ali bin Isma'il, Maƙalat al-Islamiyyin wa Ikhtilaf al-Musallin, Beirut, Gidan Buga Franz Steiner, 1400ƙ.
  • Amirkhani, Ali, "Nass", Kitabe (Majmu'eh Maƙalat) Ma'arif i Kalami Shi'ah; Kulliyat i Imamati, Qom, Mawallafar Jami'ar Addinai da Mazhabobi, Tehran, Ƙungiyar Bincike da Rubutawa Ilmin Addinin Musulunci na Jami’o’(SAMT), 1393SH.
  • Bahrani, Sulaiman bin Abdullah, Al-Arba'una Hadithan fi Ithbati Imamati Amir il-Mu'uminin, Qom, Mahdi ar-Raja'i, 1417ƙ.
  • Bahrani, Hashim bin Sulaiman, Al-Insafu fi an-Nassi ala al-A'immah al-Isna Ashar, Fassara: Rasuli Mahallati, Tehran, Ofishin Yaɗa Al’adun Musulunci, 1378 ƙ.
  • Bahrani, Hashim bin Sulaiman, Bahjat un-Nazar fi Ithbati al-Wisayati wa al-Imamati lil A'immah al-Isna Ashar, Mashhad, Astan ƙuds Razavi.Gidauniya ta Binciken Addinin Musulunci, 1385SH.
  • Burujirdi, Muhammad Husain, An-Nass al-Jali fi Ithbati Wilayati Ali, Mashhad, Al-'Atabat ur-Radawiyyat ul-Muƙaddasah. Cibiyar Binciken Addinin Musulunci, 1383SH.
  • Baihaƙi, Ahmad bin Husain, Al-I'tiƙadu wa al-Hidayatu ila Sabil ir-Rashadi ala Mazhab is-Salaf i Ahl is-Sunnati wa al-Jama'ah, Beirut,Gidan buga litattafai na l-Yamamah, 1423ƙ.
  • Tirmidhi, Muhammad, Sunan, tare da kokarin Ahmad Muhammad Shakir da sauransu, Al-ƙahirah, 1357ƙ.
  • Taftazani, Mas'ud bin Umar, Sharh al-Maƙasid, Qom, Wallafar Ash‑Sharif ar‑Raḍi, 1412ƙ.
  • Ja'far bin Mansur al-Yaman, Sara'iru wa Asrar un-Nutaƙa, tare da kokarin Mustafa Ghalib, Beirut, 1404ƙ.
  • Tare da wasu mawallafa, Sharh al-Mustalahat al-Kalamiyyah, Mashhad, Al-'Atabat ur-Radawiyyat ul-Muƙaddasah, Majalisar Bincike na Addinin Musulunci, 1415ƙ.
  • Jawhari, Ahmad bin Muhammad, Muƙtadab al-Athari fi an-Nassi ala al-A'immah al-Isna Ashar, Qom, Gidan Littattafai Tabataba'i, ba tare da kwanan wata ba.
  • Juwayni, Abdul-Malik bin Abdullah, Lama' al-Adillati fi ƙawa'id i Aƙaid i Ahl is-Sunnati wa al-Jama'ah, Beirut, Gidan Littattafai Alam, 1407ƙ.
  • Habibi Mazahiri, Mas'ud, "Isma'il bin Ja'far", Dayirat ul-Ma'arif i Buzurg i Islami Juz'i 11, Tehran, Cibiyar Ƙamus da Babbar Ma’lumotar Musulunci.
  • Husayni Khatib, Abdul-Zahra, Al-Shafi fi al-Imamati (Sayyid Murtaza) , Gabatarwar Bincike, Tehran, Cibiyar As-Sadiƙ, 1407ƙ.
  • Khawaja Nasir Tusi, Muhammad bin Muhammad, Tajrid al-I'tiƙad, Tehran, Ofishin Yaɗa Labarai na Musulunci. 1407ƙ.
  • Dailami, Hasan bin Muhammad, Irshad al-ƙulub, Bincike: Sayyid Hashim Milani, Tehran, Gidan Uswat don Buga da Yaɗa Littattafai, 1417ƙ.
  • Sijistani, Abu Dawud, Sunan, tare da kokarin Muhammad Muhyiddin Abdul-Hamid, Al-ƙahirah,Cibiyar Farfaɗo da Sunnah ta Annabi (S.A.W).
  • Sadabadi, Ubaidullah bin Abdullah, Al-Muƙna' fi al-Imamati, Qom, Jama'at ul-Mudarrisin fi al-Hawzat il-'Ilmiyyah bi Qom. Gidan Littattafan Nashr al-Islami, 1414ƙ.
  • Sayyid Murtada, Ali bin al-Husain, Al-Shafi fi al-Imamati, Tehran, Gidan Littattafan As-Sadiƙ, 1407ƙ.
  • Sayid Murtada, Ali bin Husain, Al-Fusul al-Mukhtaru min al-'Uyun wa al-Mahasin Sheikh Mufid, Najaf, Gidan Littattafan Haydariyyah, ba tare da kwanan wata ba.
  • Suyuti, Jalal al-Din, Jami' al-Ahadith, babu wuri, bugun Hasan Abbas Zaki, ba tare da kwanan wata ba.
  • Shadhan Qomi, Shadhan bin Jibril, Al-Fada'il li-Ibn Shadhan, Qom, Gidan Littattafan Radi, 1363SH.
  • Shu'airi, Taj al-Din, Jami' al-Akhbar, Qom, Gidan Littattafan Radi, 1363 SH.
  • Shahrastani, Muhammad bin Abdul-Karim, Al-Milal wa al-Nihal, Beirut, Gidan Littattafan Ma'rifah, 1415ƙ.
  • Sheikh Hurr al-Amili, Muhammad bin al-Hasan, Ithbat al-Hudati bi an-Nusus wa al-Mu'jizat, Beirut, Gidan Littattafan Al-A'lami, 1425ƙ.
  • Sheikh Saduƙ, Muhammad bin Babawayh, 'Uyun Akhbar al-Rida, mawallafar -Jahan, 1378ƙ.
  • Sheikh Saduƙ, Muhammad bin Ali, Kamal al-Dini wa Tamam an-Ni'mah, Tehran, Gidan Littattafan al-Islamiyyah, 1395ƙ.
  • Sheikh Saduƙ, Muhammad bin Ali, Man la Yahduruhu al-Faƙih, Qom,Gidan Buga Littattafan Musulunci da ke da alaƙa da Ƙungiyar Malamai Masu Koyarwa ta Hauzar Ilimi ta Qum., 1413ƙ.
  • Sheikh Tusi, Muhammad bin al-Hasan, Al-Iƙtisadu fi ma Yata'allaƙ bi al-I'tiƙad, Beirut, Gidan Littattafan Adwa', 1406ƙ.
  • Sheikh Tusi, Muhammad bin al-Hasan, Al-Ghaybah, Qom, Cibiyar Gidan Littattafan Ma'arif al-Islamiyyah, 1411ƙ.
  • Sheikh Mufid, Muhammad bin Muhammad, Al-Fusul al-Mukhtaru min al-'Uyun wa al-Mahasin, Gyara: Ali Mirsharifi, Qom, Kungiriyi Sheikh Mufid, 1413ƙ.
  • Sheikh Mufid, Muhammad bin Muhammad, Mas'alatani fi an-Nassi ala Ali, Beirut, Gidan Littattafan-Mufid, 1414ƙ.
  • Saffar, Muhammad bin al-Hasan, Basa'ir al-Darajat al-Kubra, Qom Gidan Littattafan Haidariyyah, 1384SH.
  • Tabatabai, Sayyid Muhammad Husain, Al-Mizan fi Tafsir al-ƙur'an, Qom, Isma'iliyan, 137SH.
  • Tabrasi, Ahmad bin Ali, Al-Ihtijaju ala Ahl il-Lijaj, Najaf, Gidan Littattafan-Nu'man, 1386ƙ.
  • Tabrasi, Fadl bin al-Hasan, I'lam al-Wara bi A'lam al-Huda, Tehran, Gidan Littattafan Musulunci, ba tare da kwanan wata ba.
  • Tabari, Muhammad bin Jarir, Tarikh al-Tabari, Misra, Wallafar Gidan buga litattafai na Ma'arif, 1387ƙ.
  • Tabari, Muhammad bin Jarir, Kitab Tahdhib al-Athar; Musnad Ali, Al-ƙahirah, Mabugar Madani, ba tare da kwanan wata ba.
  • Adud al-Din al-Iji, Abd al-Rahman bin Ahmad, Sharh al-Mawaƙif, Qom, Gidan Buga Littattafai na Sharīf ar‑Raḍī, ba tare da kwanan wata ba.
  • Allamah Amini, Abdul-Husain, Takmilat al-Ghadir: Thamarat al-Asfar ila al-Aƙtar, Beirut, binciken Markaz al-Amir li Ihya' it-Turath al-Islami, bita da gyara Cibiyar Al‑Ghadīr don Nazari, Bugawa da Rarrabawa', 1429ƙ.
  • Fadil al-Miƙdad, Miƙdad bin Abdullah, Al-Lawa'ih al-Ilahiyyatu fi al-Mabahith al-Kalamiyyah, Qom, mawallafar Ofishin Sashen Yaɗa Addinin Musulunci na Hauzar Ilimi Qom, 1380SH.
  • Qadi Abdul-Jabbar, Ibn Ahmad, Al-Mughni fi Abwab al-Tawhidi wa al-Adl, Bincike: ƙasim Mahmud Muhammad, babu wuri, babu mawallafi, ba tare da kwanan wata ba.
  • Qushayri Naisaburi, Muslim bin Hajjaj, Al-Musnad al-Sahih al-Mukhtasar bi naƙl il-'adli anil 'adli ila Rasulillah, Beirut, Gidan Raya Gadon Adabin Larabawa, ba tare da kwanan wata ba.
  • Qommi, Muhammad Tahir bin Muhammad Husain, Al-Arba'una fi Imamati al-A'immah al-Tahirin, Qom, Gidan buga litattafai na Musulunci,Mahdi ar-Raja'i, 1418ƙ.
  • Karajaki, Muhammad bin Ali, Dalil un-Nass bi Khabar il-Ghadiri ala Imamati Amir il-Mu'uminin, Qom, Cibiyar Alu al-Bayt li Ihya' it-Turath, 1419ƙ.
  • Karajaki, Muhammad bin Ali, Al-Intisar fi al-Nassi ala al-A'immah al-Athar, Beirut, Gidan buga litattafai na Adwa', 1405ƙ.
  • Kashi, Muhammad bin Umar, Ikhtiyar Ma'rifat al-Rijal, tare da kokarin Hasan Mustafawi, Mashhad, Gidan buga litattafai na Jami'ar Mashhad, 1409ƙ.
  • Kalantari, Sajjad, F. Boushasb da N. Jafari, "Tahlil Wa Tabyin Iddi'aye Imamat Abdullah Aftah Wa Dalayil Radde Imamat We", Fasalin tarihi da na Iran na Jami'ar Al-Zahra, shekara ta 32, fitowa ta 54, mai lamba 144, bazara 1401SH.
  • Kulaini, Muhammad bin Ya'ƙub, Al-Kafi, Tehran, Gidan buga litattafai na Musulunci,, 1407ƙ.
  • Majlisi,Muhammad Baƙir, Mir'at al-Uƙul fi Sharh Akhbar Al al-Rasul, Tehran, Gidan buga litattafai na Musulunci, 1404ƙ.
  • Majlisi, Muhammad Baƙir, Bihar al-Anwar, Beirut, Cibiyar ul-Wafa', 1403ƙ.
  • Malikmakan, Hamid, "Imamat Az Negahe Ahlus-Sunnat", Littafin (Tarhin Kasidu) Ma'arif i Kalami Shi'ah; Kulliyat i Imamati, Qom, mawallafar Jami'ar Adddinai Da Mazhabobi, Tehran, Ƙungiyar Nazari da Rubuta Littattafan Ilimin Musulunci na Jami’o’i (SAMT), 1393SH.
  • Nabati Amili, Ali bin Muhammad, Al-Sirat al-Mustaƙim ila Mustahiƙƙi al-Taƙdim, Tehran, Gidan Buga Littattafai na Murtadawiyyah, 1384ƙ.
  • Nasiri, Muhammad, "Imamat Az Diggahe Isma'iliyye", Littafin (Majmu'e Maƙalat) Ma'arifi Kalami Shi'ah; Kulliyat i Imamati, Qom, mawallafar Jami'ar Adddinai Da Mazhabobi, Tehran, Kungiyar Nazari da Rubuta Littattafan Ilimin Musulunci na Jami’o’i (SAMT), 1393SH.
  • Nu'mani, Muhammad bin Ibrahim, Al-Ghaybah, Tehran, Ofishin Wallafa na Saduƙ, 1397ƙ.