Ma'abota Alkibla

Daga wikishia

Ahlil-kibla (Larabci: أهل القبلة) ishara ce zuwa ga baki dayan musulmi da suka yi imani suka yarda da Ka'aba matsayin Alkibla gare su, amfanin wannan Isdilahi shi ne taka birki daga kafirta musulmi, jini da dukiya da mutuncin Ahli-kibla yana da alfarma a mahangar galibin Malamai daga Ahlus-sunna da `yan Shi'a, kan wannan asasi kafirta Ahlil-kibla ko kashe su ko rikar su fursunan yaki baya halatta kuma wajibi ne ayi sallah a kan gawar su idan suka rigamu gidan gaskiya.

Ta'arifi

Ahlil-kibla shi ne mutumin da yake danganewa da addinin muslunci,[1] da wannan ne zai kasance baki dayan kungiyoyin musulmi da suka yarda da Ka'aba matsayin Alkibla ana kiran su da Ahli-kibla,[2] Muhammad Jawad Mugniyya daya daga cikin Malamin tafsirin Shi'a a karni na 14 yana cewa: wannan isdilahi na Ahlil-kibla ko kuma Ahli-Kur'an ko Ahlil-Shahadataini ko ace Musulmai duk yana da ma'ana guda daya, manufa shi ne wadanda suka yi imani da Allah da Manzon Allah (S.A.W) da sunnarsa kuma suke fuskantar Ka'aba (Alkibla)[3] lokacin da suke salla, Shaik Mulla Ali Kari'u makarancin Kur'ani daga Malaman Mazhabar Hannafiya yana cewa: ana fadin Ahlil-kibla ga duk mutumin da baya inkarin larura daga laruran addini, a fadin sa a mahangar Malaman Ahlus-sunna ba a kidaya mutumin da yake inkarin larura daga laruran addini misalin kasancewa Kadimancin duniya da tashi daga kabari ko da kuwa ya karar da rayuwarsa cikin ibada ga Allah.[4]

Hukunce-hukuncen Fikihu

Rai da dukiya da mutuncin Ahli-kibla a mahangar Akasarin Malaman `yan Shi'a da Ahlus-Sunna suna da alfarma,[5] haka zalika kafirta su[6] ko kashe fursunansu baya halasta,[7] kuma wajibi ayi salla kan Jana'izar su, [8] Mulla Ali Kari'iu: Abu Hanifa da Muhammad Ibn Idris Shafi'I basa Kafirta duk wani ma'abocin Akibla, [9] haka kuma ance yawancin Malaman fikhu na Ahlus-sunna basa kafirta Ma'abota Alkibla.[10]

Amma tare da haka an samu wasu bangare daga kungiyoyin musulmi da suke kafirta wanda ba su ba kuma suna halasta kashe su,[11] Muhammad Ibn Abdul-Wahab wanda ya assasa Wahabiyanci ya halasta kashe wadanda suke Imani da cewa Annabawa da Mala'iku da Waliyyai suna ceto kuma tsaninsu zuwa ga Allah, yana ma ganin wajbacin kashe su ko da kuwa sun yi ikrari da dayanta Allah da Tauhid Rububi ubangijintakarsa.[12]

Damgane da Nasibawa, Kawarijawa wasu musulmi ne da suke inkarin laruran addini duk da cewa sun yarda da Ka'aba matsayin Alkiblarsu tare da haka Malaman muslunci sun yi fatwa kan kasancewarsu Kafirai [13] Najasa.[14]

A isdilahin fikhu [15] Ahlil-Kibla da cikin hukunce-hukuncen Matattu da hukunce-hukuncen Jihadi,[16] Malamai sun ce hakika musulmai kafin Yakin Jamal yaki da Ahlil-kibla ba a ma san isdilahin Ahli-kibla ba an fara jinsa ne daga bakin Imam (A.S) a lokacin yakin.[17]

Bayanin kula

  1. Naraghi, Rasail wa Masail, 1422 AH, juzu'i na 2, shafi na 335.
  2. Dehkhoda,Luggatnameh ƙamus, ƙarƙashin kalmar.
  3. Mughniyeh, Tafsir al-Kashif, 1424 AH, juzu'i na 1, shafi na 231.
  4. Qari, Sharhin Fiqhul Akbar, 1428H, shafi na 258.
  5. Rostami, “Mmnu'iyat takfir Ahli Kibleh az nigahe Fakihan wa mutakilaman shi'eh wa tasannun na Ahlul Kiblah” shafi na 71.
  6. Misali, duba: Qari, Sharhin Kitab al-Fiqh al-Akbar, shafi na 258; Taftazani, Sharh al-Maqasid, 1409 AH, juzu'i na 5, shafi na 228.
  7. Montazeri, Darsat fi Wilayat al-Faqih da Fiqhu Daulah al-Islamiyya, 1409 AH, juzu'i na 3, shafi na 296.
  8. Tusi, Tahdhib al-Ahkam, 1407 AH, juzu'i na 3, shafi na 328.
  9. Qari, Sharhin Fiqhul Akbar, 1428H, shafi na 257.
  10. Qari, Sharhin Fiqhul Akbar, 1428H, shafi na 285.
  11. Mamnu'iyat Takfir Ahli Kibleh az Nigahe Fakihan wa Mutakkilam Tashayyu wa tasannun shafi na 71
  12. Muhammad bn Abdil Wahhab, Kashfu Shubhat, 1418 s, shafi na 7.
  13. Naraghi, Rasail wa Masael, 1422 AH, juzu'i na 2, shafi na 336.
  14. Muqaqiq Karki, Jami Al-Maqasid, 1414 AH, Juzu’i na 1, shafi na 164.
  15. Tusi, Al-Astabsar, 1390H, juzu'i na 1, shafi na 468.
  16. Mustadrak Wasal al-Shia, Mujalladi na 11, shafi na 55.
  17. Ƙungiyar masu bincike, Jihad a cikin madubi na Hadisai, 1428 AH, juzu'i na 1, shafi na 188.

Nassoshi

  • Taftazani, Saad al-Din, Sharh al-Maqasid, Abd al-Rahman Umira, Qom, al-Sharif al-Razi, 1409 H.
  • Kungiyar masu bincike a Cibiyar Nazarin Musulunci, Jihadi a Madubin Hadisai, Qum, Zamzam Hedayat Publications, 1428H.
  • Rostami, Abbas Ali, "]",
  • «ممنوعییت تکفیر اهل قبله از نگاه فقیهان و متکلمان تشیع و تسنن»، Binciken Imani na Tauhidi, No. 30, Summer 2018.
  • Qari, Mulla Ali bin Sultan, Sharhin littafin Fiqhu al-Akbar, Ali Muhammad Dandal, Beirut, Darul Kitab Al-Ilamiya, Muhammad Ali Bizoun, 1428H/2007 Miladiyya.
  • Tusi, Mohammad Bin Hasan, Al-Istbasar Fima Akhtolf Man Al-Akhbar, Tehran, Dar al-Kitab al-Islamiya, 1390H.
  • Tusi, Muhammad bin Hasan, Tahzeeb al-Ahkam, Tehran, Dar al-Kitab al-Islamiya, 1407H.
  • Karki, Ali bin Hossein, Jame al-Maqasad fi Sharh al-Qasas, Qum, Al-Bait Institute, 1414H.
  • Muhammad bin Abd al-Wahhab, Kashf al-Shabhat, Arabia, Ministry of Islamic Affairs and Endowments and Dawa and Al-Irshad al-Mullikah Al-Arabiya al-Saudia, 1418 AH.
  • Moghniyeh, Mohammad Javad, Tafsir al-Kashif, Tehran, Dar al-Kitab al-Islamiya, 1424H.
  • Muntzari, Hossein Ali, Darsat fi Wilayat al-Faqih da Fiqhu Daulah al-Islamiyya, Kum, Nisfar Tasfar, 1409H.
  • Naraghi, Ahmed bin Muhammad, Rasail and Issues, Qum, Congress of Naraghi Mullah Mahdi and Mullah Ahmad, 1422 AH.