Nazariyyar Jihadi Zubbi
Nazariyyar jihad zubbi ko ace kare samuwar asalin Muslunci, wata nazariyya ce a babin jihadi da take ɗauke da ma'anar kare asalin tabbatuwar Muslunci da darajojin addini.[1] Kan asasin wannan nazariyya, jihadi zubbi kaɗai yana faruwa ne domin kare Muslunci. Saboda haka idan ya zamana ana jin tsoron kawar da muslunci daga samuwa a wani yanki a dukkanin faɗin duniya, a irin wannan hali kare asalin Muslunci wajibi kan baki ɗayan musulmi kuma wajibi aini (Ma'ana wani ba ya iya ɗaukewa wani).[2]
Nazariyyar jihadi zubbi, karon farkon an bijiro da ita ta hannun Muhammad Jawad Fadil Lankarani, malami a darasin bahasil kharij fiƙhi wa usul a hauzar ilimi ta Ƙum. Fadil Lankarani ya ciro wannan nazariyya ta jihadi zubbi daga kalaman malaman fiƙihu.[3]ya ajiye kishiyar jihadi ibtida'i da jihadi difa'i..[4]Jihadi zubbi, saɓanin jihadi difa'i da jihadi ibtida'i, bai kasance yana sharɗantuwa da wani sharaɗi, kuma babu larura ace dole sai an samu yaƙini kan tasirin yunuƙurin yinsa, kamar dai yadda tsoron taɓuwar rai da dukiya da mutunci ba sa iya zama dalili ɗaukewar wajabcin yinsa, kuma idan aka kashe wani cikin hanyar wannan jihadi, ana lissafa shi matsayin shahidi, kuma za ayi aiki da hukunce-hukunce shahidi a kansa..[5]
Fadil Lankarani ya tafi kan cewa jihadi zubbi ya dogara ne da kur'ani,[Tsokaci 1] riwayoyi,[6] ijma'i,[7] hankali[8] da rashin amincewar mai shari'a kan barin lamurran hisba.[9]
A imanin Fadil Lankarani asalin dalilin miƙewar Imam Husaini (A.S), ya kasance domin baiwa Muslunci kariya, bawai jihadi ibtida'i ba ko jihadi difa'i ba; saboda Imam Husaini (A.S) bisa zaɓinsa ne ya bar garin Makka[10] a ra'ayin malamin, miƙewar Imam Husaini (A.S) ba ta kasance kan asasin umarni da kyakkyawa da hani da mummuna ba, saboda babu ɗaya daga cikin sharuɗɗan umarni da kyakkyawa da hani da mummuna da ya kammala, misalin lazimcin sanin tasiri da kuma rashin samuwar cutuwar rai da dukiya, cikin wannan yunƙuri sam ba su kammala ba, hadafin miƙewar Imam, ba komai bane sai kare addini, saboda babu wani abu kyakkyawa da ya wuce asalin addini, kuma babu wani mummunan abu mafi girma daga halakar da addini.[11]
Malamin yana ganin yaƙin da al'ummar Falasɗinu da Hizbullahi Lubnan suke yi da Isra'ila, da kuma yaƙar ƴan ta'addan Da'ish ɗaya ne daga abubuwan da suke amsa sunan Jihadi zubbi.[12]
Bayanin kula
- ↑ Fazil Lankarani, "Jihadin Zubbi", shekara ta 1401 Hijira, shafi na 7.
- ↑ Fazil Lankarani, "Jihadin Zubbi", shekara ta 1401 Hijira, shafi na 32.
- ↑ Fazil Lankarani, "Jihadin Zubbi", shekara ta 1401 Hijira, shafi na 30.
- ↑ Fazil Lankarani, "Jihadin Zubbi", shekara ta 1401 Hijira, shafi na 52.
- ↑ Fazil Lankarani, "Jihadin Zubbi", shekara ta 1401 Hijira, shafi na 15.
- ↑ Hamīriy Qumī, "Qurb al-Isnād", shekara ta 1413 Hijira, shafi na 345.
- ↑ Najafi, Jawāhir al-Kalām, shekara ta 1404 Hijira, juzu’i na 22, shafuffuka 24–26
- ↑ Sabzuwari, Muhadh-dhab al-Aḥkām, Dar al-Tafsīr, Juzu’i na 15, Shafi na 101.
- ↑ Fazil Lankarani, "Jihadin Zubbi", shekara ta 1401 Hijira, shafi na 25.
- ↑ Fazil Lankarani, "Jihadin Zubbi", shekara ta 1401 Hijira, shafi na 11.
- ↑ Fazil Lankarani, "Jihadin Zubbi", shekara ta 1401 Hijira, shafi na 13.
- ↑ Fazil Lankarani, "Jihadin Zubbi", shekara ta 1401 Hijira, shafi na 51
Tsokaci
- ↑ 1Suratul Baqarah (2:193), Suratun Nisa (4:75–76)
Nassoshi
- Abdullāh b. Jaʿfar al-Ḥimyarī al-Qummī – Beirut – Mu’assasat Āl al-Bayt (‘a) – Buga na Farko – 1413 H
- Sayyid ʿAbdul-Aʿlā Sabzuwārī – Qum – Dār al-Tafsīr – ba tare da shekara ba. A juzu’i na 15, shafi na 101:
- Muḥammad-Jawād Fāḍil Lankarānī – Qum – Markaz al-Fiqhī li-Aʾimmat al-Aṭhār (‘a) – 1401 H.
- Muḥammad-Ḥasan Najafī – Beirut – Dār Iḥyāʾ al-Turāth al-ʿArabī – Tabbaci na 7 – 1404 H. A juzu’i na 22, shafuffuka 24–26