Jump to content

Kafirta Ma'abota Alkibla

Daga wikishia
(an turo daga Kafirta musulmi)

Kafirta Ma’abota Alkibla (Larabci: تكفير أهل القبلة) ko Kafirta Musulmai yana nufin wasu su danganta Kafirci ga wani mutum ko wasu Jama’a daga Musulmai, wanda haka yake haifar da miyagun sakkonni misalin Halasta jinins da, kwace dukiyarsu, Wahabiyawa kan asasin gurguwar Fahimtar da suka yiwa wasu abubuwa misalin Tauhidi, Ziyara, Tawassuli, suna Kafirta duk Musulmi da ya sabawa Fahimtarsu Akidarsu da tunaninsu musammam ma `Yan Shi’a. Akasarin Malaman Muslunci suna ganin bakin iyakar Muslunci da Kafirci shi ne Furta Kalmomin Shahada guda biyu, kuma ba su yarda da halascin Kafirta Mabiya Mazhabobin Muslunci ba, amma tare da haka a tsawon tarihin Muslunci a kowanne zamani akan samu wasu Ba’arin Musulmai da suke Kafirta wanda ya sabawa Mazhabarsu, Kafirta Imam Ali (A.S) a Waki’ar Tahkim wacce ta afku ta hannun Kawarijawa da kuma Kafirta wanda aka kira su da Ahlu Ridda a zamanin Halifa na Farko suna daga Samfuri na farko-farko na Kafirta Ma’abota Alkibla, an kashe Musulmi masu tarin yawa sakamakon wannan Akida tsakanin Mabiya Mazhabobi, Kafirta Musulmi bai takaitu ba cikin Mazhabobi, wani lokaci zaka samu Malaman Fikihu suna Kafirta `Yan Falsafa da Arifai wadanda dukkanin `Yan Mazhaba daya ne, cikin Fitinar Khalk Kur’an (Halittar Alkur’ani) wata fitina da ta faru tsakanin Ahlus-sunna da ta haifar da Kafirta Junansu. Bayan samuwar Wahabiyawa Kafirta Ma’abota Alkibla ya karu Matuka tsakanin musulmi, haka kuma karkashin tunanin Wahabiyanci tare da goyan bayansu an samu Kungiyoyin Ta’addanci misalin Daish suna Kafirta Musulmai musammam `Yan Shi’a, an yi rubuce-rubuce masu yawan gaske dangane da batun Kafirta Ma’abota Alkibla galibin Mihwarin rubuce-rubuce ya karkata kan sukan tushen Tunanin Kafirta Musulmai, haka kuma an shirya Manyan Tarurruka na kowa da kowa cikin Nakadi da sukan Akidar Kafirta Musulmai.

Muhimmanci da Matsayi

Takfiriyya, Kafirta Musulmai wani Maudu’i ne na Fikihu da Kalam wanda ya kasance a tsawon Tarihi Sakamakon dangantawa wani mutum ko wasu jama’a daga musulmi kafirci jininsu da dukiya na Halasta, daga karshe ya haifar da Yaki da zai sanadiyar mutuwar mutane masu yawan gaske da korarsu daga gidajensu [1] haka kuma Natijar danganta Kafirci ga wasu Mabiyan Mazhabobin Muslunci ya Haifar da ruguje wasu gine-gine da wurare masu daraja da tsarki [2] a Karni na Karshe-karshen nan tare da yaduwar tunanin Kafirta Musulmi ta hannun Masu irin wannan Tunani, Bahasin Kafirta Musulmi ya cika Matsugunan Karatu na Musulmai, anyi rubuce-rubuce daban-daban kan Maudu’in [3] tare da shirya Manya-Manyan Tarurruka.

Sanin Mafhumi da Rabe-Rabe

Takfiriyya na nufin kiran wani Musulmi da Kafiri [4] ko kuma danganta Kafirci ga Ma’abota Alkibla [5] Na’am an rarraba Kafirci zuwa kashi biyu Kafirci na Fikihu da Kafirci na Akida, danganta kowanne dayansu ga Musulmi yana dauke da kebantaccen sako:

  • Kafirci Na Fikihu ko na Zahiri yana da ma’anar fita daga Addinin Muslunci, ta wannan fuskar ne ake Mu’amalar Kafiri tareda dukkanin Mutumin da ya kafirta Kafirci na Fikihu.
  • Kafirci na Akida ko na Badini yana da ma’anar fita daga Imani bawai Muslunci ba, da wannan fuska ne ake Mu’amalar Musulmi tare da Kafirin Akida kamar dai misalin Munafuki wanda shi a Zahiri Musulmi ake masa hukunci amma a hakika bai yi Imani ba [6] a cewar Imam Khomaini, riwayoyin da suke Kafirta wadanda ba `Yan Shi’a ba, idan mun kaddara mun karbe su, to suna Magana ne kan Kafircin Akida [7]

Haramcin Kafirta Ma’abota Alkibla

Kan asasin Fatawar Malaman Mazhabobin Muslunci baya halasta ka danganta Kafirci ga wani ba tare da kwakkwaran dalili ba, yin hakan zai Haifar da a ladabtar da wanda ya Kafirta Musulmi [8] a imanin Malaman Fikihu iyakar Muslunci da Kafirci shi ne furta Kalmomin Shahada guda biyu da Imani da Ma’ad (Ranar Alkiyama) [9] da wannan dalili ne Malaman Fikihu suke taka tsantsan cikin Kafirta wasu tare da samuwar Kusa-kusai cikin Akidun Ba’arin wasu Firkoki [10]

Tarihin Kafirta Musulmi

Hakika kafirta Ma’abota Alkibla ba sabon abu bane a tsakanin Musulmai, yana komawa ga Karni na farko h Kamari, bayan wafatin Annabi (S.A.W) a lokacin Halifancin Abubakar an samu wasu Jama’a da ba su yarda da Halifancin Abubakar ba, kai tsaye wasu Musulmi suka Kafirta su da kiransu Murtaddai (wadanda suka fita daga Muslunci) sannan suka je suka dinga Yakarsu da karkashe su, ana kiran Yakin da sunan Yakin Ridda, [11] a cewar Rasul Jafariyan Masanin Tarihin Muslunci, wanda aka Haifa a shekara ta 1343 h shamsi ya bayyana cewa cikin wadanda ake cewa sun yi Ridda akwai mutane misalin Malik Bn Nuwaira wanda Musulmi ne kuma yana yin sallah sai dai cewa bai yarda da Halifancin Abubakar ba, ya nemi a dawo da Mulki zuwa ga Ahlil-baiti (A.S) [12] da wannan dalili ne yaki aikawa da Abubakar da Zakka da wannan dalili ne suka Kafirta shi suka kuma Kashe shi [13] A lokacin Hukumar Imam Ali (A.S) Kawarijawa sun kafirta Hazrat Ali (A.S) kan batun tahkim [14] da wannan dalili ne ma suka janye cigaba da kasancewa cikin Sojojinsa a yakin da yake da Mu’awiya Bn Abi Sufyan [15] sannan suka juya baya suka yake shi a yakin da ake kira da suna Yakin Naharawan [16] Haka kuma kamar yanda Jafar Subhani daya daga cikin Maraji’an Taklidi na Shi’a wanda aka Haifa a shekara ta 1308 h shamsi, a cikin littafinsa mai suna (Buhus Fi Al-Milalu Wan-Annihalu ya kawo rahotan cikin fitinar Khalk Kur’an, kowanne bangare daga masu Imani da halittar Kur’ani da Masu cewa Kadimi ne ba a halicce shi, dukkaninsu Ahlus-sunna ne, da suka kasance suna kafirta junansu, [17] a Karnoni na Karshe tare da yaduwar Akidar Salafanci da Wahabiyanci Mabiyan wannan Tunani sun dinga Kafirta Musulmai musammmam ma `Yan Shi’a

Dalilan da suka Motsa `Yan Takfiriyyya zuwa ga Kafirta Musulmai

Shaik Muhammad Bn Sulaiman Kurdi Ustaz Muhammad Bn Abdul-wahab
“Ya `dan Abdul-wahab! Don girman Allah, ina ba ku shawara da ku guji yin magana a kan Musulmi... ba za ku iya ba, kuma ba ku da ikon fitar da gama-garin Musulmi daga muslunci; Domin kaima `da ne a wannan al'ummar. Kuma kafirta wanda ya bar al’ummar musulmi shi ne mafi kusanci da gaskiya; Domin ya bi wanin tafarkin daban wanda ba na muminai ba.

Tarikh Bayigani, Zainidahlan"فتنة الوهابیة"

Kafirta Musulmai ya faru ne daga dalilai daban-daban, daga cikinsu akwai:

  • Karkacewar Fahimta da dauka abu ba a asalinsa ba daga koyarwar addini: Kawarijawa karkashin kebantacciyar Fahimta daga ayar :
لَا حُكْمَ إِلَّا لِله

Babu wani Hukunci sai na Allah. [yadahst 1] a waki’ar Tahkim A lokacin Yakin Siffin sun yi bore ga Imam Ali (A.S) tare da Kafirta shi [18] haka kuma Wahabiyawa suma da ta su kebantacciyar gurguwar Fahimtar daga Tauhidi, Shirka, Ziyara, Tabarruki, Tawassuli, Sun kafirta Musulmai masu yawan gaske musammam ma `Yan Shi’a [19] Muhammad Bn Abdul-Wahab wanda ya assasa Wahabiyanci wanda ya mutu a shekara ta 1206 h kamari, ya Kafirta Musulmai da dalilin cewa suna tawassuli da nufin kamun Kafa da Annabawa da Salihai don samun kusanci zuwa ga Allah ya kuma halasta zubar da jininsu da kashe su. [20]

  • Abisa Imanin Akida a wurin Kawarijawa suna Kafita Musulmin da ya aikata daya daga cikin Manya-Mayan zunubai [21] suna dogara da ayar
«وَمَن لَّمْ يَحْكُم بِمَا أَنزَلَ اللَّـهُ فَأُولَـٰئِكَ هُمُ الْكَافِرُونَ

Duk wanda bai yi hukunci da abin da Allah ya saukar ba wadancananka Kafirai ne. [22] kan Kafirta Musulmai,[23] amma a ra’ayin sauran Musulmai aikata babban zunubi yana fitar da mutum daga Imani ne, amma banda Muslunci natija zai zamana Musulmi Fasiki bawai Kafiri ba [24] haka kuma a cikin fitinar Khalk Kur’an Abu Hassan Ash’ari [25] da Ahmad Bn Hanbal [26] sun kafirta Musulmi daga Mu’utazilawa da suke ganin an Halicci Kur’ani bawai Kadimi ne ba, [27] cikin Hadisan Shi’a an Kafirta wadanda ake kira da Gullatu Mutane ne da suke wuce gona da iri cikin Imamai Ma’asumai (A.S) da kuma Imani da cewa Allah ya fawwala la’amarin halittunsa a hannun Imamai (A.S) [28] Ta’assubancin Mazhaba tsakanin juna bisa dogara da rahotannin Tarihi ya haifar da kafirta juna tsakanin Mabiya Mazhabobin Muslunci, alal misali a Karni na takwas a daurorin wasu ba’arin Mabiya Mazhabobin Ahlus-sunna sun kasance suna Kafirta Mabiyan Mazhabar Hanbaliya sakamakon ayyukan Ibn Taimiyya, a gefe guda kuma Ibn Hatim Mabiyin Mazhabar Hanbaliya shima ya kafirta baki dayan Musulmin wanda ba Mabiyan Hanbaliya ba [29] haka kuma wannan Kafirtawa daga bangaren Ahlus-sunna kan Shi’a haka kuma daga bangaren Shi’a kan Ahlus-sunna duk yana faruwa kowa yana kafirta kowa, Ibn Jubairi Mufti Bawahabiye ya kafirta yan Shi’a kan tuhumarsu da Akidar Jirkitar Alkur’ani, Kafirta akasarin Sahabbai, Kafirta Ahlus-sunna da ce musu Najasa da kuma wuce gona da iri cikin soyayyar Ali (A.S) da `Yayansa [30] sai dai cewa kuma `Yan Shi’a ba su da wadannan Akidu da yake tuhumarsu da su. Yan Shi’a kusan sunyi Ittifaki kan cewa Ahlus-sunna Musulmai ne ba Kafirai, [31] idan an samu wani wuri ana kafirta su to ba kifirci ne na fikihu ba kafirci ne na Akida kuma ana tawilinsa [32] A cikin Bahasin Kalam Irfani da Falsafa: wasu ba’arin Malaman Musulmai sun kafirta `yan Falsafa da Arifai, alal misali Gazzali cikin littafin Tahafutul Al-Falasifa ya kafirta `yan Falsafa [33] a cewar Sayyid Muhammad Bakir Kuwansari wanda ya mutu a shekata ta 1313 h shamsi, hakika wasu Jama’a daga Malaman Fikihu sun Kafirta Mulla Sadra a dalilin zantukansa da suke cin karo da zahirin Shari’a [yadasht 2] [34] Haka kum daya daga cikin dalilin yaduwar Akidar Kafirta Musulmai akwai Kasashe Makiya Muslunci don kare wanzuwar gwamnatocinsu da shirya makirci da tuggu kan Muslunci. [35]

Sakonni

Kafirta Musulmai ya biye da wasu Sakonni mara kyau kamar haka:

  • Kashe Musulmai: koda yaushe a tsawon tarihin Muslunci an kashe musulmai masu tarin yawa sakamakon Akidar Kafirta Musulmai.
  • Ruguje Wuraren Tarihi da gine-ginen Mazhaba: Wahabiyawa sun rushe wurare masu daraja a wurin Musulmai misalin Haramin A’imma (A.S) da fakewa da hujjar yaki da Shirka.
  • bata sunan Muslunci a duniya: ayyukan Kungiyoyin Ta’addanci na Takfir da sunan Muslunci ya zama sanadiyar samun dama ga Makiya Muslunc wurin siffanta shi a matsayin Addini na Rashin Tausayi [36]

Haka kuma yiwa Gwamnatocin Muslunci bore dauke da Makamai ya raunana wadannan hukumomi, rarrabuwar kai tsakanin Hukumomin Muslunci da halasta alfarmomin Musulmai da kama Musulmai matsayin Fursunonin yaki duka da masau Kafirta musulmai suka yi tayi yana daga sauran miyagun sakonnin Kafirta Ma’abota Alkibla [37] Samuwar Kungiyoyin Takfiri (Masu Kafirta Musulmai) A Karni na karshe-karshe an samu bullar Kungiyoyin Ta’addanci Misalin Daish wadanda suke karkashin Tasirantuwa da kulawar Wahabiya, sun dinga afkawa Musulmai suna kashe su da kwace musu dukiyoyi [38] suna masu fakewa da ayoyin Kur’ani da Dabbaka su a kan Musulmai [39] daidai lokacin da Malaman Musulmai basu aminta da wannan danyen aiki na Kungiyoyin Ta’addanci ba, a fatawar Malaman Addini kadai ana kafirta Mutum ne idan ya yi inkari da karyata Laruran Addinin Muslunci Misalin Tauhidi da Annabta [40] suma din idan ya Inkarinsu yana fadake ba cikin yanayin da zasu iya karbar tawili ba [41]

Babban Taron Kowa da Kowa na Kasa da Kasa

A shekarar 1393 h shamsi an shirya babban Taro na kowa da kowa mai taken (World congress of extremist and takfiri currents from the perspective of Islamic scholars) wannan taro ya kasance karkashin kulawar Ayatullahi Mukarim Shirazi daya daga cikin Maraji’an Taklidi, anyi Taron ne a birnin Qum, Malamai 80 daga Ahlsunna da `Yan Shi’a daga Kasashe daban-daban na duniya sun Halarci wannan taro [42] sannan an gabatar da rubutacciyar Kasida har guda 830 a cikin Mujalladi 10 a Mai taken (wasu adadin Kasidu na Babban Taron Duniya dangane da Batun Takfiri da wuce gona da iri da sunan Muslunci) haka kuma Babban Sakatare na dindin na wannan Taro ya yada littafi daidai har guda Arba’in da Mujallar Ummatu Wahida Islami ta tsara su cikin harshen Larabci da Farisanci [43]

Jerin Litattafai

Dangane da batun Kafirta Musulmai da Nakadin wannan Akida anyi rubuce-rubuce daban-daban cikin (Kitab Shinasi Takfir) kusan talifi 528 cikin harshen larabci da Farisanci karkashin wannan talifi an fitar da adadin litattafai 235 da Kuma Kasida 240 da kuma Risala 49 da Risala ta musammam guda hudu [44]

  • Littafin( Ara’u Ulama’il Al-Muslimin wa Fatawahum fi Tahrim takfiri Atba’il Al-Mazahibil Al-Islamiyya) Talifin Shaik Fu’ad Kazim Mikdadi wanda ya assasa Darul At-Takrib Irak, wannan littafi ya kunshi bincike kan fatawowi da ra’ayoyin Malaman Shi’a da Ahlus-sunna dangane da Kafirta Mabiyan Mazhabobin Muslunci, Majma As-Saklaini Ilimi Tahran suka buga wannan littafi a shekara ta 1428 h Kamari [45]
  • (Al’Islam Wal-unfu Kira’atu fi Zahirati At-Takfir) Talifin Husaini Ahmad Khashan don Nazarin mas’alar Kausasawa da Takfiriyya cikin Muslunci da kuma Asalai da Ma’aunan Takfiriyya, Ya bayyana asalinsa da nau'o'insa da kuma Siiffofin Takfiriyya, wannan littafi yana dauke da taken (Islam wa Kushunat Negahi No beh Padide takfir) littfafi da yake dauke da shafi 344 an tarjama shi ne zuwa harshen Harshen Farisanci a shekara ta 1390 h shamasi [46]

Bayanin kula

  1. Agha Salehi da wasu Marubuta, "Takfir wa Payamadhaye An dar Jawami'eh Islami, shafi na 95.
  2. Agha Salehi da wasu Marubuta, "Takfir wa Payamadhaye An dar Jawami'eh Islami, shafi na
  3. Nasrasafhani, “Kitab Shenasi Takfir”, shafi na 258.
  4. Fiumi, Zailu "Takfir".
  5. Abd al-Moneim, Mujamu Almusdalhat wa Alfaz Al-Faqhiyyah, Darul Fadilah, Mujalladi na 1, shafi na 487.
  6. Duba Imam Khumaini, Kitab al-Tahara, 1427H, juzu'i na 3, shafi na 437-438.
  7. Misali, duba Imam Khumaini, Kitabul Tahara, 1427H, juzu’i na 3, shafi na 432.
  8. Misali, duba Shahid Sani, al-Rawda al-Bahiya, 1403 AH, juzu'i na 9, shafi na 175;Jaziri, Kitab al-Fiqh Ala Al-Mazaheb al-Arba'a, 1410 AH, juzu'i na 5, shafi na 194-195.
  9. Duba Imam Khumaini, Kitab al-Tahara, 1427H, juzu'i na 3, shafi na 437-438.
  10. Duba Allameh Majlesi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 54, shafi na 246-247.
  11. Moghdisi, al-Mishada da al-Tarikh, Makarantar Al-Taqfah al-Diniya, juzu'i na 5, shafi na 152.
  12. Jafarian, Tarikh Khulafa, 1380, juzu'i na 2, shafi na 32.
  13. Waqidi, Ar-Riddatu, 1410 AH, shafi na 106-107.
  14. Sobhani, Buhus fi Almilalu Wan- Annehal, 1427-1428 AH, juzu'i na 5, shafi na 97.
  15. Dinouri, Al-Akhbar al-Tawwal, 1368, shafi na 206.
  16. Yaqoubi, Tarik Yakubi, Beirut, juzu'i na 2, shafi na 192-193.
  17. Sobhani, Buhusu Fi Almilal wa An-Nehal, 1427-1428 AH, juzu'i na 2, shafi na 336.
  18. Dinouri, Al-Akhbar al-Tawal, 1368, shafi na 206
  19. Duba Mughniyyah, Hazihi Heyal Al-Wahhabiyyah, 1408 AH, shafi na 74-76.
  20. Muhammad bin Abd al-Wahhab, Kashf al-Shubhat, 1418 AH, shafi na 7.
  21. Shahrashtani, Al-Malal wa Al-Nehal, 1387 Hijira, juzu'i na 1, shafi na 122, 128, da 135.
  22. Suratul Ma’edah, aya ta 44.
  23. Jurjani, Sharh al-Mawakif, 1325 AH, juzu'i na 8, shafi na 334-338.
  24. Sobhani, Almuhadart fi Al-Ilahiyat, 1428 AH, shafi na 462.
  25. Abul Alhasan Ash’ari, Al-Ebanatu, 1397H, shafi na 89.
  26. Ibn Hanbal, Al-Sunnah, 1349H, shafi na 15.
  27. Sobhani,Buuhus Fi Almilal wa Al-Nehal, 1427-1428 AH, juzu'i na 2, shafi na 336.
  28. Hurrul Ameli, Wasa'el Al-Shia, 1409 AH, juzu'i na 28, shafi na 348.
  29. Haider, Al-Imam Al-Sadiq wa Al-Mazaheb Al-Arba'a, Dar Al-Taqran, mujalladi na 1, shafi na 200-202.
  30. Ibn Jibrin, Al-Llull al-Makin Min Fatawi al-Shaykh Ibn Jibrin, shafi na 25.
  31. Jaziri, Kitab al-Fiqh Ali al-Mazaheb al-Arba'a, 1410 AH, juzu'i na 5, shafi na 194-195.
  32. Misali, duba Imam Khumaini, Kitabul Tahara, 1427H, juzu’i na 3, shafi na 432.
  33. Duba Ghazali, Tahafut Al-Falasafeh, 2002, shafi na 295-94.
  34. Khansari, Rowzat al-Jannat, 1390, juzu'i na 4, shafi na 121.
  35. Hasanlu, “Zamineh Faidayesh Takifr miyan Muuslman wa Payamad An dar jahane Islami”, shafi na 54.
  36. <a class="external text" href="https://makhaterltakfir.com/fa/ejlashaview/8789">«کنگره جهانی جریان‌های افراطی و تکفیری از دیدگاه علمای اسلام»</a>
  37. Agha Salehi da wasu Marubuta, "Takfir wa barasi Payamdamhaye An Dar Jawami'eh Islami", shafi na 110-100.
  38. Duba: Bakshi Sheikh Ahmad da Behari, "Barasi Ayidiyoloji Gurahak Takfiri-Wahabi Daulat Islami Irak wa Sham (ISIS)", shafi na 141-144.
  39. Agha Salehi da wasu Marubuta, "Takfir wa barasi Payamdamhaye An Dar Jawami'eh Islami", shafi na 97.
  40. Misali, duba Rashid Reza, mujallar al-Manar, Beta, juzu'i na 35, shafi na 573.
  41. Duba Rashid Reza, Mujallar Al-Manar, Beta, Mujalladi na 35, shafi na 573.
  42. <a class="external text" href="http://makhaterltakfir.com/fa/ejlasha/View/1069">«کنگره جهانی جریان‌های افراطی و تکفیری از دیدگاه علمای اسلام».</a>
  43. <a class="external text" href="https://www.hawzahnews.com/news/369921">«۴۰عنوان کتاب کنگره ضد تکفیر به پنج زبان زنده دنیا چاپ شده است.»</a>
  44. Nasransari, Kitab Shinaseh Takfir, 2014, shafi na 21.
  45. Kitab Shinaseh Takfir, 2014, shafi na 25
  46. Kitab Shinaseh Takfir, 2014, shafi na 29

Nassoshi

  • «کنگره جهانی جریان‌های افراطی و تکفیری از دیدگاه علمای اسلام»،Sakatariyar Majalisar Dinkin Duniya kan Yaki da Tsattsauran ra'ayi da Takfiri Currents, wanda aka buga a ranar 13 ga Yuni, 1395, aka duba ranar 10 ga Mayu, 1401.
  • «۴۰ عنوان کتاب کنگره ضد تکفیر به پنج زبان زنده دنیا چاپ شده است.» Kamfanin dillancin labarai na Hohza, wanda aka buga a ranar 8 ga Fabrairu, 1394, an duba shi ranar 10 ga Mayu, 1401.
  • Agha Salehi, Ali, Khosro Momeni, Mojtaba Jafari, and Alireza Sabrian.«تکفیر و بررسی پیامدهای آن در جوامع اسلامی» Nazarin shari'a da ƙa'idodi, lokaci na biyu lamba 2, kaka da hunturu 2018.
  • Abul Hasan Ash'ari, Ali Bin Ismail, Al-Abaneh akan Usul al-Dianeh, binciken Hossein Mahmoud a sama, Alkahira, Darul Ansar, 1397H.
  • Ibn Jabrin, Al-Llull al-Makin Man Fatawi al-Sheikh Ibn Jabrin, Lambobi: Abdullah bin Yusuf al-Ajlan, Compilation: Salman bin Abdulkadir Abu Zayd, Bija, Bita.
  • Ibn Hanbal, Ahmad, Al-Sunnah, Abdullah bin Hasan al-Sheikh, Makka, al-Mutababa al-Salfiyyah da makarantu, 1349H.
  • Imam Khumaini, Sayyid Ruhollah, Kitabul Tahara, Tehran, Cibiyar Gyara da Buga Ayyukan Imam Khumaini (AS), 1427H/1358H.
  • Bakhshi Sheikh Ahmed, Mehdi da Behnam Behari da Peyman Wahabpour, «بررسی ایدئولوژی گروه تکفیری - وهابی دولت اسلامی عراق و شام (داعش)»Jaridar Kimiyya da Bincike na Kwata-kwata na Kimiyyar Siyasa na Jami'ar Bagheral Uloom, Juzu'i na 16, Lamba 46, Winter 2013.
  • Jurjani, Ali binu Muhammad, bayanin mukamai, Muhammad Badrul-Din Nasani Halabi, Masar, ya yi bincike, 1325 AH/1907 AD (Offest Qom, 1370).
  • Jaziri, Abdul Rahman, Kitab al-Fiqh Ali al-Mahabh al-Araba, Beirut 1410/1990.
  • Jafarian, Rasul, Tarihin Khalifofin Qum, Dalil, 1380.
  • Khansari, Seyyed Mohammad Baqir, Ruzat al-Jannat fi Akhval al-Ulama wa Al-Sadat, Qom, Ismailian, bugun farko, 1390.
  • Har Amili, Muhammad Bin Hasan, Hanyoyin Koyan Matsalolin Shari'a na Shi'a, Cibiyar Al-Baiti, Qum, 1409H.
  • Hassanlou, Amir Ali, «زمینه‌ها و عوامل پیدایش تكفیر در میان مسلمانان و پیامدهای آن در جهان اسلام»، Halin addini na Epistemological a fagen duniya, lamba 16, 1396.
  • Dinouri, Abu Hanifa Ahmad Bin Dawud, Al-Akhbar al-Tawwal, Bincike na Abdul Moneim Amer, Qum, Al-Razi Manshurat, 1368.
  • Zinidahlan, Seyyed Ahmad, Fatnah al-Wahhabiyyah, B.T.
  • Sobhani Tabrizi, Ja'afar, Buhusu fi Al-milal wan-Nihal, Qum, Al-Nashar al-Islami Est., 1427-1428H.
  • Sobhani, Jafar, Al-Muhadar Al-Ilahiyat, Buga Cibiyar Imam Sadik, 1428H.
  • Shahrashtani, Muhammad bin Abdul Karim, Al-Milal wa An-Nehal, wanda Muhammad Seyedkilani ya buga, Alkahira, 1967/1387.
  • Shahid Thani, Zain al-Din bin Ali, al-Rawda Al-Bahiyyah fi Sharh al-Lum'a Al-Damashqiyyah, bugun Mohammad Kalantar, Beirut 1403/1403.
  • Abdul Baqi, Mohammad Fouad, Mu'jam Al-Musdalaht Al-faz Al-Qur'an Al-Karim, Alkahira 1364, Tehran Offset Printing, 1397.
  • Abdul Moneim, Mahmoud Abdur Rahman, Mujam Almusdalahat Al-Faz Al-Fiqhiyyah, Juzu'i na 1, Alkahira, Dar Al-Fazilah, [1999 AD].
  • Ghazali, Faisal al-Tafqarah bainal al-Islam wa al-Zindaqah, bugun Riaz Mustafa Abdullah, Damascus 1417.
  • Fayoumi, Ahmad bin Muhammad, Al-Mesbah Al-Munir fi Gharib al-Sharh al-Kabeer na Rafa’i, Beirut: Dar al-Fikr, Bita.
  • Majlesi, Mohammad Baqer bin Mohammad Taqi, Bihar al-Anwar, Beirut 1983/1403.
  • Mughniyah, Mohammad Javad. Hazihi Hiyal Wahabiyyah, Tehran, Kungiyar Yada Labarai ta Musulunci, 1408H.
  • Mofid, Muhammad bin Muhammad, al-Fusul al-Mukhtarah Min al-Ayoun wa Al-Mahasen, Qom 1413.
  • Moghadsi, Motaher bin Taher, al-Midah da al-Tarikh, Bor Saeed, Al-Taqfah al-Diniyah School, Bita.
  • Nasrasafhani, Abazar, Kitab Shinasi Takfir, Qum, Dar al-Alam for Madrasa Ahl al-Bait (AS), 1393.
  • Waqidi, Muhammad bin Omar, al-Ridda, wanda Yahya al-Jubouri, Beirut, Dar al-Gharb al-Islami ya yi bincike, bugu na farko, 1990 miladiyya/1410H.
  • Yaqoubi, Ahmad bin Abi Yaqoob, Tarikh Yaqoubi, Beirut, Dar Sadir, Bita.
  • Ghazali, Mohammad bin Mohammad, Tahaft al-Falasfa, Shams Tabrizi, Tehran, 1382.
  • Rashud Rida da sauran Marubuta: مجلة المنار، *Muhammad bin Abd al-Wahhab, Kashf al-Shabhat, Al-Malmakah Arabiya al-Saudi, Ministry of Affairs and Endowment and Dawa and Guidance, 1418 AH.