Watanni Masu Alfarma
Wannan wani rubutu ne na siffantawa game da wata ma'ana ta fiƙihu, kuma ba za ta iya zama ma'auni ga ayyukan addini ba, domin ayyukan addini sai a koma zuwa ga wasu madogaran na daban. |
Watanni masu alfarma, (Larabci: الأشهر الحرم) wasu watanni ne da yin yaƙi a cikinsu ya haramta, waɗannan watanni sune kamar haka:Zil-Ƙa'ada, Zil-Hijja, Muharram da Rajab. A cikin Kur'ani bayani ya zo cewa wajibi kiyaye alfarmar waɗannan watanni kuma bai halatta a yi yaƙi a cikin waɗannan watanni ba, sai dai idan yaƙi ne na kare kai, ma'ana ba Musulmi ne suka fara yaƙin ba, an dai tilasta musu kare kansu ne. Daga cikin hukunce-hukuncen watanni masu alfarma akwai cewa idan wani ya aikata kisan ganganci ko wanda ba na ganganci ba, wajibi cikin biyan diya ya yi ƙari da kaso ɗaya cikin uku na diyya.
Haramcin yaƙi cikin wattani masu alfarma ya kasance tun zamanin jahiliyya a cikin Larabawa: sai dai kuma a wasu lokuta Larabawa sukan ɗauke haramcin waɗannan watanni su kai shi wasu watannin daban domin su samu damar yin yaƙi cikin waɗannan watanni masu alfarma. Ana kiran wannan aiki na su da sunan "Nasi'u" Kur'ani ya siffanta hakan a matsayin babban zunubi.
Me Ake Nufi Da Watanni Masu Alfarama Kuma Waɗanne Watanni Ne?
A Muslunci, kan asasin ayoyin Kur'ani da riwayoyi an ambaci watanni huɗu da sunan watanni masu alfarma.[1] Dalilin kiransu da wannan suna ya samo asalin daga haramcin yaƙi cikinsu[2] Wannan ne dalilin alfarmar waɗannan watanni[3] ƙari kan haka, Shaik Ɗusi a cikin Tafsirul Tibyan, ya tafi kan cewa haramcin yana da ma'ana cewa aikata haramun a cikin waɗannan watanni yafi tsanani da munana daga sauran watanni.[4] Haka nan a cewar malaman Muslunci, ladan kyawawan ayyuka a cikin waɗannan watannin ya fi yawa daga wasu watannin daban.[5]
Cikin Kur'ani magana ta zo ƙarara kan wannan batu. Cikin aya ta 36 suratul Tauba ya zo cewa adadin watannin a wurin Allah guda goma sha biyu ne kuma cikinsu guda huɗu watanni ne masu alfarma. Bisa wata riwaya daga Annabin Muslunci (S.A.W), cikin watannin huɗu masu alfarma guda uku suna jere da juna sune: Zil-Ƙa'ada, Zil-Hijja da Muharram, sai kuma guda ɗaya da ya zo a ware wato Rajab.[6]
Lokacin Da Aka Kafa Haramcin Watanni Masu Alfarma
Bisa imanin aksarin malaman tafsiri, haramcin watanni masu alfarma an fara kafa shi a cikin shari'ar Annabi Ibrahim (A.S)[7] kuma ya ci gaba har zuwa zamanin jahiliyya[8] Wannan alfarma ta kasance da ace wani mutum zai haɗu da wanda ya kashe babansa cikin waɗannan watanni da ba zai kula shi ba.[9] Ahmad Baihaƙi malamin musulmi (Rasuwa: 458 hijira) ya rubuta cewa mutanen jahiliyya a lokacin watan Rajab sun kasance suna ajiye makamansu a gefe, mutane na rayuwa cikin kwanciyar hankali da cikakken aminci da zaman lafiya, babu wanda yake tsoron cutuwa daga wani.[10] Wannan al'ada ta Ibrahimiyya ta ci gaba tsakankanin Larabawa har zuwa lokacin bayyanar Muslunci, kuma Kur'ani ya jaddada tafiya kanta.[11]
Hukunce-hukuncen Watanni Masu Alfarma
Hukunce-hukuncen watanni masu alfarma, daga ciki akwai haramcin yaƙi cikinsu; idan aka kai hari kan musulmi, suna da haƙƙin kare kansu.[12] Wani hukunci na fiƙihu na daban akwai cewa diyyar kisa cikin waɗannan watanni tana ƙaruwa da kaso ɗaya cikin uku na diyya a cikin sauran watanni,[13] kuma babu bambanci kisan ganganci ne ko kisa makamancin ganganci ko kuma kisa wanda bana ganganci ba.[14]
Cikin Kur'ani an yi bayanin haramcin yaƙi a watanni masu alfarma. A cikin aya ta 217 suratul baƙara ya zo: «یسْأَلُونَكَ عَنِ الشَّهْرِ الْحَرَامِ قِتَالٍ فِيهِ. قُلْ قِتَالٌ فِيهِ كَبِيرٌ؛ ( Suna tambayarka game da watanni masu alfarma ka ce musu yaƙi cikinsu zunubi ne babba) haka ya zo: (Wata mai alfama da wani wata mai alfarma kuma alfarmomi cikinsu akwai ƙisasi, idan abokin gaba ya keta alfarma ya yaƙe ku cikin waɗannan watanni, kuma kuna da haƙƙin ramawa, ku ji tsoran Allah ku sani lallai Allah yana tare da masu taƙawa).[15]
Nasi'u
Nasi'u yana da ma'anar jinkirtar da watanni masu alfarma.[16] A zamanin jahiliya, wani lokaci wata ƙabila da take son yin yaƙi a cikin ɗaya daga watanni masu alfarma, tare da biyan wasu kuɗaɗe tana aikawa zuwa ga masu kula ga ka'aba ta nemi su halatta mata wani wata cikin masu alfarma a haramta wani watan daban maimakonsa.[17] Watan da aka ɗauke alfarmarsa ana kiransa da sunan "Nasi'u".[18] Kur'ani a cikin aya ta 36 da 37 suratul Tauba, ya yi suka kan al'adar nasi'u ya kuma bayyana ta matsayin abin da yake janyo kafirci da ɓata ga mutane.[19]
Falsafar Haramcin Watanni Masu Alfarma
A cewar Nasir Makarim Shirazi, malamin tafsiri a Shi'a, haramncin yaƙi a cikin watanni masu alfarma, ɗaya ne daga cikin hanyoyi na kawo ƙarshen yaƙe-yaƙe da suke cin dogon zango, an yi hakan ne don ya zama wani tsani da za a fake da shi cikin kira zuwa ga sulhu da zaman lafiya, yayin da aka ajiye makamai cikin watanni huɗu a shekara, za a samu buɗewar fagen tunani da nutsuwa, tsammanin kawo ƙarshen yaƙi yana ƙaruwa matuka.[20] Sayyid Muhammad Husaini Ɗabaɗaba'i shi ma ya tafi kan cewa tare da tsagaita wuta da dakatar da yaƙi zaman lafiya zai mamaye baki ɗayan ƙasa domin mutane su samu damar tanadin kayayyakin rayuwa su kuma su ci gaba da rayuwarsu ta yau da gobe tare da neman kusanci zuwa ga Allah cikin ɗa'arsa.[21]
Bayanin kula
- ↑ Kashani, Manhaj al-Sadiqin, Tehran, juzu'i. 4, shafi. 265; Tusi, Al-Tabyan, Dar Ihya al-Turat al-Arabi, juzu'i. 5, ku. 214; Suyuti, Al-Durrul al-Manthur, Dar al-Fikr, juzu'i. 4, ku. 183; Tusi, Tahdhib al-Ahkam, 1407 AH, juzu'i. 4, shafi. 161; Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i. 55, shafi. 339.
- ↑ Tusi, Al-Ta=ibiyan, Dar Ihya al-Turat al-Arabi, juzu'i. 2, shafi. 149; Tabari, Jami'ul al-Bayan, 1412 AH, juzu'i. 10, shafi. 56.
- ↑ Tabarsi, Majma'ul al-Bayan, 1372, juzu'i. 2, shafi. 551.
- ↑ Tusi, Al-Tebyan, Dar Ihya' Al-Turaht Al-Arabi, juzu'i. 5, shafi. 214.
- ↑ Qomi, Tafsir al-Qommi, 1404 AH, juzu'i. 1, shafi. 67; Jassas, Akhmul al-Quran, 1405 AH, juzu'i. 4, shafi. 308.
- ↑ Tusi, Tahdeeb al-Ahkam, 1407 AH, juzu'i. 4, shafi. 161; Majlesi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 55, shafi na 339.
- ↑ Kashani, Manhaj al-Sadiqin, Tehran, juzu'i. 4, shafi. 267; Tabataba'i, Tafsir al-Mizan, 1421 AH, juzu'i. 9, shafi. 271; Ibn Arabi, Ahkam al-Qur'an, 1408 AH, juzu'i. 2, shafi. 943; Suyuti, Al-Durrul al-Manthur, Dar al-Fikr, juzu'i. 4, shafi. 188.
- ↑ Tayeb, Atyab Al Bayan, 1369, juzu'i. 8, shafi. 218.
- ↑ Tusi, Al-Tabyan, Dar Ihya' Al-Turaht Al-Arabi, juzu'i. 5, shafi. 214.
- ↑ Bayhaqi, Sha’ab al-Iman, 1423H, juzu’i. 5, shafi. 338.
- ↑ Tabataba'i, Tafsir al-Mizan, 1421 AH, juzu'i. 9, shafi. 266.
- ↑ Imam Khumaini, Istifta'at, juzu'i. 1, shafi. 515.
- ↑ Imam Khumaini, Tahrir al-Wasilah, juzu'i. 2, shafi. 530;سیستانی، توضیحالمسائل جامع، ج۴، مسئله ۱۳۶۱.
- ↑ سیستانی، توضیحالمسائل جامع، ج۴، مسئله ۱۳۶۱.
- ↑ Suratul Baqarah, aya ta:194
- ↑ Jafari, Bahasi Darbaraye “Nasi'u” Wa Rabiɗe An Ba Hajji, shafi. 119.
- ↑ Sobhani, Manshor Javid, Imam Sadiq Institute, juzu'i. 6, shafi. 35.
- ↑ Tabataba'i, Tafsir al-Mizan, 1352, juzu'i. 9, shafi. 271.
- ↑ Suratul Tauba, aya ta 36 da ta 37.
- ↑ Makarem, Tafsir-Numno, 1371, juzu'i. 7, shafi. 408.
- ↑ Tabataba'i, Tafsir al-Mizan, 1421 AH, juzu'i. 9, shafi. 268; Al-Durrul al-Manthur, Dar al-Fikr, juzu'i. 4, shafi. 185.
Nassoshi
- Ibn Ashur, Muhammad al-Tahir, Al-Tahrir wa al-Tanwir, Tunisia, Al-Dar al-Tunisiyyah, 1984.
- Ibn Arabi, Muhammad bn Abdullah, Ahkamul Alqur'an, bincike, Ali Muhammad Bejawi, Beirut, Dar al-Jil, bugun farko, 1408H.
- Abu al-Futuh Razi, Hussein bn Ali, Rawd al-jinan Wa Ruh al-jinanFI Tafsiri Alqur'ani, bita, Muhammad Mahdi Nasih; Muhammad Jafar Yahaqi, Mashhad, Astan Quds Razavi, bugun farko, 1408H.
- Imam Khumaini, Istifta'at, Ofishin Daba'ar Musulunci, Kaka 1372.
- Imam Khumaini, Tahrir al-Wasilah, Cibiyar Tattaunawa da Buga Ayyukan Imam Khumaini, Shekara ta 1379 / Rabi al-Awwal 1421.
- Ansari Masoud, Mahaye Haram Dar Qur'an Kareem, Encyclopedia of the Quran and Quran Studies, edited by Baha' al-Din Khoramshahi, Vol. 2, Tehran: Dostan [da] Nahid, 1377.
- Ansari Masoud, Nasi'u, Daneshnameh Quran Wa Quran Pajuhi, tare da taimakon Baha’ al-Din Khorramshahi, Vol. 2, Tehran: Dostan [da] Nahid, 1377.
- Bayhaqi, Ahmad bin Husayn, Shi’ib al-Iman, Abdul Ali Hamed, India, Maktaba al-Rushd, ya yi bincike, 1423H.
- Jassas, Ahmad bn Ali, Akhmul al-Quran, Muhammad Sadiq Qamhawi, Beirut, Dar Ihya al-Turat al-Arabi, ya yi bincike, 1405H.
- Ja’afari, Ya’aqub, Bahasi Darbaraye Nasi'u Wa Rabiɗe An Ba Hajji, Mikat al-Hajj, No. 3, Spring 1372H.
- سیستانی، سیدعلی، توضیحالمسائل جامع، ج۴، مسئله ۱۳۶۱., Shafin yanar gizo na ofishin Ayatollah Sistani.
- Suyuti, Abd al-Rahman, Al-Durrul al-Manthur, Beirut, Dar al-Fikr, Beta.
- Tabatabaei, Muhammad Hussein, Al-mizan Fi tafsir alqur'ani, qum, bugu na 6, 1421H.
- Tabarsi, Fadl bn Hassan, Tafsir al-Jami'ul al-Jami', Abu al-Qasim Gorji, Qum, Seminary Qum, bugu na 1, 1412H.
- Tabarsi, Fadl bn Hassan, Majma'ul-Bayan Fi Tafsir Alqur'ani, Tehran, Nasser Khosrow, bugu na 3, 1372H.
- Tabari, Muhammad bn Jarir, Jame'ul-Bayan Fi Tafsir Alqur'ani, Beirut, Darul Mar'afa', bugu na 1, 1412H.
- Tusi, Muhammad bn Hassan, Al-Tabiyan Fi Tafsir Alqur'ani, Beirut, Dar Ihya' al-Turat al-Arab, Beta.
- Tusi, Muhammad bn Hassan, Tahdhib al-Ahkam, Hassan al-Musawi, Tehran, Darul Kuttab al-Islamiyya, bugu na hudu, 1407H.
- Tusi, Muhammad bn Hassan, al-Tebyan fi tafsir al-Qur'ani, Beirut, Darul-Ihya al-Turat al-Arabiyya, bi-ta.
- Tayyib, Abdul-Husayn, Atyab al-Bayan fi tafsir al-Quran, Tehran, Nash-e-Islam, bugu na biyu, 1369H.
- Qummi, Ali ibn Ibrahim, Tafsir Qummi, wanda Sayyid Tayyib Musavi Jazayeri ya yi bincike, Qum, Darul Kuttab, bugu na uku, 1404H.
- Kashani, Fathullah, Manhaj al-Sadiqin fi zaml al-Mukhilifin, Tehran, kantin sayar da littattafan Islama, bugun farko, bi-ta.
- Majlisi, Muhammad Baqir, Bihar al-Anwar, Beirut, Darul-Ihya al-Turat al-Arabiyya, bugu na biyu, 1403H.
- Makarem Shirazi, Nasser, Tafsir Numno, Tehran, Darul Kuttab al-Islamiyya, bugu na sha tara, 1377H.