Ayar Izinin Jihadi
| bayanan aya | |
|---|---|
| sunan aya | Izinin Jihadi |
| akwai shi cikin sura | Suratul Hajji |
| lambar aya | 39 |
| sha’anin sauka | Mahajirun, Ahlil-Baiti |
| bayanan abin da yake ciki | |
| wurin sauka | Madina |
| maudu’i | Fiƙihu |
| game da | Izinin yaƙi da Mushrikai |
| ayoyi masu alaqa | Ayar Saifi |
Ayar izinin jihadi, (Larabci: آية إذن الجهاد) suratul hajji aya ta 39, ita ce aya ta farko da ta baiwa musulmi izinin jihadi kan mushrikai. Wannan aya ana lissafa ta cikin ayoyi muhkamat a cikin kur'ani, kuma aya ce da ta goge bin mushrikai ta lallami. Wannan aya bayan ta sauka ne bayan hijira zuwa Madina sakamakon cutarwa da mushrikan Makka suke yi kan musulmi; gabanin saukar wannan aya Annabi (S.A.W) ya kasance yana rarrashin musulmi da su yi haƙuri da cutarwar da suke fuskanta daga mushrikai.
Malaman tafsiri na Shi'a da Ahlus-Sunna tare da jingina da wannan aya, sun yi bayanin sharuɗɗa wajabcin jihadi, daga jumlarsu akwai batun cewa wannan aya ta sauka ne game da jihadi difa'i (Jihadin kare kai) nau'in wannan jihadi ba ya buƙatar izinin Imami. Ba'arin malamai sun tafi kan cewa wannan aya ta na nuni zuwa ga iyakokin jihadi da kuma watsi da tuhumar Muslunci da cewa addini ne mai son kausasawa, saboda shi yaƙi kaɗai yana kasancewa halastacce bayan zalunci da kuma korar musulmi.
Cikin riwayoyin Shi'a, an yi aiki da wannan aya kan Ahlul-baiti (A.S) da Imam Mahadi (A.F), Har ila yau, sahabbai da tabi'ai su ma sun yi amfani da wannan aya domin samun halasci kan matakai da suka ɗauka, haka kuma sun kafa hujja da ita, kamar dai misalin Usman a lokacin da aka kewaye gidansa, Imam Ali (A.S) a lokacin yaƙin siffin ko Jamal da Ibrahim Imam a lokacin miƙewar Abu Muslim Khurasani.
Bayar Da Izinin Yaƙar Mushrikai
Ana kiran aya ta 39 suratul hajji da sunan ayar jihadi.[1] Haka nan wannan aya ta samu shahara da sunan ayar yaƙi[2] ko ayar izinin yaƙi[3] A cikin wannan aya an baiwa musulmi da mushrikai suka zalunta izinin jihadi da su. Kuma ana lissafa wannan aya cikin jerin ayoyin kur'ani muhkamat.[4] Aya ce ta farko da aka halastawa musulmi jihadi tare da mushrikai domin kare kawukansu da kuma kare da'awar Annabi (S.A.W).[5]
Ayar izinin jihadi aya ce da ta goge ayoyi misalin aya ta 48 suratul ahzab wace ta kasance tana ƙarfafa lalami da bi a sannu-sannu tare da mushrikai.[6] An ce a cikin kur'ani akwai ayoyi fiye 70 da suka sauka wurin Annabi (S.A.W) game da bi sannu-sannu da lalami tare da Mushrikai.[7] Har ila yau, wannan aya ta goge aya 14 suratul jasiya.[8]
أُذِنَ لِلَّذِينَ يُقَاتَلُونَ بِأَنَّهُمْ ظُلِمُوا وَإِنَّ اللَّهَ عَلَى نَصْرِهِمْ لَقَدِيرٌ
An ba da izini ga waɗanda ake yaƙi da su, saboda an zalunce su. Kuma lallai Allah Mai iko ne a kan taimakon su
(Quran: Hajji: Aya ta 39)
Malaman tafsiri suna ganin gaɓar «أُذِنَ لِلَّذِينَ يُقَاتَلُونَ» a cikin ayar jihadi, a matsayin dalili da yake nuna cewa Annabi (S.A.W)[9] da musulmi sun kasance gabanin saukar wannan aya an hana su jihadi da mushrikai.[10] Amma tare da saukar wannan aya sai suka samu izinin yin jihadi kan mushrikai.[11] Har ila yau, an ce jihadi tare da hijira sun kasance sababin nasarar Muslunci.[12]
Sha'anin Sauka
Dangane da sababin saukar ayar izinin jihadi, malamai sun ce mushrikan Makka sun kasance suna takurawa sahabban Annabi (S.A.W) da wannan dalili suka kai kukansu wurin Annabi (S.A.W) cikin rarrashi da kuma umartar sahabbansa da bi a sannu, ya kasance yana gaya musu ni har zuwa yanzu ba umarce ni da jihadi ba, bayan yin hijira zuwa Madina sai wannan aya ta sauka.[13] Bisa dogara da wata riwaya daga Imam Sadiƙ (A.S) wannan aya ta na magana ne da waɗanda suka yi hijira da ƙuraishawa suka kore su daga garin Makka.[14]
Ayar izinin jihadi ta sauka wata bakwai bayan hijira zuwa Madina.[15] Wannan aya da take a suratul hajji, ta na jerin surori madaniyya. Ba'arin malaman tafsiri suna da ra'ayin cewa kaɗai wasu ba'arin ayoyi ne daga wannan sura aka saukar da su a Makka.[16] Kishiyar wannan magana, wasu adadin malamai sun tafi kan cewa suratul hajji sura ce da aka saukar da ita a Makka, kaɗai ayoyi biyar ne aka saukar da su a Madina.[17]
Ayyana Sharuɗɗan Jihadi A Cikin Wannan Aya
Wasu adadi daga malaman fiƙihu na Shi'a da Ahlus-Sunna tare da dogara da ayar izinin jihadi sun yi bayanin sharuɗɗan wajabcin jihadi; daga jumlar wannan malamai akwai Husaini Ali Muntazari ɗaya daga cikin maraji'an taƙlidi na Shi'a, bisa wannan aya, yana ganin cewa jihadi difa'i baya buƙatar izinin Imam.[18] Saraksi daga malaman fiƙihu na Ahlus-Sunna shi ma bisa wannan aya, yana da ra'ayin cewa kaɗai musulmai suna da izinin yaƙi da mushrikai idan mushrikan suka fara kai hari a kansu,[19] Na'am Shafi'i malamin fiƙihu na Ahlus-Sunna ya tafi kan cewa cikin wannan aya Allah ya baiwa musulmi izinin jihadi ibtida'i kan mushrikai.[20]
Hassan Jawahiri ɗaya daga cikin malaman fiƙihu a hauza ilmiyya Najaf, yana ganin ayar izinin jihadi ba ta taƙaita da muƙamin bayanin halascin jihadi ba kaɗai, aya ce da take bayanin iyakoki da sharuɗɗan jihadi.[21] Ba'arin malaman Shi'a suna ganin sharaɗin izinin yaƙi a wannan aya ya dogara da sharuɗɗa guda biyu: na farko: ya zamana an zalunci mutane, na biyu bisa lura da «الَّذِينَ أُخْرِجُوا مِنْ دِيَارِهِمْ بِغَيْرِ حَقٍّ...» (Waɗanda aka kore su bisa zalunci daga garuruwansu) da take cikin ayar.[22]
A cewar Jawahiri, ba'ari tare da jingina da wannan aya, sun bayyana Muslunci matsayin addinin kaifin Takobi; a daidai lokacin da ya kamata a ba da amsa ga wannan da'awa da cewa shi Muslunci kafin ya fitar da umarnin yaƙi, ya fara da amfani da hanyar hujja da kyakkyawan jidali cikin magana da mutanen da yake magana da su, kuma ya yi baƙin ƙoƙarinsa na kaucewa yaƙi, amma lokacin da aka zalunci mabiyansa sai ya ba da izinin yaƙi domin kare kai.[23]
Aiki Da Wannan Aya Kan Ahlul-baiti
Kan asasin wata riwaya daga Imam Kazim (A.S), an bayyana cewa ayar izinin jihadi ta sauka ne game da iyalan Muhammad (S.A.W).[24] Zaidu Bin Ali shi ma yana ganin wannan aya ta sauka game da Ahlul-baiti (A.S).[25] Har ila yau, bisa riwaya daga Imam Sadiƙ (A.S) gaɓar «أُذِنَ لِلَّذِينَ يُقَاتَلُونَ» cikin wannanta kasance game da Imam Ali (A.S), Jafar Bin Abi Ɗalib da Hamza Bin Abdul-Muɗɗalib.[26] A wata riwayar daban ya zo cewa wanda ayar take magana da su, su ne Sayyidina Ali (A.S), Imam Hassan (A.S) da Imam Husaini (A.S).[27]
Ba'arin malaman Shi'a tare da jingina da wata riwaya, sun bayyana cewa mutanen da aka ambata su ne waɗanda aka baiwa izinin jihadi.[28] Haka nan abin nufi da waɗanda aka zalunta a cikin ayar, su ne Imam Zaman (A.F) da sahabbansa.[29] Haka nan an naƙalto daga Imam Sadiƙ (A.S) cewa musulmin da ba ƴanshi'a ba suna raya cewa wannan aya ta sauka ne a daidai lokacin da Annabi (S.A.W) yake hijira daga Makka zuwa Madina, sai dai kuma a tawilin ayar tana magana ne da Imam Zaman (A.F) a lokacin da zai fito neman fansar jinin Imam Husaini (A.S).[30]
Har ila yau, an jingina da wannan aya kan tabbatar da raja'ar Ahlul-baiti (A.S), kan wannan asasi ne aka ce, ita raja'a tana cikin mafi girman alamomi bayyanannu a cikin shi'anci,[31] kuma bisa dogara da wata riwaya ita raja'a alƙawari ne na Allah ga Ahlul-baiti (A.S), saboda haka wajibi ne Ahlul-baiti (A.S) su yi raja'a domin Allah ya taimaka musu.[32]
Kafa Hujja Da Wannan Aya Cikin Abubuwan Da Suka Faru A Tarihi
Daidai da abin da ya zo a wasu rahotanni na tarihi, wasu adadi daga sahabbai da tabi'ai a ƙoƙarinsu na tabbatar da gaskiyarsu da manufofinsu sun jingina da ayar izinin jihadi; daga jumla an ce a lokacin da aka kewaye gidan Usman a kwanakin ƙarshen halifancinSa, an zaɓi Sa'asa'a Bin Suhan domin ya je ya tattauna da Usman, lokacin da Sa'asa'a ya samu ganawa da Usman ya karanta ayar izinin jihadi, cikin raddin da Usman ya yi wa Sa'asa'a, ya gaya masa cewa wannan aya ba ta sauka ba kanka da sahabbanka, ta sauka ne kaina da sahabbaina;[33] a lokacin da aka kore mu daga garin Makka.[34]
A wani rahoto daban ya zo cewa a lokacin yaƙin siffin[35] ko Jamal, Sayyidina Ali (A.S), domin kutsawa gumurzun gaba da gaba domin kada a gane shi ya sanya kayan Abbas Bin Rabi'a ya kutsa fagen yaƙi, tare da karanta ayar «أُذِنَ لِلَّذِينَ يُقَاتَلُونَ...» ya gwabza yaƙi da mutanen da suke neman gwabza yaƙi da shi.[36]
Har ila yau, an ce Ibrahim Imam (Daga cikin jikokin Abdullahi Bin Abbas kuma ɗan uwa ga Saffahu Da Mansur daga halifofin Abbasiyawa) lokacin da suka zaɓi Abu Muslim Khurasani domin miƙewa, sun ɗaura masa wata tuta wace cikin aka rubutu ayar «أُذِنَ لِلَّذِينَ يُقَاتَلُونَ...» (An yi izini ga waɗanda ake yaƙa…).[37] Na'am a wasu madogaran an ba da rahoto cewa Ibrahim bayan ɗaura tuta ya kasance yana karanta ayar izinin jihadi.[38]
Bayanin kula
- ↑ Ayat Namedar na Khurasani, a shafi na 368
- ↑ Najafi – Jauharul Kalam, Jild 21, Shafi 57 (1362 Hijira Qamariyya). Sabzuwari – Muhadh-dhabul Ahkam, Jild 15, Shafi 119 (1416 Hijira Qamariyya)
- ↑ Tafsirul al-Mizaan na Allama Tabataba’i – Jild 14, Shafi 384 (1412 Hijira Qamariyya
- ↑ Ibn Jauzi – "Nawasikhul Qur’an", Shafi na 225
- ↑ San'ani – al-Musannaf, Jild 5, Shafi 397. Shaykh Tusi – al-Tibyan, Jild 7, Shafi 321. Hakim Nishaburi – al-Mustadrak, Jild 2, Shafi 246. Sayyid Sabiq – Fiqh al-Sunnah, Jild 2, Shafi 620. Hasani – Tariikh al-Fiqh al-Ja’fari, Shafi 56.
- ↑ Najafi – Jauharul Kalam, Jild 21, Shafi 57 (1362 H.S). Sabzuwari – Muhadh-dhabul Ahkam, Jild 15, Shafi 119 (1416 H.Q). Qurtubi – al-Jami’ li Ahkam al-Qur’an, Jild 12, Shafi 68 (1405 H.Q).
- ↑ Shafi’i Baydawi – Anwar al-Tanzil (Tafsirin Baydawi), Jild 4, Shafi 73 (1418 Hijira Qamariyya)
- ↑ Sheikh Tusi – al-Tibyan (Jild 9, Shafi 252). Ibn Jauzi – Nawasikhul Qur'an (Shafi 225)
- ↑ Sheikh Tusi – Tafsir al-Tibyan, Jild 1, Shafi 407 (1409 H.Q)
- ↑ Abdulrahman bin Nasir al-Sa’di – Taysir al-Karim al-Rahman (1418 Hijira Qamariyya), Shafi 539
- ↑ Ibn Jauzi – Nawasikhul Qur’an, Shafi 225
- ↑ Fassarar Hausa ta al-'Ayni – Umdatul Qari
- ↑ Wahidi Nishaburi – Asbab al-Nuzul, Shafi 208 (1388 H.Q). Ahmad ibn Hanbal – Musnad Ahmad, Jild 1, Shafi 216. Imam Tirmidhi – Sunan at-Tirmidhi, Jild 5, Shafi 7 (1403 H.Q)
- ↑ Allama al-Majlisi – Bihar al-Anwar, Jild 19, Shafi 183 (1403 Hijira Qamariyya)
- ↑ Ibn Shahrasub – Manaqib Aal Abi Talib, Jild 1, Shafi 161 (1376 H.Q)
- ↑ al-Sam’ani – Tafsīr al-Sam‘ānī, Jild 3, Shafi 416 (1418 Hijira Qamariyya)
- ↑ al-Firuzabadi – Tanwīr al-Miqbās min Tafsīr Ibn ʿAbbās, Shafi 276
- ↑ Ayatollah Hussain Ali Montazeri – Dirasāt fī Wilāyat al-Faqīh, Jild 1, Shafi 121 (1408 H.Q)
- ↑ Sarkasi – Al-Mabsūṭ, Juz’i na 10, Shafi na 2 (1406 H.Q)
- ↑ Imam Shāfi’ī – Al-Umm, Shafi na 169 (1403 H.Q)
- ↑ Jawahiri – Buḥūth fī al-Fiqh al-Muʿāṣir, Jild 6, Shafi na 232 (1429 H.Q)
- ↑ Fyaz Kashani – Al-Wafi, Jild 15, Shafi 70 (1411 H.Q). Majlisi – Rawdat al-Muttaqīn, Jild 3, Shafi 164
- ↑ Jawāhirī – Buḥūth fī al-Fiqh al-Muʿāṣir, Jild 6, Shafi na 239 (1429 H.Q)
- ↑ Qummi – Tafsīr Kanz al-Daqā’iq, Jild 9, Shafi 102 (1411 H.Q)
- ↑ Shawāhid al-Tanzīl, Jild 1, Shafi na 520 (1411 H.Q)
- ↑ Ali ibn Ibrahim al-Qummi – Tafsīr al-Qummi, Jild 2, Shafi na 84 (1387 H.Q)
- ↑ Ibn Qulawayh – Kāmil al-Ziyārāt, Shafi na 135 (1417 H.Q)
- ↑ Naʿmānī – Al-Ghayba, Shafi na 248 (1422 H.Q). Nūrī – Khātimat al-Mustadrak, Jild 1, Shafi na 125 (1415 H.Q)
- ↑ Alī al-Kūrānī – Muʿjam Aḥādīth al-Imām al-Mahdī, Jild 5, Shafi na 264 (1411 H.Q)
- ↑ Ali ibn Ibrahim al-Qummi – Tafsīr al-Qummi, Jild 2, Shafi na 84 (1387 H.Q)
- ↑ Ayatollah Muhammad Reza Golpāyegānī – Irshād al-Sāʾil, Shafi na 203 (1403 H.Q)
- ↑ Aḥmad al-Qaṭīfī – Rasā'il Āle Ṭawq, Jild 1, Shafi na 126 (1422 H.Q)
- ↑ Ibn Abī Shaybah – Al-Muṣannaf, Jild 8, Shafuka 585 & 681 (1409 H.Q)
- ↑ Kanzul-Ummāl na Alā’uddīn al-Muttaqī al-Hindī, 1409 Hijira – Juz’i na 2, shafuffuka 470 da 471. Tārīkh Madīnat Dimashq na Ibn ʿAsākir, 1415 Hijira – Juz’i na 24, shafi na 88
- ↑ Tafsīr al-ʿAyāshī, Juz’i na 2, Shafuka 79–82
- ↑ Ibn Shahrāshūb, Manāqib Āl Abī Ṭālib, Juz’i na 2, Shafi na 359
- ↑ Ibn Shahrāshūb (Juz’i na 3, Shafi na 86) da Nūrī (Juz’i na 3, Shafi na 328). Mustadrak al-Wasā’il – Juz’i na 3, Shafi na 328:
- ↑ A Tārīkh al-Ṭabarī – Jild 6, Shafi 25. A al-Kāmil fī al-Tārīkh – Jild 5, Shafi 358:
Nassoshi
- Ibn Abī Shaybah – Al-Muṣannaf: Majmu'ar hadīth da ra'ayoyi na sahabbai da tabiʿai; yana da muhimmanci a fiqhu da tarih.
- Ibn al-Athīr – Al-Kāmil fī al-Tārīkh: Littafin tarihi da ke bayani dalla-dalla kan siyasar farko ta Islam.
- Ibn al-Jawzī – Nawāsikh al-Qur’ān: Bayanai kan ayoyin da suka soke wasu ayoyi a Qur’ani, da misalai daga jihād da hukunci.
- Ahmad ibn Ḥanbal – Musnad Ahmad: Majmu'ar hadīth daga Manzon Allah (SAW), da sahabbai.
- Ibn Shahrāshūb – Manāqib Āl Abī Ṭālib: Tattara tarihin Ahlul-Bayt, da misalai daga jihādul-difā’i.
- Ibn ʿArabī – Aḥkām al-Qur’ān: Tafsīri mai zurfi kan hukumomin da suka fito daga ayoyin Qur’ani.
- Ibn ʿAsākir – Tārīkh Madīnat Dimashq: Tarihi da ruwayoyi kan ayyukan sahabbai da Imamai.
- Ibn Qulūyah – Kāmil al-Ziyārāt: Tattara ruwayoyi kan ziyāra da hurumin Ahlul-Bayt.
- Al-ʿAynī – ʿUmdat al-Qārī: Sharhi kan Ṣaḥīḥ al-Bukhārī, tare da fahimtar fiqh.
- Al-Bayhaqī – Maʿrifat al-Sunan wa al-Āthār: Majmu'ar hadīth da fiqhu.
- Al-Tirmidhī – Sunan al-Tirmidhī: Ɗaya daga littattafan Sittah na Ahlus-Sunnah.
- Ḥasan al-Jawāharī – Buḥūth fī al-Fiqh al-Muʿāṣir: Nazari da ruwayoyi fiqhu a zamaninmu.
- Al-Ḥākim al-Naysābūrī – Al-Mustadrak ʿala al-Ṣaḥīḥayn: Littafi da ya tattara hadīth da suka cika sharuddan Ṣaḥīḥ al-Bukhārī da Ṣaḥīḥ Muslim.
- Al-Ḥaskānī – Shawāhid al-Tanzīl: Ruwayoyi da dalilai na tafsīrin Qur’ani, musamman dangane da ʿAhlul-Bayt.
- Tariikhul-Fiqh al-Jaʿfari – Hasani, Hashim Maʿruf An bincika littafin nan da Muhammad Jawad Mughniyah. An wallafa shi ba tare da ambaton wuri da shekara ba, ta Dar al-Nashr lil-Jamiʿiyyin. Fassara: Tarihin Fiqhun Jaʿfari – Hasani Hashim Maʿruf, tare da gyara daga Muhammad Jawad Mughniyah, ba a bayyana wurin bugawa da shekarar ba, Dar al-Nashr lil-Jamiʿiyyin
- Āyāt-e Nāmdār – Khorasani, Ali Wannan yana cikin Dāʾirat al-Maʿārif al-Qurʾān al-Karīm, an wallafa shi a Qom ta Bustan-e-Ketab a shekarar 1382 Hijri Shamsi. Fassara: Ayoyin da suka shahara – Ali Khorasani, cikin Dāʾirat al-Maʿārif al-Qurʾān al-Karīm, Qom, Bustan-e-Ketab, 1382 H.S
- Muhadhdhab al-Aḥkām fī Bayān al-Ḥalāl wa al-Ḥarām – Sabzawari, Abdul-Ali An wallafa shi ba tare da ambaton wuri ba, ta Maktab Ayatollah al-ʿUzma al-Sayyid al-Sabzawari a shekarar 1416 Hijri Qamari. Fassara: Tsabtace Hukunci a Bayanin Halal da Haram – Abdul-Ali Sabzawari, ba a bayyana wurin bugawa ba, Maktab Ayatollah al-ʿUzma al-Sayyid al-Sabzawari, 1416 H.Q.
- Muhadhdhab al-Aḥkām fī Bayān al-Ḥalāl wa al-Ḥarām – Sabzawari, Abdul-Ali An wallafa shi ba tare da ambaton wuri ba, ta Maktab Ayatollah al-ʿUzma al-Sayyid al-Sabzawari a shekarar 1416 Hijri Qamari. Fassara: Tsabtace Hukunci a Bayanin Halal da Haram – Abdul-Ali Sabzawari, ba a bayyana wurin bugawa ba, Maktab Ayatollah al-ʿUzma al-Sayyid al-Sabzawari, 1416 H.Q.
- Al-Mabsūṭ – Sarakhsi, Shams al-Din An wallafa shi a Beirut ta Dar al-Maʿrifah a shekarar 1406 Hijri Qamari. Fassara: Al-Mabsut – Shams al-Din al-Sarakhsi, Beirut, Dar al-Maʿrifah, 1406 H.Q.
- Ysīr al-Karīm al-Raḥmān fī Kalām al-Mannān – Saʿdi, Abdulrahman bin Nasir An bincika littafin nan da Ibn ʿUthaymin, an wallafa shi a Beirut ta Muʾassasat al-Risālah a shekarar 1421 Hijri Qamari. Fassara: Sauƙaƙe Alƙawarin Mai Rahama cikin Maganar Mai Kyauta – Abdulrahman bin Nasir al-Saʿdi, tare da gyara daga Ibn ʿUthaymin, Beirut, Muʾassasat al-Risālah, 1421 H.Q.
- Tafsīr al-Samʿānī – Samʿānī, Mansur An bincika littafin nan da Yasir bin Ibrahim da Ghunaym bin Abbas, an wallafa shi a Riyadh ta Dar al-Waṭan a shekarar 1418 Hijri Qamari. Fassara: Tafsirin Samʿānī – Mansur Samʿānī, tare da gyara daga Yasir bin Ibrahim da Ghunaym bin Abbas, Riyadh, Dar al-Waṭan, 1418 H.Q
- Fiqh al-Sunnah – Sayyid Sabiq An wallafa shi a Beirut ta Dar al-Kitab al-‘Arabi, bugun na uku, shekara ta 1397 Hijri Qamari. Fassara: Fiqhun Sunnah – Sayyid Sabiq, bugun na uku, Beirut, Dar al-Kitab al-‘Arabi, 1397 H.Q
- Anwār al-Tanzīl wa Asrār al-Taʾwīl (Tafsīr al-Bayḍāwī) – ʿAbdullāh ibn Muḥammad al-Shāfiʿī al-Bayḍāwī An wallafa shi a Beirut ta Dar al-Fikr a shekara ta 1418 Hijri Qamari. Fassara: Hasken Saukar Alƙalami da Sirrin Fassara – Tafsirin Bayḍāwī, Beirut, Dar al-Fikr, 1418 H.Q
- Al-Umm – Muḥammad ibn Idrīs al-Shāfiʿī An wallafa shi a Beirut ta Dar al-Fikr a shekara ta 1403 Hijri Qamari. Fassara: Ummul-Fiqh – Muḥammad ibn Idrīs al-Shāfiʿī, Beirut, Dar al-Fikr, 1403 H.Q
- Al-Tibyān fī Tafsīr al-Qurʾān – Shaykh al-Ṭūsī, Muḥammad An gyara shi ta Aḥmad Ḥabīb Qaṣīr ʿĀmilī, an wallafa shi ba tare da ambaton wuri ba, ta Maktab al-Iʿlām al-Islāmī, shekara ta 1409 Hijri Qamari. Fassara: Bayani a Fassarar Alƙur’ani – Shaykh Ṭūsī, tare da gyara daga Aḥmad Ḥabīb Qaṣīr ʿĀmilī, ba a bayyana wurin bugawa ba, Maktab al-Iʿlām al-Islāmī, 1409 H.Q.
- Tahdhīb al-Aḥkām fī Sharḥ al-Muqniʿa – Shaykh al-Ṭūsī, Muḥammad An gyara shi ta Ḥasan Mūsawī, an wallafa shi a Tehran ta Dar al-Kutub al-Islāmiyya, bugun na huɗu, shekara ta 1365 Hijri Shamsi. Fassara: Tsabtace Hukunci a Sharhin Muqniʿa – Shaykh Ṭūsī, tare da gyara daga Ḥasan Mūsawī, Tehran, Dar al-Kutub al-Islāmiyya, bugun na huɗu, 1365 H.S.
- Al-Muṣannaf – ʿAbd al-Razzāq al-Ṣanʿānī An gyara shi ta Ḥabīb al-Raḥmān al-Aʿẓamī, an wallafa shi ba tare da ambaton wuri da shekara ba, ta Al-Majlis al-ʿIlmī. Fassara: Majmu’ar Hadisai – ʿAbd al-Razzāq al-Ṣanʿānī, tare da gyara daga Ḥabīb al-Raḥmān al-Aʿẓamī, ba a bayyana wurin bugawa da shekarar ba, Al-Majlis al-ʿIlmī.
- Al-Mīzān fī Tafsīr al-Qurʾān – Muḥammad Ḥusayn al-Ṭabāṭabāʾī An wallafa shi a Qom ta Muʾassasat al-Nashr al-Islāmī a shekara ta 1412 Hijri Qamari. Fassara: Mizani a Fassarar Alƙur’ani – Muḥammad Ḥusayn al-Ṭabāṭabāʾī, Qom, Muʾassasat al-Nashr al-Islāmī, 1412 H.Q
- Tārīkh al-Umam wa al-Mulūk (Tārīkh al-Ṭabarī) – Muḥammad ibn Jarīr al-Ṭabarī An wallafa shi a Beirut ta Muʾassasat al-Aʿlamī lil-Maṭbūʿāt
- Tanwīr al-Miqbās min Tafsīr Ibn ʿAbbās – Muḥammad ibn Yaʿqūb al-Fīrūzābādī An wallafa shi a Beirut ta Dār al-Kutub al-ʿIlmiyyah, ba tare da ambaton shekara ba. Fassara: Haske ga Tafsirin Ibn ʿAbbās – Muḥammad ibn Yaʿqūb al-Fīrūzābādī, Beirut, Dār al-Kutub al-ʿIlmiyyah
- Al-Wāfī – Muḥammad Muḥsin Fayḍ Kāshānī An gyara shi ta Ḍiyāʾuddīn Ḥusaynī, an wallafa shi a Isfahan ta Maktabat al-Imām Amīr al-Muʾminīn, shekara ta 1411 Hijri Qamari. Fassara: Al-Wāfī – Muḥammad Muḥsin Fayḍ Kāshānī, tare da gyara daga Ḍiyāʾuddīn Ḥusaynī, Isfahan, Maktabat al-Imām Amīr al-Muʾminīn, 1411 H.Q
- Al-Jāmiʿ li-Aḥkām al-Qurʾān – Muḥammad al-Qurṭubī An gyara shi ta Aḥmad ʿAbd al-ʿAlīm, an wallafa shi a Beirut ta Dār Iḥyāʾ al-Turāth al-ʿArabī, shekara ta 1405 Hijri Qamari. Fassara: Majmu’ar Hukuncin Alƙur’ani – Muḥammad al-Qurṭubī, tare da gyara daga Aḥmad ʿAbd al-ʿAlīm, Beirut, Dār Iḥyāʾ al-Turāth al-ʿArabī, 1405 H.Q.
- Rasāʾil Āl Ṭawq – Aḥmad ibn Shaykh al-Qaṭīfī An gyara shi ta Shirkah Dār al-Muṣṭafā, an wallafa shi a Dimashq ta Shirkah Dār al-Muṣṭafā li-Iḥyāʾ al-Turāth, shekara ta 1422 Hijri Qamari.
- Tafsīr al-Qummī – ʿAlī ibn Ibrāhīm al-Qummī An gyara shi ta Ṭayyib Mūsawī Jazāʾirī, an wallafa shi a Qom ta Dār al-Kitāb, bugun na huɗu,
- Tafsīr Kanz al-Daqāʾiq wa Baḥr al-Gharāʾib – Muḥammad ibn Muḥammad Riḍā al-Qummī An gyara shi ta Ḥusayn Dargāhī, an wallafa shi a Tehran ta Maʾsasat al-Ṭabʿ wa al-Nashr na Ma'aikatar Al'adu, shekara ta 1411 Hijri Qamari.
- Uṣūl al-Kāfī – Muḥammad ibn Yaʿqūb al-Kulaynī An yi taƙaitaccen sharhi ta ʿAlī Akbar Ghafārī, an wallafa shi ba tare da ambaton wuri ba, ta Dār al-Kutub al-Islāmiyyah, shekara ta 1367
- Jawāhir al-Kalām fī Sharḥ Sharāʾiʿ al-Islām – Muḥammad Ḥasan al-Najafī An gyara shi ta Maḥmūd Qūchānī, an wallafa shi a Tehran ta Dār al-Kutub al-Islāmiyyah, bugun na biyu, shekara ta 1366 Hijri Shamsi
- Al-Ghaybah – Muḥammad ibn Abī Zaynab al-Nuʿmānī An gyara shi ta Fāris Ḥassūn, an wallafa shi a Qom ta Anwār al-Hudā, shekara ta 1422 Hijri Qamari
- Khātimat al-Mustadrak – Ḥusayn al-Nūrī An gyara shi ta Muʾassasat Āl al-Bayt, an wallafa shi a Qom ta Muʾassasat Āl al-Bayt, shekara ta 1415 Hijri Qamari. Fassara: Ƙarshe ga Mustadrak – Ḥusayn al-Nūrī, tare da gyara daga Muʾassasat Āl al-Bayt, Qom, 1415 H.Q.
- Mustadrak al-Wasāʾil wa Mustanbaṭ al-Masāʾil – Ḥusayn al-Nūrī An gyara shi ta Muʾassasat Āl al-Bayt, an wallafa shi a Beirut ta Muʾassasat Āl al-Bayt, bugun na biyu, shekara ta 1408 Hijri Qamari. Fassara: Cikakken Ƙarin Wasāʾil da Masāʾil – Ḥusayn al-Nūrī, tare da gyara daga Muʾassasat Āl al-Bayt, Beirut, bugun na biyu, 1408 H.Q.
- Asbāb Nuzūl al-Āyāt – ʿAlī ibn Aḥmad al-Wāḥidī al-Nayshābūrī An wallafa shi a Cairo ta Muʾassasat al-Ḥalabī wa Shurakāʾ, shekara ta 1388 Hijri Qamari. Fassara: Dalilan Saukar Ayoyi – ʿAlī ibn Aḥmad al-Wāḥidī al-Nayshābūrī, Cairo, Muʾassasat al-Ḥalabī wa Shurakāʾ, 1388 H.Q.