Makaman Kisan Ƙare Dangi
- Maƙalolin Wikishia ana wallafa su ne kan salo da tsari na makarantar Ahlul-Baiti, domin samun bayani game da sauran sasanni batutuwa, ke nemi wasu madogaran
Makamin kisan ƙare dangi, (Larabci: أسلحة الدمار الشامل) wasu makamai ne da amfani da su yake haifar da asarar rayukan dubban fararen hula da lalata mahalli da ba za a iya dawo da shi yadda yake ba, a ra'ayin malaman fiƙihu na Shi'a, haramun ne fara amfani da wannan makami, ma'ana gabanin abokan gaba su fara amfani da shi kan muminai, amma game da amfani da wannan makami a halin larura. Ma'ana lokacin da ba za a samu nasara ba kan maƙiya dole sai ta hanyar amfani da shi, malamai suna da mabambantan ra'ayi. Wasu sun ce ya halasta a yi amfani da wannan makami, wasu kuma sun yi fatawa haramcin amfani da shi hatta cikin irin wannan yanayi.
Bisa la'akari da ɓullowar sabbin samfuran makaman kisan ƙare dangi, misalin makamin nukiliya da makamai masu guba, ba'arin malaman fiƙihu sun yi fatawa kansu, daga jumlar malamai da suka yi fatawa akwai misalin Sayyid Ali Khamna'i jagoran jamhuriyar Muslunci ta Iran kuma daga cikin maraji'an taƙlidi na Shi'a, cikin fatawar haramcin ƙera makamin nukiliya da amfani da shi, sun yi la'akari da nau'in wannan makamai matsayin barazana ga mutane, kuma amfani da shi ko ajiye shi haramun ne.
Gabatarwa Da Kuma Muhimmanci
Makaman kisan ƙare dangi, makamai ne da lokacin da ake amfani da su cikin kai hare-hare kan sansanonin soja suna kaiwa ga asarar rayukan fararen da lalata mahalli da ba za a iya dawo shi da yadda yake a baya ba.[1]
Batun makaman kisan ƙare dangi wanda lokacin amfani da shi akwai tsammanin kashe fararen hula da suka haɗa da ƙananan yara, tsofaffi da ma fursunonin yaƙi, tun farkon Muslunci a lokacin Annabi (S.A.W) akwai waɗannan makamai, kuma riwayoyin Shi'a sun magana kan wannan makamai.[2] Abul ƙasim Ali Dusti, malamin Hauza da yake ba da darasin kharijul fiƙhi a birnin Ƙum, ya ba da rahoto cewa malaman fiƙihu na Shi'a, alal aƙalla ƙarni goma da ya gabata, an yi bahasi kan wannan mas'ala..[3]
A ƙarni na goma sha huɗu da na goma sha biyar, an samu ɓullar sabbin nau'ukan makaman kisan ƙare dangi misalin makamin nukiliya da makamai masu guba[4] wanda suka haifar da mummunar ɓarna da ba a taɓa ganin irinta ba a baya, da wannan dalili ne aka yi ɗauki wannan mas'ala cikin jerin layin sabbin mas'alolin fiƙihu.[5]
Hukuncin Shari'a Kan Makaman Kisan Ƙare Dangi
Malaman fiƙihu na Shi'a sun yi bincike kan mas'alar makaman kisan ƙare dangi daga adadin zawiyoyi: fara amfani da wannan makamai (Kafin maƙiya su fara amfani da shi) da ƙera da ajiye shi da kuma amfani da shi a halin larura:
Bisa bincike, baki ɗayan malaman fiƙihu na Shi'a sun haramta amfani da makaman kisan ƙare dangi.[6] Abul Ƙasim Ali Dusti ya ce: alal aƙalla ƙarni goma da ya wuce sun yi fatawar haramta amfani da makaman kisan ƙare dangi da suke haifar da kisan dubban mutane da halaka dabbobi da lalata mahalli.[7]
Game da ƙera wannan makamai da ajiye su, sakamakon ɓullar sabbin nau'ukam makaman kisan ƙare dangi,[8] wasu jama'a daga malaman fiƙihu daga jumlarsu akwai Ayatullahi Sayyid Ali Khamna'i, sun yi fatawar haramta ƙera ko amfani da makaman nukiliya da makaman isan ƙare dangi, sun kuma bayyana cewa waɗannan makamai barazana ne ga ɗan Adam[9] Ba'arin maraji'an taƙlidi misalin Makarim Shirazi, Nuri Hamadani, Jafar Subhani da Jawadi Amoli sun goyi bayan wannan ra'ayi na fiƙihu.[10] Makarim Shirazi, ƙera makaman kisan ƙare dangi da ajiye su ya saɓawa tsarin halittar ɗan Adam.[11]
Ra'ayin malaman Shi'a ya bambanta game da samun kai cikin halin larura , ko lokacin da nasarar musulmi kan maƙiya ta dogara ne da amfani da makaman kisan ƙare dangi: ba'arin malaman fiƙihu na Shi'a, misalin Muhaƙƙiƙ Hilli (Rayuwa: 602-676) Shaik ɗusi (Rayuwa: 385-460) da Shahis Sani (Rayuwa: 911-955 ko 965) suna da ra'ayin cewa amfani da irin waɗannan makamai a irin wannan wurare,[12] Kishiyarsu, Agha Diya'u Iraƙi (Rayuwa: 1278-1361) yana da ra'ayin cewa amfani gubar da ake yin makaman kisan ƙare dangi haramun ne ko da kuwa nasara da galaba kan abokan gaba ya doga da wannan makamai.[13]
Bayanin kula
- ↑ Rostami Najafabadi, Farhadian, "Jurme Budane Iqdam Alaihi Bashriyyat Beh Wasile Silahe Haste'i Az Negahe Fiqhe Ba Ruyeerdi Fatawa Maqam Mu'azzam Rahbari, shafi. 103; Abdi et al., “Barsi Tahlili Mafhume Silahehaye Kushtare Jam'i wa tadbiki AN Bar Didgahe Islami Ba Taakidi Bar Araye Maqam Mu'azzam Rahbari,” shafi. 720.
- ↑ Tabataba'i, Riyad Al-Mas'eel, 1418H, juzu'i. 8, shafi. 70.
- ↑ «بررسی تحریم سلاح کشتار جمعی در تاریخ تشیع»، Ayatullah Alidoust Information Center.
- ↑ Abdi Wa Digaran, Barsi Tahlili Mafhume Silahaye Kushtare Jam'i Wa Tadbiki AN Bar Didgahe Islami Ba Taakid Bar Araye Maqam Mu'azzam Rahbari, shafi. 717; Rabbani Wa Digaran., Barsi Adille Jawaz Ya Hurmat Taulid Wa Anbashat Silahaye Kushtare jam'i, shafi na. 90.
- ↑ Bagherzadeh Meshkibaf, Anasir Taayin Konande Dar Halli Masa'il Mustahadasa, shafi. 50.
- ↑ Rostami Wa Digaran, "Jurme Budane Iqdame Alaihi Bashariyat Beh Wasile Silahaye Haste'i Az Negahe Fiqhi shafi 110.
- ↑ «بررسی تحریم سلاح کشتار جمعی در تاریخ تشیع»،Ayatullah Alidoust Information Center.
- ↑ Abdi Wa Digaran, Barsi Tahlili Mafhume Silahaye Kushtare Jam'i Wa tadbiki An Bar Didga Islami Ba taakid Bar Araye Maqam Mu'azzam Rahbari," shafi. 717; Rabbani Wa Digaran, Barsi Adille Jawaz Ya Hurmat Taulid Wa Anbashte Silahaye Kushtare Jam'i, shafi na. 90.
- ↑ «پیام به نخستین کنفرانس بینالمللی خلع سلاح هستهای و عدم اشاعه»،Ofishin kiyayewa da buga ayyukan Ayatullah Khamenei.
- ↑ «تحریم سلاح کشتار جمعی در تاریخ تشیع»، Kamfanin Dillancin Labarai na ISNA.
- ↑ Makarem Shirazi, Mabani Tahrime Silahaye Kustare Jam'i Az Manzare Mu'azzam lahu, Baligh News
- ↑ Mohaqiq Hilli, Shara'i al-Islam, 1418 AH, juzu'i. 1, shafi. 283; Tusi, al-Mabsut, Juz. 2, shafi. 11; Shahid Thani, Masalak al-Afham, 1413 AH, juzu'i. 3, shafi. 25.
- ↑ Agha Zia Iraqi, Sharh Tabsarat al-Mu'tallimeen, 1414 AH, Juz. 4, shafi. 404.
Nassoshi
- Agha Zia Iraqi, Ali bin Mulla Muhammad, Sharhu Tabsiratil Muta'allimin, Qum, Ofishin Daba'ar Musulunci, 1414H.
- Bagherzadeh Meshkhibaf, Mohammad Taghi,«عناصر تعیینکننده در حل مسائل مستحدثه»،Mujallar Kaweshi No Dar Fiqih, Qum, Ofishin yada farfagandar Musulunci na Makarantar Sakandare na 43, bazara 2005.
- «تحریم سلاح کشتار جمعی در تاریخ تشیع»،Kamfanin Dillancin Labarai na ISNA, ranar bugawa: Yuni 17, 2014, ranar ziyarta: Janairu 10, 2023.
- Khamenei, Sayyid Ali,«بیانات در دیدار دانشمندان هستهای»،Yanar Gizo na bayanai na ofishin kiyayewa da buga ayyukkan Jagora Ayatullah Khamenei, ranar shiga: 2 ga Maris, 2011, ranar ziyarar: 29 ga Oktoba, 2024.
- Hurr Amili, Muhammad bin Hassan, Wasa'lush Shi'a Ila Tahsil Masa'il Shari'a, Qum, Mu'assasa Ahlul Baiti, Amincin Allah ya tabbata a gare su, 1409H..
- Mohaqiq Hilli, Ja’afar bn Hassan, Shara'i'il Islam Fi Masa'ilil Halal Wal Haram, Qum, Cibiyar Ismaili, 1408H.
- Rabbani, Mehdi and Abbasali Rouhani,«بررسی ادله جواز یا حرمت تولید و انباشت سلاحهای کشتار جمعی»،Jaridar Kwata-kwata na Shari'a da Ka'idoji, Lamba 123, 2020.
- Rostami Najafabadi, Hamed da wasu، «جرم بودن اقدام علیه بشریت بهوسیله سلاحهای هستهای از نگاه فقه»،Jaridar kwata-kwata Fiqhu da Hakkoki Shari'ar Musulunci, Lamba 4, 2020.
- Shaheed Thani, Zain al-Din bin Ali, Masalik al-Afham ila Tankih Shaaree al-Islam, Qum, Islamic Encyclopaedia Foundation, 1413 AH.
- Tabataba'i, Sayyid Ali bn Muhammad, Riyad al-Mas'eel fi Tahqiq al-Ahkam al-Bid dala'il, Qom, Mu'assasa Al-Bait (AS) 1418H.
- Tousi, Muhammad bin Hassan, Al-Mabsut fi Fiqh al-Imamiyah, Sayyid Mohammad Taqi Kashfi, Tehran, Al-Mortazawiyya School for Revival of Al-Jaafari's Antiquities, 1387 AH.
- Abdi, Hassan da Mohammad Javad Hashemi,«بررسی تحلیلی مفهوم سلاحهای کشتار جمعی و تطبیق آن بر دیدگاه اسلامی با تأکید بر آرای مقام معظم رهبری امام خامنهای»، Mujallar Kwata-kwata, Siyasa, fitowa ta 3, 2018.
- مکارم شیرازی، ناصر، «مبانی تحریم سلاحهای کشتار جمعی از منظر معظم له»،Labaran Baligh, kwanan wata ziyara: Oktoba 19, 1403.