Wajibi Aini
Wajibi aini (Larabci: الوجب العيني) wani nau'i ne daga wajiban addini da ya zama dole dukkanin mukallafai su sauke shi. Wajibi aini kishiya ne na wajibi kifa'i, wanda idan wasu suka sauke shi sun ɓauke was aura, babu buƙata sai sun ui, sallolin yau da kullun, azumi da zakka su cikin wajibi aini.
A cewar malaman usulul fiƙhi, lokacin da ake da shakka shin wajibi kifa'i ne ko wajibi aini, a irin wannan hali dole a yi gini kan kasancewa wajibi aini.
Bayani Na Fiƙihu
Wajibi aini, wajibi ne da ake cewa sauke shi ya hau wuyan baki ɓayan mukallafai; ma'ana mukallafi ba zai wadatu da saukewar da wasu suka yi ba, dole shi da kansa ya sauke nauyin da yake wuyansa.[1] Sallolin yau da kullun, azumi, hajji[2] da zakka[3] su na cikin wajibai aini.
Bambanci Da Wajibi Kifa'i
Wajibi aini yana kishiyantar wajibi kifa'i bai magana da wani keɓantaccen mutum; ma'ana a mahangar shari'a duk wanda ya aikata ya wadatar. Saboda haka idan wasu daga mukallafai suka yi, sun ɓaukewa sauran mukallafai;[4] misalin umarni da kyakkyawa da hani da mummuna, jihadi, amsa sallama[5] likkafi da binne gawa da sallar gawa da tseratar da ran mutum.[6]
A cewar malaman usulul fiƙhi, dalilin da ya sanya a cikin wajibi kifa'i idan wasu suka yi su na ɓaukewa saura, shi ne cewa akwai buƙatar su yi wannan aiki dama kuma yin sa yake da muhimmanci ba wai wanda zai yi ba.[7]
Kokwanto Cikin Kasancewar Aiki Wajibi Aini Ne Ko Kifa'i
Malaman usulul fiƙhi suna cewa akwai cikin wurare da ba mu da dalili kan cewa umarnin da Allah ya yi shin wajibi ne aiki ko kifa'i, a irin wannan hali dole mu yi gin ikan kasancewa aini;[8] Saboda hankali ya na hukunci a lokacin da ba mu samu nutsuwa da saukewar wasu za ta wadatar mana daga sauke wa da kan mu, to fa wajibi ne mu sauke wannan nauyi da kan mu.[9]
Ku Duba
Bayanin kula
- ↑ Muzaffar, Usul al-Fiqh, 1430 AH, juzu'i. 1, p. 140; Hosseini, al-Dalil al-Fiqh, 2007 AD, shafi. 309; Vela'i, Farhange Tashrihi Istilahate Usul, 1387 AH, shafi. 336.
- ↑ Hosseini, Al-Dalil Al-Fiqhi, 2007, shafi. 301.
- ↑ Al-Ajam, Mausu'atu Mustakahat usulil Fiqhi Indal Muslimin, 1998, juzu'i na 2, shafi na 1690.
- ↑ Muzaffar, Usul al-Fiqh, 1430 AH, juzu'i. 1, p. 140; Hosseini, al-Dalil al-Fiqh, 2007 AD, shafi. 309; Vela'i, Farhange Tashrihi Istilahate Usul, 1387 AH, shafi. 337.
- ↑ Al-Ajam, Mausu'atu Mustakahat usulil Fiqhi Indal Muslimin, 1998, juzu'i na 2, shafi na 1690.
- ↑ Muzaffar, Usul al-Fiqh, 1430 AH, juzu'i. 1, shafi. 140.
- ↑ Misali duba Muzaffar, Usul al-Fiqh, 1430 AH, juzu'i. 1, shafi na 140-141.
- ↑ Misali duba Muzaffar, Usul al-Fiqh, 1430 AH, juzu'i. 1, shafi. 124; Akund Khorasani, Kifayat al-Usul, 1409 AH, shafi. 252; Sobhani, Al-Wasit, 1388 AH, juzu'i. 1, shafi. 100.
- ↑ Muzaffar, Usul al-Fiqh, 1430 AH, juzu'i. 1, shafi. 124.
Nassoshi
- Akhund Khorasani, Muhammad Kazim, Kifayat al-Usul, Qum, Al-Bait Institute, bugun farko, 1409H.
- Al-Ajam, Rafiq, Mausu'atu Mustlahate Usul iqhi Indal Muslimin, Beirut, Lebanon Publishers, 1998 Miladiyya.
- Husseini, Muhammad, Al-Dalil al-Fiqhi: Tadbiqat Fiqhiyya Limustalahat Ilmil Usul Dimashqi, Ibn Idris al-Hilli Center for Jurispruddential Studies, bugu na farko, 2007 AD.
- Subhani Tabrizi, Jafar, Al-Wasit fi Usul al-Fiqh, Qum, Cibiyar Imam Sadik, bugu na hudu, 1388 miladiyya.
- Muzaffar, Muhammad Reza, Usulul Fiqh, Qum, Islamic Publications, bugu na biyar, 1430H.
- Welai, Isa, Farhange Tashrihi Istilahat Usul,Tehran, Nay Publications, bugu na shida, 1387 miladiyya.