Kankare zunubai

Daga wikishia

Kankare zunubai (Larabci: تكفير الذنوب) ko kuma mu ce goge su ko kawar da duk wani tasirin su a ranar Alkiyama a kan kufaifayin ladan ayyuka nagargaru, kalma ce da ake fadin ta da sunan Kankare Zunubi, hakika a cikin Alkur’ani da Hadisan Muslunci an bayyana Imani, Ayyuka nagari, Tuba, Jihadi, Sadaka a boye, da kuma ibada a matsayin abubuwan da suke sanya a kankare zunubai.

Kankare zunubai wani bahasi ne na ilimin Kalam da masana ilimin suka ajiye shi karkashen bahasin su mai take Ihbadu (lalacewar ayyuka) da kuma Takfir (kankare zunubai), gurbacewar ayyuka da halascin haduwar lada da ukuba. Imamiyya da Asha’ira suna karbar batun Takfir a iya zawiyya zunuban da aka ambace su cikin Kur’ani da hadisai, amma Mu’utazilawa sun tafi kan cewa Takfir yana kankare da goge dukkanin zunubai, Malam Kalam na Imamiyya da Ash'ariyya sabanin Mu’utazilawa sun kafa hujja da ayoyin Kur’ani da suke tabbatar da cewa ubangiji yana ware hisabin ladan kyawawan ayyuka da kuma ware ukuba kan munanan ayyuka kowanne daban-daban.

Sanin Mafhumi

Takfir yana nuni lullubewa da boyewa [1] da wannan ma’ana ne wanda yake inkarin ni’imomin Allah ake kiransa da Kafiri [2] Takfir a ilimin Kalam yana bada ma’anar goge ukuba cikin kufaifayi da tasirin kyawawan ayyuka, da wannan dalili ne Takfiri yana matsayin Ihbadu wanda yake daukar ma’anar lalacewar kyawawan ayyuka. [3] Takfir yana daukar ma’anar jingina kafirci ga musulmi, ana kiransa da kafirta ma’abota Alkibla. [4]

Sabubba

Alkur’ani da riwayoyi sun yi bayani kan sabubban Kankare da goge zunubi, daya daga ciki akwai Imani da kuma ayyuka nagari, [5] Tuba, [6] nesantar aikata manya-manyan zunubai, [7] Sadaka a boye, Jihadi, [8] Ibada, [9] dukkanin su sabubba ne da suke kankare zunubi da goge shi, haka kuma riwaya ta bayyana cewa Shafa’a [10] da ziyartar Imam Husaini (A.S) [11] Karanta Kur’ani, [12] Sallar dare, [13] sabubba ne na kankare zunubai da goge su.

Takfir a cikin ilimin Kalam

Kankare zunubai bahasi ne na ilmin Kalam da ake yinsa tare da bahasin Ihbadu Amali [14] Malaman ilmul Kalam sun ajiye bahasin Takfir a jelar take misalin Ihbadu [15] (ihbadu wa Takfir) [16] gurbacewar ayyyuka [17] halascin haduwar lada da ukuba. [18] Wasu ba’arin Malaman Shi’a da Ahlus-sunna sun ajiye shi cikin mas’alar Ma’ad (makoma) [19] su kuma Mu’utazilawa sun sanya shi cikin bahasin wa’adu da wa’idu [20] Malaman ilmul Kalam sun yi ittifaki idan wani Kafiri ya muslunta, ba zai ayi masa azaba kan kafircin sa ba da kuma zunuban da ya aikata lokacin da yake Kafiri, [21] amma dangane da zunuban da Musulmi ya aikata akwai sabani ra’ayi tsakankanin su.

  • Mu’tazilawa sun yi imani da cewa ana kankare dukkanin zunubai da sunansu ya zo a Alkur'ani da Riwaya da ma wadanda bai zo ba, ba tare da togaciya ba, sun tafi kan cewa kyakkyawan aiki yana goge zunubai. [22]

Dalilin imanin su da wannan mahanga ya samo asali ne daga sakamakon sun fuskanci matsala lokacin da suke bahasi kan idan aiki ya cudanya da lada da ukuba hakan yana lazimta a lokaci guda daya mutum yana cancantar lada a ukuba su kuma a wurin su wannan wani abu ne da ba zai taba yiwuwa ba. [23] da wannan suka bijirar da bahasin Ihbadu wa Takfir. [24]

  • Yan shi’a da Asha’ariyya basu yarda da nazariyar (Ihbadu Kulli) [25]gurbacewar baki dayan aiki ba, sun tafi kan cewa kadai ayyukan kirki suna goge zunuban da sunayen su ya zo a cikin Kur’ani da riwaya, [26] a wannan fage yan shi’a tare da dogara da wasu ba’arin ayoyi daga cikin su aya 7-8 cikin suratul Zalzala : (duk wanda ya aikata aiki nagari gwargwadon kwayar komayya zai gan shi; duk wanda ya aikata aiki mummuna gwargwadon kwayar komayya zai gan shi) sun tafi kan cewa Allah yana lissafa kyawawan ayyuka da munana kowanne rarrabe ba tare da cudanyar su. [27]

Goge Zunubi ko kuma Goge Azaba kan Aikata shi

Shin Tafkir yana bada ma’anar goge zunubi ko kuma dauke ukubar sa, akwai sabanin Malamai kan wannan bahasi, Abu Ali Jubbayi daya daga cikin manyan Malaman Mu’utazilawa ya tafi kan cewa Takfir yana kankare zunubi da goge shi, amma shi kuma Abu Hashim Jubbayi ya ce: a’a azabar zunubin ake kankarewa da gogewa. [28] haka kuma wasu ba’arin Malaman Falsafa daga Musulmi suma sun tafi kan cewa Takfir shi ne kankare zunubi da goge shi, saboda sun yi Imani da cewa samammen abu babu lokacin zai zama babu shi, sun yi bayanin goge zunubi da surorin da za su a kasa:

  • duk wani zunubi ta fuskanin kasancewar sa zunubi wani abu ne da bai da samuwa ba a ma halicce shi ba, kamar dai yanda samuwar Mai zunubi take canjawa da idan ya Tuba zuwa wata samu daban
  • to haka lamarin yake miyagun ayyuka suna canjawa zuwa kyawawa. [29]

Bayanin kula

  1. Rageb, Mofradat, 1412 AH, shafi na 714.
  2. Rageb, Mofradat, 1412 AH, shafi na 714.
  3. Mohammadi, Sharh Kashf al-Morad, 1378, shafi na 553; Qazi Abdul Jabbar, Sharh al-Asul al-Khamsa, 1422 AH, shafi na 422.
  4. Mahmoud Abdur Rahman Abd al-Moneim, Mujamu Musdalahat wa-Alfaz Fikhiyya, ƙarƙashin kalmar"Takfir", 1999.
  5. Suratul Muhammad, aya ta 2
  6. Suratul Tahrim, aya ta 8.
  7. Suratul Nisa’i, aya ta 4.
  8. Al-Imran, shafi na 195.
  9. Suratul Nuhu, aya ta 3-4.
  10. Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 8, shafi na 34.
  11. Ibn Qolwieh, Kamel al-Ziyarat, 1356, shafi na 126.
  12. Shayiri, Jame Al-Akhbar, Heydarieh Press, shafi na 39.
  13. Ayashi, Tafsir al-Ayashi, 1380H, juzu'i na 2, shafi na 162.
  14. Qazi Abdul Jabbar, Sharh al-Asul al-Khamsa, 1422 AH, shafi 422-427.
  15. Eji, Sharh al-Maqsih, 1325 AH, juzu'i na 8, shafi na 309
  16. Qazi Abdul Jabbar, Sharh al-Asul al-Khamsa, 1422 AH, shafi 422-427
  17. Homsi Razi, Al-Manqidh Man al-Taqlid, 1412 AH, juzu'i na 2, shafi na 42.
  18. Duba Ibn Maitham Bahrani, Qa'aa al-Maram, 1406H, shafi na 164.
  19. Eji, Sharh al-Massiq, 1325 AH, juzu'i na 8, shafi na 289-309.
  20. Qazi Abdul Jabbar, Sharh al-Asul al-Khumsa, 1422 AH, shafi 422-427.
  21. Duba Shabar, Haq al-Iqin, 1424H, shafi na 551.
  22. Shir, Haq al-yaqin, 1424H, shafi na 550.
  23. "Ehbadu wa Takfir", shafi na 59
  24. Qazi Abdul Jabbar, Sharh al-Asul al-Khamsa, 1422 AH, shafi 422, 423.
  25. Duba Iji, Shahr al-Mawakif, 1325 Hijira, juzu'i na 8, shafi na 309.
  26. Shabar, Haqqu al-yaqin, 1424H, shafi na 549.
  27. Tabatabai, Al-Mizan, 1417 AH, juzu'i na 2, shafi na 170.
  28. Qazi Abdul Jabbar, Sharh al-Asul al-Khamsa, 1422 AH, shafi 425-426.
  29. Dayiratu Maref Alqur'anil Kareem , "Ihbadu wa-Takfir".

Nassoshi

  • Ibn Qolwieh, Jafar bin Muhammad, Kamel al-Ziyarat, revised by: Abdul Hossein Amini, Najaf, Dar al-Mortazawieh, 1356.
  • Ibn Maitham Bahrani, Qawaed al-Maram fi ilm al-kalam, bincike: Seyed Ahmad Hosseini, Kum, mazhabar Ayatullah al-Marashi al-Najafi, 1406H.
  • Ayji- Mirsyyed Sharif, Sharh Mawakif, editan: Badr al-Din Nasani, Kum, al-Sharif al-Razi (Qom offset), 1325H.
  • Jafar Yakoubi <a class="external text" href="http://www.noormags.ir/view/fa/articlepage/247606">آشنایی با چند اصطلاح قرآنی</a>
  • Homsi Razi, Sadid al-Din, Al-Munkiz Min al-Taqlid, Qom, Al-Nashar al-Islami Foundation, 1412 AH.
  • Dayiratu Maref Kur'anil Kareem <a class="external text" href="http://www.noormags.ir/view/fa/articlepage/247606">آشنایی با چند اصطلاح قرآنی</a> <a class="external text" href="http://www.webcitation.org/6tFvQZzmq">احباط و تکفیر</a>
  • Ragheb Esfahani, Hossein bin Muhammad, Mofradat Alfaz Kur'an, bincike: Safwan Adnan Davoudi, Syria-Lebanon, Dar al-Alam - Al Dar al Shamiya, 1412 AH.
  • Shabar, Sayyid Abdullah, Haq Al-yaqin Fi Mafarah Usul Al-Din, Qom, Anwar Al-Hadi, 1424H.
  • Shayiri, Mohammad bin Mohammad, Jame Al-Akhbar, Najaf, Heydarieh Press, Beta.
  • Tabatabaei, Mohammad Hossein, Al-Mizan fi Tafsiril Qur'an, Qum, Al-Nashar al-Islami School, 1417H.
  • Ayashi, Muhammad Bin Mas'ud, Tafsir Al-Ayashi, bugun Seyyed Hashim Rasouli Mahalati, Tehran, Al-Muttabah Al-Alamiya, 1380H.
  • (Qazi Abd al-Jabbar da Qawam al-Din Mankadim, Sharh al-Usul al-Khamsa, dakatarwa: Ahmad bin Hossein Abi Hashem, Beirut, Darahia al-Arabi, 1422H.
  • Goruhi Daneshnameh Kalam Islami, <a class="external text" href="http://www.noormags.ir/view/fa/articlepage/23975">احباط و تکفیر</a>
  • Majlesi, Mohammad Baqir, Bihar al-Anwar, Beirut, Dar Ahya al-Trath al-Arabi, 1403 AH.
  • Mohammadi Gilani, Takmilatu Shawarikul Al-Ilham, Qum, Mazhabar Al-Alam al-Islami, 1421H.
  • Mohammadi, Ali, Sharh Kashf al-Morad, Kum, Dar al-Fikr, 1378.
  • Mahmoud Abd al-Rahman Abd al-Moneim, ƙamus na al-terminants da al-faz al-fiqhiyyah, Alkahira, 1999.