Fasiƙi

Daga wikishia
(an turo daga Fasikai)

Fasiƙi (Larabci:الفاسق) shi ne wanda yake saɓawa Allah maɗaukaki ba ya bin umarni shi, daga cikin siffofin shi akwai ƙaryata ayoyin Kur'ani da karya alƙawari, yanke zumunci ɓarna da fasadi suna daga cikin siffofin Fasiƙi .

Akwai hukunce hukunce a kan fasiƙi daga cikin su akwai; Munafiki ba zai taɓa samun mukamin imamanci ba, kuma ba zai taɓa zama limami ba, kuma ba za a karɓi shaidar shi ba, kuma Shi'a sun tafi kan cewa musulmi fasiƙi, ba kafiri ba ne, kuma suna ganin babu wanda yake dauwama a wuta sai kafiri kaɗai.

Sanin Mafhumi

Fasiƙanci a Lugga yana nufin, ƙin bin umarnin Allah, da nisantar hanyar Allah da kuma karkata zuwa ga saɓon Allah, sabo da haka, fasiƙi shi ne wanda yake saɓawa Allah,kuma ya sauka daga kan hanyar gaskiya.[1] Amma malaman Luga sun tafi kan cewa ma'anar fasiƙanci ita ce,fitar wani abu daga wani abu, sabo da ya lalace,kamar fitar ɗanyan dabino daga fatar shi.[2] malam Hassan Almusɗafawi marubucin littafinan mai suna Attahaƙiƙ fi Kalimatil ƙur'an, ya tafi kan cewa shi fsiƙanci ya nufin fita daga dokokin addini da na hankali da na yanayin rayuwa ta yau da kullin, daga cikin abin da fasiƙanci yake nufi shi ne kangarewar bawa daga biyayar ubangijin shi,da ƙin bin hukunce-hukucan muslinci da rashin aklaƙ, da kuma siffa irin su Hassada, rowa, girman kai da kwaɗayi,da kuma fita da barin dokoki na rayuwar yau da kullin,kamar fitar ɗanyan dabino daga fatar shi,kuma siffofin barin umarnin Allah da karkata zuwa ga saɓo da yin zalinci suna daga cikin siffofi da tasiri na fasiƙanci.[3]

Siffofin Fasiƙi a cikin Alƙur'ani

kur'anin ya anbaci siffofi daban-daban na fasiƙi,daga cikinsu akwai, karya alƙawarin Allah da katse duk abin da Allah ya yi umarni ayi da kuma ɓarna a duran ƙasa.[4] da karyata ayoyin Allah.[5] da zalinci.[6] da rashin bin umarnin Allah.[7] da girman kai.[8] da manta anbataun Allah, daga ƙarshe ya kai shi ga manta kanshi.[9]

Imani da Azabtar da Fasiƙi

Shi'a sun yi imanin cewa fasiƙi ba kafiri ba ne, kuma kafiri ne kawai zai dauwama a cikin azaba. da ace musulmi zai zama fasiƙi,to ba zai dauwama a cikin azaba ba har abada, kuma zai yi wu ya sami ceto ko kuma Allah ya yi mishi gafara.[10] Amma Alwa'idiyya wanɗada su gungu ne daga cikin Khawarijawa sun tafi kan cewa ayyuka na gari ɓangari ne na imani.[11] saboda hakane suka tafi kan cewa, duk wanda yake aikata manyan zunubai, to kafiri ne, sakamakon haka to zai daumama a wuta.[12] Su kuma Murji'ah sun tafi kan saɓanin abin da Wa'idiyya suka tafi akai, kuma sun yi imani da cewa aikin alheri ba ya cikin imani, kuma duk wanda ya yi babban zunubi ba ya cutar da imanin shi, kuma a lahira ne zai bayyana cewa shi ɗan wuta ne ko ɗan aljanna. kuma a nan duniya ba a san halin da yake ciki ba.[13] Amma su Mu'utazilawa sabanin wadannan ra'ayoyi, sun gabatar da ka'idar su a tsakanin gidaje guda biyu: aƙidar su ita ce shi fasiƙi ba mumini ba ne, kuma ba kafiri ba ne, amma yana tsakanin imani da kafirce ne; Don haka makomar lahira ba ta da wani lada mai girma, kuma ba ta da wata azaba mai tsanani, shi munafiki za a yi mishi azaba ne tsakanin azabar kafiri da azabar musulmi munafiki kafiri.[14] Da kuma akidar Al-Mu'utazila cewa duk wanda ya shiga wuta ba zai taba fita daga cikinta ba.[15]

Kuma babu saɓani kan cewa fasiƙi wanda ya tuba Allah zai gafarta mashi kuma Allah zai shirye shi, kuma ba zai dawwama a cikin azaba ba har abada:[16] Ya zo a cikin Alkur'ani cewa, duk wanda ya yi imani kuma ya tuba zuwa ga Allah Mabuwayi tuba da gaske, to Allah Ta'ala zai gafarta mashi zunuban shi, kuma zai shigar da shi Aljanna.[17]

Fasiƙi da Imamanci

Shi'a Imamiyya sun yi imani da cewa fasiƙi ba zai taɓa zama imami ba ko ya kai matsayin Imamanci; Domin kuwa fasiƙi ya kasance azzalumi.[18] kuma shi fasiƙi ba zai taɓa kaiwa matsayin imami ba,[19] Amma mafi yawan Sunnah sun yi imani da cewa bayan nada kalifa ko imami kuma sai ya zama mai fasiƙanci, saboda zalunci da kwacen dukiya da sauransu.to baza'a taɓa sauke shi daga kan matsayin shi na khalifan musulmi ba kuma zai zamo halattaccan khalifa.[20]

Hukunce-hukuncen Fasiƙi a Fiƙihu

Akwai wasu hukunce-hukuncen fikihu wanda suka kebanta da fasiƙi, daga cikinsu akwai: ba haramin bane ayi da shi wato ayi gulmar shi, wanda ya kasance mai aikata laifi a bayyane da fasikanci,[21] kuma baza'a karbar sheda ba,[22] kazalika baza'a karɓa duk abin da ya rawaito ba, kuma wajibi ne a binciki ingancin maganar shi,shin gaskiyace ko karya. [23] kuma bai halatta ba ya zama limamin jam'i.[24]

Bayanin kula

  1. Farahidi, Al-Ainu, juzu'i na 5, shafi na 82; Ibn Manzoor, Lasan Al-Arab, juzu'i na 10, shafi na 308
  2. Fayyumi, Ahmad bin Muhammad, Al-Misbah Al-Munir, 1418 AH, juzu'i na 1, shafi na 245.
  3. Mustafaɓi, Al-Tahbƙ fi Kalamat al-ƙur'an al-Karim, 1368, juzu'i na 9, shafi na 89A
  4. Suratul Baƙarah, aya ta:27
  5. Makarem, Tafsir Namuneh, 1374, juzu'i na 1, shafi na 153-155.
  6. Suratul An'am, aya ta 49.
  7. Suratul A'araf, aya ta 165.
  8. Suratul Kahf, aya ta 50.
  9. Suratul Ahkaf, aya ta:20.
  10. Suratul Hashr, aya ta 19.
  11. Allameh Hilli, Kashf Al-Morad, 1382, shafi na 274-276; Sobhani, Lectures in Theology, 1428 AH, shafi na 461-463.
  12. Tusi, Al-ƙawa'id Al-Aƙa'ed, 1413H, shafi na 106.
  13. Shahrashtani, Al-Milal wa Al-Nihal, 1364, juzu'i na 1, shafi na 132.
  14. Shahrashtani, Al-Milal wa Al-Nihal, 1364, juzu'i na 1, shafi na 162.
  15. ƙazi Abdul Jabbar, Sharh al-Usul al-Khamsa, 1422 AH, shafi 471-472.
  16. Sobhani, Jafar, Manshur Jaɓed, 2004, juzu'i na 5, shafi na 561.
  17. Sobhani, Jafar, Manshur Jaɓed, 2004, juzu'i na 5, shafi na 561.
  18. Suratul Tahrim, aya ta 8.
  19. Suratul A'araf, aya ta 165
  20. Suratul Baƙarah, aya ta 124; jam'i az Nawisandegan, Imamat Pajuhi (bararsi didigahaye Imamiyyya, Mu'utazila, wa Asha'ira ), 2013, shafi na 268.
  21. Alameh Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 75, shafi na 261; Makarem Akhlak dar Alkur’ani, 1377, juzu’i na 3, shafi na 127.
  22. Sheikh Mufid, Al-Maƙna, 1413 AH, shafi na 726-727.
  23. Suratul Hujurat, aya ta 6
  24. Tusi, Al-Khilaf, 1407H, Mujalladi na 1, shafi na 471.

Nassoshi

  • Al-Farahidi, Al-Khalil bin Ahmed, Al-Ain, Bija, Binna, Bita.
  • Alameh Hilli, Kashf Al-Murad fi sharh Tajtreed Al-Itiƙad , ƙum, Cibiyar Imam Sadik (AS), 1382.
  • Allameh Majlesi, Bihar al-Anwar, Beirut, Al-Wafa Institute Publications, 1403 AH.
  • Baghalani, Abu Bakar, Tamhid al-Awael fi Talkhis al-Dalael, Lebanon, Al-Katb al-Thaƙafiyya Foundation, 1407 AH.
  • Ibn Manzoor, Lasan Al-Arab, bija, bina, bita.
  • Jam'i Nawisandegan, binciken Imamanci (nazarin ra'ayoyin Imamia, Mu'tazila da Ash'ari), Mashhad, Jami'ar Kimiyyar Musulunci ta Razaɓi, 2008.
  • Makarem, Nasser, Tafsir Namuneh Tehran, Dar al-Katb al-Islami, 1374.
  • ƙazi Abd al-Jabbar, Sharh Al-Usul Al-Khumsa, Dar Ihya al-Trath al-Arabi, 1422H.
  • Shahrashtani, Muhammad bin Abdul Karim, Al-Milal wa Al-Nehal, ƙom, Al-Sharif Al-Razi, 1364.
  • Sheikh Mofid, Al-Maƙna, ƙom, Sheikh Mofid Hazara World Congress, 1413 AH.
  • Sobhani, Jafar, Lakcocin Tauhidi, ƙum, Cibiyar Imam Sadik (AS), 1428H.
  • Tusi, Muhammad bin Muhammad, Al-Khilaf, ƙum, ofishin wallafe-wallafen Musulunci, 1407H.
  • Tusi, Nasir al-Din, Al-ƙawa'id Al-Aƙa'eed, Dar Gharba Publications, 1413 AH.