Daƙiƙa:Wankan Ziyara
Wannan wani rubutu ne na siffantawa game da wata ma'ana ta fiƙihu, kuma ba za ta iya zama ma'auni ga ayyukan addini ba, domin ayyukan addini sai a koma zuwa ga wasu madogaran na daban. |
| Sashe dagaHukunce-hukuncen Aiki da na Fiƙihu |
|---|
Wankan ziyara shi ne wankan da ake yi yayin ziyartar kabarin Ma'asumai (A.S). Wasu daga cikin malaman fikihu suna ganin wannan wanka a mustahabbi ne, yayin da wasu kuma suke cewa yin sa ya halatta ne kawai da niyyar raja'i ko fatan samun lada, ba tare da tabbatar da mustahabbancinsa ba.
Wankan ziyara wani wanka ne da ake yi yayin ziyartar kaburburan Ma'asumai (A.S).[1] A cewar Kashiful Giɗa wasu malamai sun haɗa da ziyartar kaburburan Annabawa a cikin wannan hukunci.[2] Haka kuma akwai riwayoyi daga Imam Sadiƙ (A.S) da suka yi umarni da yin wanka yayin ziyartar Ka'aba.[3]
Wasu daga cikin fuƙaha'u sun ɗauki wankan ziyara a matsayin mustahabbi,[4] Ibn Zuhra ma ya yi iƙirarin akwai ijma'i a kan mustahabbancinsa,[5] yayin da Muhammad Hassan Najafi, marubucin Jawahirul Kalam, ya bayyana cewa wannan shi ne mashahurin ra'ayi a tsakanin malamai.[6]
A cikin ruwayoyi, an yi umarni da yin wanka na musamman lokacin ziyartar kabarin Annabi (S.A.W), Imam Husaini (A.S) da Imam Rida (A.S). Wahid Bihbahani daga maraji'an taƙlidi ya kafa dalili da cewa tunda Imamai duk haske guda ne, wannan hukunci ya shafi dukan Ma'asumai.[7] Wasu malamai kuma sun ce ana iya yin wankan ziyara ko da mutum zai yi ziyara daga nesa.[8]
Sai dai wasu fuƙaha'u kamar Sayyid Abul Ƙasim Khuyi, Sayyid Ali Sistani da Nasir Makarim Shirazi ba su yarda da cewa wankan ziyara mustahabbi ne kai tsaye ba. A ganinsu, ana iya yin sa ne kawai da niyyar raja'i (fatan samun lada), wato mutum ya yi shi da fatan cewa Allah yana son a yi shi.[9]
A ra'ayin wasu malaman Shi'a, wankan ziyara mustahabbi ne domin shiga haramin Ma'asumi ko da mutum bai yi niyyar ziyara ba.[10]
Wasu malamai sun bayar da fatawa cewa ana iya yin salla da dukkan wanka na wajibi da na mustahabbi, banda wankan istihada matsakaiciya. Duk da haka, abin da ya fi kyau a matsayin ihtiyaɗi mustahabbi shi ne a yi alwala bayan kowane wanka da ba wankan janaba ba.[11]
Duba Bincike Masu Alaƙa
Bayanin kula
- ↑ Kashiful Giɗa, Kashful Giɗa, juzu'i na 2, shafi na 309; Najafi, Jawahirul Kalam, juzu'i na 5, shafi na 45; Shaik Ansari, Kitab Aɗ-Ɗahara, juzu'i na 3, shafuka na 64–67.
- ↑ Kashiful Giɗa, Kashful Giɗa, juzu'i na 2, shafi na 309.
- ↑ Kulaini, Al-Kafi, juzu'i na 3, shafi na 40; Ɗusi, Tahzibul Ahkam, juzu'i na 1, shafuka na 104 da 114; Hurru Amili, Wasa'ilush Shi'a, juzu'i na 3, shafi na 304.
- ↑ Kashiful Giɗa, Kashful Giɗa, juzu'i na biyu, shafi na 309; Najafi, Jawahirul Kalam, juzu'i na 5, shafi na 45; Shaik Ansari, Kitab Aɗ-Ɗahara, juzu'i na uku, shafuka na 64–67.
- ↑ Ibn Zuhra, Ghunyatun Nuzu'u Ila Ilmil Usul Wal Furu'u, shafi na 62.
- ↑ Najafi,Jawahirul Kalam, juzu'i na biyar, shafi na 46.
- ↑ Bihbahani, Masabihuz Zalam, juzu'i na 4, shafuka na 88–90.
- ↑ Yazdi, Al-Urwatul Wusƙa, juzu'i na 2, shafi na 154.
- ↑ Yazdi, Al-Urwatul Wusƙa, juzu'i 1, shafi na 462; Ɗabaɗaba'i Hakim, Mustamsakul Urwatul Wusƙa, juzu'i 4, shafi na 281; Hamadani, Misbahul Faƙih, juzu'i 6.
- ↑ Rashidi, Risalatu Taudihul Masa'il 9 Maraji, shafuka na 367–368.
- ↑ Ayat Tabrizi, Nuri da Wahid: Rashidi, Risalatu Taudihul Masa'il 9 Maraji, Mas'ala ta 391 da 646.
Nassoshi
- Bihbahani, Muhammad Baƙir, Masabihuz Zalam, Qom, Cibiyar Allama Mujaddid Wahid Bihbahani, 1424H / 1382Sh.
- Hamadani, Rida, Misbahul Faƙih, Qom, Cibiyar Jafariyya Li Ihaya'i Turas, 1376Sh.
- Ibn Zuhra, Ḥamza bin Ali, Ghunyatun Nuzu'u Ila Ilmil Usul Wal Furu'u, Qom, Imam Sadiƙ (A.S), 1417H.
- Kulaini, Muhammad Bin Yaƙub, Al-Kafi, Tehran, Darul Kutubil Islamiyya, 1363Sh.
- Kashiful Giɗa, Jafar, Kashful Giɗa An Mubhamat Ash-Shari'a Al-Gharra, Qom, Ofishin Tabligate Islami Hauze Qom, 1422 AH.
- Najafi, Muhammad Hassan, Jawahirul Kalam Fi Sharhi Shara'i'il Islam, gyaran rubutu: Abbas Quchani da Ali Akhundi, Beirut, Dar Ihya'i Turasil Arabi, bugu na bakwai, 1404H.
- Rashidi, Laɗif, da Sa'id Rashidi, Risalatu Taudihul Masa'il 9 Maraji, Qom, Mawallafar Payame Adalat, bugu na farko, 1385Sh.
- Shaik Ansari, Murtada, Kitab Aɗ-Ɗahara, Qom, Kongire Buzurg Dasht Shaik Al-A'azam Ansari, 1415H.
- Yazdi, Sayyid Muhammad Kazim, Al-Urwatul Wuska, Qom, Mawallafar Dawari, 1414H.
- Hurru Amili, Muhammad Bin Hassan, Wasa'ilush Shi'a, Qom, Alul Bait, 1414H.
- Ɗabaɗaba'i Hakim, Sayyid Muhsin, Mustamsakul Urwatul Wusƙa, Qom, Darul Tafsir, 1374Sh.
- Ɗusi, Muhammad Bin Hassan, Tahzibul Ahkam, bincike: Sayyid Hasan Khursan, Tehran, Darul Kutubil Islamiyya, 1364Sh.