Majhulul Malik
Majhulil Malik, (Larabci: مجهول المالك) ita ce dukiyar da ba san mai ita ba ko kuma dukiyar da ba za a iya isar da ita zuwa ga ma’abocinta ko magadansa ba, bisa fatawar mashhur ɗin Malaman fiƙihu na Shi’a dukiyar da ba a san ma’abocinta ba dole ne a bayar da sadaƙarta ƙarƙashin izinin Hakimul Shar’i (Marja’i) ba ya halasta a yi amfani da wannan dukiya ba tare da izinin Hakimul Shar’i ba, cikin fiƙihu an ambacin misdaƙan Majhulul Malik ko wuraren hukunce-hukuncenta, daga jumlarsu akwai bashin da ba za a iya mayar da shi zuwa ga ma’abocinsa ba.
Mafhumi da Hukuncin Shari’a
Majhulul Malik, wata dukiya cewa da ba a san ma’abocinta ba ko kuma ba a san inda ma’abocinta ko magadansa suke ba. [1] Bisa fatawar Malaman fiƙihun Shi’a dukiyar da bayan gama bincike an ɗeba tsammani da sa rai daga samun ma’abocinta wajibi ne a bayar da ita sadaƙa, na’am wasu ba’arin Malaman fiƙihu misalin marubucin littafin Jawahir [2] da Imam Khomaini [3] sun tafi kan cewa wajibi ne a nemi izinin Hakimul Shar’i, a kishiyarsu an samu wasu Malamai misalin Sayyid Abu ƙasim Khuyi da yake ganin ba dole bane sai an nemi izinin Hakimul Shar’i, 4 Bashir Husaini Najafi daga Maraji’an Taƙlidi shima ya tafi kan cewa a nemi izini bisa Ihtiyaɗi na mustahabbi, [4] haka kuma cikin dokokin ƙasar Iran an rubuta cewa idan aka samu wata dukiya da ba a san mai ita ba to za a rabawa talakawa wannan dukiya bayan samun izini daga Hakimul Shar’i ko kuma daga wanda yake da izini daga Hakimul Shar’i. [5]. Haka kuma an ce an fitar da natija daga wasu riwayoyi cewa babu mai iko kan dukiyar da ba a san ma’abocinta ba sai Hakimul shar’i a duk inda ya ga maslaha zai iya amfani da ita. [6]
Misdaƙai
Cikin fiƙihu an ambaci wurare da ake ƙirga su cikin jerin misdaƙan Majhulul Malik; daga jumlarsu akwai:
- Tsintuwa: idan ƙimar abin da aka tsinta ta wuce dirhami ɗaya giram sha biyu da ɗigo shida wajibi kan wanda ya tsinceta ya yi cigiyarta tsawon shekara guda, idan bayan shekara ba a samu ma’abocinta ba dole ne ya yi ɗaya cikin wannan ayyuka: mallakawa kansa, ya yi sadakarta da sunan ma’abocinta, ya cigaba da ajiyarta matsayin amana, [7] ko miƙata hannun Hakimul shar’i, [8] an ce miƙata hannun Hakimul Shar’i yana kasancewa daga babain Majhulul Malik. [9]
- Kuɗaɗen Riba, kwace, caca da sata: kuɗaɗen da aka same su ta hanyar riba, kwace, sata ko caca, cikin surar rashin sanin ma’abocinsu da kuma ɗeba tsammanin samunsa, ana hukunta su da kuɗaɗen Majhulul Malik. [10]
- Daɗaɗɗun kayan gargajiya da tarihi: bisa ra’ayin Malaman fiƙihu, kayayyakin tarihi da suke cikin ƙasa da babu mai su ko kuma aka sameta cikin dukiyar da aka saye su domin raya ƙasar da babu mai ita ana musu hukunci da Majhulul Malik idan ya zamana an gano cewa dukiyar ta musulmi ce amma ba a san shi ba. [11]
- Bashi da wanda ma’abocinsa ya yi nisan kiwo: wanda lokacin biyan bashinsa ya yi amma ba zai iya isa ga ma’abocin bashin ba, wajibi ya bada wannan bashi a hannun Hakimul Shar’i, idan babu Hakimul Shar’i, bisa ra’ayin mashhur wajibi ne ya bada sadaƙar wannan bashi da sunan ma’abocinsa. [12]
- Dukiyar da babu magadanta: dukiyar da babu magadanta ana mata hukunci da Majhulul Malik. [13]
- ƙasar da babu ma’abocinta, rayayyar ƙasa da masu rayata suka mutu: ɗaya daga cikin waɗannan ƙasa ita ce ƙasa wacce ba a san ma’abocinta ba, a cewar Sayyid Musɗapa Muhaƙƙiƙ Damad Malamin fiƙihu kuma masanin shari’a a wannan zaman, bisa ra’ayin wasu ba’arin Malaman fiƙihu ana lissafata cikin Majhulul Malik, amma mashhur ɗin Malamai suna ganin za a iya mallakar wannan ƙasa. [14]
- Mallakar gwamnati: a ra’ayin ba’arin Malaman fiƙihu dukiyar da take ƙarƙashin mallakar Gwamnati, tana cikin misdaƙan dukiyar Majhulul Malik, saboda gwamnati ba ta da haƙƙin mallakar dukiya. [15]
Bayanin kula
- ↑ Seifi Mazandarani,Dalil Tahrir Al-Wasila - Al-Waƙf, 1430H, shafi na 434.
- ↑ Najafi, Jawaher Al-Kalam, 136, juzu'i na 38, shafi na 336.
- ↑ Imam Khumaini, Risaleh Tauzihul Al-Masa'il, shafi na 466.
- ↑ Najafi, Buhus Fiƙhiyya Mu'asira, 1427 AH, shafi 104.
- ↑ ƙanun Mudni Iran, Madda 28
- ↑ Sanaei wa Digaran, "Mudiriyat Amwale Majlulul Malik ba Tawajjuhe be sharayiɗ Jami'eh Imruz", shafi na 460.
- ↑ Mohaghegh Damad Yazdi, ƙawa'id Fikih, 1406 AH, Mujalladi na 1, shafi na 262; ƙanun Mudni, da aka gyara labarin 162 kuma an gyara 163.
- ↑ Haeri, "Luƙɗa wa Majhol Al-Malik (3)", 2018, shafi na 42.
- ↑ Haeri, "Luƙɗa wa Majhol Al-Malik (3)", 2018, shafi na 52.
- ↑ Allameh Hali, Tazkirah Al-Fuƙaha, Mujalladi na 10, shafi na 209 da 210; Seifi Mazandarani, Dalil Tahrir Al-Wasila: Fiƙhu Al-Riba, 1430 AH, shafi na 133.
- ↑ Hashemi Shahroudi, “Asar Bastani”, juzu’i na 1, shafi na 106.
- ↑ Hashemi Shahroudi, "Dinu”, juzu’i na 3, shafi na 681; Najafi, Jawahirul Al-Kalam, 1362, juzu'i na 25, shafi na 44.
- ↑ Mohagheƙ Damad Yazdi, Wasiyyi: Tahlil Fiƙhi Wa Huƙuƙi, 1420 AH, shafi na 123.
- ↑ Mohagheƙ Damad Yazdi, ƙawa'id Fikh, 1406 Hijira, juzu'i na 1, shafi na 243.
- ↑ Najafi, Buhus Fikhiyya Mu'asira, 1427 AH, shafi na 86-99.
Nassoshi
- Imam Khumaini, Sayyid Ruhollah, Tahrir Al-Wasila, ƙum, Dar Al-Alam, Bita.
- Imam Khumaini, Sayyid Ruhollah, Risaleh Tauzihul Almas'il Imam Khumaini, Tehran, Cibiyar gyara da buga ayyukan Imam Khumaini, 1381.
- حائری، سید کاظم، «لقطه و مجهولالمالک(۳)»، در فصلنامه فقه اهل بیت(ع)، شماره ۵۸و۵۹، تابستان و پاییز ۱۳۸۸ش.
- Khoi, Sayyid Abul ƙasim, Mausu'atu Al-Imam Al-Khoei , Imam Al-Khoei Islamic Foundation, Beta.
- سنایی، حسین، و دیگران، «مدیریت اموال مجهول المالک با توجه به شرایط جامعه امروزی»، پژوهشهای فقهی، دوره ۱۵، شماره۳، پاییز ۱۳۹۸ش.
- Seifi Mazandarani, Ali Akbar, Dalil Tahrir Al-Wasila - Al-Waƙf, Tehran, Cibiyar gyara da buga ayyukan Imam Khumaini, bugu na farko, 1430H.
- Seifi Mazandarani, Ali Akbar, Dalilin rubuta al-Wasila - Fiƙh al-Arba, Tehran, Cibiyar gyara da buga ayyukan Imam Khumaini, bugu na farko, 1430H.
- Allameh Hali, Hasan bin Yusuf, Tazkira Al-Fuƙaha, ƙum, Al-Bait Institute (A.S.), bugun farko, 1414H.
- ƙanun Madani Iran.
- Mohagheƙ Damad Yazdi, Sayyid Mustafa, ƙawa'id Fikihi. Tehran, Cibiyar Buga Ilimin Musulunci, bugu na 12, 1406H.
- Masanin binciken Damad Yazdi, Sayyid Mustafa, Wasiyya: nazarin shari'a da shari'a, Tehran, Cibiyar Buga Ilimin Musulunci, bugu na uku, 1420H.
- Najafi, Bashir Hossein, Najaf, Ofishin Ayatullah Najafi, bugun farko, 1427H.
- Najafi, Mohammad Hassan, Jawahirul Al-Kalam, editan Ali Akhundi, Beirut, Dar Ihya Al-Tarath al-Arabi, bugu na 7, 1362.
- Hashemi Shahroudi, Sayyid Mahmoud, Farhang Fiƙh mutabiƙ Mazhab Ahlul Baiti (AS), ƙom, Encyclopedia of Islamic Fiƙhu Mazhab Ahlul Baiti (AS), Mujalladi na 1, 2, 3, 1st. Bugu, 1426H.