Wankan Janaba

Daga wikishia
Wannan wani rubutu ne na siffantawa game da wata mas'ala ta fiƙihu, ba za iya zama ma'auni ayyukan addini ba, ku duba wasu madogaran daban domin ayyukan addini.
Risala Amaliyya

Wankan janaba (Larabci: غسل الجنابة) wani wanka ne da ake yinsa sakamon tsintar kai cikin halin janaba. Wankan janaba a kankin kansa ba wajibi bane, amma domin sauke ayyukan wajibi waɗanda ɗahara ta kasance sharaɗi cikinsu, misalin salla yana zama wajibi, wankan janaba ana yinsa ta hanyoyi guda biyu, wanka tartibi da wanka irtimasi, cikin wankan janaba ta hanyar tartibi da fari ana faraway da wanke kai da wuya, bayan nan sai a wanke ɓarin daman a gangar jiki sannan a tsallaka a wanke ɓarin hagu. Wankan janaba ya isar wa alwala, ma'ana idan aka yi wankan jababa ba sai anyi alwala ba domin ayyukan ibada.

Janaba

Wankan janaba ɗaya ne daga cikin rabe-raben wanka na wajibi a addinin muslunci.[1] an yi bahasi dangane da wannan wanka da hukunce-hukuncensa a litattafan[2] fiƙihu[3] da risalolin ilimi.[4] Mutum yana shiga halin janaba sakamakon fitar maniyyi (A halin bacci ko farke) ko ta hanyar jima'i (ko da kuwa maniyyi bai fita ba).[5] a ra'ayin malaman fiƙihu, yin ba'arin ayyukan ibada yana kasancewa makaruhi ko haramun ga wanda yake cikin janaba, amma idan ya yi wankan janaba wannan haramci da makaruhancin yana ɗaukewa.[6] misali yin sallah, tsayuwa cikin masallaci, karatun surori masu ayoyin sujjada da taɓa rubutun kur'ani da sunayen Imamai haramun ne ga wanda yake cikin janaba.[7] haka nan cin abinci ko shan abin sha, karanta fiye ayoyin kur'ani guda bakwai, taɓa fatar kur'ani, zuwan wurin wanda yake shirin mutuwa da…. Duka makaruhi ne ga wanda yake cikin janaba.[8] na'am ba'ari daga wannan makaruhi ana magance shi karhancin ta hanyar alwala.[9]

Shin Wajibi Ne Gaggauta Wankan Janaba?

Bisa fatawar malaman fiƙihu wankan janaba yana wajabta ne domin waninsa;[10] ma'ana a kankin kansa mustahabbi ne ba wajibi ba.[11] amma yana zama wajibi domin sauke ayyukan wajibi da ɗahara ta kasance sharaɗi cikinsu,[12] haka nan yana zama wajibi kamar misalin sallah.[13] bisa fatawar malaman fiƙihu wankan janaba yana jerin wajibi muwassa (wajibi da yake da yalwar lokaci) da wannan ne za a iya jinkirta yinsa har zuwa lokacin sauke ayyukan ibada na wajibi.[14]

Ingancin Azumin Mai Janaba Ya Dogara Da Wankan Janaba

Tushen Kasida: Zama Da Janaba

wanda ya yi janaba a watan ramadan, wajibi kansa ya yi wankan janaba gabanin asubahi; idan ya zamana da gangan bai yi wanka har zuwa asubahi, azuminsa ya lalace, dole ya yi ramuwarsa tare da bada kaffara.[15]

Yaya Ake Wankan Janaba

Tushen ƙasida: Wanka

Wankan janaba misalin sauran rabe-raben wanka ana yinsa ta hanyoyi biyu: tartibi da irtimasi.[16] cikin hanyar tartibi da farko za fara wanke kai da wuya. Bayan nan sai a wanke gangar jiki ɓangaren dama, daga nan kuma sai a tsallaka ɓangaren hagu.[17] amma shi hanyar wanka irtimasi karo guda ne za a nutsar da bakiɗayan jiki cikin ruwa; na'am wajibi a hanyar irtimasi ruwa ya isa ga bakiɗayan jiki a lokaci guda.[18]

Ladubban Wankan Janaba

  • Idan ya zamana ya shiga janaba sakamakon fitar maniyyi, bisa fatawar malaman fiƙihu mustahabbi ne ya fara yin fitsari kafi fara yin wanka.[19]
  • Wanke hannuwa, kurkurar da shaƙa ruwa cikin hanci kafin fara wanka da karanta bismilla da addu'o'i da ake yayin wanka duka mustahabbi ne.[20]

Wadatarwar Wankan Janaba Daga Alwala

A ra'ayin malaman fiƙihu na shi'a wankan janaba yana isar wa daga alwala.[21] mashhur malaman fiƙihu ba sa ganin halascin alwala tare da wankan janaba.[22] na'am a cewar Allama Hilli, Shaik Ɗusi saɓanin sauran malamai ya na ganin mustahabbancin yin alwala tare da wankan janaba.[23]

Idan ya zamana yayin da mutum yake wanka janaba sai ya yi hadasul asgar (ƙamin ƙari, abin da lalata alwala) misalin fitsari da tusa) malaman fiƙihu sun yi saɓanin cikin ingancin wankansa da rashinsa; bisa ƙaddara ingancin wankan, nan ma akwai saɓanin malamai cikin wadatarwar wannan wanka daga alwala.[24] bisa fatawar Sayyid Kazim Ɗabaɗaba'i Yazdi wanka baya lalacewa sai dai kuma wajibi a ƙara da alwala bayan wanka.[25]

Falsafar Wankan Janaba

Bisa riwayar da ta zo a littafin Ilalul Ash-shara'i an naƙalto cewa illar da ta sanya wajabta wanka janaba shi ne tsafta da tsarkake jiki daga najasa, saboda cewa ita janaba tana fitowa ne daga bakiɗayan jiki saboda haka wajibi ne a wanke bakiɗayan jiki.[26] haka nan cikin Tafsirul Al-amsal ya zo cewa, kan asasin bincike masana, a jikin mutum akwai silsila guda biyu na jijiyoyin tsiro da sune suke konturol ɗin ayyukan gangar jiki, yayin motsin sha'awa waɗanda jijiyo suna fita daga konturol, bisa bincike na kimiyya amfani da ruwa da mutum yake yi yana dawo da daidaituwar waɗannan jijiyo, sakamakon motsin sha'awa yana ɓuɓɓugowa ne daga bakiɗayan gaɓɓan jiki, sai aka bada umarnin wanke bakiɗayan jiki bayan shiga janaba.[27]

Bayanin kula

  1. Tabatabai Yazdi, Al-Urwa Al-Wuthqi, 1417 AH, juzu'i na 1, shafi 493.
  2. Misali, duba Hurrrul Ameli, Wasa'il al-Shia, Est.
  3. Tabatabai Yazdi, Al-Urwa Al-Wuthqa, 1417 BC, juzu'i na 1, shafi na 521.
  4. Bani Hashemi Khomeini, Tauzihul al-Masa'il al-Masa'il, 1381, juzu'i na 1, shafi na 208.
  5. Tabatabai Yazdi, Al-Urwah Al-Wuthqa, 1417 AH, shafi na 507-509.
  6. Tabatabai Yazdi, Al-Urwa Al-Wuthqa, 1417 AH, juzu'i na 1, shafi na 507.
  7. Tabatabai Yazdi, Al-Urwah Al-Wuthqa, 1417 AH, shafi na 507-509.
  8. Tabatabai Yazdi, Al-Urwa Al-Wuthq, 1417 AH, juzu'i na 1, shafi 520.
  9. Tabatabai Yazdi, Al-Urwa Al-Wuthqa, 1417 AH, juzu'i na 1, shafi 520.
  10. Najafi, Jawahir al-Kalam, 1362 AH, juzu'i na 1, shafi na 46.
  11. Tabatabai Yazdi, Al-Urwa Al-Wuthqa, 1417 AH, juzu'i na 1, shafi 521.
  12. Muassaseh Dayiratul Al-marif Fikihu islami, Farhange Fiqhu mutabaik Ahlul Baiti (AS), 2007, juzu'i na 5, shafi na 558.
  13. Tabatabai Yazdi, Al-Urwa Al-Wuthqa, 1417 BC, juzu'i na 1, shafi na 521.
  14. Ƙarshen Ibn Idris, Ibn Idris, Mausu'atu Ibn Idris al-Hilli, 1387 AH, juzu'i na 7, shafi na 111.
  15. Tabatabai Yazdi, Al-Urwa Al-Wuthqa, 1420 AH, juzu'i na 3, shafi na 563.
  16. Tabatabai Yazdi, Al-Urwa Al-Wuthqa, 1417 AH, juzu'i na 1, shafi na 522-523.
  17. Hakim, Mustamsik al-Uruwah, 1968 miladiyya, juzu'i na 3, shafi na 79.
  18. Hakim, Mustamsik al-Uruwah, 1968 miladiyya, juzu'i na 3, shafi na 85-86.
  19. Najafi, Jawahir al-Kalam, 1362 AH, juzu'i na 3, shafi na 108.
  20. Tabatabai Yazdi, Al-Urwa Al-Wuthqa, 1417 AH, juzu'i na 1, shafi na 541-542.
  21. Sheikh Tusi, Al-Khalaf, Mu'assasar Bugawa ta Musulunci, juzu'i na 1, shafi na 131; Najafi, Jawahir al-Kalam, 1363 AH, juzu'i na 3, shafi na 240.
  22. Najafi, Jawahir al-Kalam, 1362 AH, juzu'i na 3, shafi na 240.
  23. Allameh Hali, Mukhtalaful al-Shia, 1412 AH, juzu'i na 1, shafi na 340
  24. Tabatabai Yazdi, Al-Urwa Al-Wuthqa, 1417 AH, juzu'i na 1, shafi 547.
  25. Tabatabai Yazdi, Al-Urwa Al-Wuthqa, 1417 AH, juzu'i na 1, shafi 547.
  26. Saduq, Ilal al-Shara’i’, Al-Haidariyya Library and the printing in Najaf, juzu’i na 1, shafi na 281.
  27. Makarem Shirazi, Tafsir Namuneh, 1374 AH, juzu'i na 4, shafi 292-294.

Nassoshi

  • Muassaseh Dayiratul Al-marif fiqihu islami, Farhang Fikhi mutabik mazhab Ahlul-Baiti (amincin Allah ya tabbata a gare shi), Qum, Mu'assasa ta ilmin fikihu, 1387H.
  • Allama Hali, Hassan bin Yusuf, Mukhtalaful Al-Shi'a, Cibiyar Bincike da Nazarin Musulunci ta Bah Kushsh, Qum, Littafin Rubutun Musulunci, Bugu na Farko, 1412 Hijira.
  • Bani Hashemi Khomeini, Muhammad Hassan, Tauzihul Al-masa'il, Qum, Littafin wallafe-wallafen Musulunci, 1381H.
  • Hakim, Sayyid Mohsen, Mustamsik al-Urwah al-Wuthqa, Najaf, Bina, 1968 miladiyya.
  • Hurrul Ameli, Muhammad bin Hassan, Wasa’il Al-Shi’a, Kum, Mu’assasa Al-Baiti, Amincin Allah ya tabbata a gare su, don raya al’adun gargajiya, Beta.
  • Ibn Idris, Ibn Idris Al-Hilli Mausua' Ibn Idris Hilli, Qum, Dalil Ma, 1387H.
  • Makarem Shirazi, Nasser, Tafsir Namouneh, Tehran, Dar Al-Kutub Al-Islamiyyah, pdf: Sy and Dom, 1374 AH.
  • Najafi, Muhammad Hassan, Jawahir al-Kalam fi Sharh Sharia al-Islam, Beirut, Dar Ihya’ al-Tarath al-Arabi, Jafa Hiftam, 1362 AH.
  • Saduq, Muhammad bin Ali, Illal al-Shara’i, Al-Haidariyya Library da kuma ma'ajin bugawa a Najaf, Beta.
  • Sheikh Tusi, Muhammad bin Hassan, Kitabul Al-khilaf, Qum, Mu’assasar Buga Musulunci, Beta.
  • Tabatabai Yazdi, Sayyid Muhammad Kazem, Al-Urwah Al-Wuthqa (juzu'i na 1), Qum, Mu'assasar Daba'ar Musulunci, bugu na farko, 1417H.
  • Tabatabai Yazdi, Sayyid Muhammad Kazem, Al-Urwah Al-Wuthqa (juzu'i na 3), Qum, Mu'assasar Daba'ar Musulunci, bugu na farko, 1420H.