Jump to content

Daƙiƙa:Salmanu Minna Ahlal-Baiti

Daga wikishia
Salmanu Minna Ahlal-Baiti
Hadisin "Salmanu Minna Ahlal-Baiti" cikin fasahar rubutun salon khaɗɗul Sulsi na Muhammad Ta'arifi
Hadisin "Salmanu Minna Ahlal-Baiti" cikin fasahar rubutun salon khaɗɗul Sulsi na Muhammad Ta'arifi
Maudu'iFalalolin Salmanu
Ya Fito DagaSayyidina Muhammad (S.A.W)
Ingancin IsnadiSahihi Mutawatiri
Madogaran Shi'aUyunu Akhbarir RidaMisbahul MutahajjidMajma'ul BayanAl-Ikhtisas
Madogaran Ahlus-sunnaAɗ-Ɗabaƙatul Kubra•As-Siratun Nabawiyya
Hadis Silsilatuz ZahabHadis SaƙlainiMaƙbulatu Umar Bin HanzalaHadis Ƙurbu NawafilHadis Mi'irajHadis WilayaHadis WisayaHadis Junud Aƙli Wa JahalHadis Shajara


Salmanu Minna Ahlal Baiti, (Larabci: سَلْمانُ مِنّا أهل‌َ البيت) ma'ana Salmanu daga gare mu mu Ahlul-baiti, wani shahararren hadisi ne mutawatiri kuma sahihus sanad da aka rawaito shi daga Annabi (S.A.W) game da falaloli da muƙaman Salmanul Farisi. Ba'arin imaman Shi'a kamar Imam Ali (A.S), Imam Sajjad (A.S) da Imam Baƙir (A.S) suma sun yi bayanin wannan hadisi ko dai cikin yanayi mai cin gashin kansa, ko kuma ƙarƙashin naƙaltowa daga Manzon Allah (S.A.W).

Labarin haƙa ramin Khandaƙ a lokacin yaƙin Ahzab da maganar da Umar Bin Khaɗɗab ya yi game da rashin kasancewar Salman daga ƙabilar Larabawa, wani ɓagare ne daga abubuwan da aka bayyana su matsayin sanadin da dalilin fitowar wannan hadisi daga Manzon Allah (S.A.W).

Shaik Saduƙ, Shaik Ɗusi da Shaik Mufid suna daga malaman Shi'a, Ibn Sa'ad da Ibn Hisham daga malaman Ahlus-Sunna da suka naƙalto wannan hadisi a cikin litattafansu.

Wasu adadin malamai sun ce, abin da Manzon Allah (S.A.W) yake nufi daga "Salmanu Minna Ahlal-baiti". shi ne cewa Salmanu yana kan addininmu. Wasu kuma sun ce wannan hadisi yana bayanin muƙamin Salamu bisa la'akari da kusanci na aƙida, akhlaƙ da ayyukansa ya ka samu kusanci da Sayyidina Muhammad (S.A.W).

Muhammad Ali Asbar a shekarar 1413H, ya wallafa wani littafi mai suna "Salmanu Minna Ahlal-baiti" an buga wannan littafi a Bairut, cikin wannan littafi ya yi bincike kan yanayin rayuwar Salmanul Farisi da kuma nazari kan wannan hadisi.

Gabatarwa Da Kuma Matsayi

"Salmanu Minna Ahlal-baiti" Salmanu daga gare mu yake mu Ahlul-baiti, a cewar masu bincike na Shi'a wani hadisi da a karon farko aka fara jinsa daga Annabi (S.A.W).[1] Kan asasin madogaran hadisi, ba'arin Imaman Shi'a sun yi bayanin wannan hadisi ko dai cikin yanayi mai cin gashin kansa ko kuma ƙarƙashin naƙalinsa daga Annabi (S.A.W).[2] Alal misali, Imam Ali (A.S) cikin amsarsa ga wata tambaya da aka yi masa game da Salmanu, ya ambaci cewa shi Salmanu daga Ahlal-baiti (A.S) yake.[3] Cikin littafin Al-Kafi na Kulaini (Rasuwa: 329H) ya naƙalto wani hadisi daga Imam Sajjad tare bambancin lafazi da yake cikin hadisin, da cewa Salmanu daga gare mu yake mu Ahlul-baiti.[4] Haka nan kan asasin wani hadisi da ya zo a littafin Raudatul Wa'izin na Fattal Naishaburi, an yi magana game da Salmanul Farisi a wurin Imam Baƙir (A.S). sai Imam ya umarce su da yin shiru, ya ce ku dinga kiransa da Salmanul Muhammadi; saboda shi daga Ahlul-baiti (A.S) yake.[5] A cikin littafin Rijalu Kasshi nan ma daga Imam Sadiƙ (A.S) an naƙalto wata riwaya cikin babin Salmanu Minna Ahlal-Baiti (A.S).[6]

Tushen Fitowar Hadisin

Game da faruwar abin da ya janyo furta wannan hadisi daga bakin Annabi (S.A.W), akwai saɓani cikin abin da litattafai suka kawo.[7] Ɗabrisi malamin tafsiri na Shi'a da Ibn Sa'ad marubucin sira Ahlus-Sunna, sun ba da rahoto cewa Annabi (S.A.W), a lokacin yaƙin Ahzab ya ayyana wa Musulmi wani wuri domin su haƙa rami. Muhajirun da Ansar sun yi saɓani kan Salmanu wanda ya kasance ƙarfafaffan mutum, ko wannensu ya nemi Salmanu ya kasance tare da shi, sai Annabi Akram (S.A.W) ya raba rigima da jayayya cikin furta wannan jumla Salmanu Minna Ahlal-baiti (A.S) ya kira shi da cewa daga gare mu yake mu Ahlil-baiti (A.S).[8]

Shaikh Mufid cikin mabambantan rahotanni ya rubuta cewa Sayyidina Muhammad (S.A.W) yayin da ya ji maganar da Umar Bin Khaɗɗab ya faɗa game da rashin kasancewar Salmanu daga ƙabilar Larabawa, sai Annabi ya hau mimbari ya yi huɗubar tare da bayyana cewa su mutane ba sa fifita kan junansu bisa ƙabila ko kalar fatarsu kaɗai suna samun fifita bisa tsoran Allah, ya kira Salmanu da teku mara iyaka kuma taska mara ƙarewa, ya bayyana cewa shi daga Ahlal-baiti yake.[9] A cikin littafin Sulaimu Bin Ƙaisi akwai wata riwaya da aka naƙalto cewa Annabi (S.A.W) ya yi umarni da kowa ya tashi daga majalisinsa in banda Ahlul-baiti. Sai Salmanu ya yunura zai tashi sai Annabi ya ce ya zauna, saboda shi daga Ahlul-baiti yake.[10]

Inganci Da Madogaran Wannan Hadisi

Hadisin "Salmanu Minna Ahlal-baiti" yana daga shahararrun hadisai[11] kuma mutawatiri.[12] Ba'arin masu bincike suna ganin hadisi ne sahihus sanad kuma mai ƙarfin gaske, bawai kawai hadisi da ya zo ta fuska guda ɗaya ba, bari jumla ce da sashenta ya yi tarayya cikin wasu adadin hadisai[13] daga Annabin Muslunci (S.A.W) da Imamai (A.S).[14]

Wasu adadin malaman Shi'a sun naƙalto wannan hadisi kamar Shaik Saduƙ a cikin Uyunu Akhbarir Rida,[15] Shaik Ɗusi a cikin At-Tibyan da Misbahul Mutahajjid,[16] Shaikh Mufid cikin Al-Ikhtisas,[17] Ibn Shahre Ashub a cikin Manaƙib Ale Abi Ɗalib,[18] Ahmad Bin Ali Ɗabrisi cikin Al-Ihtijaj[19] da kuma Sulaimu Bin Ƙaisi[20] Ibn Sa'ad a cikin Aɗ-Ɗabaƙatul Kubra[21] da Ibn Hisham a cikin As-Siratun Nabawiyya[22] sun kasance malamai biyu daga Ahlus-Sunna da suka naƙalto wannan hadisi.

Fahimtoci Daban-daban Daga Wannan Hadisi

Malaman Muslunci sun fitar fahimtoci daban-daban daga hadisin "Salmanu Minna Ahlal-baiti": Fadlu Bin Hassan Ɗabrisi da Shaik Ɗusi sun ce abin da Manzon Allah (S.A.W) yake nufi daga wannan hadisi shi ne cewa Salmanu yana kan addininmu.[23] Wasu kuma sun rubutu cewa wannan hadisi yana bayanin muƙamin Salmanu bisa la'akari da aƙida, kyawawan halaye da ayyukansa, ya kasance makusanci ga Sayyidina Muhammad (S.A.W).[24]

Littafin Salmanu Minna Ahlal Baiti, na Muhammad Ali Asbar

Ibn Arabi, daga Musulmi mabiya tafarkin sufanci , yana ganin wannan jumla matsayin shaidar Annabi game da zurfin darajar tsarkaka, kariyar Allah da kuma isma ga Salmanu, bisa dalilin da yake cikin ayar taɗhir, Allah ya tafiyar da ƙazanta daga barin Annabi da iyalan gidansa, saboda tsantsar bautarsu, kuma duk wanda ya yi kamanceceniya da su cikin haka za a riskar da shi cikinsu, kan wannan asasi wannan aya ta taɗhir za ta kasance tana haɗowa da Salmanul Farisi.[25] Sai dai cewa Mulla Muhsin Faizul Kashani ya yi watsi da maganar Ibn Arabi ta gangarar ayar taɗhir kan Salmanu da wasunsa waɗanda ba Ahlul-baiti (A.S) ba, kai yana ganin bai ma halasta wani ya furta wannan magana ba.[26]

Wasu adadi daga masu bincike, suna ganin cewa ilimin da Salmanu yake da shi game da haƙiƙanin matsayin Ahlul-baiti (A.S)[27] Wasu kuma suna ganin siffarsa ta musamman[28] suna daga sirrikan da suka sanya shi samun nasarar kaiwa ga wannan muƙami da Annabi (S.A.W) da Imamai (A.S) suka bayyana cewa Salmanu yana daga gare mu Ahlal-baiti.

Bayanin kula

  1. Husaini Amini Musawi, "Barrasi Wijegihaye Minna" Budane Salmane Farisi Bar Asase Tahlili Riwayat Laisa Minna, sh 50
  2. Husaini Amini Musawi, "Barrasi Wijegihaye Minna" Budane Salmane Farisi Bar Asase Tahlili Riwayat Laisa Minna, sh 50
  3. Tabrisi, Al-Ihtijaj, 1403q, J 1, sh 260
  4. Kulaini, Al-Kafi, 1363shamsi, J 1 sh 401.
  5. Fattal Nishaburi, Raudatul Wa'izin, 1375shamsi,J 2, sh 283.
  6. Kasshi, Rijalu Kasshi, 1348shamsi, sh 12 bsa nakali daga Husaini Amini Musawi, "Barrasi Wijegihaye Minna" Budane Salmane Farisi Bar Asase Tahlili Riwayat Laisa Minna, sh 49
  7. Shaik Saduƙ, Uyunu Akhbarir Rida (A.S), Jahan, j 2, sh 64; Shaik Tusi, Misbahul Mutahajjid, 1411q, j 2, sh 817
  8. Tabrisi, Majma'ul Bayan, 1408q, j 2, sh726 da j 8, sh 533; Ibn Sa'ad, Attabakatul Kubra, 1408q, j 4, sh62
  9. Shaikh Mufid, Al-Ikhtisas, 1413q, sh 341
  10. Husaini Amir wa Musawi, Barrasi Wijegihaye Minna Budane Salmane Farisi Bar Asase Tahlil Riwayat Laisa Minna, sh 49
  11. Juya, Akhbare Mashkuke Dar Mirase Ma'asure Akhlaqi, sh 102
  12. Husaini Amini Wa Musawi, Barrasi Wijegihaye Minna Budane Salmane Farisi Bar Asase Tahlil Riwayat Laisa Minna, sh 65; Basiri Wa Shafi'i, Barrasi Tahlili Hadise " Salman Minna Ahlal Baiti" sh 163 da 169
  13. Basiri Wa Shafi'i, Barrasi Tahlili Hadise " Salman Minna Ahlal Baiti" sh 163 da 169
  14. Husaini Amini Wa Musawi, Barrasi Wijegihaye Minna Budane Salmane Farisi Bar Asase Tahlil Riwayat Laisa Minna, sh 50.
  15. Shaik Saduƙ, Uyunu Akhbarir Rida (A.S), Jahan, j 2 sh 64.
  16. Shaik Ɗusi, Misbahul Mutahajjid , 1411q, j 2 sh 817.
  17. Shaikh Mufid, 1413q, sh 341.
  18. Ibn Shahre Ashub, Manaƙib Ale Abi Ɗalib, 1379q, j 1, sh 85.
  19. Ɗabrisi, Al-Ihtijaj, 1403q, j 1, sh 260.
  20. Sulaimu Bin Ƙaisi, 1405q, j 2, sh 965. bisa nakali daga Husaini Amini Wa Musawi, Barrasi Wijegihaye Minna Budane Salmane Farisi Bar Asase Tahlil Riwayat Laisa Minna, sh 49.
  21. Ibn Sa'ad, Aɗ-Ɗabaƙatul Kubra, 1410q, j 4, sh 62.
  22. Ibn Hisham, As-Siratun Nabawiyya, Darul Marifa, j 1, sh 70.
  23. Ɗabrisi, Majma'ul Bayan, 1408q, 1408q, j 5, sh 253. Shaik Ɗusi , Attibyan, Daru Ihya'il Turasil Arabi, j 5, sh 494.
  24. «حدیث «سلمان منّا اهل البیت» با انحصار «اهل البیت» در پنج تن آل عبا در آیه تطهیر چگونه قابل جمع است؟»، shafin yanar gizo na Muassate Tahqiqati Hazrate Wali Asre (A.F) Rasuli da wasu, "Tarjama", a Majma'ul Bayan, j 26, sh 174.
  25. Ibn Arabi, Al-Futuhatul Makkiya, Darul Sadir, j 1, sh 195-196.
  26. Mulla Muhsin Faizul Kashani, Buharatush Shi'a, sh 152, bisa nakali daga: Husaini Tehrani, Ruhe Mujarrad, 1425q, sh 446.
  27. «سرّی که سلمان را جزو اهل‌بیت ساخته، چیست؟»، Shafin yanar gizo na Khabar Online؛ «دکتر بابک عالیخانی عنوان کرد: سلمان در آیینه فتوحات»، Shafin Mu'assase Fajuheshi Hekmat Wa Falsafe Iran.
  28. Husaini Amini Musawi, "Barrasi Wijegihaye Minna" Budane Salmane Farisi Bar Asase Tahlili Riwayat Laisa Minna, sh 52-53

Nassoshi

Shafin Khabar Online, tarihin shigarwa: 12 ga watan 12 shekara ta 1402 kalandar Farisa, tarihin ziyara 20 ga watan 3 kalandar Farisa.

  • «سلمان منا اهل البیت»، Shafin laburaren Amirul Muminin Ali (A.S), tarihin ziyara: 22 ga watan 3 shekara 1403 kalandar Farisa.
  • Shaik Saduƙ, Muhammad Bin Ali, Uyunu Akhbarir Rida (A.S), gyara Mahadi Lajurdi, Tehran, Jahan, Babu shekara.
  • Shaik Tusi, Muhammad Bin Hassan, Attibyan Fi Tafsiril Kur'an, gyara Ahmad Habib Amili, Bairut, Daru Ihya'il Turasil Arabi, babu shekara.
  • Shaik Tusi, Muhammad Bin Hassan, Misbahul Mutahajjid, gyara Ali Asgar Marwarid da Abu Zar Bidar, Bairut, Mu'assase Fikhush Shi'a shekara 1411q.
  • Shaik Mufid, Muhammad Bin Muhammad, Al-Ikhtisas, tahkiki da gyara Ali Akbar Gafari da Mahmud Mahrami Zarandi, Qom, Almutamar Alami Li Alfiyyatish Shaik Mufid, bugu na farko, 1403 kalandar Farisa.
  • Tabrisi, Ahmad Bin Ali, Al-Ihtijaj, gyara Muhammad Baƙir Khirsan, Mashad Nashar Almurtada, shekara ta 1403 kalandar Farisa.
  • Tabrisi. Fadlu Bin Hassan, Majma'ul Bayan, cikin tarjama da gyaran Hashim Rasuli da wasu, Bairut. Darul Marifa, shekara 1408q.
  • Fattal Naishaburi, Muhammad Bin Ahmad, Rudatul Wa'izin Wa Basiratul Mutta'izin, Qom, Intisharatu Radiyi, bugu na farko, shekara ta 1375 kalandar Farisa.
  • Kulaini, Muhammad Bin Yaƙub, Al-kafi, gyara Ali Akbar Gafarida Muhammad Akundi, Tehran, Darul Kutubil Islamiyya, 1363 kalandar Farisa.