Kamfanin dillancin labarai na iqna

Daga wikishia
Kamfanin dillancin labarai na Iqna

Kamfanin dillancin labarai na iƙna (Larabci: وكالة إكنا للأنباء) ko kuma kamfanin dillancin labaran kur’ani na ƙasa da ƙasa (Iƙna), (wanda aka kafa:2013) kamfanin dillancin labaran kur’ani ne na musamman. An dauki Iƙna a matsayin kamfanin dillancin labarai na farko kuma daya tilo da ya kware kan kur’ani a duniyar Musulunci. [1] Wannan kamfanin dillancin labarai yana aiki a cikin harsuna 22: Persian, Larabci, Ingilishi, Faransanci, Urdu, Italiyanci, Sinanci, Rashanci, Sifen, Bengali, Hausa, Pashto, Hindi, turke, Swahili, Azeri, Andunusiya, Filipin, Jamusanci, Portuguese, Malay da kuma Tajik...[2]

Kamar yanda Kamfanin dillancin labaran iƙna ya labarta: Haduffan wannan Kamfani sun kasance kamar yanda bayani zai zo a ƙasa:

  • Sanarwa cikin sauri tare da dandaƙe bincike kan labarai da al'amuran kur'ani da addini a Iran da duniya
  • Kokarin tabbatar da samuwar al'adun Kur'ani a Iran da ma duniya baki ɗaya
  • kwaɗaiatr da al'umma zuwa ga salon rayuwar Al-ƙur'ani
  • kawar da ɓarnar ƙauracewa koyarwar Kur’ani a fagage daban-daban3.

An bude IKNA ne a ranar 20 ga watan Aban shekara ta2013m, daidai da 15 ga Ramadan shekara ta 1424 bayan hijira, tare da halartar Sayyid Muhammad Khatami shugaban jamhuriyar Musulunci ta Iran a lokacin [3] kuma ana gudanar da ita karkashin kulawar ƙungiyar malaman kur'ani mai alaka tare da Kungiyar Jihadi ta Ilimi [4] Wannan kamfanin dillancin labarai na reshe guda tara daga Sashin labarai, kowannen su yana da bangarori daban-daban; da suka hada da ayyukan kur’ani, siyasa da tattalin arziki, tunani, zamantakewa, al’adu da na ƙasa da ƙasa [5].

Ofishin Kamfanin dillancin labaran iƙna da yake da matsuguni a birnin Tehran ƙarƙashin rubutarwar sashen yaɗa labarai na iƙna ya labarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ‘game da mu’’ na wannan kamfanin dillancin labarai cewa, yana da rassa a Jahohi 30 na ƙasar Iran da kuma rassa guda shida (tsakiyar Asiya, Gabashin Asiya, Yammacin Asiya, Amurka, Turai da Afirka). [6]

Bayanin kula

  1. class="external text" href="http://www.isca.ac.ir/Portal/home/?news/434932/435685/759979"«معرفی خبرگزاری بین المللی قرآنی (ایکنا)»
  2. class="external text" href="https://iqna.ir/fa/about"«درباره ما»
  3. class="external text" href="https://iqna.ir/fa/about">«درباره ما»
  4. class="external text" href="https://iqna.ir/fa/about«درباره ما»
  5. class="external text" href="https://iqna.ir/fa/about"«درباره ما»
  6. class="external text" href="https://iqna.ir/fa/about" «درباره ما»

Nassoshi